Hausa novels

Haihuwa Da Hanji Page 25 Hausa Novel

Sulaiman kaman zai kama hannunta haka ya tsaya gabanta yana kallonta.”Da gaske ke ce? Ashe zan sake ganinki Afeefah? Ina kika shiga? Kin san irin neman da na miki?”Idanunta na sauƙa kanshi ta miƙe tsaye, ganin irin kusancin su ya sa ta ɗan yi taku biyu baya fuskarta a sake tace “Ina nan Dr. Allah ya haɗa ni da mutanen kirki””Afeefah me yasa ba ki zo office na ba? Me yasa ba ki neme ni ba da mahaifiyar saleem ta kore ki?”Idanunta ne suka cika taf da kwallah a hankali tace “Ban san inda zan sameka bane ban san sunan asibitin ku ba ko in ce ban riƙe ba, ko ma na riƙe ba ni da ko biyar da zan hau abin hawa in ce a kawo ni”Idanu ya ɗan runtse kaɗan ya buɗe da sauri sai ya ga kaman za ta iya ɓace mishi any moment “Ina kika shiga to? Waye ya taimake ki?””Na haɗu da mutanen kirki sun tallafeni daidai lokacin da na buƙata kuma suna riƙe ni tamkar ɗaya daga cikinsu yanzu haka ina makaranta””Alhamdulillah!”Zama yayi saboda a lokaci ɗaya daaɗi da baƙin ciki duk suka haɗu mishi, itama ta zauna a hankali ya ce “Afeefah har Dutsen-wai na je nemanki”Da sauri ta ɗago ido suka haɗa idanu ya gyaɗa mata kai alamun tabbaci.”Gidan kawu ka je?”Kai ya gyaɗa cikin nuna damuwa ya ce “Abin da muka tarar ba karamin tsoro ya bamu ba Afeefah, ban so ba, ban san hakan zai kasance ba da ban yi ganganci da kuskuren tafiya da manya na ba”A lokaci daya ta zama very confused sun je gidan kawu? Me suka tarar? Me yasa yaje da wasu?.”ko da ban furta miki ba kin dai san Sonki nake ko Afeefah?”Lumshe ido tayi kalamar na sauka mata wani iri a zuciya.”A lokacin da na samu labarin tafiyar ki i was very disturbed na ɗauka chan gida za ki koma, ko da na koma gida na samu mahaifiyata da labarin ban gama bata ba Abba ya shigo ya ji zancen, dama ya matsu kuma da maganan aurena dole ya haɗa ni da Yayyenshi kuma ya kafa hujja ne da cewa a musulunce ma bai halatta namiji ya fara taran mace ba tare da sanin iyayenta ba.. Dole ta sa muka tafi tare da su ba don na so ba”Hawaye ne ya zubo mata a kan fuska ta ɗan yi murmushi mai yanayi da wani ciwo a ƙasan rai ta ce “Sun ji kunya ko? Na tabbatar ba su amince maka ba kuma ba za su taɓa amince maka ba..! Ka yi haƙuri, da na san za ka aikata hakan da ni da kaina na faɗa maka wacece ni kafin ma ka je”Ya ɗan haɗiye wani abu mai ciwo a hankali yace “Afeefah sun yanke min hukunci mai girma a yanzu haka ina da aure, an ɗaura min aure last week saturday amma har yanzu zuciyata ke take so, ke take marararin rayuwa da ba wata ba. Na haƙura na karɓi auren ne saboda ban san inda zan ganki ba ban san inda zan sameki ba, a ina ne gidan da kika koma? Idan kin ga da takura za ki iya dawowa wurin Umma na tabbatar ita me riƙe ki ce tamkar ɗiyar da zata haifa a cikinta”Rayyan ne ya fito sai idanunshi ya faɗa kan su, a kan hawayen dake bin ƙuncin ta ya ɗan tsayar da idanun kan ya ɗauke kai ya zo ya wuce su kaman bai gane su waye ba, Afeefah da suka haɗa ido ta sa hannu ta share hawayen fuskarta ta dubi Sulaiman “Zan tambayi Mammi zan zo in gaishe Da Umma! Amma batun soyayya don Allah ka ajiye shi a gefe Dr. Kai fa ka gayamin irin abubuwan da Kawu ya muku na ba da kunya, taya za ka yi convincing iyayenka su sake komawa irin gidan chan?””Zan iya Afeefah kawai ki ba ni dama!”Ta girgiza kai “Aurenka