Hausa novels

Zakuna Biyar Page 31 By Princess Teema

Afkawa cikin hospital ɗin suka yi suka fara nemansa, Harleen ya ɗaga waya zai kira Aryan Faryan ya dakatar da shi, cike da tashin hankali ya ce. “Yah Aryan ba zai ɗauki kiran kowa ba, a yadda ya bar gida a fusace ba zai waiwayemu yanzu ba, ka kyalesa kawai, kuma Abba yana jin haushinsa, idan ya zo faɗa zasu sake yi, kasan halinsu ai, dik sai zuciyar balai, gara ka kyalesa, dan Abba zai ce sai Yah Aryan ya bashi hakuri, shi kuma kasan abin da ba za taɓa yi ba kenan”. Tarar numfashinsa Harleen yai da cewa. “Ban san me ainahin matsalar Abba da Yah Aryan ba, Abba fushi Yah Aryan zuciyar balai da kafiya, Abba ya ce sai Yah Aryan ya ce mashi sorry, shi kuma ya ce da ya ce sorry gwara a kashesa, kai wannan balai dayawa take, ni nama rasa me zan ce da Abba, ka dubi faɗar da suka yi kwanaki, sai da Yah Aryan ya fi 1 year bai tako gida ba, dan kawai Abba ya ce sai ya bashi hakuri, sai da Ammie ta dinga rokon Abba, kai ni wlh wani lokaci suna jefani cikin tashin hankali da kaɗawar zuciya”.Faryan ya ce. “Babu ranar sassautuwar al’amurra, dan ni banga ranar ba, ka yi duba da yadda Yah Aryan yake mana, ai exactly yadda Abba yake ne a lokacin da yake matashi kamar yadda Ammie ta faɗa mana, kaga kuwa gyaruwan wannan al’amari sai wani ikon ALLAH”.Harleen ya ce. “Ɗan nagada kuma ya fi ɗan na koya ba, ai Yah Aryan ma ya fi Abba zafin zuciya, ALLAH dai ya shirya mana shi, amma ni ina ganin idan ya yi aure zai canza”…… Ɗan zaro ido Faryan ya yi, sai kuma ya ɗan saki one side smiling kafin ya ce. “Kuma kana da gaskiya, Abba da yai aure ai ya canza, auren ya ɗan sassautasa, da a baya kafin ya yi aure ne ai Yah Aryan bai isa ya dinga mashi wasu abubuwan ba, amma yanzu Alhamllh Ammie ta sassauta mana zuciyar Abba”. Mood na Harleen ne ya ɗan canza, da kyar ya iya cewa. “Ammie ta canza Abba ko kuma Ummie?”…….. Shiru Faryan yai bai sake yin magana ba, da alama an taɓo chapter ɗin da baya so ko kuma chapter da tafi karfinsa. Cigaba da zarya suka yi a kofar da suke tinanin nan aka sanya Abba duba da cikan gomannin nurses da manyan likitoci a wajen, sai kai komo ake yi.Dik wani likita dake asibitin a yau yana wannan ɗakin, sun bar duba kowa, sun tashi daga kan kowa, dik sun gudo izuwa wajen Abba…….. Harleen yana tsaye a wajen sai ga wani babban Dr ya fito, cikin girmamawa ya ce. “Who’s Faryan and Harleen?”.Suna kallonsa suka amsa da su ne. “Sir Muhammad Khaiza’an need you inside”…….. Alhamdllh suka furta a tare kafin su wuce su ƙarisa ciki, Harleen ne ya fara wucewa, shi kuma Faryan ya rike hannun Dr game da cewa. “Dr a ina kasan Abba? And me yake damunsa? Ya aka yi ka dubasa ba tare da mun buɗe mashi file ba, ba CP note-B da kowa yake da shi a hospital ɗin nan, bamu zo da nasa ba saboda tashin hankali da muka shiga, mun manta a gida, amma kuka dubasa?”.Dr yana murmushi kafin ya ce. “Dik wanda ya kwana ya tashi a wannan hospital ɗin matsayinsa na ma’aikaci hakika yasan waye Muhammad Khaiza’an, ai shi ya wuci sai ya zo da note ɗinsa zamu duba shi, wajibi ne a kanmu mu duba shi, batu na file kuma ina ga tin bai haifeka ba yake da shi a nan”………. Cike da mamaki Faryan ya sake cewa. “Ya kake bani labari kamar Abba ne mamallakin CRYSTAL PALACE HOSPITAL?”