Zakuna Biyar Page 24 By Princess Teema
“NEXAPOX-31 wata cuta ce mai ƙwayoyin virus, tin da nike project a kan cututtuka ban taɓa yin makamancin wannan ba, ya sha bamban da dik wata cuta da ya wanzu a baya, wannan cuta na ciro kwayoyin cuta da dama daga jikin dabbobi masu haɗari kamar su bats, rodents, and reptiles da sauran dabbobi, na jima ina shirya wannan project ɗin”…… Ya ɗan nisa kafin ya cigaba da cewa. “Na faɗa maku ta zarce cututtukan da suka wanzu a baya irin COVID-19, HIV, Ebola da dai sauran manyan cututtuka masu haɗari da suka gigita duniya, to wannan ya damesu ya shanye, domin kuwa shi ne cuta na farko da yake ƙunshe da DNA da RNA a lokaci guda, wadda ke ba ta damar canzawa da wuri da tserewa immune system watau garkuwar jikin ƴan adam”. Ya sake ɗan dakatawa ya nisa kafin ya cigaba da cewa. “Wannan cuta zata yi balain girgiza duniy fiye da yadda su COVID-19 suka girgiza duniya a baya, chemicals da na ruɓar tsawon shekaru uku a wannan cuta ba karamin abu bane, dole wannan cuta ta gigita duniya, hankula zasu tashi, asibitoti zasu cika, rayuka zasu salwanta, tattalin arzikin duniya zata girgiza, manyan ƙasashen da cutar zata fi shafa zasu shiga wahala, tattalin arzikinsu zai ruguje, za’a rufe ƙasashen ba shiga ba fita, kuɗi ba zasu shiga ba kuma ba zasu fita ba, zasu cinye abin da suka tara, wahalar zata zarce yadda ake zato”. Ya dakata yana mai da numfashi. Dr Mark ne ya ce. “Good job, gaskiya wannan cuta da alama da zafinta take tafe, amma a wannan karon ta yaya (WS) World system suk shirya baza cutar ta isa ga in da ake so?”. Shiru Dr James ya ɗan yi na ɗan lokaci kafin ya ce. “Ta kasuwannin nama masu ɓoyayyen tsari watau wet markets, kasan na tsara cutar ta yadda zata iya ɗaukar makonni biyu a jikin mutum bata nuna ba, so zata iy makonni uku a jikin dabobbi bata nuna ba, dan haka zamu yi amfani da kasuwannin dabbobi, zamu samo kosassun dabbobi mu yi masu alluran cutan sai mu kaisu kasuwannin, mutane zasu sayesu, dik wanda ya ci namansu ya kamu kenan, idan aka yanka dabbar masu saya suka sayi nama shikenan kuma! Dole cutar zata bazu”. Ya nisa kafin ya cigaba da cewa. “Wani abin birgewa kuma a nan shi ne cutar zata bazu a cikin mutane ne ta hanyar airtight aerosol droplets, zata shiga ta hanci ko baki, ta dai hanyar iskar da mai ɗauke da cutar yake fitarwa kamar numfashinsa kenan, dik wanda ya ci namar dabbar a gida idan ya yi numfashi kusa da wani shikenan shi ma zai ɗauki cutar, daga nan cutar zata ratsa jikinsa har ta shiga huhu, a ƙasa da sati biyu zata fara tarwatsa dik wasu kariyar jikinsa”.”Hanya ta biyu da cutar zata shiga shi me ocular membrane, idan mai ɗauke da kwayar cutar ya taɓa idanun wanda bai da shi yakan iya kamuwa shi ma, ta hakan ma ta fi haɗari, dan zata shiga cikin jini ne kai tsaye daga ido”. “Hanya ta uku shi ne cin abinci mai ɗauke da cutar, kamar namar dabbobin da zamu yi wa alluran, ko kayan lambun da zamu yi wa dajuka feshin cutar, muddin mutane basu wanke kayan lambun da gishiri sosai ba tabbas zasu kamu”. Ya kai karshen jawabin yana binsu da kallo. Dr Kamal ne ya ce. “Nice work, amma kuma wani irin illah zasu yi wa ɗan adam baka faɗa mana ba”…….. Ajiyar zuciya ya sauƙe tare da taɓa screen na computer, ya shiga cikin folder ɗin cutar da kyau, take bayanai suka bayana rututu, ƴar sandar dake hannunsa ya gyara tare da fara yi masu nuni da jikin screen ɗin before ya fara bayani.”Na faɗa maku wannan cutar ta fi COVID-19 haɗari nesa ba kusa ba, cuta ce dake ƙunshe da DNA da RNA a lokaci guda, shi ne illar farko, illa ta biyu cutar tana lalata lungs, tana sa huhu ya cika da ruwa mai guba, wanda ke janyo mutuwa cikin awanni 72, amma kada ku manta na faɗa maku cutar tana ɓuya a jiki ba’a ganeta da wuri, tana kai 2 weeks kafin ta bayyana, a wannan 2 weeks ɗin cutar zata yi yawo a cikin jinin mutum, ta bi ko’ina ta kashe garkuwar jiki a saiɓaɓe, so zata kashe dik wani garkuwar jiki ta yadda idan ta bayyana jikin mutum ba zai karɓi maganin kowani iri ba sai maganin da na kirkiran wa cutar, sannan sai ta bayyana ne take kashewa a awanni 72”.Ya ja numfashi kafin ya cigaba da cewa. “Illah ta biyu da zata yi wa mutum shi ne acute respiratory collapse, ciwon ɗaukewar numfashi mai karfi, sannan ya haifar da zazzaɓi mai zafin gaske, ciwon kai mai tsanani, da ciwuka a fata irin na bullae kuma irin na monkeypox dake fashewa suna zubar da jini, and za’a su haifar da karancin jini da platelets, wanda ke haifar da zubar jini daga hanci, kunne, idanu, da al’aura, dik zasu faru ne idan cutar ta bayyana a jiki, kuma dik zasu faru da mutum ne a ƙasa da waɗan nan 72 hours ɗin”.”Idan mutum yana da sauran kwana a gaba bai mutu a cikin 72 hours ɗin nan ba to fa zai kamu da cerebral infiltration, dan karfinta zai sanya ta shiga blood brain barrier, watau jinin kwakwalwa ta janyo hauka, da kurmancewa”. Ya sake sauke ajiyar zuciya kafin ya cigaba da cewa. “Mortality wannan cuta ta fi COVID-19 da yawa, saboda zata kashe mutane 40 cikin ɗari 100 na duniya a cikin kwanaki 5 zuwa 7 da bayyanarta idan ba ayi maganinta da gaggawa ba, wanda kuma kun san da cewa maganinta babu wanda ya isa ya yi ta a duniya! Babu mai maganinta sai makirkirinta”. Ya kai karshen maganar tare da sakin wani irin one side smiling na zallar mugunta yana wani ɗaure fuska at the same time kaman wani shaiɗani.Hannu suka ɗaga suka jinjina mashi, sannan Dr Mark ya ce. “Amma kai tsaye me zai sa wannan cuta ta fi COVID-19 da sauran cutukan baya ban tsoro da firgitarwa?”