Uncategorized

Abubuwan Dake Kawo Cutar Basir Da Kuma Maganinsa A Likitance

ABUBUWAN DAKE KAWO BASIR DA KUMA MAGANINSA A LIKITANCE.

Wannan cuta ce da take faruwa a  dubura.

Mutane suna yawan danganta basir da wasu cututtukan wanda azahiri bahaka bane.

Anan zamuyi takaitaccen bayani akan basir tare da alamominsa yadda mutun inyana dasu toh bamakawa yana dauke da ita.

 A duniya kusan hudu na mutanen duniya suna fama da wannan cutar. A Nigeria kusan kaso hamsin zuwa tamanin nayan kasar suna kamuwa da ita aduk shekara,wanda hakan yana karuwa da yawan shekarun mutum.

Karanta : Mane ne Ciwon Sanyi Da Hanyoyin Magance Shi Cikin Sauƙi

Meke kawo Basir?

 Babu wani taka mai-mai abinda yake kawo basir saidai ana alakanta shi da abubuwa kamar:

1. Rashin yin bayan gida ko yawan rike bayan gida.

2. Daukan ciki.

3. Masu Shekaru sama da 45.

4. Cin abinci mara sinadarin “fibre”

5. Yawan yinkuri

6. Kiba 

7. Tiyata aciki ko dibira

8. Yawan daukan abu mai nauyi.

9. Masu fama da cututtukan huhu

Alamomin Basir

Mafi shahara daga ciki sun hada da:

1. Zazzagowar dubura.

2. Fitar jinni ta dubura.

3. Zafin dubura.

5. Kai-kayin dubura.

6. Rashin samun gamsasshen saduwa.

7. Yin kashi mai tauri ko yawaan kashi.

8. Yakan fito wajen dubura alokacin dayakai wani matakin.

Maganin Basir

Alokacin da kaji alamomi na basir Yana da kyau da kaje asibiti adubaka a asibiti akwai bincike da zaayi kamar haka kafin afara magani.

1. hotunan dubura (colonoscopy, proctoscopy).

2. Gwajin swab mcs 

3. Gwajin jini (BP)

Magani yadanganta da girman basir din ko matakin sa kamar haka:

– Akwai basir mara tsiro wanda baya fitowa wajen dubura.

– Akwai mai tsiro wanda yake fitowa amma yana komawa dakansa basai ammayar dashi ba

– Akwai wanda inyafito sai an mayar da shi watoh baya komawa da Kansa

– Akwai Wanda inyafito baya komawa Koda kuwa an mayar da shi

Daga mataki na daya zuwa na uku :

Maganin mataki na daya zuwa na uku sun hada da:

1. magunguna na kwaya: 

Ana Shan magunguna irinsu 

– Daplon

– Nitroglycerin

– Antibiotics

– Maganin kashe zafi

– Maganin saka kashi laushi

 

Sannan zaka iya gwada magani na shafawa Wanda mutane dayawa sunyi amfani dasu Kuma sun gamsu,Amma ba a tabbatar da ingancinsu ba a likitance. Wadannan sune:

– Dictami haemorrhoid cream

– Anusol suppositories 

2. Shiga ruwan gishiri:

Shiga cikin ruwan gishiri na akullun da safe da yamma na tàimakawa kwarai wajen warkar da basir.zaasamu ruwa mai Dan dumi kadan ba sosai ba sai adebo gishiri cikin hannu azuba acikin ruwan dumin sannan arunka shiga ciki.

idan magani na kwaya da shiga ruwan gishi baiyi aiki ba ana iyayin wadannan abubuwa a asibiti:

Rubber Band ligation

Laser theraphy

Electrocoagulation theraphy

Cryosurgery

Tiyata

 Ana yin tiyata ne (stepple hemorrhoidectomy) Idan:

1. Wadancan abubuwan da muka lissafo basuyiwa mara lafiya amfani ba,ma’ana Basu warkar masa da basir din ba.

2. Idan basir din yakai mataki na hudu. 

Shawarwari

1. Da zarar mutun yaji kashi toh yana da kyau mutun yaje yayishi rike kashi kan iya janyo wannan cuta ta basir.

2. Yawan cin abinci masu dauke da sinadir ‘fiber’ kamar alkama, wake, spageti, dankali, biredi, lemon zagi, piya, ayaba, tuffa, karas da sauransu.

3. Yawan shan ruwa akai akai yana taimakawa matuka .

4. Rage daukan abubuwa masu nauyi.

5. ziyarar likita akai akai da bin kaidojin da ya gindaya.

Back to top button