Halysaah Page 69 By Khaleesat Haydar
HALYSAAH PAGE 69…Khaleesat ta bi Jay da kallo ganin ya nufi parlor, kana ganinsa zaka gane shi ma bai so abinda yayi ba don bai yarda ya sake hada ido da ita ba, kamar bai san sanda ma yayi hakan ba, ganin ya zauna a parlon ta sauke idonta daga kallonsa, sai kuma ta juya ta koma kitchen, Jay yayi dialing number AJ amma har ya katse bai yi picking ba, bai yi zaton zai shigo parlon ba don har yana ce masa kar ya bata masa lokaci, ya mike ya tafi window din parlon yana duba garage amma sai yaga ya tafi don babu motarsa a garage din, komawa yayi ya zauna ya cire face cap dinsa, Khaleesat na fitowa kitchen ya maida face cap din without raising his head, ita dai kanta a kasa ta karaso parlon tana rike da bottle water da glass cup ta duka gabansa ta ajiye masa, still not looking at him a hankali tace “Sannu da zuwa” Sai a sannan ya ɗan kalleta, ganin ba kallonsa take ba with calm in his voice yace “How are you Halysaah?” Cikin sanyin murya tace “Alhamdulillah, ya hanya?” Yace “Cool” Tana wasa da fingers dinta tace “Yaushe ka dawo?” Har sannan bai cire idonsa a kanta ba yace “Not less than an hour ago Housemate” A hankali tace “Ya su Mama da mutanen gida?” Yace “They are all good Halysaah, ya karatu? In few weeks time za ku fara Spring semester exams ko?” Ta gyada masa kai, shi dai kallonta kawai yake, can yace “How is Safiyyah?” Ta kwantar da kanta saman gwiwowinta har sannan tana jin kamshin turarensa na tashi a jikinta tace “She left not long ago” Sai kuma ta daga kai ta kallesa, sauke idonsa yayi daga kallonta, ita ma ta sunkuyar da kai tace “What should i make for you? Daxu danwake Sophie tayi mana and it’s finished, should i make you pasta or rice?” Yace “No don’t worry Housemate, Ajay made some food for me back home” Ta ɗan bude ido tana kallonsa tace “Can he cook?” Kawai yayi murmushi wanda iyakarsa lips bai bata amsa ba, sai kuma ya nuna mata trolley din da ya shigo da shi parlon yace “I got you some stuffs, hope you will love it” Shiru tayi tana kallon akwatin, yace “Check them” Ta sauke idonta sai kuma ta mike ta bude akwatin, tsadaddun Abaya ta fara cin karo da tana bude akwatin, ta daga kai ta kallesa suka hada ido ya sakar mata murmushi, sauke idonta tayi ta rufe akwatin kawai, cikin sanyin murya tace “Thank you soo much, Allah ya saka da alkhairi, Allah ya kara budi” Yace “Ameen Halysaah” Still bata dago kanta ba a hankali tace “And i also want to appreciate you for what you did to my parent, Allah Ubangiji ya sa kafi haka, Allah ya biya maka duk bukatun ka na alkhairi….” Bai tanka ta ba yana kallon agogon wrist dinsa ganin bakwai saura yace “I will take my leave now Housemate, it’s late already” Ita dai bata ce komai don sai taji babu dadi da yace zai tafi, ya mike yana kallonta yace “Kina da lectures gobe ne?” A hankali tace “Sai karfe daya na rana” Yace “Ohk, i will come before then in sha Allah, Aunty Farida ta bada sako a kawo maki, yana mota kuma Ajay ya tafi da motar” Ita sai a sannan ma ta tuna ashe Ajay ya shigo gidan fa, ta kallesa tace “Ohk, but how are you going back home tunda ya tafi da motar? Kayi order din Uber ne?” Jay yace “Ohh, na ma manta” Komawa yayi ya zauna yana danna wayarsa yace “Let me order the ride now” Ita dai tayi shiru tana kallonsa babu ko kiftawa, har ya gama order din ya daga kai suka hada ido, sunkuyar da kanta tayi tana jan yatsunta tace “Toh baza kayi sallah ba kafin ride din ya karaso?” Yace “Ohk bari in yi alwala” Mikewa yayi ya nufi bandakin dake parlon, ita ma ta tashi ta tafi sama dauko masa darduma, bayan Jay ya idar da sallah Khaleesat na kallonsa daga bayan kujeran da take tsaye tace “Or should i make you tea?” Yace “My ride is waiting Outside Housemate” Ta gyada masa kai kawai, tana biye da shi a baya har suka fita daga apartment din, ta rakasa har gun Lyft din dake jiransa, yana kallonta kafin ya shiga motar yace “Sai na zo gobe, take care of ur self” Ta gyada masa kai don har cikin ranta take jin da ma kar ya tafi, sai yanxu ta