Hausa novels

Halysaah Page 195 By Khaleesat Haydar

HALYSAAH PAGE 195…Bayan Ajay sun fito bangaren Mai martaba ya kalli wayar hannunsa dake vibrate ya ga Jay ne ke kiransa, tun daxu Jay ke waje yana jiran fitowar su, Ajay ya kalli Khaleesat ganin hanyar part din Hajja ta nufa yace “Ina kuma za ki wife?” Ta juya ta kallesa tace “I want to meet Hadiyah, ba mu yi sallama da ita ba” Bai ce mata komai ba ya bi ta da kallo har tayi corner sannan yana tafiya slowly ya nufi hanyar fita waje, har sannan maganganun Sarki basu dena yi masa yawo a kai ba, tun Khaleesat bata karasa part din Hajja ba ta hadu da Hadiyah a hanya, Hadiyah tace “Na je side din Mami naga baku nan” Khaleesat tace “Eh tun daxu muka bar part din, dama ce maki zan yi we are leaving now….” Hadiyah ta sauke ajiyar zuciya su ka ci gaba da tafiya a tare tace “Yanxu wata nawa za ku yi a can idan kun je?” Khaleesat na kallonta tace “I don’t really know… Na gan ki wani iri hope all is well?” Hadiyah ta daga ido ta kalleta, ɗan murmushi tayi irin na karfin hali tace “Nothing, har naji na fara missing din ku wallahi….” Khaleesat tace “To ko za ki bi mu?” Hadiyah tayi er dariya tace “A’a ai it’s too late kuma, after the surgery zan zo in duba yaya in sha Allah” Khaleesat tace “Da gaske?” Hadiyah tace “Yeah, amma idan zan samu Visa within the period in sha Allah zan gaya ma Mai martaba sai in je” Khaleesat tace “To Allah ya sa ki zo din” A haka suka fita har haraban gidan, Ajay da Jay suna jingine jikin mota suna jiran fitowar Khaleesat, Jay dai kallon Hadiyah yake har suka karaso wajen motar, Hadiyah na kallon Ajay da murmushi fuskarta tace “Yaya Allah ya kai ku lafiya, Allah kuma ya baka lafiya” Ajay yace “Ameen” Ta juya ta kalli Khaleesat tace “We will speak on phone in sha Allah Halysaah, wishing you all safe trip and journey mercies” Khaleesat ta ɗan yi murmushi tace “Thanks dear” Hadiyah bata yarda ta kalli Jay ba, ta juya ta bar wajen, Jay ya bude front seat ya shiga, dogarin dake tsaye wajen ya bude back seat da sauri, Khaleesat ce ta fara shiga motar sannan Ajay ma ya shiga dogarin ya kulle motar yana jera masu kirari tare da masu fatan Allah ya kiyaye hanya. Washegari da yamma sosai suka sauka kasar America, Lyft da Jay yayi order ya daukesu daga airport zuwa gida, Jay ya sauka daga Lyft din tare da drivern suka zaga bayan trunk din motar don fiddo da akwatunan su, Ajay dai kallon Khaleesat kawai yake ganin tayi nisa cikin tunanin da take, ya kai hannu lap dinta yana shafawa a hankali in a romantic way, lokaci daya ta dawo reality ta juya da sauri ta kallesa, ya jingina jikinta murya can kasa yace “Tunanin me kike Slushie?” Tayi murmushi a hankali tace “Ina tunanin ranan farko da na fara ganin ka ne” Ya ɗan bude ido yace “Really, a ina kika fara gani na?” Ta saka hannunta cikin nasa slowly tace “A kofar gidan nan, dai dai inda Lyft din nan yayi parking is the exact spot da Ya jawwad yayi parking ranan da asuba, ka fito gida tare da karen nan naku” Yace “Sai me ya faru?” Still smiling tace “A ranan na fara ganin ka, kawai naji gabana ya fadi sosai” Tana fadin haka ta daga kai ta kallesa taga kallonta yake babu ko kiftawa, tana murmushi tace “Sosai fa gabana ya fadi da na gan ka that very night, shi ne na fara boye fuskata da mayafina da sauri, sai abun yake min kamar na taɓa sanin ka a wani waje, bayan ni dai nasan ban san ka ba, ban kuma taɓa ganin ka ba sai a wannan ranan, but you know what?? I just realized probably a mafarki na nasan ka, i might have dreamt of you, shi yasa nake jin kamar na san ka da na ganka….” A hankali yace “You felt our connection right from day one Jeeddah, sign ne aka maki a ranan cewar i am the Man for you, ni kuma ranan ban ga fuskar ki ba, i only knew that a lady was sitting at the front seat” Ta jinginar da kanta a jikinsa a sanyaye tace “Har muka isa apartment dina gabana bai dena faduwa ba ranan, sai kuma muka hadu a eatry few weeks later, nan ma sai da naji gabana ya fadi da na gan ka, but before then duk sanda ka