.Bottle water ya wuce cikin freezer ɗinsu ya ɗauko tare da glass cup, wajen ya dawo, saman sofa ya zauna tare da ɓalle bakin robar ruwan, ya daddala a cup, a natse ya kai ɗan bakinsa. Mai ɗan yawa ya sha tare da ajiye cup ɗin, sannan ya miƙe ya koma gaban computer bayan ya ajiye cup ɗin a saman glasa table dake gabansu.A natse ya ɗaura hannunsa kan screen na computer, ƙasa ya yi da bayanan izuwa kan amsar tambayar Dr Mark. Cikin natsuwa ya fara bayani kamar haka. “Abin da yasa ya fi COVID-19 ban tsoro shi ne yana ɓoyewa a jiki har tsawon sati biyu ba tare da wata alama ba, sannan yana yaɗuwa ne ta cikin iska, ruwa, goganyar fata, ya fi COVID kamuwa da sauri, bugu da kari shi yana kaucewa rigakafi, wato da wuya allurar rigakafi ta yi aiki da sauri saboda canjin DNA na wuce misali da yake da shi, wannan sati biyu da yake yi a ɓoye a jikin mutum yana sanyawa ya lalata garkuwan jiki ta yadda babu wani maganin da jikin zata karɓa face maganin da na basu da kaina, haɗarinta ya zarce tinaninku”. Dr Kamal ne ya katse shi da cewa. “Hope ka shirya maganinta?”…… Jinjina kai ya yi tare da cewa. “Ka san bama ƙirƙirar cuta haka ba tare da mun shirya mataninta ba”……. Kai 2D suka jinjina mashi kafin su hau zuba mashi jinjinar ban girma da kwarara mashi gwiwa.A dake ya ce. “Sai duniya ta gigita zamu fitar da even rigakafin cutar, da rigakafin kawai nike son mu tara billiyoyin daloli kafin mu je kan maganin, dan a wannan karon kamar yadda cutar take special haka maganinta yake special, maganin zamu zuba mashi maƙudan kuɗi na wuce misali ta yadda zai sa a rasa rayuka dan ba kowa zai iya mallakar maganin ba”. Cike da zallar rashin imani ya kai karshen maganar.Watau duniya ta zarce yadda dik ɗan adam yake tinani, zasu kirkiri cuta dan raje yawan al’umma kuma dan kasuwanci, domin kuwa suke da riba, ko rigakafin cutar kawai suka fitar a guje za’a bi maganin dan ana tsaka mai wuya, a rigakafin kawai ba karamin kuɗi zasu samu ba, kun ji sun ce sai duniya ta jigata ta rasa madafa zasu saki maganin cutar, hakan ma da mugun tsada zasu saki maganin ta yadda ba kowa zai iya saya ba. A nan ina da tambaya! Kun taɓa tambayar kanku cewa waɗan nan cututtuka da suke ɓullowa duniya daga ina suke ɓullowa?…… Bayan na gama jin bayanan Dr James na yi wani tinani fa my people, amma bari in barwa zuciyata wannan tinani, ALLAH yasa shiruna ya zame mun alkhairi! Wai ko dai in faɗa ne kawai?……..🤔 Amma ku kuma ku faɗa mun bayan kun gama jin wannan bayani na Dr wani tinani kuka yi? Ko dai har yanzu kuna nan jiya iyau? Ba cigaba?Sai jinjina mashi su Dr Kamal suke yi suna yaba muguntarsa, suna kuma kara mashi kwarin gwiwa. Shi kuwa sai kara jin kansa na kara girma yake yi. Cikin wani irin murya mai amo ya ce. “A yanzu duniya a tafin hannuna take! Sai yadda na yi da ita! Ni ne Devil wanda da zai yi wa mai gida Dujjal tarba ta ban girma a lokacin da zai iso! Wannan project yakamata na canza mashi suna daga PC izuwa Death is inevitable! Ko kuma a death that wipes out an entire family!!”…….. Dr Mark ne ya ce. “Ka barsa a PC ɗin ma ya yi”. (PC yana nufin Population Control, na ji wasunku suna cewa CRYSTAL PALACE ne PC da yake nufi, to ba haka bane, CRYSTAL PALACE fa CP ne ba PC ba kusan ɗaya suke yasa kuka ruɗe)Dr Mark ne ya ce. “Amma meyasa WS ta hura mana wuta kan mu saki project ɗin nan yanzu? Mun yi da ita ai sai shekaru uku zuwa huɗu gaba, meyasa suka ce lallai mu saketa yazu?”. Nisawa ya ɗan yi kafin ya ce. “Kasan a wasu ƙasashen za’a kafa sabuwar gwamnati, ma’ana zaɓe ta ƙarato saura shekara ɗaya da ƴan watanni, sannan kasan akwai manyan ƙasashen da suka gwadawa WS taurin kai, kuma da alama ƙasashen sun tsaya da ƙafafuwansu, suna da karfin tattalin arziki da karfin faɗa aji, sannan da alama suna da power da WS take shakkarsu shiyasa suka buƙaci project ɗin nan dan su gigita kowa, a taƙaice dai gargaɗi mai karfi suke son yi wa duniya, a karkashin ƙasa kuma akwai plan na ruguje ƙasashen da suka kawo karfi suke ganin suna da murya mai karfi, sannan a gefen ƙasashen dake biyayya ga WS kuma su za’a haɗasu da wannan cuta ne domin sabuwar gwamnatin da zasu kafa, a hargitsa ƴan ƙasa ta yadda gwamnatin da ta hau sabuwa ba za’a ga laifinta a farko ba, za’a ce duniya ta shiga rikici, so ko gwamnatin ta yi shekarun mulkinta bata yi wa ƴan ƙasa komai ba za’a ce ai dama wannan balain da ta faru na wannan cuta gwamnatin ba zata iya shawo kan matsalar lokaci guda ba, so kunga a nan dik badakalar da gwamnatin zata yi babu wanda zai mai da hankali ko ya zargesu, daga nan WS zata cinwa abin da take so”. Wannan bayani nasa ya mugun gamsar da su, watau WS basa sakar cuta sai idan za’a samu sabbin gwamnatin dake masu mubaya’a, watau a kowani gwamnati sau ɗaya suke sake cuta ko da wannan gwamnatin zata sake maimaita shekarunta a mulki ba zasu saki wata cuta ba sai idan sabuwar gwamnatin ce zata hau, sannan suna yin hakan kuma dan su ruguje ƙasashen dake ƙoƙarin tasowa! Tab akwai matsala. Dr Mark zai yi magana suka ji alamar motsi a office na Dr James, Dr Kamal ne ya ce. “Ko su Maya ne?”……. Kai Dr James girgiza kafin ya ce. “Sai dai Lazy”……. Wani irin shu’umin murmushi Dr Mark ya saki kafin ya ce. “Ce mun zaka yi mutuniyarka, James Lazy fa sonka take yi”…… Wani irin ɗaure fuska ya yi kafin ya ce. “Me zan yi da tsohuwar da komanta ya kare? Kada ka manta Lazy ta haura 47 years, surgery ne da magunguna yasa take haka, da kaina in mata surgery ɗin sannan in dawo in kwashi ragowa? Are you out of your sense?!”.Wani irin dariyar mugunta Dr Kamal ya yi kafin ya ce. “Zakuwa ku dace, tana sonka sosai fa, kada ka manta ta yi maka abubuwa da dama a rayuwa, ita ta taimaka maka wajen kawo ƙarshen Muhammad Haiza’an, kada ka manta idan ba da sa hannunta ba baka isa shiga CRYSTAL PALACE har ka sace Muhammad mu yi nasarar cire ƙwaƙwalwansa ba, dan haka Lazy bata cancanci ka ki ta ba”. Ya kai karshe yana dariyar shakiyanci da iskanci.Kara ɗaure fuska Dr James ya yi tare da cewa. “Stop it! Dik abin da Lazy ta yi she did it because of money, na biyata hakkinta sai kuma ta ce zata yi aiki tare damu, tana sha’awar kasancewa tare da mu, na mata adalci na ɗauketa aiki, sai kuma me? Ta ce tana son ai mata surgery a canza mata kamanni kada ƴaƴanta su gane fuskanta zasu kasheta, haka nai mata surgery na canza mata kamanni, daga karshe ma ta gudu ta baro Washington ta dawo nan da zama, dik na karɓeta saboda girman aikin da ta yi mana, kunsan kwakwalwar Muhammad ba wasa ba, na bata aiki a ƙarƙashin office ɗina dik dan in yabawa ƙoƙarinta, dik ban mata adalci ba?”. Hararansa Dr Mark ya yi kafin ya ce. “Ka dai faɗi gaskiya, ba wani dan kayi mata adalci yasa ka ajiyeta a ƙarƙashin office ɗinka, kawai ka ɗauketa ne saboda nufinka a kan ƴaƴa Muhammad, kana son sperm and brain ɗinsu, kuma kasan ita kaɗai zata iya wannan aiki, saboda ita kaɗai tasan ainahin jininsu!”. Hararansu shi ma ya yi kafin ya ce. “Dik da haka dai na yi mata adalci”….. “Kai ku bar tuna mana baya, bamu taɓa aiki mai tsananin wahaka ba irin waɗan nan ayyuka guda biyu”. Cewar Dr Kamal.”Wani aiki kenan?”. Dr James ya tambaya. Dr Kamal ya ce. “Aikin ƙwaƙwalwar Muhammad da kuma aikin ƙwaƙwalwa Namjoon, mun wahala a kan ayyuka biyun nan”……. Kai kawai Dr James ya girgiza alamar wahalar ta zarce ayi magana. WAYE NAMJOON? WANI IRIN AIKIN ƘWAƘWALWA AKA YI MASHI? NASAN KUN GANE WAYE MUHAMMAD KAM AI! WATAU MAHAIFIN SU LION! KENAN A WANNAN HOSPITAL ƊIN AKA CIRE ƘWAƘWALWARSA? LALLAI AKWAI GAGARUMIN MATSALA NA KIN ƘARAWA KUWA!.Kamar yadda suke zaune suke wannan hira cikin nishaɗi da tsokanar juna haka suma su Maya suke zaune suke hira. Bayin ALLAH kansu ya shiga ruɗani ne, sun shiga tsananin tashin hankali na ganin irin aikin da aka sanyasu, wannan document da aka basu su karanta, jerin sunayen chemicals da ake son su zaƙulo su haɗe masu ne, wani chemical ɗin idan sun haɗa shi da wani sai an barsa ya yi sati biyu ya gama tsumuwa sai a sake suba wani.Da farko da suka fara aiki ba su damu sosai ba, sai yanzu da aikin ya yi nisa, suna isa kan manya-manyan chemicals masu haɗari kuma masu tsanani a guba shi ne fa hankulansu ya tashi, sun san idan aka haɗa kaza da kaza ga abin da zai haifar, nan fa suka yi mugun gigita, dik sun sha jinin jikinsi.Sister Maya ta fi tausayi da saurin karaya, cike da tashin hankali ta ce. “Sister Zinta kina ganin me nike gani kuwa? Me kike tinanin zasu yi da wannan abin?”…… Sister Zinta da ta gama shan jinin jikinta ne ta amsa da. “Sister Maya na fara fita a hayyacina ne ko kuwa dai mafarki nike yi? An taɓa haɗa waɗan nan sinadaran waje ɗaya ne? Kisan kai zasu yi ne?”.Dogon numfashi sister Maya ta ja kafin ta ce. “Babban tashin hankalina shi ne waɗan nan sinadaran da muƙa haɗa waje guda, kamar Dimethylmercury CHH, kin sani, sinadari ne dake shiga jiki a hankali ba tare da nuna alamu ba, sai daga baya ya haifar da matsalolin fata, kumburi, da raunuka masu wari, kuraje masu fashewa su fitar da jini, amfani da shi yana da matuƙar hatsari!”Ta ja numfashi kafin ta cigaba da cewa. “Ga kuma sinadarin cantharidin CHO, sinadarin da ake samu daga wasu kwari masu haɗari, yana sa kuraje su kumbura su fashe su fitar da ruwa wani lokaci kuma har jini suna yi. Ga kuma sinadarin ricin CHNO, sinadarin dake haddasa kumburi da kuraje masu zafi sosai. Hallau ga arsenic trioxide AsO, sinadarin dake sa mutum jin daɗi rayuwa a farko, amma daga baya yana haddasa cututtuka na fata, kumburi, da kuraje masu wari. Dik da wanna suka sake cewa mu zuba thallium sulfate TlSO a ciki, mugun sinadarin dake haddasa matsalolin fata da kumburi ba tare da an yi saurin gano shi ba”. Ta kai karshe tamkar zata yi kuka, dik da basu san me za’ayi da waɗan nan sinadaran ba tabbas sun gigita da haɗawa, suna jin kuma tamkar ba zasu iya cigaba da haɗawa ba.Na ce kun tuna cewa da Dr James yana gabar da project ɗinsa, a abubuwan da ya kirga cutar take haifarwa har da kuraje masu fashewa su yi jini? Nasan yanzu kun gane daga wani sinadari aka samu wannan, sannan ya ce ciwon yana shiga ne a hankali, yana ɓuya na sati biyu kafin ya bayyana a jiki, kenan kunga irin sinadaran da aka zuba mashi yasa zai ɓuya a jiki na tsawon sati biyu, lallai akwai matsala, mu leƙa CRYSTAL PALACE mu dawo. CRYSTAL PALACE.Shirye suke cikin tsadaddun tail coat masu bala’in kyau launin dark blue watau navy da ya yi masifar fito da tsantsar kyansu, ku hasko fararen fata a cikin navy blue ya zasu kasance?. Musamman Aryan and Lion da suka cire face mask ɗin fuskansu a yau suna karisa shiryawa, barema Lion da ya fito daga Pamira blood, hasken irin pure white ɗin nan ne mai balain kyau. Ya ilahi, tamkar ka samu waje ka zauna ne ka yi ta faman kallonsu kawai kada ka ɗauke idanu, idan kuka kalli lips ɗin Lion oooooo, ya ALLAH, zaku zaci ya sanya pink janbaki ne, ya ciza kala sosai yana wani irin kyalli, hakama lips na Aryan, bakin Lion irin round lips ɗin na ne mai masifar kyau, ga shi ɗan karami, lipa ɗinsa suna da ɗan cika daidai masha ALLAH. This two guy complete face ɗinsu ya haɗu, ga sexy gorgeous body, a gaskiya Lion yana kama da Leo sosai, kamar an tsaga kara, hatta hair ɗinsu golden white dake ta faman sheƙi kamar gold idan ya ji gyara, ya ALLAH, na sake cewa ya ALLAH.Na Lion ya sha kitso kalba a wajen Aryan, ya ɗaure mashi gashin nasa yai mashi tuntu da jelar, kitson tai masifar kara mashi kyau na gasken-gaske. Shi kuwa Aryan arabs hair garesa, kada ku manta shi bakuraishe ne, gashinsa irin dark blue ɗin nan mai sheki wanda zaku zaci ma baki ne in baku kallah sosai ba, gashin ɗan daidai ne a kan nasa, bata wuci zuwa bayan wuyansa ba, yadda dai gashin larabawa yake, yana kwance luff yana wani irin sheƙi, ga wasu gajeru guda biyu da suka zubo mashi ta gaban goshi sun yi nannaɗa sosai, while na bayan kuma suna kwance kuff sun yi bayan wuyansa. Ya ALLAH idan kuka ga Aryan ko, yadda yai gyaran gashinsa tamkar shararren ɗan soyayya, ga dikkan alamu yana cikin soyayya!. Shi kuwa guru ba zan ce komai a kansa ba saboda yana sanye da nose mask, yana zaune gefen bed rike da waya yana latsawa………. Bayan Aryan ya bar wajen Seraphina ya fita ne ya wuce office ɗinsu bai je wajen Abba ba, daga office ya dawo gida, ya rufe sim ɗinsa da su Abba suka sani ya buɗe na iya nasa da su Lion, shiyasa Seraphina ke ta faman kiransa number a kashe.Bayan sun kammala shiryawa suka ɗauko haɗaɗɗun nose mask ɗinsu suka sanya, irin nose mask masu rufe har saman hancinsu ɗin nan ne, iya kwayar ido zaku gani, and dikkansu hat suka sanya a kansu dan shi ne ya dace da shigar tail coat.Wani irin diamond watch mai bala’in tsadar gaske suka ɗauko iri ɗaya, a tare suka fara sanyawa a hannunsu, sai dai su sun kammala sanyawa na Lion kuma ya zame ya faɗi ƙasa a ƙoƙarinsa na gyara botirin tail coat ɗinsa na wajen hannu dake ƙoƙarin fita. Duƙawa Aryan ya yi ya ɗauko agogon, sai wani irin kyalli take yi. Tamkar jiya basu doka faɗa kamar zasu kashe juna ba, haka ya kama hannun Lion ya zura mashi agogon tare da sanya mashi maɓallanta, sun yi masifar kyau, suka ɗauko half covers shoes suka sanya a kafafunsu launin baki kalar hat ɗin kansu. Sai tashin daddaɗar kamshin perfume na kamfanin su Noor suke yi.A jere suka tsaya a tsakiyar ɗakin kamar wasu guards, guru dake zaune a gefen bed ne ya kwaso masu wayoyinsu wanda dik bala’in mutum ba’a iya bin diddiginsu. A tare suka jera zuwa waje, cikin zafin nama suke taku dake nuna tsantsar jarumta a tattare da su. Cikin tsadadden motar Aryan suka shiga, dan basu cika fita da motar Lion or na guru ba, dayawan lokuta dana Aryan suke fita. Suna fitowa harabar side ɗinsu sai ga wasu jiga-jigan jami’ai guda biyar sun biyo elevator sun sauko zuwa in da suke, ashe a hawan dake ƙasan nasu benen jami’ansu na SSO ne, suna tare da su dan basu tsaro na musamman, sun ki yarda su zauna gida ɗaya da jami’an ne saboda su ne IRON FIST, idan suna tare da su za’a iya samun ɓacin rana saboda jami’an SSO akwai basira.Da yake sune manya cikin hukumar SSO ba ta yadda za’ayi a barsu babu masu basu tsaro shiyasa suka kama masu benen ƙasan nasu dan kada gwamnati ta zargesu. Abin da yasa yanzu ma ba’a zargansu saboda an san su jami’ai ne dake buƙatar sirri na musamman, shiyasa idan suka yi wani abin ba’a zargansu.Dukkansu gidan baya na motar suka shiga, jami’i ɗaya ya shiga driving seat, sauran jami’ai huɗu suka tada mota guda wanda ya kasance nasu ne dama, already suna da motoci guda 3 kasancewar su 12 ne ke tare da su. Yanzu Aryan ne ya ce jami’ai 5 su zo su tafi, shiyasa basu sauƙo su dikka ba, and dikka jami’an suna sanye da black suit, sun saje da guards dan ɓadda kama.Aryan ya umarcesu da su wuce da su wuce kai tsaye izuwa airport dan ba zasu ta fi da jet ɗinsu dake saman benensu ba, kun san kowani bene a CRYSTAL PALACE a sama kololuwa akwai wajen saukar karamar jet wanda yadawa daga cikin manya a CP ɗin suna da jirgin kansu wanda yake sama a fake, daddyn Noor ma yana da shi, su Lion suna da shi. Kai tsaye airport aka wuce da su, jirgi suka hau sai Washington. Suna dira a Washington jiga-jigan motocin jami’an SSO dake wajen already sun yi wa airport ɗin diran mikiya, ta ko’ina kaki ne ke shawagi, an turo masu sojoji, ƴan sanda, har da fighter jet ta sama dan tabbatar masu da tsaro. Ƴan jaridu sun cike airport ɗin tab, ta ko’ina sai snapping ɗinsu pic’s ake yi.Dik kansu kansu a ƙasa a lokacin da suka fito daga cikin jirgin, kowa yana burin samun damar ganin faskokinsu, amma sunki bada dama. Da gudun gaske jami’an SSO suka zo suka yi masu zobe suna sara masu, ga wasu jami’an da suka jera layi tin daga wajen bakin marfin jirgin har izuwa wajen motar da aka tanada masu, rike suke da manya-manyan bindigu waɗan da basa saɓa saiti.Wargima waje yake samu, domin kuwa babu ɗan jaridan da ya iya keto tsakanin jami’an SSO ya isa wajensu Aryan wai ya ce zai masu tambayoyi, sun dai ja gefe suka masu hotuna har suka shige cikin motocin da aka tanada masu. Da gudun gaske jami’an SSO suka shiga nasu motocin suma, a tare aka tada motocin, a jere suka fita airport ɗin suka nufi white house da su, watau fadar shugaban ƙasa. Yau suna da wani zazzafar meeting ne da manya-manyan kakin dake faɗin ƙasar.Sunan wannan meeting ɗin ma National security high command meeting. A secure intelligence & defense operations room na white house za’ayi meeting ɗin. Meeting ɗin zai fara ne da misalin karfe 12:00 AM na dare kenan, zasu kammala karfe 4:00 AM, gab asuba kenan, yanzu kuma 11:30 suka isa airport, daga airport zuwa fadar shugaban ƙasa zai ɗaukesu 20 mins, zasu shiga a kan lokaci kenan.Waɗan da za’ayi meeting ɗin nan da su sun haɗa da shugaban ƙasa, ministan tsaro na ƙasa, CDS watau Chief of Defence Staff, COAS, CNS, CAS, NSA, DG, GOC, FOC, AOC da sauran manya dik zasu hallara.Kowa yasan yadda gidan gwamnatin ke da tsaro da tsari ga haɗuwa, ba sai na tsaya ɓata lokacina wajen yi maki bayani ba. An ƙawata ɗakin taron nan sosai da sosai dan ɗakin yana cikin wani ɓangare na Presidential Villa ne, wall na ɗakin mai tsawon gaske ne, CCTV ta ko’ina, rundunar tsaro ta musamman dake kai komo a arear yadda kuka san cewa idan an barsu zasu iya hana mala’ikan mutuwa ketawa ciki ya ɗauki rai! Babu alamar imani ko wasa a tattare da dik jami’an dake wajen!. Wurin yana da drone surveillance sama da counter sniper system a ko’ina.Ba a amfani da wayoyi ko internet na jama’a, dik hanyar sadarwan wajen tana military grade encrypted satellite line.Su kansu jami’an da za’ayi zaman da su kafin su shiga cikin ɗakin sai da scan na farko, na biyu voice ID da aka shiryawa na’urar already, na uku badge code da ake basu ana saura minti ɗaya meeting. Yanayin tsarin ɗakin meeting ɗin ba’a magana, dan ɗakin round ne ba kamar sauran ɗakuna ba, an yi haka ne kuma dan kowa ya dinga kallon juna.Ga wani haɗaɗɗen tangamemen table launin black oak a tsakiya, an zagaye shi da kujerun masu laushi launin baƙi, kowacce tambarin rundunar ko in ce maku kowacce hukuma kamar soja da Air Force kunga ba ɗaya bane, to kowacce kaki da chair ɗin babban General ɗinta da zai wakilcesu a wajen an manna tambarin kakinsu a jikin kujerar da zai zauna, ga sunan hukumarsu a jikin ɗan karamin signpost a gaban kujerar tasa a saman table ɗin.Sannan a gaban kowani babba na kowani kaki akwai LED screen panel dan nuna bayanan sirri, bayanan sirri suna fitowa daga secure satellite intelligence feeds mafi aka sari. Sannan akwai babban smart board mai 80 inch a ta gaban ɗakin dake ɗauke da taswirar gabaɗaya ƙasar, daga kudancin kasar har arewacin ƙasar.Sannan ga hologram table a tsakiyar table ɗin nasu, wanda ke iya nuna tsarin harin 3D simulation. CCTV da ke ɗakin an saita shi ta yadda ba zai ɗauki sautin komai ba sai dai hoto, an haɗesa da jammer system.His excellency yana da matsayi na farko a kan kujerar farko da aka tanada na musamman, dik da tsananin tsaron dake wajen hakan bai hana kasancewa yana tare da security aide ɗinsa dake tsaye a bayan kujerarsa tamkar sassaken gunki ba.Daga jujerarsa sai na Ministan tsaro, dan haka komai ya kammala, su Aryan na shigowa ɗakin his Excellency ya shigo shi ma, yana shigowa kuma aka kulle kofar babu wanda zai sake shigowa.Wani irin musulmin natsuwa ɗakin taron ya yi, daga nan zaku fahimci manyan kai ne a wajen, kuma zaratan maza ba ƙananan kwari ba. Bayan kowa ya ɗan natsu ya sauke numfashi, masu buƙatar shan ruwa sun sha daga cikin ruwan da aka jera a gaban kowannensu, hankalin kowa ya natsu, sai Ministar ɗin tsaro ya miƙe tsaye tare da gyara mic dake saitin gabansa, a natse ya gabatar da dalilin wannan zama da suke yi dik karshen wata, ya kuma gabatar da buƙata daga office ɗinsa, ya shinfiɗe dikkan rahotonnin da ya tattara daga hannun wasu manyan jami’an ƙasa da kuma wasu ƴan majalisu da dai sauransu.Bayan ya kammala gabatar da komai da shaida ne. Chief of Defence Staff watau CDS wanda shi ne general security strategy, ya miƙe ya kora nasa jawabin, baya ga shi dik Chiefs na Runduna kama daga COAS watau Army, CAS Airforce, CNS Navy, SSO da dai sauransu sai da suka yi nasu jawabin, a jawabin su Lion guru ne ya yi, dan Lion da Aryan basu motsa ba saboda ransu dake jagule, kun san IRON FIST da kaifin ƙwaƙwalwa, tuni sun gano maƙaryatan cikinsu, shi ne nan ransy tai mummunar ɓaci, idan suka ce zasu buɗe baki ko zasu motsa a wajen zasu iya tarwatsa komai, shiyasa shirunsu ya fi masu alkhairi.Bayan kowa ya gama bayanan dake a bayyane kowa yasan da su, masu karya sun shararo nasu, sai His Excellency ya buƙaci jami’an sirri na musamman da su bada nasu bayanan, watau irinsu SSO CIA da sauransu, misali kamar a Nigeria ace NSA da DG DSS, kun gane ai?.A wannan karon sai da kowa ya gama gabatar da nasa, sannan SSO sune na karshe, guru zai sake miƙewa ya wakilcesu Lion ya ɗan dakatar da shi ta hanyar ɗaga mashi hannu, sannan ya miƙe tsaye shi da kansa. Ƙara ɗaure fuskar nan tamau ya yi, babu alamar annuri a tattare da shi, gyara mic ɗin gabansa ya yi kafin ya kunnata, a natse ya fara magana kamar haka. “Bisa ga bincike na sirri ya nuna cewa akwai manya daga cikin manyan jami’anmu dake taimakawa ƴan ta’adda, akwai masu basu makamai kuma akwai masu gwada masu hanyar guduwa”. Ya ɗan ɗakata ba tare da ya ɗago ya kalli kowa ba, dik a cikinsu babu wanda ya kawo batun cewa akwai masu baiwa ƴan ta’adda makamai da sauransu sai SSO, shiyasa ya miƙe da kansa dan su gansa da kyau, kowa yana jin labarin halinsa dama, sun san ko a cikin SSO ɗin ma su basa ɗaukar raini ko wargi.”Akwai manya dake ɗaukar nauyin ta’addanci ba iya kasar nan kawai ba, harda ketare! Sannan akwai sabbin hare-hare da aka shirya dan ƙaratowar zaɓe saboda maguɗin da kuka shirya, an kuma bada damar shigo da muggan miyagun kwayoyi masu haɗari dan ƴan ta’addan su bugu a ranar zaɓe su yi aiki cikin fitar hayyaci yadda zasu yi kan mai uwa da wabi ga kowa ba tare da tausayi ko tunani ba”…….. Kai tsaye ba tare da shakkar kowa ba ya ce. “Harin ma ya shafi harda His Excellency saboda sanin cewa kujerar mulki ba zata kwace daga hannunsa ba saboda adalcinsa! A bisa binciken sirri ya nuna an hayo sabbin ƴan ta’adda bakin haure daga kasashe da dama, kuma dik wannan abin yana faruwa ne a tsakanin manyan jami’ai zuwa ministoci”. Babban GAT na sojojin kasar. (Bafa GAT namu na AVARIS ba, kada ku manta to) GAT ɗinsu ne ya ce. “Shaida zaka bada a bayyane ba wai ka tsaya ce mana binciken sirri ba!”……. Yana rufe baki conol lieutenant na Navy ɗinsu ya ce. “Shaida muke son gani, ka bamu shaida………”. Dukkansu cike da shakkarsa suka yi magana, saboda IRON FIST akwai balain kwarjini da cika ido, ga sawa mutane zarra da tsoro, sai ma idan sun kalleka da waɗan nan shaggun idanun nasu masu rikitarwa.Kasa ƙarisa magana Conol ya yi saboda ido da Lion ya wurga mashi, bai san time ɗin da ya haɗiye maganar ba….. “I am speaking, yet the soldiers and the navy officers keep interrupting me! I talk and they talk over me! What kind of disrespect is this?!”