Uncategorized

Wace Ce Ita Chapter 12 Complete Novel

WACE CE ITA⁉️ (WHO IS SHE⁉️)

Unique Barakancy 

    TWELVE📍

             Wata muguwar dariya mama ta sheka ganin gidan sai ci yake da wuta,gashi ba kowa a gidan dama,me gadi kuma ya gudu…. Fadan irin farincikin da mama take ciki bata baki ne,sai yau taji hankalinta ya kwanta tin bayan shekara shida da suka wuce,ga alhaji nan ya zama sai yanda tayi dashi ga wannan munafukar ta kone mururus, itako meya rage mata a rayuwa banda taci duniyar ta da tsinke?…… Tafin murna tashigayi fuskarta dauke da annuri sosai……. 

        Driving yake a haukace kamar ze tashi sama waya rike a hannunsa,tinda me gadi ya kirasa ya fadamasa kudirin mama be kara samun nitsuwa ba,kiran duniya yayiwa fatima zainab amma bata dagaba gashi kuma waya na ringing,rashin dagawarta ya bala’in tada masa da hankali,gashi yayi nisa sosai da gida….. A 360 yake driving amma ji yake kamar baya tafiya,a yau da yanada dama daya zama tsuntsu ya tashi ko ze samu ya isa gida da wuri,momma dama bata gida tayi tafiya,daddy ko yana office,megadi ya kuma tabbatarmasa da Fatima zainab na ciki a yayinda mama ke kokarin aiwatar da kudirinta… Number daddy ya soma kira saidai sam yaki dagawa kamar yanda ya saba masa a yan kwanakinnan tun bayan dawowar mama,changa akalar kiran yayi zuwa number yayansa dukda baya kasar….. Khaleel na dagawa abdul ya shiga masa bayanin da bala megadi ya masa,ba karamin tashin hankali khaleel ya shigaba dan yana tsaye saida ya zube a kasa,umartar abdul yayi da yayi saurin karasawa while shima ze cigaba da trying numberta,tabbas in wani abu ya samu fatima zainab yasan rayuwarsa tazo karshe dan baze iya rayuwa ba itaba…… 

Haka abdul ya cigaba da driving still yana kiranta a waya…. Kamar a mafarki yaji ta daga wayar,murya na rawa yace

     “Anty anty ki bar part dinki yanzu,mama ta siyo petrol wai zata konaki,megadi ne ya kirani ya fadamin”…… 

Shiru tayi batace komai ba,jin tayi shiru hankalin abdul ya kara tashi,cikin muryar wanda ke shirin kuka ya kuma cewa

         “Tell me you’re fine sis,your silence is sucking me up,dan Allah ki bar part dinki ASAP”..,,,,

Numfasawa tayi tana mamakin dabbancin mama,yanzu saita konata?.. A hankali cikin muryar bacci tace

       “Hey I’m fine karka damu”……

      “Dan Allah kina ina toh?” Abdul ya tambaya still hankalinsa be kwanta ba

“I’m safe,just relax okay?”…….. Ta fada tana kashe wayar,switching off wayar tayi gabadaya sannan ta cigaba da baccinta dan mama bata isa ta katse baccinta saboda itaba,saita tashi sannan zataji da ita……

A nitse abdul ya cigaba da driving dan yasan tinda tace she’s fine to hakanne,shidai ya rasa me fatima zainab ta tsarewa mama da ta tsaneta haka…. Khaleel ya kira ya fadamasa ya sameta a waya,still hankalin khaleel be kwantaba dan already yana airport ze tawo…… 

   

       Harya katse kiran sai wani tinani ya fado masa,a take ya sake dialing number sameer

    “Sam kana ina yanzu haka?”… 

  “Ina gidanku boss,mom nakeso nayi sallama da ita na tafi”.. Sameer ya fada da ladabi,irin ance zaa shigarmishi game dinnan

“Da yanzu ban kiraba haka zakamin fuck up ka gayawa mom munyi waya ko?”….

  “Oh kar in fadamata kenan?”…

  “Don’t even dare me!,ka fadamata kawai you’ll keep on finding me,in ka ganni kuma you’ll let her know,bansan hankalinta ya tashi”…. Deen ya fada da kakkausar murya gudun kar sameer ya bata masa plan…..

  “Angama boss,your wish is my command”.. Sameer ya fada yana dariya…. 

“Kaidai kasani,nasan duk akan mace kake wannan abun,kadai ji kunya wallahi”… 

   “Naji din yanzu dai kafara bani tactics dan Allah”..

Smirking Deen yayi yace “Step one kaje ka bawa yaranchan hakuri,ka nuna masa ka hakura da yarinyar, kanaso kuma ku cigaba da mu’amalarku normal,bakaso mace ta shiga tsakaninku,If you’re done let me know!”…….

