Uncategorized

Muhabbatil Qalb Hausa Novel Document – Aihausanovels

Muhabbatil Qalb written By Asmy B. Aliyu

Posted by AiHausa Novel
Price 300
Category Hausa Ebooks
Uploaded On 07 Feb, 2023
Upload Time 8:29 am
Hits 218 Views
Author

Asmy B. Aliyu

Writer Group

Writer Associat

Novel Genre

Comment No Comments

Muhabbatil Qalb Written By Asmy B. Aliyu

Drivern gidan su na danno hancin motar cikin babban compound ɗin gidan mai ɗauke da sashe har guda uku ta buɗe ido da mamaki take kallon motar Maina saraki dake fake acikin babban compound. Kara buɗe ido tayi tana kallon motar yaushe yazo? ta tambayi zuciyarta bayan ko minti talatin basuyi ba da gama waya dashi. Kai tsaye ta fice daga cikin motar, sashen dake can ƙarshe ta nufa da gudu duk da yayda ta kwaso zafin rana ga yunwa  da take ji haka ta nufi entrance ɗin shiga part ɗin. Door bell ta danna ba’a ɗauki lokaci ba mai aiki tazo ta buɗe mata, ganin Hafsat yasa ta ba ta hanya tana gaisheta, bata ko kulata ba ta shige, kai tsaye stairs ta nufa tana haɗawa da gudu. Ɗakinsa ta nufa dake ɓangaren dama da sauri ta buɗe ƙofar dai-dai lokacin Muhammad Maina ya buɗe ƙofar toilet ya fito jikinsa ɗaure da babban towel fari sol. Da gudu taje ta ƙanƙameshi tana yi masa ihu. ware manyan eye’s ɗinsa yayi masu kama da na cat yana kallonta, da wata kalan murya yake  faɗin. “Sweet zaki kada mufa.” Ta maƙe kafaɗa tana turo baki ta wani haɗe rai lokaci ɗaya ya riga da yasan laifinsa bai faɗa mata zuwansa ba. Komawa tayi kan soofa ta zauna ranta a ɓace ta tallabe fuskarta da hannayenta duka biyu. Hakan da tayi yasa Maina Saraki sakin wani irin kayattacen murmushi, hannayensa ya haɗe duka biyu da ido yake bata hakuri.

