Uncategorized

Wace Ce Ita Chapter 40 Complete Novel

WACE CE ITA⁉️ (WHO IS SHE⁉️)

Unique Barakancy

                              FORTY📍

         Juyawa yayi ya shige work room dinshi dake nan parlourn, computers ne a zube kala kala sai wasu drawers a jere daga gefe, jan kujera daya yayi ya zauna sannan ya kunna system din, saida yayi rebooting system din kafin yayi connecting tracker a jiki, saita komai yayi sannan ya dauko phone number dake cikin wayar Umm daga contact list dinsa na kan computer, imputing yayi ya kurawa system din ido ganin abun yana processing…….

       “Shit!!!”….

Ya fada yana dukan table din bayan abun yasamasa invalid means wayar a kashe take kenan, hargitsa gashin kansa ya shigayi frustratedly kamar yayi kuka, chan kuma sai ya kunna computer dake gefen wannan, latest calls din da akayi a wayar ya fara bibiya ko Allah zesa ya samu wani information ta nan, yana dubawa yaga ankira wata number kusan so biyar kuma shine last call din da akayi a wayar, sauran calls din da akayi a wayar ya kunna yaga duk office discussion ne kuma da Umm ne, dawowa yayi kan last call din ya dauki number yayi transferring dinshi to the next computer dake gefe saboda ko wani computer akwai abunda akayi designing dinshi yayi, information din me number ya duba sai gashi ‘Ibrahim khaleel Ibrahim’ yayi appearing, dukan system din yayi ya dafe kansa cikin tsananin bacin rai yace;

     “I knew it! I knew it! Ni nasan shi kikabi, why are you so stupid bitch! Meyasa zaki bishi? Meyasa zakimin haka? Yanzu da kika bishi sai kuje kuyi aure da gaske? Inaaaaaaaa! Wallahi baku isa ba! Where are youuuuuuuuuu! I’ll make sure I slaughter him duk inda na ganku, kai dole in nemo ku ko ina kuka je, Why are you so senseless baby girlllllllllllllllllll!”…

Sai kuma ya fara hargitsa dakin yana neman wani encrypted tracker dinshi da ake tracking waya ko a kashe take, saidai sama da kasa ya nemeshi ya rasa, kamar yayi ihu haka yakeji ya dai daure ya cigaba da nema, yana cikin wannan dube duben hannunshi ya tabo wani flash, dauka yayi ya shiga jujjuyawa yana tinanin a ina ya samo shi, gashi it looks like bayanan sirri ne a ciki dan haka ake encoding dinshi, har ze cillar wata zuciyar tace yayi playing dinshi yaga menene a ciki, zirawa yayi a wani system ya dan nitsu yana duba abubuwan dake ciki, kunna first voice message din yayi yana sauraran abinda ake cewa…….. 

At first nitsuwa yayi yanason tantance muryar waye but it gets to a point daya sake baki yana kallon system din……

         Kamar yanda ta bukata haka khaleel ya siyo mata pack din codeine me dauke da 12 bottles a ciki, kamar wacce bata tabacin abinci ba haka ta bude kwalbar tanasha ta baka ta hanci, tass ta shanye kwalba daya ta sake bude wani ta kafa kai khaleel na zaune yayi tagumi yana kallonta kamar yayi kuka, ba abin ya hanata ba taji haushi, ko minti biyar baa kara ba bayan ta shanye kwalba biyu ta zube a kasa tana bacci, har ze dauketa ya kaita ciki ya fasa gudun karta tashi tace meyasa ya tabata, shida zasuyi aure very soon meye abun damuwa toh? He can wait ya tabata da hujja, murmushi yayi yana ayyana yanda zasuji dadin honeymoon a dubai…..

Yana zaune yana kallonta har bacci ya kwasheshi shima akan kujerar dayake dama a gajiye suke sosai….

Karfe sha biyun rana ta farka a gigice tana dafe da mararta, wani irin masifaffen ciwo taji mararta nayi mata itada bata taba ciwon mara ba sai gashi yau rana tsaka abu yazo mata, ko meyasa oho, biting lips dinta na kasa tayi jin yanda ciwon ke dada karuwa, har wani ji take kamar tayita birgima a kasa kota samu salama, a haka khaleel ya fito ya tarar da ita tana mutsu mutsu shi dama ya dade da tashi daga bacci, cikin tashin hankali yace;

     “Wifey menene?”…..

Hannunshi ta kamo ta daura akan cikinta a raunane tace;

     “Marata!”……..

Wani irin shock khaleel yaji dukda da hijab a jikinta amma ba karamin tasiri hakan ya masa ba, daurewa yayi ya janye hannunsa cikin muryar lallashi yace;

     “Sorry love, tashi muje asibiti pls”….

    “Bazan iya tashi ba”…..