. Girgiza kai Dr ya yi, cike da girmamawa irin wanda suke baiwa dik wanda ya haɗa jini da Muhammad Khaiza’an ya ce. “CRYSTAL PALACE HOSPITAL MALLAKIN CRYSTAL PALACE ne ai, Muhammad Khaiza’an ba shi bane mamallakin CP, but ka tambayesa yana da alaƙa mai karfin gaske da mamallkin wajen, ka yi magana da shi”.Kai kawai Faryan ya jinjina tare da wucewa ciki. A zaune a saman special bed na majinya suka isko Abba, ya farfaɗo, ai yadda suka yi tururowar aiki a kansan nan dole ma ya farfaɗo a take.A kusa da shi Faryan ya zauna yana faɗin. “Abba ya jiki?”…… Shiru bai amsa ba, yana tsoron buɗe baki, dan zai iya haɗiyar zuciya, saboda har yanzu yana kan dokin zuciya bai sauƙo ba. Sai da su Faryan suka shafe 30 mins a zaune bai iya ce masu komai ba, daga karshe yai masu alamar su mayar da shi gida. Harleen ne ya fito ya nemi babban Dr, ya ce ga buƙatar Abba, da sauri suka amsa da cewa dik abin da Abba yake so shi suke yi, dan umarninsa suke bi, dan haka dole a su sallame shi. Abin dik ya ɗaurewa su Harleen kai, amma basu yi gigin tambayar Abba komai a yanzu ba, dan sun san ko sun tambaya ba zasu samu amsa ba, yana kan dokin zuciya, sai ya huce.A taƙaice haka suka koma da shi gida, Abba tamkar zuciyarsa zata fashe, ya sha alwashin sai ya yi maganin Aryan a wannan karon, sau uku kenan yanzu Aryan yana mashi irin wannan tsiya, to daga na yau ba zai sake ba, aure kuma tamkar an yi an gama ko zai mutu!! Dan rantsuwa Abba yai da ALLAH ɗaya a wannan sati mai zuwa zai ɗaurawa Aryan auren nan, kuma ya ce wlh in dai Aryan ya musgunawa yarinyar mutane ko ya ɓata mata sai dai ya nemi wani uban ba dai shi ba!! Tashin sense! Lallai akwai balai!!.A ɓangaren shi kuwa Aryan, yana fita gidan Lion ya koma, ya yi mamakin ganin Lion baya gida, shi dai yasan a wannan lokacin Lion baya fita, mafiya yawan lokutan fitan IRON FIST daga 12 na dare ne zuwa 4 na asuba, kada ku manta su SSO ne, jami’an sirri ne, kunga kuwa ba fita zasu dinga yi kasafai suna zuwa office ba, sai muhimmin abu ya taso.Toilet ya wuce, ruwa mai sanyi sosai ya sakarwa kansa tin daga tsakiyar kai, yana son samun saukin halin da yake a ciki. Ya jima ruwan nan na zuba a kansa kafin ya fito sanye da bathrobe fari kal, a lokacin ya ɗan samu sauki a zuciyarsa. A wajen dispenser ɗinsu ya tsaya, sai da ya sha ruwa mai balain sanyi cup 4 sannan ya samu zuciyar ta ɗan yi sanyi. Gado ya haye ba tare da ya sanya kaya ba, daga shi sai bathrobe, dan wani irin jiri ne mai karfi take ɗibansa, yana son kiran Lion ya ji ina ya je a wannan lokaci, amma wani irin kasala da barci sun turnukesa, kafin ya farga barci ta ci karfinsa. Kafin wani ɗan lokaci ya yi barci. ————————🔥Cike da farinciki suka shiga class, class ɗin ya yi mugun haɗuwa, kowacce ɗaliba da chair and table ɗinta, ga AC, dispenser na ruwa, ga cups a jere cikin glass wa ɗalibai, komai tsab-tsab. Zama suka yi a chair dake kusa da juna, tana dai rungume da teddy ɗinta tana murmushi. Dik wani ɗalibi or ɗalibar da ta shigo cikin class ɗin sai ta kalli Seraphina and Rimsha ta sake kallo, yaran sun haɗu fiye da tunani, kowacce student sai ta fara neman su kulla kawance, har maza suka fara yi masu tururuwan zuwa wajensu kullah abota. Su kuwa basu kula kowa ba, suka zauna suna hira, dan warning ɗin daddy Aryan ya shiga kansu. A wannan lokaci Uncle ya shigo hannunsa