Labarai

Makauniyar Soyayya Complete Document

Description/Story:

Makauniyar Soyayya! Complete Hausa Novel Document Written By Maryam Ahmed Paki

 

Description

MAKAUNIYAR SOYAYYA*💝💖💞

🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀

*STORY & WRITTING*

*BY*

*MARYAM AHMAD PAKI*
(07037004285)

 

*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION*✍🏽

 

Bismillahir rahmanir rahim
Dukkan yabo ya tabbata ga Allah (S.W.A) da ya ba ni ikon shiga sabon wani littafin.
Wannan littafin nayi shi dan fad’akarwa, nishad’antarwa, ilimantarwa da kuma du ba da halin da muke ciki a yanzu.

Dafatan za ayi amfani da darasin dake ciki ayi watsi da abin da bai da kyau a littafin

 

*Wannan shafin sadaukarwa ce ga duk wani mai son littafi na da kuma wanda su kai ta min Magana akan fitowar wannan littafin*
*Nagode da kulawa sosai*

 

*Har kullum ki na raina*
*Mufida mu’azu*
(Marubuciyar Auren dole)
*Ba zan gaji da nuna kulawa ta gare ki saboda yadda kike ba ni k’warin gwiwa*,
*ba abin da zan ce miki sai dai in ce Allah ya bar kauna kuma ya biya miki buk’atun ki*

Tunatarwa:

*Ko kasan/kinsan ina ake sanya zunuban mu yayin da muke sallah?

Manzon Allah (S.A.W) ya ce: duk lokacin da bawa yake sallah ana sanya dukkan zunuban sa a wuyan sa da kafad’un sa, duk lokacin da yayi ruku’u ko sujada zunuban sa za su dinga fadowa kamar yadda ganye yake fadowa daga bishiya don haka mu tsawaita sujada da ruku’u domin zunuban mu su ragu.

 

1&2

Yau a garin Kaduna an tashi da matsanancin zafi kasancewar zafi ya fara shigo wa wanda yake hana mutum sakat, dawo wa ta daga makaranta kenan na cire uniform d’ina na fada toilet d’in dake jingine a d’aki na, ko side d’in Ummu ban shiga ba saboda zafin da ke son sa min wani ciwon, ko minti 5 ban d’auka ba na watsa ruwan sanyi kana na fito na zira ‘yar t-shirt da wani simple skirt na nufi d’akin Ummu wanda na same ta zaune a 3 sitter rike da hisnul muslim a hannun ta tana nazari.

Sallamar da nayi ne yasa ta katse karatun da take yi ta d’ago ta na kallo na tare da murmushi a fuskar ta, jikin ta naje na kwanta kasancewa ta mai son jiki duk da yaya Aminu ba ya so amma Ummu cewa take yi a k’yaleni ni ce auta kuma d’iya mace a gaban ta.

“Ummu sannu da gida”

“Yawwa Fatima an dawo? ya lesson d’in”

Cikin shagwa ‘ba na ce “gaskiya Ummu na gaji da wannan lesson d’in waec da neco d’in nan, mutum ya dawo a gajiye gashi ba a tashi da wuri ga zafi yazo, a class mutum yaji kamar ya cire kayan jikin shi saboda zafi yanzu fa daga dawo wa ta sai da na watsa ruwa amma ji nake kamar ana kara min wani zafin, gaskiya ki yi ma yaya Aminu magana saboda shine d’an sa ido shi da wannan abokin nashi yaya Faruk, zan daina zuwa lesson d’in nan, yanzu ban da na school da nake attending kuma an kara sa ni a wani extra school ran weekend sai kace wata mango park”

Dariya Ummu tasa tace “kai auta ina laifin wanda ya damu da ilimin ka ai in ba a gode mai ba bai ci kuma a kushe shi ba, kiyi hakuri ki k’arasa lesson din tunda kun kusa zana waec da neco d’in sai ki huta gaba d’aya tun da kinyi jamb kafin admission ya fito a fara zuwa jami’a

Cikin jin dad’i na rungume Ummu ina murna ina cewa “wa ya ganni a jami’a?

dariya Ummu tayi tace “auta kenan”

sallamar yaya Khaleel ce ya katse mana hirar da muke yi

Amsawa muka yi kana ya saki murmushi yace “auta me ake tattaunawa ne don na ga hirar ta muku dadi”

Hararar wasa na mai tare da murgud’a baki nace “ba sai kaji ba kuma ni kadaina ce min auta saboda na girma kuma in k’awaye na suka ji dariya zasu min”

Dariya yayi yace “to shikenan sister na daina tun da kin girma”

Kallon Ummu yayi yace “yaya Faruk ya dawo yace in gaishe ki kafiin ya zo”

Yalwata murmushin ta tayi tace “ikon Allah yaushe ya dawo”