    “In dauke ki?”……

Shiru tayi dan bataso ya dauketa amma kuma tanajin kamar kafafuwanta bazasu iya tafiya ba, bawa kanta kwarin gwiwa tayi ta mike a daddafe, taimaka mata yayi suka nufi hanyar fita daga dakin….. 

khaleel na rike da ita kamar wanda yake tsoron a kwace masa ita suka shigo asibitin, lokacin ta kara galabaita, hankalin khaleel in yayi dubu ya tashi sai sambatu yake besan meyake fada ba, shidai burinshi kawai kar wani abu yasa meta…….

      A hankali yake tafiya shi kadai kamar yana tsoron taka kasa, kana ganin yanayin tafiyarsa kasan irin na yan koyo ne, for the past two weeks da sanda yake takawa kuma sai an rikeshi amma yau yace abarshi ya gwada tafiya shi kadai, cikin ikon Allah sai gashi yana tafiyar kuwa, ji yayi kamar an hankadasa saura kadan ya fadi Doctor din dake biye dashi yayi saurin tarosa, kallon khaleel daya bige mutumin batareda yasani ba Doctorn yayi da niyar yi masa magana mutumin ya hanashi yace ya rabu dashi kamar matarsa ce batada lafiya…….

Suna zuwa suka samu sukaga Doctor, a take akamata allura aka kara mata ruwa…….

Khaleel ne ya tambayi Doctor abinda ke kawo ciwon mara dan shi ya tsorata da yanda ta dingayi lokaci daya……

      “It’s menstral cramp!”….,,

Doctorn ya bashi amsa……

      “Amma bata tabayi ba sai yanzu, why?”…..

    “Maybe she’s getting exposed!”…..

     “Bangane ba?”..,,,

     “Kai ba mijinta bane?”…..

     “Uhm mijintane”…..

    “Good, stop beating around the bush and do the main thing”….

Khaleel zeyi magana kenan wani ya shigo, kallon khaleel yayi yace;

      “Bawan Allah dazu ka bigemana paralysis patient da muka samu Allah ya farfadosa and you left without saying a sorry”……

     “Subhanallah wallahi ban sani ba duk na rude wifey bata da lafiya, dan Allah kaini gurinsa in basa hakuri”…..

Khaleel ya fada yanajin ba dadi a ransa kasancewarsa mutum me saukin kai………

         “Ba damuwa muje in kaika”….

Tashi yayi ya bishi dake fatima zainab na chan tana bacci a room din da aka kwantar da ita for the mean time…….

Saida suka gama gaisawa cikin mutunci sannan Doctorn yayiwa mutumin bayanin khaleel daya bigesa dazu, murmushi yayi yace ya gane shi ai, sai kawai Doctor ya fita ya basu guri,  hakuri khaleel ya shiga basa, yayi murmushi yace karya damu ai komai ya wuce…..

Sosai khaleel ya kwanta masa arai, yanayin nitsuwarsa da girmama mutane sai ya burgesa sosai, har ya dan jashi da hira…….

Cikeda ladabi khaleel ya russuna yace;

         “Ya karfin jiki? Allah ya kara sauki, Doctor yacemin ka kwana biyu a asibitin ma, Allah yasa kaffara ne”….

Murmushi yayi cikin jindadin yanda khaleel ke girmamasa yace;

        “Alhamdulillah da’na, jiki yayi sauki kam, cikin ikon Allah yau na taka da kaina”….

Cikin tausayawa khaleel yace;

      “Masha Allah, Allah ya kara afuwa”….

Dubansa yayi yace;

       “Ameen, Ina patient din? Ya jikin nata?”……

     “Da sauki”…..

    “Masha Allah, Allah ya kara lafiya, matarka ce?”…

Dan jimm khaleel yayi haka kawai ya samu kansa da kasa yiwa mutumin karya saboda kwarjininsa….

      “A’a”…..

    “Kanwarka ce?”……

    “Fiancé dita ce, ankusa aurenmu”…..

     “Masha Allah, Allah ya sanya alkhairi yasa ayi damu”……

     “Ameen ya Allah, nagode”….:

     “Amma zaa gayyaceni ko?”……

Ya tambaya cikin raha…..

Dan murmushi khaleel yayi yace;

      “Ai ba lallai anan zaayi ba”….

Dariya yayi irin tasu ta dattijawa yace;

     “In dai an gayyaceni ko ina ne zanzo”…..

    “Okay sir”…

   “Call me abby”….

   “Toh abby, bari inje in dubata”

    “Ka gaidata da’na”…..

    “Zataji nagode”….

Yana komawa ward din yaga ta tashi, garau ta tashi kamar wacce bata taba jin ciwon komai ba……..

Cikin kulawa da so da kauna ya kalleta yace;

      “Wifey how’re you feeling now?”…….

    “Better, ina kaje?”…..

   “I bulge into a patient dazu da muka shigo, shine naje basa hakuri”…..

    “Is that necessary?”…

   “It is wifey”…,

Tabe baki tayi tace masa;

     “Mu tafi gida”….

Murmushi yayi yace;

     “Okay love”…..