fa?”Zai yi magana ta ce “Ka yi haƙuri Dr. Yanzu ba lokacin wannan maganan bane marar lafiya muka kawo”Shigowar Abeeha da Jannah ne ya sa ta ƙarasa share fuskarta ta ƙirƙiro murmushi ta saka, suka ƙaraso kusa da ita “Afeefah ya jikin Mammin?”Ta ce “Da sauƙi sossai amma tunda Ya Saraki ya shiga da ita ba’a fito da ita ba””Amma Yaya Rayyan ɗin yanzu muka wuce shi a waje yana waya””Eh shi kadai ne ya fito”Gaisawa suka yi da Dr. Sulaiman yana mamakin jin ana ambaton Rayyan, gidan su Rayyan ta koma?”Afeefah ko zan iya samun Layin da zan yi magana da ke?”Ya faɗa yana kallonta, kallonta Abeeha tayi sai ta ɗan yi murmushi tace mata “Dr. Sulaiman kenan!”Shima ta juya tace “Yayyena ne Addah jannah da Adda Abeeha”Murmushi yayi lallai Afeefah ta samu wurin zama idan har ta sake da ahalin haka sun zama tamkar jininta ya tabbata ba zata iya barin su ta dawo wurin ummanshi ba yadda ya ci buri.”Dr bamu natsu ba har yau bamu samu mun je mun sayi waya ba, bari na baka layina za ku iya dinga gaisawa kan ta samu nata”Godiya sossai yayiwa Abeehar, ta bashi contact ɗinta ya tafi da sauri ta juyi wurin Afeefah tana murmushi sai ta ga damuwa a kan fuskarta, dafa kafaɗarta tayi “Ya dai?””Adda wai Shima aure yayi last week saturday”Duk sun ji maganar wani iri amma sai suka dinga nuna mata babu komai kila ba rabonta bane ko kuma Allah ya kaddara za ta zama matarshi ta biyu bata san ta cewa Abeeha ba”A yaushe kenan? Aure last week Adda Abeeha kina tunanin ko shekara daya ne zata amince ya mata kishiya a kusa haka?” “Duk ba mu san tsarin Allah ba, mu yi Adu’a kawai duk abinda ya kaddara daidai ne”Ta gamsu amma har lokacin ranta na suya da abinda kawu ya aikata, kenan akwai ɗan sunnar da zai aureta a duniya kenan? Waye zai yarda ɗan shi ya auri irin ta matukar za su bincika asali da tushenta?Bata san Rayyan ya dawo ya wuce ba chan sai ga shi sun fito da Mammi, duk Miƙewa suka yi suna mata sannu tayi murmushi “Duk rigimar Saraki ne amma jikin nan bai kai zuwa Asibiti ba, Jannah ya jikin naki?””Da sauƙi Mammi, sannu Allah ya baki lafiya”Ta gyaɗa kai.Idanunta ta kai kan Afeefah dake ta murmushin yake “Afeefah kina lafiya? Na ga damuwa a fuskarki””Babu komai Mammi sannu da jiki”Kai ta gyaɗa ba wai don ta yarda ba suka nufi mota, ƙin shiga motar Rayyan tayi don wlh tsoron ko motsi take a gabanshi, motar Jannah ta tafi suka haɗu su uku suna hirarsu har gida.A babban parlor suka yi masauki don Rayyan ya riga su isa kuma ya shigar da Mammi ciki ko da ya fito a babban parlorn ya tsaya yana nuna su da yatsa”Ba ku parrots ba? To in ga watan ku ta shiga ciki tana damunta da surutu ko wata taje tana saka ta gaba da kukan banza ku ga abin da zai faru”Yana kai nan ya wuce abin shi basu motsa ba sai da ya ɓace Abeeha da Jannah suka tafa suna sheke wa da dariya, Afeefah na murmushi.”Mutum yayi ta muzurai kaman a filin daga yake”Jannah ta faɗa, Abeeha tace”Ai ke baki ganin komai tunda yanzu kin bar gidan nan da sauƙin ki”Jannah ta girgiza kai”Kema kin san babu wani sauƙi wlh sai dai in ban yi wani abin ba Ya Rayyan bai game shi ba ya je har gidan auren nawa ya zane ni tsaff”Ita dai Afeefah bata ce komai ba idanunshi kawai take gani, a hankali ta ɗan yi murmushi tana girgiza kai.Jannah bata tafi ba sai dare, sun sha hira sun ci sun sha, kuma sai da suka cika Mammin