 Maƙe kafaɗa tayi alamar bazatayi ba, ya cije lips. Warware towel ɗin ya shiga yi ta fiddo da dukkan idonta da gudu ta nufi ƙofa ya bita da kallo still da wani irin murmushi cikin fuskarsa. Har ta sauka ƙasa babu kowa cikin parlorn. Wani irin murmushi ne kwance cikin fuskarta, tana ƙaunar Maina Saraki da dukkan zuciya da ruhinta. Kai tsaye part ɗin su ta nufa. Mama ce a parlorn tana shirya lunch Asma’a ce zaune akan rug tana bitar karatunta na hadda. Dakyar Hafsat Saraki ta gaisheda Mama da suka  haɗa ido da haka ta nufi part ɗin su, Asma’a ta taɓe baki ta cigaba da abunda takeyi, Mama ta ƙaraso cikin parlorn tana faɗin. “Kije ki ɗibi abinci lokaci na tafiya kin san Shantima bai son jira nasan kuma shi zai kaiku Islamiyya tunda driver tare da Baffan ku zasu fita.” Daga haka Mama ta nufi stairs Asma’a ta turo baki tana faɗin. “Mama nifa bana son jelop rice dan Allah nayi wainar fulawa mana?” Wani kallo Mama keyi mata tana faɗin. “Har yaushe kikayi wainar kuka tafi islamiya?” Da sauri Asma’a ke cewa. “Minti nawa ne Mama? dan Allah.” Ta faɗa mata cikin sanyi murya, Mama ta girgiza kai tana cigaba da tafiya take faɗin. “Ni dai babu ruwana saboda kin san halin wanda zai kaiku islamiyyar.” Kwashe books ɗinta tayi tabi bayan Mama. Kusan biyu da rabi ta fito daga parlorn ta nufi part ɗin Ummah, Hafsat ce kawai a parlorn tana waya, kallo ɗaya Hafsat tayi mata ta cigaba da wayarta, kai tsaye ɗakinsu Ikraam ta nufa kusan cin karo sukayi da Ikraam ɗin itama ta fito cikin nata shirin islamiyyar uniform ɗin kalar light blue da hijab har ƙasa. “Ziyada baza taje ba ne? Yah Shantima zai kaimu fa.” Ikraam ta taɓe baki tana faɗin. “Wai kanta ne yake ciwo, kuma nasan karya take Ita dai bata iya hadda bane kawai.” Ɗaga kafaɗa Asma’a tayi, tare suka sauka har ƙasa Ikraam ta ƙaraso cikin parlorn tana kallon Hafsat wacce har lokacin waya takeyi. “Addah Hafsat ki bani alkawarin ɗari biyar ɗin da kikayi min.” Hafsat ta kalleta tace.
 “Kije ɗakina kan mirror dressing ki ɗauka, ɗari biyar kawai zaki dauka na gaya miki.” Daga haka Ikraam ta juya ta nufi ɗakin Hafsat Saraki wanda daman Asma’a ta daɗe da barin parlorn tana fitowa compound ta hango Yah Shantima da Maina Saraki suna tahowa. “Mugun gidan su ya dawo kenan?.” Zuciyarta ta faɗa tamkar Asma’a bata so ta gaishesu dukkan su. Shantima kawai ne ya karɓi gaisuwarta amma Maina Saraki ya nufi part ɗin Inna. Da harara ta bishi tana jin wani ɓacin rai tace. “I hate him with passion.” Ta faɗa tana wani binsa da wata hararar. Shantima Saraki ya kalleta yana faɗin. “Ina sauran kuma?” Zatayi magana sai ga Ikraam ta fito, da mamaki yake faɗin. “Ziyada fa?” Ikraam ta buɗe hannuwa tana faɗin. “Tace wai kanta na ciwo.” A fusace Shantima ya nufi sashensu yana kwalawa Ziyada kira tun daga kofar parlor. Asmaa ta girgiza kai tana faɗin. “Nidai wallahi zai saka muyi latti.” Ta faɗa tamkar zatayi kuka. Ƙarasawa sukayi wurin motar Shantima Saraki suna jiran fitowarsa. Fuska babu walwala yayi tsaye a ƙofar ɗakin yana bin Ziyada da mugun kallo, Ya kalli agogon rolex ɗin dake ɗaure cikin damtsen hannunsa yake faɗin. “Na baki minti goma kacal Ziyada Saraki ki fito, ko sakan ɗaya kika ƙara wallahi haɗuwar mu ba zai yi miki kyau ba.” Da haka Shantima Saraki ya bar room ɗin wanda kusan cin karo sukayi da Ummah, ɗauke kai yayi ya wuce. Tsaye tayi bakin ƙofar tana kallon yadda hawaye suka cika fuskar Ziyada tana saka uniform ummah ke faɗin. “Shi wannan mai yazo ya faɗa maki?” Cikin fashewa da kuka take faɗin. “Yace minti goma ya bani na saka uniform na fito mu tafi, kuma wallahi Ummah yau malam Aminu kasheni zaiyi saboda ban iya haddar da aka bani ba, kuma fa Ummah kusan shafi huɗu ake bina ko na wancan satin ban bayar ba.” Cikin wani yanayi Umma ke cewa. “Shi uban kine da zai sakaki zuwa makarantar? Kiyi zamanki babu inda zakije.” Ziyada na girgiza kai take faɗin. “Ni dai bari naje Ummah haka kawai ya zaneni a banza kuma naje islamiyya a kara zaneni.” Da haka tabi gefen uwar ta wuce. Baki Ummah ta saki tana kallon Ziyada dake tafiya cikin mugun sauri. Rai a ɓace Ummah ke faɗin. “Bari uban naku ya dawo ni dai a yiwa ƴaƴana  iyaka da Shantima tunda bashi ya haifa min ba.” Hafsat ta girgiza kai tana faɗin. “Toh meye laifinsa anan Ummah? daman kin san halin Ziyada bata son karatu.” Ummah zatayi magana Hafsat ta miƙe tsaye ta nufi ƙofa wacce kananun kayane ajikinta wanda suka kamata sosai sai ɗan ƙaramin veil da tayi rolling tana faɗin. “Zanje mu gaisa da Inna da safe ban shiga ba.” Wani kallo uwar ta riqa yi mata har ta fice daga parlorn. Tun a ƙofar parlorn shiga take jin hirar Inna, takalmin da ta gani a ƙofar parlorn ya tabbatar mata da Maina ya shigo ciki. Tsaye tayi a bakin ƙofar tasan halin Inna yanzu zata ce sabida taga Maina yazo ne shi yasa ta kwaso jiki tazo itama.” Abunda taji Innar na faɗa yasa ta kasa shiga cikin parlorn, wani irin faɗuwa gabanta yayi. “Ai ƙara a haɗe aurenku kai da Shantima a huta, toh me ake jira idan taje ɗakin kawai ba sai tayi karatun ba. Ace kaninka zaiyi aure ba tareda naka ba? ai da sake gaskiyya naga dai kai auren gida zakayi ba’a waje za’a nemo matar ba, ban san me ake jira ba har yanzu. Idan iyayen nan naku suka cigaba da biyewa bokon nasarar nan ba za’a yishi yanzu ba. Amma ai kaga shi Shantima da yafi ka hankali kaga har an kai kuɗin gaisuwa rana kawai suke jira a saka, wai fa dan haka ma na matsawa Kabirun lamba ya kiraka kazo ayi komai a ƙare.”


