Uncategorized

Macijine Shi Page 25-26 Hausa Novel

Na mammy kabeer

Elegant online writers📚📚

Free book 

Page 25/26

________________Tafiya suke cikin motar Ba tare da kowa ya ƙara cewa komai ba,ba abinda ke tashi cikin motar dai sanyi a.c da daddaɗan kamshi, gefe guda kuma ƙira’ar sudais ke tashi cikin suratul mulk.

Gaba daya zuciyoyinsu,sun sami nutsuwa,irin wacce mai sauraron Alƙur’ani ke samun tago mashi da ita.

Adeeb yana kwance cikin kujerar, idanunsa alumshe ,ahankali yake ɗan motsa bakinsa yana bin ƙira’ar,al’adar sa kenan dama shi,inda yana cikin mota ,to karatun alƙur’ani yake sauraro. Yayin da can ƙarƙashin zuciyarsa yake jin wani irin farin ciki da annashuwa,duk da baisan tsawon lokacin daya ɗauka cikin yanayi na wata halittar ba,amma yana ji ajikinsa cewa yayi kewar ahalinsa fiye da yadda yake tunani.ba abinda yake fata da buri irin ace yaganshi kusa da abie da ammi.ko wane yanayi zasu shiga idan suka ganshi?

Tunanin da Adeeb yayi tayi kenan cikin zuciyarsa.hakan ya hana masa fahimtar halin da fattu ke ciki.wato ta takure jikinsa sosai,sai rawar sanyi takeyi, sosai sanyin motar ke damunta, ga wani irin yanayi na kewar baffanta dake taso mata, sosai ta ƙunaci Jikin Adeeb ,aƙoƙarinta na samun gurin da dataji ɗumi.

Ahankali ta ɗan zakuɗa kadan zuwa jikinsa,ta yadda har kafaɗarta na gugar tasa.kuma har zuwa wannan lokacin tana riƙe da gefen rigarsa.

Shikuwa Adeeb jin anɗan bugeshi ,yasa shi buɗe idanunsa ahankali, ɗan juyowa yayi yana kallon fattu, wacce tayi lugus ajikinsa  tana karkarwa.

“Ke matsa daga jikina”ya faɗa cikin salon maganarsa ba tare da ya motsaba.

Da sauri fattu ta ɗan matsa ,daga jikin nashi,dan ita atunaninta dama yayi barcine.

Kallonsa tayi tare da marairaicewa tace “Hamma sanyi nake ji,kodai cikin ƙanƙara muke tafiya”ta faɗa zuciyarta ɗaya,tana ɗan gwabe fuska.

Kallonta yayi tare da harararta yace “dake baki san acikin ƙanƙara muke tafiyaba?ya faɗa cikin gatse.

Zato ido fattu tayi tare da dafe ƙirji,”na shiga ukuna Ni fattu ,dan Allah Hamma kayi min rai,mu canja wata hanyar wllh mutuwa zanyi idan naci gaba da jin sanyin nan”fattu ta faɗa cikin marairaita tana rawar sanyi,gaba ɗaya ta gama tsorata,idanunsa kuwa harya fara kawo ruwa.

Bamza Adeeb yayi da ita tare da maida idonsa ya rufe,wannan gaskiya ɓaci ƙauyencima akwai shirye atattare da ita,kamar ba tare suka shiga motar ba, ko ina taga alamun ƙanƙarama bare tace akanta suke tafiya?

Fattu kuwa ganin ya maida idanunsa ya rufe sai tsoro ya ƙara makata,da sauri ta cusa kanta tsakanin hannunsa da kujera, ta kara ƙanƙame gefen rigarsa tana kuka.

“Wayyo Hamma sanyi nakeji yana shiga cikin ƙashina ,jinina daskarewa yake” fattu ta faɗa cikin kuka,tsakaninta da Allah take kukanta.

Dafe kai Adeeb yayi tare da kallon Hisham yace “switch up that a.c” ya faɗa kamar baya so.

“Ok sir” Hisham ya amsa tare da kashe a.cn yana mamaki,yau yallaɓai ne da kansa yace akashe a.c?

Fattu kuwa ahankali taji ta daina jin sanyi da take ji,dan haka share hawayenta tayi tana mai cewa aranta.”anya kuwa Hamma ba so yake ya kaini gurin yan shan jini su tsotsemin jini ba? Ahankali ta dago kanta tana kallon fuskarsa ,shagala fattu tayi da kallon kyakyakywar fuskarsa ,barin ma light pink lips ɗinsa da gashin baki yayi masa ƙawayan,ga gemunsa mai kyau sai sheƙi yake,hanci kuwa kamar wanda aka ɗora masa,gaskiya Hamma akwai kyau ,inama nike da  kyansa,aikuwa danasha gayu.

“Ke meye kika ƙuramin ido haka?karki cinyeni” Adeeb ya faɗa yana mai tsare  fattu da idanunsa masu tsananin haske.

Dan duk yadda ta ƙuresa da ido yana kallonta ,dan ba duka ya rufe idon nashi ba .

Ɗan zabura fattu tayi ta matsa baya tana soso kai,dan ba ƙaramin kunya taji ba,ashe yana kallonta ta ƙuresa da ido haka? wayyo Allah Ni fattu .ta faɗa cikin ranta tana mai kwantar da kanta jikin kujera cikin kunya.

Tun daga lokacin ba wanda ya ƙarayin magana a cikinsu.

Adeeb yana cikin tunaninsa yaji fattu ta langaɓo kansa,dan dubawa yayi saiyaga ashe ma barci tayi.kafeta yayi da idanuwansa yana kallon zallar kyau irin na fattu,duk da ƙarancin shekarunta ,amma Allah yayi mata baiwar kyau,irin kyanda sai kana kallon mutum kake ƙara ganin kyan nashi .

Gyara mata kwanciyar yayi agefen kafaɗarsa ,duk da yadda yake jinsa atakure,kasancewar kusancinsu yayi yawa ,amma haka ya daure ya barta akan kafaɗar tashi taci gaba da barcinta.

Fattu na cikin barci taji  ana dan taffing kumatunta, Ahankali ta buɗe idanunta da sukayi mata nauyi saboda barci.

“Dagani malam duk cin batani da yawun barci ko” Adeeb ya faɗa yana hararar fattu

Wacce ke kif-kifta idanunta tana mai daga masa kafaɗa,kallon kafaɗar tashi tayi,amma ita bata wani ga yawu agurin ba.

Suna fita daga Motar fattu ta gansu kusa da  wani ƙaton jet ,Aida sauri ta kamo hannun Adeeb ta rike ƙam cikin nata tana mai zaro ido.

Fizge hannunsa Adeeb yayi yana hararar fattu “stop touching please” ya faɗa yanayin gaba binsa.

Da sauri fattu ta mara masa baya,tana binsa ƙafa ƙafa.tab yaushe zata tsaya kusa da wannan abu mai kama da girman duniya?haka kawai ya fado kanta ta mutu ?

Wani farin Balarabe ne ya fito daga cikin wata ƙofa,dake ɗan nesa da inda jet ɗin ke tsaye. 

Da gudu naga ya taho ya ruƙunƙume Adeeb yana sunbatarsa,kuma yana hawaye.

“Habeebi ina ka shiga ?me yasameka?kasan irin tashin hankalin da muka shiga?kowa na gida yana cikin damuwa,abie yana nan akwance ba  lafiya tunda aka rasaka”Balarabe ya faɗa cikin harshen larabci.

Murmushi kawai Adeeb yayi yana mai shafa kan wannan balaraben ,sannan  yace ” where is the imam?

Cikin share hawaye mutum yace “yana ciki kai kawai muke jira.

Kallon fattu Adeeb yayi yace “jirani ana karki biyoni” ya faɗa cikin hade fuska.kafin yayi gaba.

Da sauri fattu ta kamo hannunsa cikin marairaita tace “tsoro nakeji Hamma dan Allah karka gudu ka barni”ta faɗa cikin kwabe fuska.

Zare hannunsa kawai yayi baice komai ba suka shige cikin dakin da wanann balaraben ya fito. Zama fattu tayi akan wata kujera dake gefen ta,da alama kujerar sassaƙata akayi dan zama agurin,tagumi tayi rungume da yan kayanta,tunani take yanzu idan Adeeb ya gudu ya barta anan yazatayi? Gurin wa zata?dan ita dai yadda take ganin garin nan da zungura- zunguran gidajen dake cikin garin ,zaiyo wahala idan ba shan jini akeyicikin gidajen ba.shikenan ba ita ba ƙara ganin baffanta.

Daga kanta tayi ta kalli inda aka daka motar da suka zo cikinta amma watan bataga motar ba,saidai taga wasu tarin motocin can gefe guda arufe da wani abu.

Ƙila duk waɗanda aka kawo su cikin motocin can an shanye musu jininsu.yanzu itama haka za’a shanye nata jinin idan Hamma ya gudu?”wayyo ni fattu naga rayuwa “ta faɗa tana mai leave fuska da waige waige .

 Shikuwa Adeeb koda suka shiga ƙofar nan,

Kusan minti talatin suka ɗauka cikin dakin kafin suka fito,  ,lokacin fattu hatta fara kuka, tana ganinsa taji wani sanyi cikin ranta,da hanzarin ta ta miƙa tare da nufarsa tana kuka,tana zuwa ta kama hannunsa cikin kuka take cewa”Hamma harba fara kuka ,nayi tunanin gudawa kayi ka barni, anan ado a shanye min jinina, dan Allah Hamma karka ƙara tafiya ka barni” fattu ta faɗa tana mai ɗora kanta akan damtsen hannunsa. Wani irin yanayi na tausayinsa Adeeb yaji yana ratsa zuciyarsa,Allah Sarki,yasan ahalin yanzu bata da wani gata saina Allah saikuma shi,shi kaɗai ta sani,zaiyo iyakar ƙoƙarin sa ,wajen kula da ita har su cimma burin su. hannunta kawai Adeeb ya kama ,  tare da  nufar cikin jirgin nan.