rike da books da dama. A saman haɗaɗɗen table da aka tanadawa malami Uncle ya shirge littafan hannun nasa kafin ya ɗago ya kalli ɗalibai.Yana ɗagowa suka yi 4 eyes da Seraphina dake ta faman aikin kallonsa, tabbas ta gane da shi suka haɗu a shopping, kuma ta gane shi ne ya taɓa mata jaka ɗazun, idan ta cinka daidai shi ne ya bata teddyn nan dake hannunta. Kyafta mata idanunsa sau biyu yai ganin yadda ta tsare shi da kallo.Lokaci guda ta saki haɗaɗɗen murmushin da bata san ta sake ba, da sauri ta ɗaga teddyn hannunta ta rufe fuska tana cigaba da murmushi. Ƙayataccen murmushi shi ma ya saki tare da zaro book guda ɗaya daga cikin littafan nasa, ya fara rubutu a board da maker dake gefen board ɗin a ajiye.Topic ɗinsu ya rubuta da date kafin ya juyo da kallonsa a kan ɗaliban, dik sun fito da note books ɗinsu, ajiye dik wata shirme ya yi ya fara koyar dasu yadda yakamata, da yake su a kan abin da suke so babu abin da ha zasu iya ba, sai ga shi ya iya koyarwan, kuma bai taɓa yi ba fa, wannan ne karonsa na farko.Bayan ya gama sai ya ce ya basu 5 mins su yi copying na note zai goge board ɗin, da sauri suka fara rubutawa. Kewaye ya fara yi yana duba handwriting ɗinsu, sai yaba masu yake yi, ba laifi sun iya rubutu sosai. A daidai saitin chair ɗin Seraphina ya tsaya, zubawa rubutunta idanu ya yi, sosai ta iya rubutu wanda yasa ya dinga yaba mata. Juyawa yai zai tafi sai ya ajiye mata wani haɗaɗɗen chocolate a kusa da hannunta, ba tare da ya kalli face ɗinta ba ya wuce gaba, ya koma wajen table ɗinsa. A saman chair na malamai ya zauna kafin ya ɗago da kallonsa a kanta.While shi ita ma take kallo, irin kallon nan na Uncle chocolate kuma?. Kashe mata ido ɗaya ya yi wanda ya sanyata sakin murmushi, ta sunkuyar da kai ta cigaba da rubutunta, after ɗan lokaci sai ta ɗago ta saci kallonsa, dik in zata ɗago sai sun haɗa ido, dan ita ya tsare da kallo kawai babu ko kyaftawa. Kallonta ya ɗauke mashi hankali yasa ya wuce 5 mins da ya ɗeba masu, har 10 mins ta kai, sai da Rimsha ta ce. “Done sir”……. Da sauri ya zare kallonsa daga kan Seraphina tare da miƙewa tsaye, ya ce dik su ɗaga pen ɗinsu sama, zai goge board lokaci ya cika, in ma basu gama ba su suka sani.Tamkar zata yi kuka ta ce. “Please sir ka kara mana five mins, ban ƙarisa ba”…. Ya ALLAH, ai wani irin spark da zuciyansa ya yi bai san lokacin da ya amsa mata da okey ba. Murmushin da ta sakar mashi gabaɗaya ya yi melting heart ɗinsa, sai ya zauna saman chair yana sakin murmushin shi ma.Yaki sake ɗagowa ya kalleta dan ma kada ta sanya ya manta lokaci. After 5 mins ya ce kowa ya ɗaga pen ɗinsa sama, da sauri suka ɗaga pen ɗinsu alamar dik sun kammala. Share board ɗin ya yi kafin ya sake fara wani rubutun yana bayani. Bayan ya gama rubutu ya sake yi masu bayani da kyau, sannan ya ce 10 mins su yi copy a notebooks ɗinsu.Ya sake komawa saman chair ya zauna, kaman shi ne master na class ɗin nasu. A wannan karon babu wasa, a gaggauce suka yi copy suka kammala. Bayan sun gama ya ce da Seraphina ta zo ta goge board ɗin yana da ga zaune. Kawai so yake ta miƙe ya kara kallonta da kyau. A natse ta miƙe tazo ta ɗauki doster ta goge board ɗin, tin da ta miƙe ya tsareta da idanu har ta zo ta goge ta koma seat ɗinta. Shiru class ɗin yai, ya ce su karanta abin da ya koya masu