kara tabbatar da irin missing dinsa da tayi, memories dinsu tare na old apartment dinta ya dinga dawo mata a kai, and she misses every bit of those moment, she wish it’s gonna happen again, a hankali ta juya bayan ya shiga Lyft din tana tafiya kamar mara lafiya ta koma apartment dinta ta kulle kofar. Jay na komawa gida ya bude kofa parlor ya tarar da Legend zaune bakin kofar alamar shi yake ta jira, tun da ya dawo gidan daxu bayan Ajay ya daukosa a airport Legend ke ta tsalle kansa yana haushi kamar zai rungumosa wanda hakan ke nuni da yayi missing dinsa ba kadan ba kuma ya bi sa har daki yana wagging tail dinsa yana kada kai alamar farin ciki ya nemi waje ya zauna a dakin, kafin su fita daxu kuwa sai da Jay ya kullesa a Cage dinsa don bin sa ya so yi yana ta haushi, Jay ya kalli Ajay dake zaune parlorn yana danna wayarsa ko dago kai bai yi ba, dukawa Jay yayi gaban Legend yana patting kansa ya bude steak din da ya siyo masa a hanya ya ajiye masa a pack din sannan karen ya kyalesa ya maida hankali kan Steak din, Jay ya mike ya karasa cikin parlon yana kallon Ajay yace “Didn’t you see my call?” Ba tare da Ajay ya kallesa ba yace “I didn’t” Jay bai sake ce masa komai ba ya nufi kitchen, bayan wasu yan mintoci ya fito yana kallon Ajay yace “Where is the food you said you made?” Still not looking at him Ajay yace “Nayi zaton can zaka kwana ae, i gave all the food to the workers” Kallonsa kawai Jay yake, can ya juya ya koma kitchen din to make a cup of tea for him self, ko kafin ya fito kitchen din Ajay ya bar parlon. Washegari wajen karfe sha daya Khaleesat ta sauko downstairs jin ana danna bell, bayan ta tambayi waye ta bude kofar parlon, gaishesa tayi tana kallonsa, ya amsa da murmushi, zata amshi ledan hannunsa yace “Don’t worry Halysaah” Juyawa tayi ta koma cikin parlon, ya bi bayanta, bayan ya ajiye ledan yana kallonta yace “Sakon Aunty Farida da tace a kawo maki” Khaleesat ta karasa ta dau ledan ta kallesa tace “Thank you so much” Kitchen ta tafi da shi ta duba taga cin cin ne me yawa aka yi packaging sai alkaki da dublan, a wani ledan kuma ta ga kayan kamshi na dafa shayi, sai flour, kuka da kanwa, da dakakken yaji me yawa, tana gani ta gane saboda danwake aka aiko mata, ɗan murmushi tayi sai kuma ta dau take away a kitchen ta dibi cin cin din da su alkaki ta saka a wani ledan ta dawo parlor da shi, dukawa tayi gefensa da ledan, yana kallonta yace “What’s that?” Tace “Cin cin ne da alkaki da Aunty Farida ta bada a kawo, i fetch some for you” Ya ɗan bude ido yace “No, ta bamu namu ni da Ajay, it’s at home wannan naki ne” Ta wani kallesa tace “Ban yarda ba” Yace “I am serious, har da tea spice da grounded pepper duk ta bamu” Khaleesat tayi murmushi tace “To na yarda” Mikewa tayi ta maida cin cin din kitchen, sannan ta fito tace “I made you some food in kawo maka yanxu?” Yace “I had breakfast before leaving home Halysaah” Ɓata fuska tayi tana kallonsa, yayi murmushi ya sauke idonsa yace “Ohk… amma kadan zaki zubo min ba da yawa ba” Juyawa tayi ta koma kitchen din, ba a dau lokaci ba ta kawo masa shinkafa da stew din kaza da tayi, yana kallon abincin yace “Wannan ai yayi yawa” Tace “Eat and remain” Shi dai murmushi kawai yayi, ta koma kitchen ta dauko masa ruwa da glass cup ta ajiye masa, yace “Karfe nawa kika ce kina da lectures?” Tace “Karfe daya” Yace “Ohk to ki shirya idan na gama sai inyi dropping dinki nima zan shiga school din” Tace “Ohk, nagode” Sama ta wuce ta bar sa a parlon. Ko da Khaleesat ta sauko downstairs wajen karfe sha biyu da rabi ta gansa kwance kan 3 sitter idonsa a lumshe, murmushi tayi cause this is one of the part she misses so much about him, ta dafa bayan kujeran a hankali ta duka tana kallon innocent face dinsa, zagawa tayi tana tafiya a hankali ta tafi gun Vase din artificial flower dake parlon ta zari daya ta dawo gabansa ta duka dai dai fuskarsa ta kai flower din a hankali moving it back and forth his face, cikin bacci ya kai hannu fuskarsa da sauri ya kauda kai, hakan bai sa ta dena abinda