da surutu don yana fita daga gidan suka yi ɗakin suna bata labarin gargadinshi tana dariya ta dubi Afeefah “Afeefah ke ce me kukan banza kenan? Me aka yi miki za ki zo ki min kukan?””Ba ayi komai ba fa Mammi””Afeefah ki faɗa min damuwarki wlh ina hangar damuwa a tattare da ke”Kanta ta duƙar Mammi ita uwa ce, uwar ma ta wannan baudadden mutum ai dole ta san expression na kowa.Abeeha tace “Mammi Dr. Sulaiman yayi aure shima ashe”Mammi ta kalli Abeeha kan ta kalli Afeefah tace “Auren ne ya dame ki ɗiyata? Kin ga fa duk abin da Allah ya hanaka ba rabonka bane wanda kika ga kin samu shi ne rabon ki, in shaa Allahu za ki samu miji na nunawa sa’a”A hankali tace “Mammi ba auren shi bane damuwata””Toh menene Afeefah?””Mammi bana tunanin zan auru, Musulunci ya yarda a auri mace don kyaunta, dukiyarta ko nasabarta, sannan bincike a aure kaman dole ne a musulunci akwai dangi na ƙwarai da za su je bincike a kaina su yarda su bar ɗan su ya aureni? Mammi kin ji abinda su Sulaiman suka samu kawu suna yi a kan layi? Kin ji abinda aka fada musu a kaina daga shigar su kauyenmu?”Hawaye ne ya tsinke mata ta fashe da kuka tana jin ciwon Taɓon ta da bata tunani har Abada zai gogu.Jannah da Abeeha har sun fara tayata hawaye don idan ka ji yadda take maganan za ka san abin na mata ciwo kwarai da gaske..”Afeefah zo nan”Mammi ta ƙirata, Miƙewa tayi ta isa kusa da ita Mammin ta ɗora ta akan kafaɗarta tana shafa mata kai.”in shaa Allahu Afeefah sai kin auri mijin da kowa sai ya ji sha’awar kasancewa ke, nagartaccen namiji kuma mai tarin ilimi da baiwa na musamman, kawunki ko mutanen garinku ba su isa sun shafe abin da Allah ya rubuta ba, ko kin manta Allah da kanshi ya faɗa mana yana fitar da mummuna cikin kyakyawa ya kuma fitar da kyakyawa cikin mummuna? Ba fa a suffa ko sura ake magana ba ana magana ne akan hali da ɗabi’a. To ki sa a ranki mijin da Allah ya zaɓa miki yana nan kuma idan lokaci yayi za ki aure shi ba makawa kar ki wani damu kanki kin ji?”Kai ta gyaɗa cike da gamsuwa”Na gode Mammi””na ƙara ji sai na Buge bakin godiyar”Murmushi duk suka yi don da wasa tayi maganan.*****Hajiya Hussaina tun fa tana tunanin abin na Saleem da Sabrina wasa ne har ta fahimci da gaske ne, domin yau tana zaune a parlor Sabreenar ta sauƙo ta ɗan kalleta tace “Sannu Mommy”Bata jira ta amsa ba ta wuce kitchen ta samu Talatuwa na aiki, ta ce “Talatuwa me kike dafawa?””Tuwo ne da miyar egusi shi mutanen gidan suka ce a dafa musu””Toh bari ki ɗora min fried Rice da kaji iyayena za su zo ganin ɗakina ba zan tarbesu da tuwo ba””Amma S…””Kin yi abinda nace ko sai na bi ta kanki? Har kin isa ja da ni typical ‘yar aiki? Toh wallahi ki kiyaye ni”Sadiqa da ke shigowa ne tace “Haaa me ke faruwa da ihu haka?”Talatuwa ce ta mata bayani sadiqa ta kalleta sama da kasa “Amma ba ki da hankali yanzu su Gajen ne baƙi da har za’a dafa musu kaza da wani fried Rice? Dama shi suka saba ci a gida?”Sabreena ta riƙe baki tana kallonta na seconds kan tayi wani murmushi kawai ta juya fuuuuu ta fice.Mommy na nan zaune tana tunanin wannan lamarin da bata gane kanshi ba bare ƙasan shi ta ga wucewarta kamar iska, ba’a fi mintuna biyu ba sai Ga saleem rike da belt nashi na sojoji ko mommy bai kalla ba ya shiga kicin ya ya kuwa samu Sadiqa ya rufeta da dukar kawo wuka….

Back to top button