zuwa break time, haka kuwa aka yi, dik suka buɗe littafansu suka fara karatu. Shi kuma ta ɗauko wayansa yana dubawa, amma fa Seraphina yake kallo ba wayar ba, dan wayar kam ya riketa ne kawai dan kada ƴan aji su zargi wani abin.A haka suka kasance har lokacin tashi break, ana buga break matasan dik suka fara fita waje. Kowa ya fita ya bar Rimsha da Seraphina. Miƙewa Rimsha ta yi tana faɗin bari ta ɗauko lunch box ɗinta, ita kuma Seraphina bag ɗinta ta ɗauko zata buɗe ta fito da kayan cimarta, dan bata zo da lunch box ba, ta ce wa daddy sai next week zata fara zuwa da shi, wai sai ta zo ta ga yanayin makarantar sai ta yanke shawarar zata dinga zuwa da abinci ne ko dai iya small chop ya isheta! Rimsha na fita zuwa in da aka tanada dan ajiye lunch box ya miƙe ya nufi Seraphina dake ƙoƙarin fito da kayan cimarta. A kan chair ɗin dake gaban nata ya zauna tare da miƙa hannu ya ɗauki chocolate da ya ajiye mata ɗazun, ya ɓare ledar, mai ƴaƴa ne, sai ya ciro ɗaya ya kai saitin ɗan bakinta yana faɗin. “Please don’t say no, don’t say anything”. Cikin muryar shagwaɓa ya ɗan faɗa, ashe Noor gadon shagwaɓa ya yi.Muryan nasa ya daki zuciyanta matuƙa, sai ta tsinci kanta da murmusawa kafin ya buɗe baki ya sanya mata a ciki, siririn murmushin da ta ƙara mashi kyau ya yi kafin ya ce. “You’re so cutie, jiya na kwana mafarkinki, can you be my girlfriend please?”. Ya kai karshe tare da ɗaukar chocolate ɗaya yasa a bakinsa……. Ai gabaɗaya ya goge mata hadda, ya ALLAH, ya haɗu, ta ko’ina, ga iya zallar madarar soyayya, ga salo mai ɗaukar hankali da shagwaɓa, kalamai masu narka zuciya, ya rabb.Miƙewa ya yi, bai jira amsarta ba, ya ɗan sunkuyo kanta kaɗan, tamkar zai yi kissing ɗinta, ta ɗago kai suka kurawa juna idanu, muryanta na rawa tana ɗan kyafta idanu ta ce. “Yeah, why not?”. Wani irin musulmin ajiyar zuciya ya sauke tare da sumbatar forehead ɗinta. “I love you”. Ya furta tare da miƙewa, ya juya ya nufi chair ɗinsa, bayansa ta bi da kallo tana jin wani irin daɗi a cikin ranta. A daidai lokacin Aisha da Rimsha suka shigo. Saita natsuwarta ta yi tare da karisa fito da small chop ɗinta. A chair ɗin da uncle ya miƙe a kai Aisha ta zauna, ita kuma Rimsha ta jawo chair ɗinta zuwa kusa da Seraphina, ta hau fito da kular abincinta, tin bata gama fitarwa ba kamshi ya buɗe ko’ina a cikin class ɗin, mandi rice ce da ya ji nama da kayan kamshi, sai drinks da Ammie ta haɗa mata, dama ta ce a sanya mata a babban kula saboda tare da Seraphina zasu ci.A natse suka fara cin abincin, Uncle ya zubawa ɗan bakinta idanu tana kara narka mashi zuciya, ya mace a kaunarta. Ita ma dik bayan minti ɗaya sai ta ɗago ya saci kallonsa, ya ALLAH, dik ya narka zuciyar baby cherry ɗin daddy.Bayan sun kammala cin abincin suka tattare komai, suka gyara komai, Rimsha na ɗagowa ta ga Uncle na kallonsu, cike da kunya ta ce. “Sorry Uncle bamu ce ka zo mu ci ba”……. One side smilling ya saki tare da cewa. “Thank you dear”. Dik kunya ya kamasu basu ce mashi ya zo su ci ba, a haka aka dawo class suka cigaba da karatu. 1:30 daidai suka tashi school, fitowa suka yi ita da Rimsha, Aisha dake SS1B ma ta fito, su kuma SS1A suke. A ƙasar wata bishiya dake kusa da gate na garden ɗin makarantar suka tsaya. Rimsha ta ce. “Zamu ga waye za’a riga zuwa ɗauka, nasan Uncle Faryan ɗina yana hanya”.