take ba, yana kokarin mikewa zaune ya kusa cin karo da ita banda tayi saurin matsawa baya, ta dinga kyalkyala dariya tana kallonsa, murmushi yayi ya jinginar da kansa da kujeran yace “See this girl, wa yace maki ban ga sanda kika sauko ba, i just pretended i was sleeping” Tana dariya tace “Wallahi baka gan ni ba, you were sleeping” Shafa kansa yayi still smiling ya mike tsaye yace “I am waiting for you at the garage, amma ni dai nasan ba bacci nake ba i was just meditating…” Daga haka ya nufi kofa ta bi sa da kallo tana murmushi, ta kalli wayarsa da ya bari kan kujera without noticing, sai da ta jira har ya fita daga parlon sannan ta duka kusa da kujeran ta dau wayar taga babu lock, miss calls ta gani guda hudu na wani number da aka yi saving with Hadiyah tare da text message dinta, call logs din duk yawanci miss calls dinta ne, amma kuma yana picking wasu call din nata, Khaleesat ta dinga kallon number, can ta shiga cikin message din da ta turo masa, “You should have at least pick, just wanted to know if you’ve arrived safely” shine content din message din, A hankali Khaleesat ke strolling text messages din taga inda Hadiyah ta turo masa “I love you so much Baby, and i want to spend forever with you” Da bai mayar mata reply ba sai ta sake tura masa uhmm, sai ya mata reply da “Love yah 2” Fita daga messages din Khaleesat tayi without going any further, tana kokarin clearing duk inda ta shiga don kar ya gani kawai taga kamar hoton da suka yi a park da shi among many other apps da ya bude a ranan, tayi tapping zata shiga hoton kawai ya nuna mata wajen is locked, ta fi minti biyu durkushe a wajen rike da wayar don gaba daya jikinta yayi sanyi ko motsin kirki ta kasa, can dai ta mike a hankali ta dau jakar laptop dinta ta nufi kofa walking slowly, kafin ta bude kofar ya riga ta budewa har sai da ya ci karo da ita, komawa baya yayi da sauri, ita kuma ta dafe kanta, Ya shigo parlon yana kallonta da damuwa yace “Hope u are not hurt? I am sorry i should have knock” Ta girgiza masa kai kawai ba tare da ta kallesa ba, yace “Are you sure you are okay Housemate?” Zame hannunta tayi daga fuskarta tana kallonsa, a hankali yace “Sorry Halysaah, i forgot my phone shi ne na dawo dauka…” Mika masa wayar tayi ya amsa yana kallonta, ita dai ta sauke idonta, bude mata kofar yayi ta fara fita sannan shima ya fita, ta mika masa makullin apartment din ya amsa ya kulle sannan suka nufi motarsa har a lkcn bai daina waigawa yana kallonta ba to be sure she is okay har suka iso garage, ita dai bata sake yarda ta kallesa ba, ya bude mata gaban motar yana kallonta, ɗan murmushin karfin hali tayi still not looking at him murya can kasa tace “Thank you” Sannan ta shiga motar, tana shiga ya daga mata veil dinta da ya fito waje ya daura kan cinyarta yana kallonta, sae a sannan ta daga manyan idanuwanta ta kallesa ya sakar mata murmushi, ita ma murmushin tayi har sai da dimple dinta ya lotsa ta sunkuyar da kai tana wasa da gefen veil dinta, ya kulle motar ya zaga ya shiga driver seat yayi igniting motar, bayan sun yi nisa ya ɗan kalleta murya can kasa yace “Are you sure you are okay Halysaah?” Khaleesat ta ɗan bude ido tace “Sure…” Don tabbatar masa da hakan tayi kokarin creating conversation tace “Ya Junaid fa?” Jay ya maida dubansa kan titin gabansa yace “Ba kuna magana da shi ta waya ba” A hankali Khaleesat tace “A’a, sai if there is something important” Without looking at her yace “Something important like?” Tace “May be idan ya kawo min abu apartment” Yace “Abu kamar me?” Khaleesat ta juya ta kallesa tace “Grocery shopping” Jay ya gyada mata kai yana ci gaba da driving dinsa, har suka isa school babu wanda ya sake cewa komai a cikinsu, ita kam Khaleesat ta tafi duniyar tunanin da take…..*Halysaah is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u send ur evidence of payment 07087865788 👈🏻, it’s better ki ji tsoron Allah ki sauke nauyi kiyi karatunki cikin kwanciyar hankali don littafin na kudi ne, in kika karanta with no payment i owe you 500*