 Wani irin murmushi yake ya yiwa Inna, baki sake Inna ke kallon sa, ya shafa sumar kansa still wearing a smile, mitsi-mitsi da Ido Inna tayi tana kallonsa, zatayi magana ya rungumeta cikin jikinsa yana sauke wani irin numfashi saboda bai san dame zai sakawa Inna ba, daman kullum Hafsat Idan yace ayi aure sai ta kawo masa uzurin karatunta, shi kuma baya son abunda zai ɓata ran Hafsat Saraki dan yana yi mata soyayyar da shi kansa bai san adadinta ba. kullum azumin Litinin da Alhamis baya wucesa akan Allah ya mallaka masa Hafsat Saraki dukan ta. Bai taɓa sawa ransa abubuwa zasu zo haka cikin sauqi ba. Yanzu idan su Baffa da Inna suka yanke hukunci yasan ba zata yi jayayya ba, haka kuma bazata ɗauka da saka hannunsa acikin lamarin ba. Da baya -baya take barin part ɗin Inna tana jin idonta na rufewa, tafiya kurum take ba tare da ta san inda take saka ƙafafunta ba. Tana son Maina Saraki da dukkan zuciya da gangar jikinta. Sai dai idan kuma sukayi aure zai rabata da Besty ɗinta data zamar mata rabin jiki.


 Cikin ƙanƙani lokaci wani irin zazzabi ya rufe Hafsat. Kai tsaye part ɗin su Hafsat Maina ya nufa daman bai shiga ba, da Mama suka fara gaisawa da fara’a take faɗin. “Yaushe a gari?” Ya shafa sumar kansa yana faɗin. “Ɗazu na shigo Mama Abba fa?” Ya tambaya yana sakin murmushi. “Bai dawo daga kasuwa ba.” Mama ta tambayeshi ya aiki ya faɗa mata “Alhamdulillahi.” Tayi masa tayin abincin rana ya faɗa mata Alhamdulillahi ya koshi, da haka ya shiga part ɗin Ummah itama da fara’a ta tarbesa tana yi masa sannu da zuwa. A nan kuma take tambayarsa zuwa babu sanarwa? yana shafa sumar kansa yake faɗin. “Wallahi kuwa ai ba daɗewa zaiyi ba. Mai aiki Ummah ta saka ta kawo masa ruwa da snacks ya faɗa mata a koshe yake. “Abban ku yana kasuwa sai zuwa anjima zakaga ya shigo.” Maina yace. “Haka Mama take gaya min.” Yana jin kunyar ya tambayi Ummah Hafsat da haka yayiwa Ummah sallama. Har ya kai ƙofa take faɗa masa Hafsat tana bacci itama bata daɗe da dawowa daga makaranta ba.” Yace.” “Anjima ai zan dawo gaisheda Abba.” Da murmushi Ummah tayi masa fatan sauka lafiya sannan ta faɗa masa ya gaisheda Hajiarsu. Kai tsaye ɗakin Hafsat ta nufa ta sameta a kwance, ta kira sunanta daga bakin ƙofa, ɗagowa tayi tana kallon Ummah lokaci ɗaya Ummah ta zaro ido tana ƙarasowa cikin ɗakin cike da tashin hankalin take faɗin. “Meya samu idonki?” Tamkar jira take ai mata magana, kawai Hafsat Saraki ta fashe da kuka. Da tashin hankali Ummah ta wani daka mata tsawa tana faɗin. “Wai uban me akayi maki ne?” Cikin kukan take faɗawa Ummah hirar da taji Maina Saraki nayi da kakar su, baki wangale Ummah ke kallonta tana cewa. “Ban taba sanin ke shashasha bace sai yau Hafsat, Abunda zakiyi murna sai kuma ki fara kuka?” Cikin ihun kuka Hafsat ke faɗin. “Karatuna fa Ummah? kin san idan auren nan ya tabbata Yah Maina zai iya saka a ɗaukeni daga nan a mai dani Sokoto, ni kuma bana son karatu a Sokoto na fison  anan, ni dai ban shirya aure yanzu ba saboda duk friend’s ɗina ba wacce tayi aure yanzu saini.” Tagumi Ummah tayi da mugun mamaki tana kallon ƴartata, ba tare da Ummah ta ƙara magana ba tabar mata ɗakin. Tana ganin yadda Maina Saraki ke faman kiranta a waya amma ta share kiran taki dagawa……

Domin Sauke Littafin Sai Ku Dannan inda aka saka Download Now!


Download

Click the below button to download, pls in case you get trouble trying to download kindly drop a comment.


Download any type of hausa novel which include Hausa Love, Adventure, fiction, Fantasy and other genre Hausa Novel paid and free and read them in confort of your zone at ArewaBooks.Com

 

Author’s Contact

  • Name : Asma’u B. Aliyu
  • Wattpad Handle : @ Asmy B. Aliyu
  • Nick Name : Asmy B. Aliyu
  • Whatsapp Number : 
  • Nationality : Nigeria
  • Email :
  • