Hausa novels

Halysaah Page 79 By Khaleesat Haydar

HALYSAAH PAGE 79…

Khaleesat tayi shiru tana kallon Jay da idonsa ke lumshe har na kusan minti uku, after another minute ya bude idonsa a hankali ya kalleta, tayi murmushi tace “Ai na zata bacci ka fara yi” A hankali yace “Eh mana, kuma har da mafarki nayi” Bata san sanda tayi dariya ba tace “Mafarki kuma?” Ya gyada mata kai yana kallonta calmly yace “Yea, i dreamt we got married and made 2 beautiful girls” Dauke kai tayi da sauri tana murmushi, shi ma yana murmushin yace “Yanxu dai ba babu abinda zaki bani kika sa na zo cikin ruwa ko?” Chocolate din hannunta ta mika masa without looking at him, yana murmushi ya amshi chocolate din yana kallo, can ya kalleta yace “Na Ajay kika dauko…” Dariya tayi tace “How did you know?” Ya gyara zama yace “How won’t i know, ai nasan Chocolate din da yake ci” Khaleesat tace “Wayo nayi masa na tafi kitchen na dauko bai sani ba” Jay ya ɗan yi shiru, sai kuma yace “I see, dama kin saba dauka kenan” Tayi er dariya tace “Bayan inda height dina bazai kai ba yake ajiye chocolate din a kitchen, bai san idan nayi tsalle ina iya daukowa ba….” Jay dai kallonta kawai yake babu ko kiftawa, can yace “Naga you are so comfortable together with him, gashi har kun saba ko?” Lkci daya abinda Safiyyah tace mata ya dawo kanta, ta kallesa ta girgiza masa kai da sauri tace “A’a ba haka bane….” Yace “You mean you are not comfortable with him a gidan?” A hankali ta gyada masa kai tana kallonsa, yace “Ohk, akwai wani frnd dina muna PhD under same course, tare suke apartment da cousin sister dinsa, but she just got her apartment recently nan kusa da school, although ba John Hopkins take ba ita, will you mind staying with her during ur exam period tunda apartment dinta kusa yake da school?” Khaleesat tayi shiru tana kallonsa kamar yanda yake kallonta yana jiran jin me zata ce, sauke idonta tayi, yace “If you are not okay with that kawai ki gaya min, kar ki ji komai” A hankali tace “I am not okay with it…” Yana kallonta yace “Why?” Ita dai bata yarda sun sake hada ido ba, she wasn’t expecting him to ask her why she is not comfortable, ta ma rasa me zata ce masa, taji yace “I am listening Halysaah” A hankali tace “I…. i don’t want to inconvenience her, kuma kullum Safiyyah zata dinga zuwa wajena muna karatu tare, and you know how loud Safiyyah can be, kaga kar mu takura ta” Jay dai kallonta kawai yake, kamar bazai ce komai ba sai kuma ya ɗan yi murmushi yace “Yarinyar bata da matsala ko kadan, amma don kar mu yi inconveniencing dinta we can give her half of the house rent since you won’t be staying long, just for 2 weeks ne, kinga baza ki ga kinyi inconveniencing dinta ba ke da Safiyyah, amma in kin fi son Apartment din ki together with Ajay, it’s fine” Da sauri Khaleesat ta kallesa tace “A’a shikenan, zan koma can din, ya ma fi hakan” Yace “Are you sure?” Ta gyada masa kai tana kallonsa, yace “Ohk, i will speak to Ayo about it this night sai yayi ma cousin din tasa magana, kafin ma ki koma can after speaking to the girl zan fara kai ki, ki ga apartment din gobe” A hankali tace “Allah ya kai mu” Ɗan murmushi tayi yace “Za ki koma ciki ki ci gaba da karatu?” Tace “Na ma yi karatun, kawai ina son inyi bacci da wuri ne” Yace “Are you going to school tomorrow?” Ta gyada masa kai tace “Za mu yi revision da wasu coursemate din mu” A hankali yace “Alright Halysaah” Tayi murmushi tana kallon chocolate din hannunsa tace “To bani in shanye tunda baza ka sha ba” Ya kai mata chocolate din baki yace “Bude bakin” Rufe fuskarta tayi tana murmushi sai kuma ta bude baki ya saka mata chocolate din yana kallonta, murya can kasa yace “I love you so much Halysaah” Ta ɗan juya tana murmushi, yace “Is that the reply?” Kasa kallonsa tayi, a hankali tace “Ni kunya nake ji” Ya ɗan yi murmushi yace “Za ki san kunya…” Ita dai taki juyowa tana murmushi, Yace “Good night Halysaah, Sleep like a baby…” Tana murmushi a hankali tace “Thank you so much” Shi dai kallonta kawai yake baya ko kiftawa, ta bude motar ta sauka, ya bi ta da kallo har ta isa kofar apartment din, tana murda kofar taji a kulle, knocking kofar tayi ta ɗan jira amma shiru, ta sake knocking nan ma taji shiru, sai da ta kwankwasa kofar kusan sau biyar ba a bude ba, ta juya ta kalli Housemate dinta don bai tafi kuma duk yana kallonta, ta kalli kofar ta daure fuska tace “Ni ka bude min kofa baka san akwai sanyi ba, wallahi nasan kana parlon” Shi dai Housemate kallonta kawai yake, har zai kirata su tafi can gidansu sai kuma kawai ya bude motar yana rike da makullin apartment din ya karasa ya bude mata kofar, Khaleesat da tasan akwai makulli wajensa da tunda tayi knocking sau daya bazata sake ba zata tafi ta amso key a wajensa, bayan Jay ya bude kofar ya kalleta yace “Good night” Tayi murmushi tace “Allah ya tashe mu lafiya” Juyawa yayi ya koma gun motarsa ta bude kofar ta shiga sannan ta rufe tana kallon Ajay dake zaune parlon yana shan parfait yana kallon American movie, ta hade rai tace “Shi ne kaki ka bude min kofa kana ji ina knocking?” Ko kallon inda take tsaye bai yi ba, hakan yasa ta tura baki tayi wucewarta sama kamar zata tashi, ya bi ta da wani kallo….. Washegari tun karfe bakwai da rabi Safiyyan ta dinga doka ma Khaleesat waya, Khaleesat dai bata biye ta ba, ta gama shiryawa wajen karfe goma ta sauko downstairs, as usual Ajay ya gyara ko ina na parlon, every where is just sparkling, ta shiga kitchen tana kallon lafiyayyen Salad din da ya hada, plate ta dauko ta fara diba da sauri sauri ta bar kitchen din kafin ya shigo, kawai taji muryarsa a bayanta yana tsaye bakin kofar kitchen din yace “Mayar min kar ki sha mari….” Juyawa tayi ta kallesa, sai kuma ta langwabar da kai a hankali tace “Kadan fa dama zan diba, i am going to school” Ganin kallon da yake mata ta juye salad din ta dungurar da plate din hannunta ta bi gefensa ta fice daga kitchen din ya bi ta da kallo yace “Ba abinda kika iya sai ki fesa turare ki dau handbag ki ce kin tafi school, what is the use of ur hands da baza kiyi naki salad din ba, common gyaran gida baki iya ba, sai dai kiyi wanka ki fesa turare” Khaleesat dai ko kallonsa bata yi ba ta tafi sama ta dauko handbag dinta da waya ta sauko downstairs ta fice daga gidan, a nan waje ta jira har Lyft dinta ya karaso sannan ta shiga zuwa makaranta. Safiyyah na zaune tana ta jiran Khaleesat a school din don tun karfe bakwai da rabi ta shigo, tana hangota ta fara washe baki Khaleesat ta zauna gefenta tace “Toh meye na shigowa school da sassafe” Safiyyah tace “Kin mance apartment din ki za mu koma tare ne, ko yana gida ne yau?” Khaleesat tace “Ya ma shirya zai fita shi ma” Safiyyah na murmushi ta makale handbag dinta a kafada tace “Yi mana order din ride mu koma gidan da sauri” A hankali Khaleesat tace “kinsan me Sophie?” Safiyyah ta wani kalleta tace “Me?? Ni fa in kika ga ban je na buga PS5 yau ba to Ajay ne ya koreni, bayan mun gama tsarinmu tun jiya yanxu kuma kina wani ce min nasan me, ba a abun arziki dake din nan dama” Khaleesat tace “A’a ba shi ba fa” Safiyyah ta gyara zama tace “Aiho, to menene?” Khaleesat bata boye ma Safiyyah duk yanda suka yi da Housemate dinta daren jiya ba, Safiyyah ta bude baki tana kallonta, can ta ajiye jakarta a gefe tace “A’a wannan karan Housemate ya zo da bidi’a, sai kika ce masa me ke kuma? To wai ma menene don kina zaune da ɗan uwansa na jini a gida daya da har zai dinga yi kamar kina zaune da wani bare? Wanda a class irin na Ajay ma ko kallo nasan baki ishesa a gidan ba in ba ke kika shiga harkarsa ba, me yasa Housemate yake haka? Gaskiya kice masa ke a’a kin fi son Apartment din ki, kuma da Ajay ne a shoe din Jay wallahi ko a jikinsa, insecurity ne kawai ke azabtar da Jay da bakin kishi, tun yaushe aka dena yayin kishi kowa ya waye yanxu, wallahi kice masa ke ba inda zaki je, da abinda zai saka ma Ajay kenan da ya yarda ya zauna yake ta masa gadin ki? Ke kuma maimakon kice masa kin fi gane apartment dinki akan ko ina shine kika masa shiru?” Khaleesat ta sauke ajiyar zuciya tace “To na rasa me zan ce masa ne, kuma bana son in bata masa rai” Safiyyah tace “Ai ko sai dai ran nan nasa ya baci, ni da nake murna ga ps5 a gida sai yanda muka yi da shi, shi ne Housemate zai kirkiro wannan abu kawai don ya bata ma Ajay rai ya kwashe PS5 dinsa ya bar gidan? Shi fa Ajay mutum ne da ba ruwansa ba sa wa ba hanawa tuni na gano haka, A’a gaskiya Ajay na hakuri da Housemate dinki, balle ma me Ajay zai yi da budurwarsa sai kace a garin gaɓa gaɓa? Jay ya canza hali gaskiya, da kyar wannan ya bari ki gama karatun bai je an daura auren ba idan muka koma hutu bayan exams, irin yanda Abdul yayi haka shi ma zai yi sai dai ki dawo Amurka da aurensa a kanki…” Ita dai Khaleesat tayi shiru don bata ma san me zata ce ba, Safiyyah tace “Ki tashi mu tafi ko ki ban makulli ni inyi tafiyata, da Ajayn zai yarda ai har ni komawa gidan zanyi in ce ma Ya Musty a makaranta muke kwana saboda jarabawa” Khaleesat tace “Wai fa yau yace zai kai ni gidan in gani” Safiyyah ta hade rai tace “Ki ce masa baki da lokaci muna ta revision a school kuma ba da wuri za mu gama ba saboda course ne me uban yawa ga exam ranan Monday, haba ya fiye fitina wannan Housemate din naki wallahi, Ajay ya fi sa saukin kai shi sa tamu ta zo daya da shi tun asali” A haka Safiyyah ta ja Khaleesat suka koma apartment dinta, banda murmushi babu abinda Safiyyah take bayan ta sauka a Lyft taga babu motar Ajay a parking space… Khaleesat da Safiyyah sun sakankance suna ta game tun shigowarsu apartment din ko wacce rike da Wireless Controller a hannu, Safiyyah sai nishadi take abun nema ya samu bakinta har kunne, wayar Khaleesat ne ya fara vibrate a jaka, Safiyyah tayi pausing game din da suke, Khaleesat ta ciro wayar a jaka ta kalli Safiyyah tace “Shi ne yake kirana” Safiyyah tace “Housemate din?” Khaleesat ta gyada mata kai, Safiyyah ta hade rai tace “Ɗaga kice masa muna ta jin yunwa mun dawo apartment dinki muna girki yanxu” Khaleesat tace “Toh” Picking call din tayi ta kai kunne a hankali tayi masa sallama, Safiyyah ta mike ta tafi kitchen don yunwa ma take ji, hadadden Jollof rice ta gani da chicken lap har biyu, ta juyo masu jollof din da chicken laps biyu a plate ta saka cokali ta bude fridge ta debi soft drink biyu ta dawo parlon, bude baki Khaleesat tayi tana kallonta, sai kuma ta fara dariya tace “Wallahi ba ruwana na Ajay ne, ni ban yi girki ba, gwara ki maida masa abincinsa” Safiyyah ta zauna tace “Ke ya fa ci ya rage ne, raguwa ne wannan…” Khaleesat tana kallon abincin tace “A ina kika gani?” Safiyyah ta fara cin abincin tace “A gantale a kitchen mana, alamar ya koshi” lumshe ido Safiyyah tayi tace “Ke kin ji dadin abincin kuwa? Wallahi wannan matarsa ta huta, ko ince ya huta, duk ranan da matarsa ke jin iskanci taki masa girki ya girka kayansa, gaskiya wannan yarima ne me capacity, uwa uba ga tsafta” Khaleesat ta dau spoon ta debi abincin ta kai baki, sosai ya mata dadi ita ma, ko wa ya koya masa girki haka oho, Safiyyah na cika baki da shinkafa tace “Kin gaya ma Housemate din abinda nace maki?” Khaleesat ta gyada mata kai alamar ta gaya masa, tass suka cinye abincin suka ci gaba da game dinsu dama gashi duk ba sallah suke ba, Wajen karfe biyu da rabi aka bude kofar parlon, daga Safiyyah har Khaleesat suka juya da sauri, Tsaye Ajay yayi a bakin kofar parlon yana kallonsu, a hankali Safiyyah ta dora ma Khaleesat Game controller din hannunta a kan cinyarta, cikin dubara ta matsar da plate din abincin da suka ci kusa da Khaleesat.

Halysaah is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah, ur evidence 07087865788

Back to top button