Fatalwar Delu Part 9
🤡 FATALWAR DELU 🤡
Part 9
Kingboy Isah 👑
Short story
ZAMANI WRITERS ASSOCIATION
Na dube shi hade da cewa, “Bukar akwai babbar matsala fa, wallahi akwai matsala ya kamata mu sama waje muyi magana”. Yanayin yadda na ga ya cigaba da dariyar da yake mun na gane cewa bai dauki maganar tawa da muhimmanci ba. Don haka na ce, “Bukar laifin me kayi wa Fatalwar Delu take son kasheka?”. Kamar na sani rufe bakina yayi dai-dai da yin shirun Bukar dariyar ma ya daina, alamun tsoro duk ya bayyana a fuskarsa. “Nura me kake nufi laifin me nayi mata kuwa? To kai me ma ya kawo maganar fatalwa yanzu rana tsaka, dan Allah ka daina bana son irin wannan wasan”. Ajiyar zuciya nayi hade da cewa, “Ba wasa nake ba, jiya da dare na hadu da yar Fatalwa Delu mai suna Surayyah, kuma yanzu ma da ka ga na dawo ba kowa ne ya dawo da ni ba sai ita dai wannan fatalwar”. Ai ina gama fadin haka na ga tsoro ya sake mamaye fuskar Bukar, idan na lura da kyau ma ya fara karkarwa. Don haka na ce, “Bude daki na ajiye jakar nan, mu sama waje mu zauna dole muyi magana da kai a nemo mafita”. Ai kuwa ba musu ya bude dakin muka shiga.
Bayan mun zauna na ce masa, “Kamar yadda kaji na fada tabbas jiya ina kwance a waje wata budurwa ta zo ta tayar da ni ta ce kai ta zo nema na ce baka nan, don haka ta bukaci in rakata garinsu tana jin tsoro, sai da mukayi nisa na fahimci cewa fatalwa ce bayan ta bayyana mun suffarta ta zahiri. Sannan kuma zarginka ya tabbata wannan jaririn da muka daukko ranar nan tabbas ba mutum bane, na tabbata yana da alaka da wannan fatalwa. Kuma abinda ya faru yau ya nuna cewa da sa hannunsu a cikin mutuwar mashin da ake fuskanta a duk lokacin da na hau. Hakan na nufin fatalwar bata so na bar garin”. Bukar kamar zai zunduma ihu ya ce, “Ba ka gani ba, sai da na fada ma, na ja ma kunne tun randa ka zo garin nan ba’a fita da dare, ba’a fita amma kai ka nace wai kai ga ka jarumi ko? To yanzu wa gari ya waya, gashi kana neman daukkowa kanka masifar da ta fi karfinka fatalwa fa”. Na ce, “Hmm Bukar kenan ai kai baka san masifar da take bibiyarka ba ne, duk da dai nima na fada cikin amma ina tunanin ka fini shiga hatsari, domin kuwa fatalwar mai suna Surayyah a jiya ta tabbatar min da cewa sai ta kasheka hankalinta zai kwanta”.
Ai ina fadin haka na ga Bukar ya mike tsaye zumbur! Lokaci guda zufa ta fara jikasa, yana tsaye cikin rudani ya kasa yi mun magana sai kallona yake, Na gyada kai hade da cewa, “Duk abinda ka ji na fada gaskiya ne, na tambayeta laifin me kayi mata amma ta ce na tambayeka”. Nan take sai na ga Bukar ya zube kasa a inda yake tsaye, jikinsa a matukar sanyaye, kamar zaiyi kuka ya fara magana, “Shikenan ta faru ta kare, zargina ya tabbata itace wallahi ita ta kashesu duka a lissafina saura ni kadai”. Na dubeshi da kyau hade da cewa, “Malam kayi mun bayani yadda zan fahimta, ita wa kuma su wa ta kashe sannan me kukayi mata da naji kana cewa saura kai kadai?”. Ya lumfasa fuskarsa cike da nadama kana ya fara da cewa, “Shekaru biyar baya da suka wuce, wata mata ta zo garin nan ita da yaranta biyu, daya na goye yarinyar kuma ta dan fara girma. Dukkansu farare ne kamar buzaye ko larabawa, sun shigo garin ba tare da ansan daga inda suke ba, kuma suma babu wanda suka sani a garin nan. Don haka suke bi gida-gida suna bara, a kalla sun kai sati biyu a garin. Duk da mutane da yara suna tsoronsu saboda kyawonsu yayi yawa zargi ya shiga zukatan mutane, amma duk da haka mutane suna taimaka musu da abinda zasu ci”.
“A karon farko mutane sun nemi mai garin ya sa a koreta, amma mai gari ya bawa jama’a hakuri, a cewarsa kamata yayi a kirawota a gaban mutane a tambayeta daga ina take kuma me ta zo yi garin, haka kuwa akayi, bayan an gayyaceta sai ta bayyana sunanta Delu yarta Surayyah da kaninta Iman. Ta dai ce bata san daga ina ta fito ba, kuma bata san me ya faru da ita ba kawai ta tsinci kanta a cikin daji ne tana tafiya har Allah ya kawota garin nan. Jin hakan yasa mutane duk aka tausaya mata, shiyasa ma aka barta a garin bayan ta nemi alfarmar a barta ta zauna na dan lokaci ta huta kafin ta kara gaba”. Bukar yayi ajiyar zuciya kafin ya dora da cewa, “To a kwana a tashi kwatsam ranar nan taje wani gida an bata sadakar fura ita da yaranta, suna tsakar sha a kofar gidan tun kafin su bar wajen yarinyar da ta kai musu furar ta fara rashin lafiya washe gari ta mutu. Wannan ya wuce ba’a kawo komai a rai ba, ba’a fi sati ba irin haka ta sake faruwa nan ma akayi katari tana kofar gidan, don haka mutane suka ce Delu mayya ce ita da ‘ya’yanta sune suke kashe mutane. Kasan mu nan kauye muna ba abinda ya shafi maita da asiri mahimmanci, don haka kowa ya yarda da hakan. Shiyasa aka kamo Delu da yaranta aka yi musu dan banzan duka har suka mutu su dukan. Sannan aka sa wuta aka kona su”.