. Lion ya faɗa yana sauke idanunsa ƙasa saboda ya ga gabaɗaya ya rikita conol yasa sai zufa yake ta faman haɗawa na tsaresa da kallo da ya yi, yasa bawan ALLAH shiga ruɗu da tashin hankali tamkar ba jami’i ba, kun san su fa SSO kowani kaki shakkansu suke ji, ai na faɗa maku matsayinsu da kuma horonsu, musamman su da suka matsayin admirals ai sama suke da sojoji da sauran kaki.Cikin zafin nama GAT and CONOL suka miƙe, at the same time suka sara mashi game da cewa. “Sorry sir”……… Shiru bai yi magana ba, dan yana son zuciyarsa ta ɗan sauƙa ne kafin ya yi magana, watau Lion shi irin mutanen nan ne masu balain saurin fusata, dan dai baya son hargitsa taron nan ne, akwai wani saƙon da yake son isarwa, ba dan haka ba yadda yake da saurin fushin nan da ya jima da kai masu duka sai dai su ji hakwaransu a ƙasa lokacin da suka shiga maganarsa, amma ya daure yana dannar zuciyar kada ya sumar da mutum.Hasbiyallahu waniimal wakil kafa 10 ya maimaita a cikin ransa, take zuciyar ta sanyayya, ajiyar zuciya ya sauke kafin ya cigaba da cewa…….. “Dik wasu jami’ai dake da sa hannu a kan ta’addanci, da waɗan da suke tallafawa masu tada zaune tsaye, harda masu sai da makamansu ga ƴan ta’adda dik ku kwana da shirin cewa SSO idanunta na kanku, kuma aikinmu tamkar iska yake, babu wanda yake iya sanin lokacin da aikinmu zai biyo ta kansa, kamar yadda babu wanda yake da sanin lokacin zuwan iska ko guguwa waje!”. Ya ɗan dakata saboda baya iya juran dogon magana.Zazzaro idanu sosai suka yi a kansa, Conol a cikin ransa ya ce kai kaga yadda yake magana yasa na ji tamkar naga mutuwa a gabana ne take mun magana!.Sai da ya nisa kafin ya cigaba da cewa. “SSO bata magana biyu, kowa kuma ya shaida!”. Yana kai karshe ya koma ya zauna tare da ɗan yin ƙasa da kai tamkar mai tinanin wani abin. Ai kusan duk jami’an dake wajen sun yi mugun shan jinin jikinsu, dayawansu tsoro ya bayyana a kan fuskokinsu, dan kamar yadda ya faɗa ne SSO basu taɓa magana biyu ba, tarihi ma ta shaida. Wani irin daɗi His Excellency ya ji na jin abin da Lion ya faɗa, watau shirin kifar da gwamnatinsa suke yi ta ƙarkashin ƙasa kenan? Lallai kuwa da matsala. Karin wani haske, kunga da His Excellency da su Lion suna da kusanci sosai, Mr President yana mugun kaunarsu sosai da sosai. Wannan tsakanina da ku ne masu karatu, zan faɗa maku abin da su Lion basu sani ba, sun ɗauka kawai Mr President yana sonsu ne saboda jajircewansu a kan aiki kuma suna taimakawa gwamnatinsa, amma a gaskiya ba haka bane, shi ɗin jininsu ne, amma daga su har shi basu san da hakan ba, sun ɗauka shakuwa ce kawai take a tsakaninsu, amma gaba zaku ji wani irin alaƙace a tsakaninsu, shin ɗan uwan waye daga cikinsu, guru ne? Ko Lion? Ko dai Aryan? Mu je dai zuwa.Wani irin musulmin shiru ɗakin taron ya kara yi, sai da Mr President ya yi gyaran murya tare da cewa su cigaba da jawabinsu. COAS ya fara bada rahoton ayyukan sojojin ƙasa a yankunan da ake fama da ƴan ta’adda.CNS ya bada bayanan ragin fashin teku, musamman dilolin kwaya, ya bada rahoton irin jajircewar da suka yi wajen ganin an daina shigo masu da kwaya. Sai dai yana magana yana kallon Lion da ya yi ƙasa da kansa, su Aryan dik sun yi ƙasa da kai, IRON FIST basa son ana kallonsu, saboda kada ma wasu su haddace wani daga cikin halittar fuskansu, kun san su ɗin ruwa biyu ne, sai da ɓoye kai, so sun tsani kallo matuƙa, shiyasa dik in da zasu je kansu a ƙasa.Bayan sun kammala jawabinsu ne aka fito da sabon tsarin zone enforcement protocol dan ƙara inganta tsaron ƙasar. Mr president ya ce a tsananta tsaro sosai, sannan dik jami’an a sabonta masu kayan aiki na zamani da sabbin makamai, aka rubuta takarda, suka tsara komai. Sai da aka gama Mr President ya kalli SSO, a natse ya ce. “Baku bamu naku tsarin ba? Kuma muna buƙatar shawarinku amma baku ce komai ba”.Shiru wajen ya yi suna jiran jin ta bakinsu. Amma babu alamar Aryan da Lion zasu motsa, saboda karairayin da wasu daga cikin jami’an nan suka sake shirgawa ya matuƙar kona masu rai, shi ne suke cooling down na temper ɗinsu kada su sanya lahira tai baƙo.Haka dik jami’an nan suka bada ra’ayoyinsu da shawarinsu game da dabarun da suke ganin ya dace abi, amma su dai SSO shiru babu wanda ya ce word. Dole aka kyalesu dan shi Mr President ya san su waye su, dan haka shirunsu shi ne mafi alkhairi ga kowa dake hall ɗin.Bayan gama jin shawarin kowa Mr President ya yanke shawarin da ta dace, sannan ya umarci sabbin matakai.Karfe 4 na asuba daidai suka gama wannan zama, Mr President ya yi wa kowa godiya game da gargaɗi mai karfin gaske, musamman ga ministan tsaro, sannan daga karshe guru ya rufe masu taron da addu’a, dan su Lion kam har yanzu sunƙi ɗago kai bare su sake yin magana.Mr president ne ya fara fita, then su Lion suka rufa mashi baya, kai tsaye cikin gidan suka shiga, dan sun saba, in sun shigo Washington a nan ma suke sauƙa, ba yadda His Excellency bai yi da su ba kan su dawo Washington da zama amma suka ƙi, a New York aka haifesu har suka girma ba zasu iya ƙaura ba.Already suna da room ɗinsu a gidan, dan haka shiryar suka yi tsab bayan sun yi wanka, suka fito zuwa masallacin shigaban kasa dake cikin fadar. Bayan sun yi sallah suka hau hanyar komawa New York, basu sake zama da Mr President ba dik da cewa ya so hakan, ya so su yi zama kan bincken nasu amma ba dama sai kawai ya hakura suka wuce. Tin da suka kama hanyar airport Lion ya kifa kansa da jikin kujerar mota yana wani irin sauke numfashi mai ɗumi. Da farko Aryan ya so sharesa, amma ya ji ba zai iya ba, sai ya matso ya dafa shi tare da tambayansa me yake faruwa?. Tamkar zai haɗiyi zuciya ya mutu, sai da ya yi shirun good 5 mins, har sun fidda ran zai yi magana, sannan in a harsh way ya ce. “Ta ya za’ayi duniya ta gyaru? Ta ko’ina gurɓatattu ne! Son kai, zalunci, cin amana, son duniya, son abin duniya, dik ya cika zuƙatan kowa! A haka ta ya za’ayi duniyar ta gyaru?”