kira Housemate dina zan tsaya in ta kallon number ka, tun ma ban gan ka ba, infact ban ma saba da Housemate dina ba a lokacin sosai, kawai dai on several occasions in na fito zan je kitchen sai in ga kana kiran wayarsa, cause he sometimes use to neglect his phone on the sofa, I don’t know ko yanda yayi saving sunanka ne yayi catching attention dina, ko kuma kawai don Allah ya rubuta kai ne future Husband dina, but I always stare at ur phone number anytime you call Ya Jawwad” Lumshe ido tayi saboda yanda memory din komai ya fara dawo mata tiryan tiryan kai, a hankali yace “I have always felt connected to you tun daga ranan da na fara ganin fuskar ki Jeeddah, the birthday gift you gave to me was one of the best thing I appreciate till date, i was so happy with the gift” Ta daga idanuwanta ta kallesa, muryar Jay suka ji dai dai side glass din back seat din yace “Ko dai ya maida ku airport din ne kawai?” Khaleesat ta ɗan yi murmushi ta bude other side din motar ta sauka, Ajay ma ya sauka daga motar, zata dau akwati daya Jay ya langwabar da kai yace “A’a ku tafi ku ci gaba da labarin ku, zan taho da su ai tun a Nigeria ni ke jigila da su” Er dariya tayi tace “A’a bari in dau karamin Yaya Housemate” Bata jira me zai ce ba ta dau karamin box din ta nufi cikin gidan, Ajay dai yaki daukar komai yayi gaba ya bar Jay da boxes din. Har wajen karfe tara Khaleesat bata gama gyaran gidan da take ba cause the House was so dusty tunda babu kowa a ciki, a haka don ma Jay yayi assisting dinta wajen gyaran parlon daga karshe ya ɓige da bacci kan kujera, bayan ta gama komai ta wuce sama zuwa side din Ajay feeling so exhausted, tun shigowarsu gidan ta fara gyara masa ɓangarensa ya shiga kafin ta sauka downstairs ta fara gyare gyaren parlor, bata samu Ajay a parlonsa ba ta kalli abincin da ya ci ya bari, ta karasa bedroom dinsa ta bude kofar a hankali ta shiga, ta gansa yayi rub da ciki cikin lallausan white bedsheet din kan gadon yana bacci, kana ganin yanda ya kwanta zaka san yayi missing gadon nasa, ta karasa ta rufa masa white duvet ta dau sauran fruits din da ya bari a bedside drawer ta fita da shi….. The next day da safe suka fita zuwa asibiti don ranan suke da appointment a John Hopkins Hospital dake nan Maryland, memories iri iri suka dinga dawo ma Khaleesat during their ride to the hospital, tana ta kallon streets din Baltimore da yanda tayi rayuwa har na shekara hudu a garin, ta tuna farkon zuwan ta Maryland tare da Abdul, how her first 3 years went with Abdul sponsoring her education and Welfare, sannan haduwar ta da Jay a apartment dinta tana dab da shiga final year a makaranta, few weeks da haduwanta da Jay kuma ta hadu da Ajay, how things suddenly took a quick U-turn and everything changed, but all this happened because of Abdul, shi ne sanadin komai da ya faru a rayuwarta, wani ajiyar zuciya ta sauke ba tare da tasan tayi hakan ba, Ajay dake gefenta ya juya ya kalleta, sauke idonta tayi, she felt like crying ta rasa dalili, amma ta dake bata yi kukan ba, but remembering her past got her so emotional, Ajay ya kamo hannunta cikin nasa kamar yasan tunanin da take, ta daga kai ta kalli Jay dake zaune gaban mota, tasan she will forever be grateful to him and Abdul, ko ba komai ita bazata manta alkhairin Abdul a gareta ba, don alkhairinsa ya fi sharrin sa yawa, he gave her a sound education, and she live a perfect life all through her first 3 years in Maryland bata taɓa rasa komai ba duk da abubuwan da yake mata, he made sure she lacks nothing duk da halinsa, a haka suka isa John Hopkins Hospital aka yi admitting Ajay don a ranan da yamma za ayi masa Surgery dinsa…. Smoothly aka yi ma Ajay surgery dinsa na raguwan fragments na bullet dake jikinsa, and they were in hospital for close to 3 weeks for the healing process, sosai Jay ke basa kulawa yanda ya kamata, don Khaleesat yawanci sai dai taje gida tayi bacci ta dawo da yamma, ranan da suka cika sati uku a asibitin ne aka yi discharging dinsu zuwa gida.

Back to top button