Amsa mata yayi da cewa “jiya ya sauka kin san ya kwana biyu bai zo Kaduna ba ya ‘boye a Abuja, kin san aikin sojoji sai a hankali ba sa samun hutu, nima na biya gidan ne in gaida momi mu ka hadu”

Ummu juyowa tayi tana kallo na wadda tun san da naji an ambaci yaya Faruk nayi shiru kamar ba na d’akin tace “kin ji yayan ku ya dawo ki tashi ki je ki shirya mai abinci saboda nasan anan zai ci na dare”

d’aure fuska nayi nace “gaskiya Ummu na gaji, kina gani yanzu na dawo daga makaranta sannan ki ce in dafa mishi abinci, ba ga iya talatu nan ba, basai ta dafa mai ba, yanzu yana zuwa ni zai fara sa wa ido da fad’a, indai ya dawo ban da sukuni a gidan nan, ya dinga d’akko laifi yana d’ora min ko banyi komai ba, Allah-Allah nake yi ya koma ga kuma takurawar yaya Aminu in yazo gaishe ku, ni ko ta ina a takure nake, na fara matse hawayen da ya fara zubo min

Shi kuwa yaya Khaleel murmushi kawai yake yi saboda yasan halina na rashin shiri da yaya Faruk saboda yadda bai wasa a family, yafi yaya Aminu zafi ko dan kasancewar sa soja ne? oho! haka kuma abokai ne shi da yaya Aminu kasancewar su sa’annin juna, don haka ya matsa kusa da ni yace ” oh Fatima miye abin kuka? kin san yaya Faruk baya cin abincin ‘yan aiki kuma ba ya d’aukan raini yanzu sai ya baki purnishment d’in da zaki kwana biyu kina jinyar kanki don ma na lura kamar ke yana raga mi ki kuma kin san indai yazo sai kin dafa abincin nan saboda shi yace a dinga barin ki kina dafa abinci, Ummu ta dinga hutawa kuma yana da gaskiya kinga kince kin girma, kwanan nan za a fara zancen auren ki kinga in kin je gidan mijin ki basai ki dinga dafa wa mijin ki kala kala abinci mai dad’i ba kinga anan ai yaya Faruk yayi taimako ya k’arasa maganar yana dariya.

Part

3&4

Mik’ewa na yi ba tare da na ce komai ba saboda in na biye ma yaya Khaleel sai ya sa ni kuka saboda in ya fara tsokana ta wani sa’in sai yaga nayi kuka yake kyale ni.

Kitchen na nufa ina tunanin mai zan dafa mai wanda bazai d’au tym ba don ni a gaskiya ta mu bata zo d’aya da shi ba kasancewar yadda yake da zafi da fad’a ga salon mugunta duk ya iya shi, ko da yake ai ba a banza ba tunda soja ne dole yasan style na mugunta ga son girma kamar gyambo, duk da wani sa’in ya na ja na da wasa amma duk da haka na kasa sabawa dashi.

Farfesun kayan ciki na dafa mai da soyayyar taliya na had’a da zob’o wanda yaji kayan had’i na ajiye akan dining table

Tun da naci abinci na wuce d’aki na fara chat da friends d’ina don ina ganin ya fi min akan in zauna ayi hira da ni in dai yaya Faruk na nan.
Ina chatting ina jin hirar su da yaya Khaleel da yaya Aminu da yazo gaishe da su Ummu kasancewar shi yayi aure, jefi- jefi nake jan tsaki saboda yadda na takura a d’akin, ban san tym d’in da na d’auka ba ina chatin sai tsayuwar mutum naji a baya na, ganin haka ne yasa na juyo don in ga wani gwanin ne ya tsaya a baya na ba tare da yayi sallama ba.

Waigowar da zanyi na gan shi ya k’ure ni da ido fuskan nan ba alamar fara’a kamar an aiko mai da sak’on mutuwar shi cikin shigar shi ta wani lallausan yadi an mishi simple d’inki.

Cikin karkarwar murya na jawo miyau da k’yar na had’iye ina addu’a a raina Allah yasa kar ya amshi wayar nan saboda ya hana ni chatting yace wai nayi yarinya da chat.

“Ina wuni…yaya Faruk! ka dawo lafiya?

Ci gaba yayi da kallo na ba tare da ya amsa gaisuwar da nayi mai ba illa hannun shi da ya mik’o min.

A raina na ce “wannan yayan akwai rainin wayau to ni mai zan mik’a mai da ba zai iya min Magana ba, amma nasan maganin shi duk da nasan waya ta yake nufin in bashi.

Juyawa nayi ina dube-dube kamar ina neman wani abu sannan na juyo na kalle shi nace “yaya me zan baka?