Ɗago kai Seraphina ta yi da nufin ta yi magana unexpected idanunta suka sauƙa a kansa, yana tsaye a kofar offince da yakasance mallakinsa, ya rungume hannaye a kirji, kallonta kawai yake yi. Suna haɗa idanu ya sakar mata ƙayataccen murmushi, tsintar kanta ta yi da mayar mashi da martanin murmushin.Daidai lokacin motar Faryan ta shararo kan titin wajen, ya gaji da jiransu a parkin lot ya ce bari ya shigo cikin school ya dubata. Rimsha na hangosa ta yi gaggawar nufo motar, yana ganinta shi ma ya kashe tsayar da motar. Kama hannun Seraphina ta yi tare da cewa. “Zo mu je ki gaisa da uncle ɗina kuma husband to be ɗinki”…… Cike da shirirta ta ce. “Husband biyu zan haɗa kenan? Daddy and Uncle Faryan”. Suna nufarsa Rimsha ta ce. “A’a ba wani daddy, ki manta da daddyn nan naki please, ni dama bana son shi tin da kika ce ya cika faɗa da sanya dokoki, idan kika bari ya aureki wahala zaki sha, gara ki manta da shi ki so Uncle ɗina, Uncle Faryan zai baki soyayya, zai kula dake, zai maki dik abin da kike so, ga shi Uncle Faryan kyakkyawa kaman mugun Uncle Aryan ɗina, da uncle Aryan ba mugu bane, da yana kula mata da shi zan yi maki fatan ki aura, amma bakin mugu ne, baya kula mata, ALLAH ki so Uncle Faryan yana kama da uncle Aryan, ki shigo cikin zuri’armu, nasan kema zaki so zama cikin familynmu, idan kika auri Uncle Faryan kullum muna tare”. Ta kai karshen maganar daidai lokacin da suka isa wajen motar.Hakika kalaman Rimsha sun fara tasiri a ranta, musamman yadda ta ce idan ta auri Uncle Faryan zasu kasance a tare, tana son Rimsha sosai, tana son zama da ita, ko dan su kasance gida ɗaya zata auri Faryan, zasu zama ƴan uwan gaske.Sauƙe glass na motar Faryan yai, a natse ya ce. “Tauraruwa mai haske, kin kara kyau sosai”……. “Good afternoon Uncle Faryan”. Ta faɗa a ɗan shagwaɓe tana turo baki……. Idanunsa a kan nata eyes ɗin ya ce. “Afternoon my princess, ya school? Hope komai daidai?”.Kai ta gyaɗa mashi alamar e kafin ta ja baya, Rimsha ta shiga gidan gaba na motar tana murmushi……. “Uncle daddyn Seraphina bai zo ba, ko zamu yi dropping a gida?”. Cewar Rimsha.Da sauri ya ce why not, su shigo ya saukesu. Da sauri ita ma Rimsha ta fito ta koma baya, Aisha ta shiga gidan baya, Seraphina ta shigo gidan gaba. Tada motar ya yi suka nufi side ma benen su Seraphina, suna tafiya yana ta jan Seraphina da hira har suka isa. Yana parking Rimsha ta kalli Seraphina, a sanyayye ta ce. “My star lady, kada ki manta idan kika yarda da uncle Faryan zamu kasance tare na har abada, zaki shigo cikin zuriarmu, zamu je school tare, shopping tare, mu ci abinci tare, komai tare zamu dinga yi”. Sosai waɗan nan kalamai suka yi tasiri a zuciyarta, sai take jin ta aminta da Faryan, amma kuma shi Aryan kada ku manta soyayyar tin yarinta tai mashi, pure soyayya kenan, hakika idan zata so Faryan yanzu sai dai dan kalaman da Rimsha ke yi mata, shi kuma Aryan sonsa yana ƙasan zuciyanta ne wanda ba zata iya haɗa shi da kowa ba, amma yanzu yarinta yasa ba zata iya banbantawa ba, a halin yanzu kowanne a cikinsu zata iya cewa tana so, amma kowanne da dalilin son nasa except daddy Aryan da pure love da babu dalili take mashi.Zata so Uncle ne kawai dan irin kulawa da kuma nuna soyayya da yake mata, kunga su IRON FIST basu iya soyayya