.Shiru dik suka yi, saboda sun san gaskiya yake faɗe, shegen son duniya ya mayar da kowa azzalumi mara imani. Gudun kada ta kwaɓe masu yasa suka yi shiru suka kyalesa, shi ma shirun ya yi, can kuma ya dunkule hannu ya daki glass na kofar motar sai da ta tarwatse saboda ba dukan wasa yai mata ba, gabaɗaya glass ɗin kuma ta farfasa mashi hannu sai jini jajir ta fara malala, takaici tamkar zai mutu, dik ta in da ya juya azzalumai ne masu son kai, su sha wahala su yi aiki tukuru amma tamkar basa yi saboda yadda zalunci ya cika ko’ina, dole ya fusata, dole ransa ta ɓaci, dole ya daki abin da ya fi glass.Cikin zafa Aryan da guru suka damki hannun nasa, har suna rige-rigen damƙa. Sai dai ina, kwace hannun ya yi tare da sake dunkuleta ya daki jikin marfin motar har sai da ta girgiza, take glass ɗin suka sake natsawa cikin hannunsa, yana wani irin huci tamkar zai kama da wuta, with harsh voice ya ce. “Is better for me to die a kan irin wannan murɗaɗɗen rayuwa, kowa burinsa ya sami duniya, kowa ya manta da ALLAH da ranar tashin alkiyama, kana ƙoƙarin gyara gabas laanannun nan na kwance maka da lalata maka yamma!”. Ya kai karshe tare da daddagewa ya buga kansa da jikin marfin motar ta wajen glass da ya fashe ya bar sauran guntu-guntu. Cikin fusata ya sake ɗaga kan nasa zai buga Aryan ya rikesa da karfi yana ƙoƙarin dannansa. Dik glass ɗin ta fashe mashi goshi, abin akwai mugun cin rai da kayan takaici ne, ace jami’an da yakamata ku haɗa kai ku gyara kasar suke da alhakin wasu kaifukan? Dole ya shiga wannan mood ɗin. Wani irin jiri ne ta fara ɗibansa a lokacin da yake ƙoƙarin kwace kansa daga damkar da Aryan ya yi mashi. Rikesa gam Aryan ɗin ya yi jini na ketowa daga gaban goshinsa in da ya buga kan izuwa kan tongue ɗinsa da ya ciza da hakwaransa tamkar zai fasa harshen nasa saboda tsananin takaici. Guru ne ya cewa driver ɗin nasu ya taka motar da gudu sosai tin da sun kusa isa cikin airport. Basu ƙara wani tafiya sosai ba Lion ya ɗauke wuta a jikin Aryan saboda zafin da zuciyansa ta ɗauka, sumewa ya yi, ga zafin da kansa take mashi tamkar zata fashe. Godiya suka yi wa ALLAH da ya sanya ya suma, zasu samu sauki. Shi ma Aryan ɗin dauriyar ce kawai, amma ji yake tamkar yai ta buga kansa a bango kada ya dakata, wannan musifa dame tai kama.To a haka dai suka dawo CRYSTAL PALACE, kai tsaye gida suka koma, Aryan da kansa ya yi treating Lion yadda yakamata, ya gyara mashi gaban goshinsa da hannun nasa, sannan ya bisa da alluran barci na good 5 hours dan ya samu barci, hakan zai sanya ya samu natsuwa kuma zuciyar ta sassauto.Bayan sun tabbatar yana cikin aminci da kariyar UBANGIJI sai suka nufi room dake kusa da wanda yake a ciki, suka yi wanka, sannan suka shirya cikin pjs dan shan iska. Parlo suka dawo suka zauna, gabaɗaya Aryan bai nemi Seraphina ba, kuma tana ransa, dik wannan abin da yake yi tinaninta na cikin ransa, amma ya daure dan ya gwada mata yana fushi da ita har sai ta bashi hakuri.Wayarsa ya ciro, ya kunne other sim ɗin tare da fara ƙoƙarin nemo number Faryan dan ya ji ya gida suke. Saƙonnin ne suka fara shigowa kamar ruwa, wasu tin daren jiya, sakonni sun kai 30, kuma dik na Seraphina ne. Kin buɗe saƙonta ya yi, ya nufi fita kan saƙonnin kawai unexpected idanunsa suka sauƙa kan sako da number Madam Rohisha.Da farko kamar ba zai buɗe ba, amma da ya tina kila wani abin ne sai ya buɗe. Saƙo ne a rubuce kamar haka. “Tin da rana muke nemanka a waya a kashe, please idan ka buɗe waya ka gani ka zo gida baby taki cin abinci, taki yin magana sai kuka kawai take yi, na yi rarrashin duniyar nan amma ta ce idan baka zo ba sai dai yunwa ya kasheta”. Yana gama karanta saƙon ta duba time da ta turo saƙon 11:30 na dare. Ya ALLAH salati ya yi a fili tare da miƙewa da sauri, ya duba time yanzu karfe 10:30 na safe, ya yi daidai da lokacin da ya bar wajenta jiya. Dafe kansa ya ɗan yi, bai yi zaton abin zai kai haka ba, ya san tana da saurin kuka, to ya ɗauka idan ta yi kukan na ɗan lokaci zata mance komai ta koma walwalarta, ban san soyayyarsa ta yi matuƙar ginuwa a ranta ba, ba laifinta bane, bata san tana yi ba, laifin zuciya ce, a hankali soyayyar daddyn nata ya gama mamaye zuciyarta ba tare da saninta ba kamar yadda shi ma soyayyarta ya gama mamaye dikkan jinin jikinsa ba tare da ya sani ba.Jin ya yi salati ne yasa guru tambayarsa lafiya! Ai ina, bai bi ta kan guru ba ya nufi waje da sauri tamkar zai tashi sama. Kai tsaye benensu ya nufa. Yana shigowa ya shiga cikin ɗakinta kai tsaye.A bakin door ya tsaya ya zuba mata ido, tana zaune a tsakiyar gado, ta rungumo katuwar teddy ɗin fari tas da girmansu kusan ɗaya da ita, sai yazamana tamkar ita da kawarta Rimsha ne suka rungumi juna, tana manne da waya a kunne, tana kuka tana faɗawa Rimsha daddynta yana fushi da ita, tin jiya da ya fita cikin fushi bai dawo ba kuma bai kirata ba, da ta kirasa yaki ɗauka, da ta matsa ya kashe wayarsa, Rimsha ta taimaka mata ba zata iya jurewa ba.Ya so ace ya ji amsar da Rimsha ɗin ta bata, amma ya cigaba da zuba mata ido yana kallon yadda take kuka tana turo baki, idanunta sun kumbura sosai, sun yi jajir, while ƙasan idanunta ya yi jajir, tsinin hancinta ma jajir, sai shessheƙa take yi. Har cikin ransa ya ji zafin ganin yadda ta sha kukan, amma ya daure yana jiran ta gama wayar, ta ɗan kifa kanta a jikin Teddy ɗin.Ba yadda Rimsha bata yi da ita kan ta faɗa mata meyasa daddyn nata ya yi fushi ba amma taki faɗe, me ta yi mashi sai ta ce babu, ta ɗaukarwa kanta alkawari ne kan ba zata sake gigin maganar hotonsa da kowa ba, shiyasa taki faɗawa Rimsha a kan hoto ne. Daga karshe dai rarrashinta Rimsha ta yi, ta ce tin da Monday zasu haɗu a school ai kada ta damu zasu san yadda zasu yi da daddyn nan.Da haka dai ta lallaɓata har ta samu ta yi shiru. Daga haka suka yi sallama, tana ajiye wayar ta ɗago kai tana jan hanci. Unexpected idanunta suka sauƙa a kansa, ya yi holding hands ɗinsa a saman chest ɗinsa, kallonta kawai yake yi. Ai wani irin zabura ta yi, da gudu ta diro kasan gadon tare da sakin Teddy ɗin nata. Sake hannayensa ya yi tare da buɗe mata, ta zo da gudu ta faɗa jikinsa tare da fashewa da sabon kukan da muryanta sam baya fita. Rungume sosai ya yi tare da ɗagata sama suka koma cikin room ɗin, a gefen bed ya sauketa, ya zaunar da ita tare da tsuggunnawa a gabanta, tana cigaba da kuka sosai mai taɓa zuciya. Hannu yasa ya ɗago haɓarta, suna fuskantar juna, ɗan shanyewa ya yi ganin yadda face ɗinta ya yi jaga-jaga da hawaye ga kumburi ido. Can ƙasan maƙoshinsa ya ce. “For give me my Cherry Bloom”. Ya faɗa tare da kamo hannunta yana ɗan rarraba ƴan yatsunta kuma yana ɗan mammatsatsu, idanunsa a kan face ɗinta.Cikin kuka tana shessheƙa ta ce. “Daddy for give me, na san na yi maka ba daidai ba, amma baka bani damar in baka hakuri, dana kiraka ma kashe wayarka ka yi”……. Manna ɗan hannun nata a kumatunsa ya yi, yana kallon cikin idanunta ya ce. “Ba saboda ke na kashe waya ba, kuma daddy ba zai taɓa yin fushi da Cherry Bloom ɗinsa ba, na yi tafiya ne zuwa…….. “. Kome ya tina sai kuma ya fasa faɗa, da ya so ce mata ya je Washington ne sai ya fasa.