   “Good wlh shiyasa nake sanka boss cuz you’re very smart,maganannan taka ta bani wani highlight wallahi”.,,,. 

    “Kaidai ka sani mayen mata kawai”… Deen na fadin haka ya kashe wayar……

Sallama yayiwa mom ya fita da sauri gudin kar khadija ta fito tace sai sunyi hira dan a halin da yake ciki yanzu baya bukatar hakan….. Har ya nufi gate ya fara tinanin to ina zashi yanzu,yaso haduwa da Deen amma Deen ya nuna masa haduwarsu hadarine,kuma yasan tinda ya fadi hakan to tabbas haduwar tasu ba karamin matsala zata haifar ba,garden ya nufa ya zauna ya shiga tinanin he has to make a move shi karan kansa,yana bukatar taimakon Deen amma dole shima yayi taking action from his side,first thing kuma is knowing WHO IS SHE? “Yes yes!” Ya fada tuno da step one din da Deen ya basa,this is why they all believe that Deen is a very smart person… Be gayamasa gaskiyar lamarin ba sai gashi ya basa shawara daidai da ainiyin lamarin.. Shi yanzu besan inda yarinyar take ba,ta hanyar khaleel ne kawai ze iya sani,gashi sunyi baran baran,yasan kuma hankalin khaleel yanzu a kwance yake ganin sameer besan komai a kan yarinyar ba,yanzu idan yabi shawarar Deen ya basa hakuri ya nuna masa komai ya wuce,he doesn’t mean duk abunda ya fada,sannan shi ya fasa game din dan be kamata ba,ze nunawa khaleel he’s so remorseful harma ya sabanta abokantakarsu da shakuwarsu ta yanda khaleel ze yadda dashi har ya masa dabara yasan WACECE ITA har ya samu ya yada mufarshi,meaning zeyi nashi game din ta karkashin kasa ne,Deen ya shiga shiwa albarka a ransa da wannan kyakkyawar shawara daya basa…….

Kamar daga sama yaji alamun ana waya daga chan gefensa,bega fuskar meshi ba kasancewar me wayan ya juya baya,sai ya kasa tantance waye dan da alama meshi ba dan gidan bane,jin sunan Deen da aka kira yasashi bude kunne sosai dayake gurin is so silent shiyasa yake iya jin abinda ake cewa,a hankali yaji an kara cewa….

    “Nan da kwana uku nakeso ku kashemin Deen!”…. A gigice sameer ya mike jin wani abu kamar saukar aradu,wai zaa kashe Deen nan da kwana uku? Toh waye wannan dayake farautar rayuwar Deen haka? Kodai shiyasa Deen yace masa haduwarsu hadari ne yanzu? Innalillahi wa inna ilaihi raji’un dole yayi wani abu…. Mikewa yayi da sauri ya nufi inda meyin wayar yake tsaye,gashi ya kasa gane muryar waye,yasan dai koma waye yanada alaka dasu Deen tinda gashi a gidan…. Da sauri meyin wayar ya bar wajan jin kamar ana nufar inda yake…….

       Sai da mama ta tabbatar komai na building din ya cinye sannan ta kira fire extinguishers sukazo suka kashe wutar ganin makota sunfara kawo agaji gudun kar a zargeta,da aka tambaya koda mutum a ciki mama tace babu incase in fatima zainab bata mutu ba ta karasa mutuwa a ciki…….

  

      Sai la’asar ta farka,addu’ar tashi daga bacci tayi sannan ta fada wanka,shiryawa tayi cikin fitted gown kasancewar tana da kaya a part din. Bacci takeji sosai kuma ka’idarta in tanajin bacci batacika magana ba, hakanne yasa ko kallon mama batayi ba data shigo,haka kawai taji bazata iya baccin a part dinta ba,harta kwanta ta mike ta fita lokacin ana sallar azahar… Part din momman su khaleel ta tafi,tashiga bedroom dinta tayi baccin,ita bata masan momma batanan ba tinda taga part din a bude…. Koda ta fito bata tarar da kowa ba dayake lokacin sallah ake so bawanda yaga fitarta daga part dinta…. A cikin bacci taji kamar wayarta na ringing,sharewa tayi sai da taga calls din yayi yawa sannan ta daga,nan abdul yake cemata ta bar part dinta hankalinsa duk a tashe wai  konata zaayi,jin abun tayi kamar a film amma fa hakan be hanata cigaba da baccinta ba…

Da yake bata sallah,karasa shiryawa tayi sannan ta fita daga dakin ko dankwali bata daura ba,jelar gashinta sai lilo yake a bayanta,ta fita ta nufi part dinta,mamaki ne ya kamata ganin lallai maganar abdul gaskiya ne,yanzu inda tana ciki shikenan saidai ta kone murus haka? Lallai mama bata da hankali,kuma yau saita nuna mata tinda ta kasa konata,toh ita bari ta konata…..