Shirye suke tsap sai tashin kamshi suke, sunyi kyau sosai kamar ka sace su a gudu, kana ganinsu kaga masoya da suke tashe dan ba karamin dacewa sukayi da juna ba, sanye take da blue black abaya ta yane kanta da mayafi daya kawata kyakkyawar fuskarta, duhun kayan sai ya kara fito da hasken fatarta da kyawunta, shi kuma ya sanya wani half jamfa blue black me kyau, yana sane yayi musu ordern kaya duka iri daya dan so yake suna matching outfits, hakan saiya bada wani style me ma’ana…… Suna tafe cikin farin ciki da nishadi irinta masoya masu so da kaunar junansu, duk inda sukabi kallonsu ake saboda dacewar da sukayi da juna, su ko basu san anayi ba saboda yanda sukejin kansu a cloud nine kamar su kadai ne a duniyar…..

       A Dubai Miracle Garden suka yada zango bayan sun gama zaga gari, sosai fresh air din garden din ya sasu ji kamar a wata duniyar suke…..

Ice cream din dake hannunsa ya shafa mata a fuska sannan ya kwaso shi ya lasa a baki yana fadin;

      “Sweet wifey!”….

     “Yes honey khal”…

Ta fada tana fari da ido fuskarta dauke da kyakkyawan murmushi….

Roses din dake hannunsa ya watsa mata a fuska yana murmushi yace;

    “That thing they say about finding your better half is completely true. I knew something was missing from me, but I didn’t know what until I met you. Ina sanki sosai my lovely wife!”…….

       “I couldn’t wish for a better life than the one I have right now, with you”…

Ta fada murmushi dauke akan fuskarta, batasan meyasa ba haka kawai takejin she wants to spend the rest of her life with khaleel….

     “Wowwww! Ya rabb you can take my life atleast my dream is fulfilled”…..

Sai kuma ya ruko hannunta murya cikin rauni yace;

     “Ni naki ne, you alone wifey! Na baki kaina kiyi duk yanda kika ga dama dani, command me instruct me I’ll be your loyal servant, ko zan rasa komai a duniya indai kina tare dani wallahi bazan damu ba”……

Dariya tayi cikin tsokana tace;

      “Ko momma da daddy?”…..

    “Yes kosu, kowa ma, your love is enough for me, dan Allah karki dena dariya, your dimples and gap teeth are so beautiful”…….

      “You’re so handsome khallllllllll”

Fatima zainab ta fada tana fashewa da dariya kamar wata mahaukaciya….

Saida khaleel ya dan tsorata amma ya daure yace;

      “I’m ugly compared to you darling”……..

     “Says who? You’re so lovely khal”….,

     “Thank you wifey! I know you don’t really share all of my passions, but that’s why I am even more thankful for the interest you show in them. You make me feel loved, and I hope that my love for you is enough to give back.”………

        “I love you! Let’s live here forever!”…..

Ta fada tanajin yanda shaukin sansa ke dibarta….

      “Really? Let’s make it proper then, will you marry?”……

Ya fada yana zaro wani gold ring daga cikin aljihunsa…….

       “Yessss”……

Ta bashi amsa tana mika masa hannunta, sa mata yayi sannan yayi hugging dinta, for the first time bata hanashi ba saima rungumeshi da tayi itama…

Haka suka cigaba da lovey dovey dinsu suna jinsu kamar sababbin masoyan tsuntsaye dake shawagi a duniya, karshe da soyayya taci karfinsu suka yanke shawarar suje a daura musu aure kawai yanda zasuji dadin yin honeymoon na gasken gaske……..

Enquiry sukayi making akayi directing dinsu zuwa wani babban masallaci gurin wani babban malami..

Ba bata lokaci sukaje, sauka me kyau aka musu kafin malamin yazo, yana zuwa ya bukaci su masa bayanin abinda ya kawosu….. Ba bata lokaci khaleel ya masa bayani, ya dai boyemasa guduwa sukayi, sai ya masa karya wai sun kusa aure amma yanzu bazasu iya jurewa ba suna kuma tsoron aikata zina shiyasa sukeso a daura musu aure…. 

Sosai ya yaba da hankalinsu da suka yanke wannan kyakkyawan shawarar akan suyi zaman haramci, mikewa yayi yace bari ya gayyato sauran mallamai sannan a kawo goro da duk wani abu daya dace na daurin aure…….

Yana fita khaleel ya daka tsallen murna ganin fah finally wifey zata zama tashi, murmushi tayi dan itama haka kawai ta samu kanta da san ayi auren..

Suna zaune mallamin ya dawo da duk wani abu daya dace sauran mallaman na biye dashi a baya, sadaki aka umarci khaleel daya fito dashi, ya kalleta yace;

       “Nawa kikeso wifey?”….

Murmushi tayi har cikin zuciyarta tace;

    “Ko nawane Allah yasa albarka”…..

Malam yace masha Allah,shiga hada hadan daurin aure akafara kamar yanda musulunci ya tanada,aka gayyato wa’yenda ke kusa da bakin masallaci da masu shaguna a kusa sannan aka dau………

A gafarceni team Deen😢

~Uniquebarakancy~

Back to top button