Ɗayan hannunta ta ɗaura a saman kyakkyawan madaidaicin sajensa dake kwance a gefen da gefen kyakkyawan face ɗinsa, ɗan shafawa ta yi izuwa lallausan kumatunsa kafin ta ce. “To daddy for give me, I promised you that ba zan sake kwatanta abin da na yi ba”……. “Daddy ya yafe maki, yanzu faɗa mun burikanki guda uku daga cikin burukanki da kike son cikawa a duniya!”. So yake ya sanyata farinciki, ya faɗa yana matsa ƴan yatsunta dake saman kumatunsa.”Ina da buri huɗu dama”. Ta faɗa tana sauke ajiyar zuciya. Zuba mata idanu ya yi ba tare da ya yi magana ba alamar yana saurarenta kenan……… A shagwaɓe ta ce. “Daddy ina son zuwa in da rana yake fitowa, ina sun zuwa garin, ina son ganin rana ya fito a kan idona, ina son yawo a tsakiyar teku cikin jirgin ruwa ina ganin manyan shark suna yawi, ina da wannan buri, kuma shi ne babban burina a duniya bayan son ganin Annabi Muhammad ko da a mafarki ne! Ka ji buri biyu! Na farko son ganin Annabi, na biyu zuwa in da rana yake fitowa, da yawo cikin tsakiyar katon teku, na uku ganin daddyna da uncle ɗina, ina son in gansu, in rungumi daddyna in ji ɗumin jikinsa, in faɗa mashi wani mugu ya shigo gidanmu ya kashe mammyna dan ya ɗauka mana fansa, daddyna fa soja ne daddy, yana da karfi kuma yana da bindiga, mammyna ta ce babban jami’i ne, shiyasa nake son in gansa sai in faɗa mashi ya ɗauka mana fansa, burina na huɗu ganin fuskan SSO jarumaina kenan a duniya”.Kamar wasa ya ce mata. “To idan kika ga wanda ya kashe mammyn naki zaki ganesa ne?”…….. Da sauri ta gyaɗa mashi kai alamar e, kafin ta ce. “Yana sanye da nose mask, amma for sure idan na ga idanunsa zan ganesa, he have jade eyes, very big and sexy, zan iya gane waɗan nan idanun nasa masu zubin ƙanƙara”.Ɗan ɗauke wuta Aryan ya yi jin ta ambaci halittar idanun Lion, a zuciyansa ya ce babbar magana, watau kallon makashin da ya kashe mammynta take yiwa mashi, lallai akwai gagarumin matsala randa gaskiya zata bayyana.Ganin ya yi shiru yasa ta ce. “Daddy kaga labarai daren jiya? SSO sun je Washington zaka da mr President da suke yi dik karshen wata? I saw them in television, daddy i really love SSO with all my heart, amma basu son a kalli face ɗinsu suna ɓoyewa, ina burin in ga face ɗinsu ko sau ɗaya ne”……. Jin waɗan nan kalamai nata ya sanya shi sauke ajiyar zuciya, yana ƙoƙarin yi mata magana sai ta rigasa da cewa. “Very soon zasu kama mana waɗan nan azzaluman IRON FISR ɗin su yi masu kisan walaƙanci, su bauwa karnuka gawarwakinsu”. Jin waɗan nan kalamai kuma yasa ya dafe kai, a ransa ya ce. “Mu dai mun shiga uku a hannun Seraphina, daga an tsanemu, sai ana kaunarmu, sai kuma aka ce Lion ne ya kashe Mammy an tsanesa, to wanne ɗaya zamu rike ne?”.Yana cikin tinani ya tsinkayo muryarta tana cigaba da yabon SSO. Nisawa ya yi kafin ya ce. “My Cherry Bloom, ke da kike cikin ɓacin rai kina ta kuka jiya yaushe kika samu damar ganin labarai kan SSO? Ko dai dama kukan gulma ne da rigima?”. Ya faɗa yana jifanta da wani irin kallo mai kama da tuhuma.Turo baki ta ɗan yi tare da fara rarraba eyes ɗinta daga nasa idanun zuwa ɗan bakinsa, sai kuma ta kawar da zancen da cewa. “Daddy I’m feeling hungry”. Tana shagwaɓe fuska ta faɗa……. Gera guda ya ɗaga mata kafin ya ce. “Answer my question first, a yaushe aka samu damar ganin labarai kan SSO?. Zaki mun wayau ki canza topic na hira ko?”. “Kai daddy kai daddy, ni kada ka tambayeni”. Ta faɗa tana kai hannu ta ja dogon hancinsa, yadda ya ɗaga mata gera gudan nan har sai da ta ji zuciyarta ta motsa, ya yi balain tafiya da ita.”See your eyes na marasa gaskiya, zaki yi bayani ne anjuma, now go and bring your breakfast so I can feed you, da wani ɗan bakinki a wajen, wai kema kin yi wayau, a haifeki a gaban nawa ne zaki mun wayau yanzu?”. Sam ba da wata manufa ya faɗi wannan magana ba face kawai hira….. Zazzaro ido a kansa ta yi, sai kuma ta ce. “Daddy dama a gabanka aka haifeni?”….. Kai ya gyaɗa mata alamar e ba tare da ya kawo komai a ransa ba.Kara zazzaro ido ta yi kafin ta ce. “Yauwa daddy to bari in baka two questions”…… Jinjina kai ya yi alamar yana jinta……… “Time da muke Jss3 an faɗa mana sai mace da namiji sun yi having sex sannan ake samun cikin da za’a haifi babys, to ina son sanin yadda ake haihuwar, then one of my classmate show me the video na yadda ake having sex between ladies and mens, and i saw the lady is crying i time da suke having sex ɗin, ina son sanin shin dama …….”. Ai ɗauke wuta da maganar ta yi ɗiff ta gagara ƙarisawa saboda zazzaro mata ido da ya yi, ya yi mugun razanata ba kaɗan ba, bare ma yadda ta ga face ɗinsa ya canza lokaci guda, take tsananin tsoronsa yakamata.Muryanta har yana ɗan rawa ta ce. “Da…… Dadd…….. Daddy…. Are you okey?”…….. Ai bai san time da ya wani irin………….. E lallai Seraphina ta ɓaro babban aiki, da matsala kuwa, watau daman tasan sex? Har video ta taɓa gani, ba shakka yau Aryan zai ɓallata kuma ya kaita asibiti ayi ɗori, baby Cherry Bloom team yau kuma ruwa tsundum.