Komawa part din momma tayi tana tinanin shigar jikinta bebi da tsarin abinda zatayi ba,wani crazy three quarter ta dauko ta saka ta dora da wata armless top sannan ta fita ta nufi part din mama…….

Banko kofar tayi ko sallama babu,husna da imaan ne zaune a hadadden parlourn mama suna kallo… Binta sukayi da kallo ganin irin shigar dake jikinta kamar zata club,matar da kullum a hijabi take,mamaki suka dingayi wai dama haka take? Tabdi jan! Lallai anyi halitta anan,sufa sun dauka wani abun take boyewa shiyasa takesa hijab ko yaushe,kullum sai sunyi da ita suna cewa kyawun fuska kawai gareta shiyasa take abunda taga dama… Imaan ce ta kasa shiru dan batasan lokacin da tace 

   “Kutumar uba! Anty dama haka kike,ya khaleel idan ya ganki a haka ai sai ya suma”……. 

Wani wawan mari ta dauke imaan dashi tace

    “Dan uwarki ni sa’ar kice da zaki tanka?,ina munafukar uwartaku take?”…….. 

Husna ce taji abun ya daketa ganin cin zarafin yayi yawa,ace a gaban idansu zata dinga zagar musu mahaifiyar su,kallon fatima zainab tayi tace 

    “Mudai mamanmu ba munafuka ba……

Bata karasaba taji saukar wani naushi a baki,take bakin ya fara zub da jini

   “Dan kaza kazanku zaku gayamin inda mahaukaciyar uwarku take ko saina muku jinajina,yan iska kawai wa’yanda sukasha nonon mahaukaciya”…. Ta fada a hassale

Murya na rawa husna da tinda taji mari take ganin wasu stars na zagayeta tace

    “Tatt tana dddaki” 

Batace komai ba ta nufi bedroom din mama…

Da karfi ta daki kofar,mama dake baccin nishadi ta tashi a firgice dan ta dauka yan fashi ne….. Dirowa kasa tayi tana kokarin shigewa karkashin gado,ganin ta kasa shigewa dayake katuwace yasa ta futo tana rarrafe,a razane take fadin

“Dan Allah dan annabi kuyi hakuri,wallahi alhaji baya…..

Fatima zainab bata bari ta karasa ba ta dauketa da wani mugun mari….. A take wani mugun fitsari ya zubowa mama dan harga Allah tayi tinanin yan fashine,rufe ido tayi ta kuma cewa

    “Wallahi kome kukeso zan baku amma dan Allah karku kasheni,ku tausayamin”…….

Wani wawan marin ta sake saukewa mama ganin kamar haryanzu bata hayyacinta….. ai saida jin mama ya dauke na wucin gadi jin saukar wani mahaukacin  marin da tinda tazo duniya baataba mata irinsa ba,take ta fashe da wani irin kuka mara dadin sauraro,irin dai kukannan na gardawa…. Sai a lokacin ta dago tana kallan fatima zainab…. Sai kuma ta sake rikicewa dan dai a iya tinaninta tasan ta kone mururus,to kodai fatalwar tace dan dagajin wannan marin kasan bana mutum bane,a rikice baki na rawa ta nunata tana fadin

    “Innalillahi ku kuke ganinmu bamu muke ganinku ba,baki kone ba dama,kardai fatalwarki ce ta dawomin…..

Bata bari ta karasaba ta sake bata wasu lafiyayyun maruka guda hutu ji kake,tass tass tass tass…….

Wani irin ihu mama ta saki ta mike ta fita a guje,binta fatima zainab tayi itama,parlour mama ta nufa tana tafe tana sakin fitsari,imaan da husna na ganin mama ta fito a guje,suma suka mike,fita daga part din suka soyi gabadaya amma kafin su karasa fatima zainab ta rigasu,ta kuma sawa parlourn key,juyawa da sauri imaan da husna sukayi mama na biye dasu a baya suka nufi sama,binsu tayi a nitse har suka karasa bedroom din dake sama ita kuma ta rufe kofar parlourn sama,husna da imaan ne suka shiga bedroom din dake saman suka kulle,mama ko kafin ta karasa sun rufe kofar kasancewarta katuwa yasa bata iya gudu sosai,gashi dama bedroom daya ne a sama saitarasa inda zatayi… Bubbuga kofar dakin take tana fadin 

   “Husna kutaimaka ku budemin in shigo karta kasheni,wallahi fatalwa ce” Ta fada jiki na rawa tana kuka wiwi

   “Mama kiyi hakuri bazamu iya budewa ba,dama ke take nema kar kuma ta hada damu”…

Mama tanajin haka tace “Wayyo Allah na mutu na lalace” Sai kuma ta zube a sume!!!

Ina sonku masoya littafina🥰

~Unique Barakancy~

Back to top button