ba, daddy Aryan bai iya dik waɗan nan tausasawa ba, sai bada umarni ya iya, ko ta ce tana son abi sai dai ya kaita ta zaɓa, ya biya kuɗi, ba irin kyautar masoyan nan, ba kalamai irin na Uncle, shi dai umarni.Jinjina kai ta yi tare da cewa. “Zan yi tinani”. Tana faɗa ta buɗe kofar motar ta fita. Da sauri Faryan ya buɗe shi ma ya fito. Zata wuce ya ambaci sunanta, juyo da kallonta a kansa ta yi. Wucewa Aisha ta yi ta basu waje.Dawowa Seraph ta yi, a kusa da shi ta tsaya, tana kallon face ɗinsa ta ce. “Uncle gani”…… Ajiyar zuciya ya ɗan sauƙe kafin ya ce. “Nasan Rimsha ta faɗa maki ina sonki, haƙiƙa haka ne, ina sonki kuma ina fatan in ɗaukeki zuwa cikin zuriarmu, please kada ki ce a’a”. Shiru ta yi tana tinanin kalaman Madam dake ce mata dik wanda ya ganta sai ya zaci wata babba ce, sai a ɗauka 16 years take da shi, yanzu kowani namiji mai lafiya ya ganta sai ya sake ganinta, samari zasu yi tururuwan zuwa wajenta, dan haka ta kula sosai, a wannan lokacin komai zai iya faruwa da ita, wannan lokacin shi ne lokaci mafi haɗari ga rayuwar ɗiya mace, kada wasu kalaman soyayya su kwasheta ta faɗa cikin wani rayuwa, su nan turawa ne, ba ruwansu da sex after marriage, su before marriage suke yi, dik wani dokokin musulunci ba binsa suke yi ba, dan haka ta rike mutuncinta, kada ta kuskura ta bari wani namiji ya shiga gonar da ba nasa ba.Waɗan nan kalamai ma Madam sun ratsa zuciyarta, hakika yanzu ta fara gasgata Madam, dan yadda ta ga kowa in ya ganta ya ce yana so, lallai ba shakka haka ne, suna mata kallon babba ne, alhalin 13 years kawai take da shi. Juyawa ta yi ba tare da ta yi wa Faryan magana ba, ta wuce cikin room da zai sadata da elevator ɗinsu. Bayanta ya bi da kallo yana jin tamkar ya mallakawa kansa ita. Sai da ta ƙurewa ganinsa sannan ya shiga mota suka bar wajen.Tana shiga gida ita kuma room ɗinta ta wuce, wayarta ta ɗauko ta hau kiran number Aryan tin kafin ta cire uniform, tana shigowa gida shi ne a ranta. Ga mamakinta sai ta ji wayansa a kashe, ta ɗan shiga damuwa na jin wayar a kashe, amma ta ajiye wayar ta hau cire uniform.A lokacin shi kuwa yana can yana barcin huce wannan zazzafar zuciyar, kuma koda idanunsa biyu ma ba zai ɗauki kiranta ba kuma ba zai je ɗaukota ba sai dai ta dawo da kanta, dan yau har ita haushinta yake ji, dik ya tsani kowa, Abba ya kara rikita mana zuciya da kwakwalwarsa, yana son mai da mana da shi ruwa mun samu mun kwatosa daga dokokin IRON FIST na babu mata a tsarinsu da kyar!.Wanka ta yi, ta canza kaya, pjs ta sanya dan shan iska, ta fito parlo dan yin lunch, a nan ta isko Aisha zaune saman dinning, zama ta yi, masu aiki suka zuba mata abinci, sai suka fara ci a tare. ————————-🔥Tafiya take yi tana ƴan waige-waige, bata ji motsin kowa ba sai ji ta yi kanta ya bugu da bayan mutum. Da sauri ta ɗago da kallonta dan ganin wanene? Daidai lokacin shi ma ya juyo slowly dan ya ga waye ya bugesa.4 eyes suka yi da juna, wani irin yawu mai wuyar wucewa ta haɗiya, ya ALLAH, sai ta tina ranar da ta fara ganinsa a school ɗinsu, ranar da ta matsa dab da shi irin na yau, ita kaɗai tasan me ta gani wannan rana.Wani irin kallo mai kama da kina da hankali kuwa Leo ya wurga mata kafin ya ɗan ɗauke kansa yana ƙara ɗaure fuska. Ɗaure fuska tamau ita ma ta yi, a ɗan ƙule ta ce. “Nan wajen tsayuwa ne da zaka tsayawa mutane a hanya?”. Shiru babu alamar kamar ya jita, sai ma juyawa da ya yi, ya gyara hannayensa dake cikin aljihu, ya cigaba da kallon sabbin sojojin dake karɓar horon bar 1. Wani irin takaici ne ya turnuƙeta, a ƙule ta ce. “Nan cikin barrack muke ba wajen aiki ba, yanzu kai ba a sama dani kake ba, ɗiya ga GAT nike, dole ka mun biyayya”. Shiru babu alamar zai amsa mata, ganin hakan yasa ta ja dogon tsaki, a fusace ta juya ta nufi office na GAT, tana zuwa ta ce mashi tana son wannan Nirash ɗin ya kaita shopping yau, kuma idan ya kaita shi zai ɗauko kayan ya shigar mata cikin mota, idan ta dawo gida ma haka ya ɗauka ya shigar cikin gida.Cike da mamaki daddy ya tambayeta meyasa? Sai ta ce ai ya cika girman kai da jiji da kai, tana son ta sauƙe mashi. GAT ya gano, dama shi yasan halin Arya bata son raini, dik yadda aka yi Leo ya nuna mata ƙasƙanci ne, haka take, bata ɗaukar raini, bata ɗaukar walaƙanci.”Baby Nirash suka ƙarƙashin Mission ne, babu wani soja dake da iko da su kai tsaye, dole sai sun gama mission sun dawo cikin barrack da aiki shi ne nike da ikon sakasu komai, yanzu suna ƙarƙashin ministan tsaro da gwamnati ne, ba sojoji ne kamar sauran sojiji ba, saɓawa dokan soja ne sanyasu wani aiki, ko shi Noor da na bashi wannan aiki akwai dalili”. Ya ɓoye mata cewa saboda Noor ƙanin matarsa ce, sai ya fake da cewa akwai dalili.Sam bata ji daɗin waɗan nan kalamai ba, ta so daddy ya bata power ta wahalar da Leo, amma ba komai, zata gwada mashi ɗiyar GAT take.Ganin tana cikin ɓacin rai ne yasa GAT ya ce. “Baby yakamata ki koya mashi hankali ne da kanki ba sai daddy ya shigar maki ba, ki kwaci ƴanci da kanki, ba ke mace bace? Ki gwada mashi dik wani jiji da kan namiji a gaban mace ba komai bane”. Dan ya sanyaya mata rai ya faɗa. Ta ji daɗin kwarin gwiwar da ya bata, a fusace ta juya ta fita, ko kaɗan bai damu ba, dan shi yana son ya ga yaransa suna yin abin da suke so, kuma suna kwatawa kansu ƴanci.Tana fita suka ci karo da Manassa wacce ita ma bata jima da barin office na GAT ɗin ba, ta tsaya a gefen office ɗin tana chat da Vash, lokacin da Arya ta zo wucewa ranta a ɓace ne yasa bata ga Manassa ɗin ba, yanzu kuma daddy GAT ya kwantar mata da hankali, zuciyar ta ɗan yi sanyi. “Bloody daddy ya ce mu je sir Noor ya kaimu shopping, suna wajen parking lot”……. Haɗe rai Arya ta ƙara yi kafin ta wuce gaba Manassa ta rufa mata baya. A zaune suka isko su Noor suna jiransu, Arya na zuwa ta ce lallai sai V ta dawo gidan baya sun zauna su huɗu kamar yadda suka saba, ai Noor boy ɗin daddynsu ne, kuma driver ɗinsu, dan haka ba zata zauna a gidan gaba.Yana jinsu bai ce ko ƙala ba, ita kuwa V ta ce ba zata koma baya ba, Angelina ta ce Arya ta kyaleta, ita kuwa Arya ta ce ba zata kyaleta ɗin ba. Ta zo ya buɗe gidan gaba na motar zata figota waje kenan daga bayansu suka ji an ce. “Me hakan?”.Da sauri suka juya, ganin Zaynish yasa Arya haɗiyar yawu, dan idan akwai wanda take tsoro a cikin sojojin team ɗinsu su biyo bayan Leo and Zaysh. Kun san dik cikin sojojin nan ma Zaynish ya fita daban, baya shiga harkar kowa, baya da yawan magana, ga ɗan banzan zafin rai, ba shiyasa basa shiri da Leo ba, to dik basu da sauƙin kai, kowa ji yake shi sarki ne, kunga kuwa ai ba zaman lafiya.Sake V Arya ta yi, ta fi jin shakkar Zaynish ma sama da Leo, dan da suka je Mission tana ganin Leo yana hira da Noor, amma Zaysh kullum fuska a ɗaure, ba zaka taɓa ganin yana magana ba, kuma kullum kansa a ƙasa. Ja da baya ta yi, da sauri ta shiga gidan baya na motar Noor bai yi magana ba ya tada motar yana ɗagawa Zaysh hannu.Kun san me? Zaynish baya banbanta su Arya, dan bai taɓa ɗaga idanu ya masu kallon tsab mai kyau ba, yanzu bai san ma wace daga cikinsu yai wa magana ba, ya ɗauka Arya V ce, saboda Noor kuma yai maganar.To bari mu taƙaita wasu abubuwan. After some days. A yau takasance ranarsu ta karshe a AZURE, dan yau zasu tafi Mission nasu na uku kuma a arewacin AVARIS, Tamkar yadda aka shirya masu komai a farko ne, sai dai a wannan karon an basu ƙarin makamai sosai, ƙarin abinci da ƙarin magunguna, bugu da ƙari an basu ƙarin kayan sakawa, watau uniform.Leo ya buƙaci da a basu laptop ɗinau after nasu Arya, dan haka su ukun nan, Zaynish, Noor and Leo ɗin an basu laptop ɗai-ɗai, su Arya an basu postol gun. Sun shirya tsab, su kashe ko a kashesu, sun shiryawa mutuwa a kowani lokaci.A wannan tafiyar ma daddyn Noor ya zo yai masu sallama, Aryan and guru sun zo, amma Leo bai zo ba, Abba da kansa ya zo this time, ya zo kuma tare da Rimsha, Aryan ne ma ya ce Abba ya je da ita dan ta ga Vash, aure tsakaninsu ba fashi. In ƙara taƙaice maku dai a yau jirginsu ya ɗaga zuwa arewacin AVARIS, an umarcesu da kada su bar ɗan ta’adda ko guda ɗaya ya yi saura, su kama kowa, su ruguje komai nasu, sun kuwa karɓi umarni.A wannan karon Ummie ta zo, tana cikin damuwa sosai, saboda yanzu dangin mijin nata sun sake sakota a gaba ganin Zaynish an ɗauki lokaci bai dawo ba, har dukanta ranar amarya ta yi, shi kuwa Faisal yana can yana faman neman yadda zai yi ya rufe masu asiri, yana ta addu’ar ALLAH ya bashi sa’a ya samo gold ɗin nan. Baiwar ALLAH ko da ta zo bata faɗawa Zaysh abin dake faruwa ba, ta ɓoye, sai ta nuna mashi tana cikin matuƙar farinciki sosai, ya ji daɗin ganinta, ya rungumeta yana jin tamkar kada su rabu, amma ina, lokacin da Captain yai kira dole ya rabu da ita, yana ɗaga mata hannu suka shiga cikin jirgi, ita ma sai ɗaga mashi hannu take yi. Sai dai ta faɗa mashi cewa ta samu ciki amma cikin ya zube, bata faɗa mashi cewa amarya ce ta daketa har cikin ya fita ba, ta dai ce mashi ta samu ciki amma bai zauna ba. Ko Faisal ɗin bata faɗa mashi sanadin zubewar cikin ba, dama yana zuwa ganin gida dik karshen wata, tin kafin ya zo cikin ya zube, ya kira abokinsa likitan da ya taimaka masu har suka samu cikin, ta je asibitin yai mata wankin cikin, ko da karshen wata Faisal ɗin ya zo taki faɗa mashi ga dalilin zubewar ciki.Da ya tambayi dalili ta ce faɗuwa ta yi kan dutse, ya dinga faɗa, ya ce in ALLAH ya basu wani cikin ko tsinke bai yarda ta ɗaga ba, ya dinga faɗa har kamar zai doketa, abin da suke wahalar nema tsawon shekaru ALLAH ya kawo ta yi sakaci da shi har ya fita, ya faɗa ya nanata. Sai hakuri ta dinga bashi.Ita kuwa amarya ƴar banza, har yau cikin da take ta ikirarin tana da shi ɗin yaki bayyana, idan baku manta ba almost 8 to 9 months kenan yanzu, ba ciki ba labarinsa, ko ina cikin ya yi?……… 👀 Anya ma ba shiyasa ta zubarwa da Aunty Ummi nata cikin ba? Dan tasan ita bata da shi, jama’a ku duba mun wannan lamari fa!

Back to top button