Sai da ya gama shan k’amshin shi kana yace “au baki san me zaki bani ba koh?
To mik’o min wayar ki tun da kin zama mai kunnen k’ashi, how many times did i warn you that i don’t want you to involve yourself in this social media amma baki ji ba? nasan matakin da zan d’auka a kanki don kin ga ina raga miki ne ki je ki tambayi Anisa za ta baki labari na don na ga alamar kin manta ni”

Raina ne ya so ma ‘baci saboda ganin har yau yaya Faruk d’in nan kallon yara yake mana, in ban da haka ya za ace ina class d’in karshe a secondary amma yace wai ban kai in yi chat ba wanda yanzu kowa yasan harkar socialization ake yi amma shi kullum yafi son ya gan mu a local.

Tsawar da ya min ce tasa hannu na yana rawa na mik’a mai hawaye na zuba a ido na.

Ko da ya amshi wayar whatsapp d’ina ya fara bincika kasancewar ina online,
ya d’au kusan 5 min yana latsa wayar kafin ya d’ago yana watsa min harara sannan yace

“Teemah! ya ambaci suna na kasancewar wani sa’in haka ya ke kira na.

d’ago wa nayi na kalle shi saboda yau ban san kalar muguntar da zai min ba, ni dai addu’a ta ita ce kar ya hana ni wayar saboda ta na min amfani, ga internet da nake research a ciki, ga chat d’in nan da nake k’aruwa dashi, ga online novels da na ke karanta wa yake sa ni nishad’i da kuma darusa da nake koya a ciki.

Katse min tunani yayi da cewa “Fatima wai ba ki ji kiran da nayi miki bane? Ko zaki nuna min yanzu kin yi girman da baza a miki fad’a bane!
Listen to me carefully!
Teemah ba na so ina miki hukunci saboda wasu dalilai amma hakan bazai hana in kin yi laifi ki amshi purnishment ba, time without numbers na sha fad’a miki bana son kina wannan chat d’in nan saboda har yanzu ke yarinya ce tunda har yau baki gama secondary ba, yanzu k’aramar ki dake har kin san ki shiga groups d’in matan aure su na bud’e miki ido kina ganin posting d’in su na zaman aure, ki bari in time yazo da kaina zan ba Ku damar chat ke da Anisa because as now you are too small, yanzu ma Allah ne ya taimake ki, ban ga alamar kina chat da maza ba, da ke da waya sai in kinyi aure ko in siyo miki k’aramar nokia in ba ki, this should be the last time da zanyi warning dinki kina ji na koh?
Gyad’a mai kai na yi saboda wani abu da ya tokare min a k’irji saboda har ga Allah yaya Faruk na matsa min, ni ban da damar yin abin da raina yake so kenan in dai yana gidan ko shi wa ya takura mai? in ban da ya mai dani wata mara class zai ce zai siyo min k’aramar nokia da haka in zauna ba wayar a hannu na mana, Shi wa ya san abin da yake yi a Abujar zai zo yana takura min, waye bai san sojoji da son mata ba zai zo yana takura min.
Kamar yasan abin da nake cewa a raina yayi wani mayaudarin murmushi yace “ki gama zagi na a ranki lokacin ki ne kin ga kin girma ne da ai baki yi ba! kin san dai hali na”

“Laifin ki na gaba shine mai ya hana ki kizo ki gaishe ni san da kika ji na shigo gidan ko ki na so ki nuna min yanzu kin wuce wannan level d’in don naga kanki na rawa.

Rasa amsar bashi nayi don haka nace ” ni banji shigowar ka ba shi yasa”

ta‘be bakin shi yayi alamar bai yadda da abin da nace ba illa cewa da yayi
“Teemah manya!

Iya k’arshe yau Yaya Faruq ya kai ni saboda Magana d’aya sai ya wa ni ce na girma to da haka yake so nai ta zama don haka ban san lokacin da na d’ago kaina na watsa mai harara don kar ya gane sai na fara murza ido na alamar wani abu ya fad’a min a ido.

re-action d’in da nayi yasa ya fara dariya saboda ko da can yasan ni da tsiwa da neman tsok’ana, bai ce min komai ba ya wurga min wayar akan gado na ya fita daga d’akin.

Wata nannauyar ajiyar zuciya na saki saboda Allah ya raba ni da d’an ka’ida lafiya kuma ni jin dad’i na da bai tafi min da wayar ba, haka nayi ta zancen zuci har bacci ya dauke ni

 

File Name   Makauniyar Soyayya Hausa Novel
Title   Makauniyar Soyayya Complete
Author    Maryam Ahmed Paki 
Group    Ai  Hausa Novels
Genre    Fiction Story
Published Date    17/07/2024
File Size    1.01 MB
Format Size    TXT
Book Price    Free
Phone No
Download Makauniyar Soyayya Complete Novel Document By Maryam Ahmed

Click the below green button to read the novel online

READ THE NOVEL


Proceed with your download by clicking the below button

 

 

Be With Us

 

DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.

Back to top button