Ko da jin haka bansan lokacin da na ce, “Tirkash ba”. Kana na ce, “To amma ni banji inda laifinka yafi na wani ba, tunda dai duka mutanen garin nan kuka aikata kisan”. Bukar ya lumfasa kana ya ce, “Eh duka garin suka goyi bayan kisan, amma matasa bakwai aka wakilta domin aiwatar da dukan, ciki kuwa harda ni. Yanzu haka maganar da nake ma duk sauran mutum shidan su mutu ni kadai nayi saura. Duk da kasancewar bayan faruwar hakan da sati guda garinmu ya kauracewa zaman lafiya da dare amma bayan mace-macen abokan nan nawa da mukayi kisan tare na yi zargin cewa fatalwar Delu tafi fushi da mu a kan sauran jama’ar garin, domin a cikin jama’ar gari ko mutum daya ba’a kashe ba, yawanci sai dai aita marin mutum ko aita razana mutum amma ba’a kashe wani ba”. Na ja doguwar ajiyar zuciya a karo na barkai, a zuciya na ce ah lalai Bukar ba a banza tsoronka yayi yawa ba ashe kasan abinda ka aikata. A zahiri kuwa shiru nayi ina ta sake-saken zuci.
Zuwa can na dago na kallesa, hade da cewa “Tabbas kun aikata kuskure ba karami ba, tunda a labarin da ka bani baku da tabbacin su Delun mayu ne amma kuka kashesu. Domin shi Allah ai ba ruwansa duk lokacin da ya so daukar ran mutum ba sai ya jira shawarar wani ba. Watakil kawai akasi aka samu na kamuwar rashin lafiyar wanda suka mutun yayin da su Delun suke wajen”. Bukar da hankalinsa idan ya kai dubu a tashe yake ya ce “Yanzu shikenan mutuwa zanyi ko auren fari banyi ba kenan? Innalillahi tabbas na cuci kaina”. Kallonsa nayi tuni har ya fara kwalla, nadama cike a kan fuskarsa. Na dan matso kadan na dafa kafadarsa hade da cewa, “Ba zaka mutu ba abokina jiya bamu rabu da fatalwar nan ba sai da na nemo mafita wacce zata tseratar da rayuwarka su yafe ma”. Ai da sauri na ji ya ce, “Dan Allah wace mafita ce, ko har sun yafe mun fada mun idan wani abu suke so nayi ko miye zanyi. Ni dama tun wancan lokacin ko kaza ban sake kashewa ba yanzu haka nake rayuwata ba ruwana da kowa”. Na ce, “Fatalwa Surayyah ta ce, zata yafe maka idan har muka je wajensu ka basu hakuri a daren yau misalin karfe daya”.
Gani nayi Bukar ya bige hannuna da na dafa kafadarsa da shi, yana yi mun wani irin kallo da na kasa gano ma’anarsa sai da naji yana fadin. “Aa Nura ka ce kawai baka kaunata, so kake na mutu kawai. Dan Allah ka fada min kaima laifin me nayi maka da kake son ganin bayana? Ai sai in baka hakuri ba sai ka kirkiri hanyar da zaka kasheni da Fatalwa ba”. Na kalleshi sosai cikin kara tabbatar da abinda na fada na ce, “Wallahi da gaske nake tayi alkawarin idan har kaje ka basu hakuri zasu yafe ma. Kuma ba kai kadai ba ta ce zasu bar garin baki daya kaga kenan garinku zai sama zaman lafiya ta dalilinka”. Bukar ya doka tsaki hade da cewa, “Garin ya dade bai dawwama a cikin yaki ba, in dai sai na kai kaina wajen fatalwa. Zuwa wajensu karfe dayan dare ai dai-dai yake da kisan kai”. Na ce, “Dan Allah ka fahimce ni mana abokina, fatalwar nan ba zata cutar da mu ba, domin kuwa tace tana sona ko dazun ma shine dalilin da yasa ta dawo dani garin nan saboda tana sona, kaga kenan ba zata cutar da ni ba”. Wani irin kallon sha tara na ga Bukar yana yi min, kafin daga bisani ya ce, “Ah to ashe ba ni kadai nake cikin bala’i ba so fa kake cewa? Anya kuwa ma Nura hankalinka daya, jaririn fatalwar nan da ka daukko ya bace a dakin nan ko dai jikinka ya shiga ya taba ma kwakwalwa ne?”. Nayi dan murmushi hade da cewa, “Malam nima fa ba jin dadi nayi da tace tana so na ba, don yanzu so nake ma idan munje anjima da dare ka tayani mu bata hakuri ta janye batun so din nan”. Bukar ya tashi yayi waje yana fadin, “Ka cire idan muka je, ka sa idan kaje don wallahi idan ka ganni a lahira to kaini akayi ba ni na kai kaina ba”. Yana fadar haka ya fuce daga shagon ya barni nan……….
😃 Ashe ba kadan din da kuke cewa na rubuta ba nayi