Noƙewa fattu ta farayi cikin rawar jiki tace”Hamma na tuba Dan Allah karka sani cikin wannan abun mai kama da kifi” fattu ta faɗa tana mai ƙoƙarin zare hannunta daga cikin nashi.

Tsayawa yayi tare da kallon wannan balaraben yace tareeƙ ka shiga ciki “ya faɗa cikin harshen larabci.

Jinjina kai tareeƙ yayi tare da kama ɗayan hannun Adeeb ya sunbata kafin ya shige cikin jet ɗin.

Kallonta Adeeb yayi yaga yadda gaba ɗaya ta firgice,sai ƙoƙarin zame hannunta take cikin nashi.

Ahankali ya sanya hannunsa ya kawota jikinsa,yayi mata side hug,kana yace ” ki nutsu kinji,ba abinda zai miki zamu tafi gidane acikinsa” ya faɗa yana mai shafa kanta.

Jinjina kai fattu tayi tare da cewa”Ni bazan bikaba Hamma kamaida Ni gurin baffa ,bazan shiga wannan abunba tsoro nakeji,kifine da,muna shiga haɗiyemu zaiyi Hamma”ta kai ƙarshen maganarta cikin kuka.

Murmushin Adeeb yayi akaro na farko tun tasowarsu daga Kano,wai haɗiyesu zaiyi ,kifine.kai wannan yarinyar akwai ƙauyanci.

Ganin dai da gaske fattu atsorace take, sai kawai ya juyo da ita zuwa gabansa ,bai jira komai ba ya haɗar da jikinsa ya rungumeta cikin faffaɗan ƙirjinsa,ahankali yake shafa kanta zuwa kafadunta .

Shiru fattu tayi sakamakon wani irin nutsuwa mai cike da sa annashuwa dataji tana ratsa dukkan sassan jikinta,luɓ tayi cikin jikinsa ta daina wannan rawar jikin,idanunta kawai ta kumshe tana shaƙar daddaɗan kamshi da Adeeb keyi.

Kusan minti uku Adeeb ya bata ajikinsa,yayinda shima yake jinsa cikin wani irin yanayi na samun nutsuwa da peace of mine ,ji yake kamar suyi ta zama ahakan, amma tunowa da yayi da abinda ke gabansa yasashi saurin ɗagota daga jikin nashi,ƙara komawa fattu tayi ta kwantar da kanta akan ƙirjinsa,ba tare da tasan tayi hakan ba,.cibiya ya karatu kafin yace “to dagamin jiki karki karyani”ya faɗa daidai saitin kunne ta. Wani yuuuuuuu fattu taji ,jiri na  neman dibanta, lokacin da iskar bakin Adeeb ta bugi kunnenta,da sauri ta rike damtsensa tana mai runtse idanunta,saida suka sake ɗiban minti kusan biyu,kafin Adeeb ya ɗagota,wanna karon bayi musu ba,saidai kanta na ƙasa cikin jin kunya.

“Ya isheki haka ko kina don daɗi?”Adeeb ya faɗa yana kallon fuskarta.

Shiru tayi kanta a ƙasa ba tace komai ba.

Hannunta Adeeb ya kama suka fara taka matakalar. Taku ɗaya biyu kawai fattu tayi luuuuuu zata daɗi ƙasa ,da sauri cikin azama Adeeb ya ruƙota ,yana mai zato idanu waje.

Fattu kuwa ji tayi kanta yana juyawa sosai,tace “Hamma ka rikeni zan faɗi “ta faɗa tana mai kumshe idanunta.

“Ina tare dake ba abinda zai sameki”Adeeb ya faɗa ,yana mai ɗaya fattu kamar ya ɗauki jaririya ya shige cikin jet din.

Wow wato shi kansa cikin jet ɗin abin kallo e ,tsayawa fasalta yadda ya tsaru kuma bata lokacine,na barku kawai ku ƙiyasta tsaruwar jet ɗin.

Sin yanufa ya zauna tare da rungume fattu cikin jikinsa,yana shafa kanta ahankali.

Belt ya ɗaura musu kafin ya ɗanan wani ɗan guri saiga kujerar ta mike ,yadda mutum zai iya kwanciya akai.

Wata har danja ya latsa ,nan danan mai tuƙin wato tareeƙ ya tada jirgin sukayi kula sukayi sama.

Ƙara gyarawa fattu kwanciya Adeeb yayi ajikinsa yana mai kallon fuskarta dake cike da tsoro,idanunta arufe gam, da hannunta shima ta rukunkume Adeeb dasu, idanunta kuma na tsiyayar da ruwan hawaye .

Ahankali Adeeb ya sanya hannunsa yana mai share mata hawayen bakinsa ya kai daidai goshinta kamar zaiyi mata kiss saikuma yayi saurin dauke kansa .

Ajiyar zuciya Adeeb yayi yana mai kallon sararin samaniya cike da jin wani irin shauƙi cikin zuciyarsa

Manage please my people,

Banda caji wllh nefa ya sami matsala.

Mrs babi ce💘💘💘

Share and comment fisabilillah

More comment 

More typing.

Back to top button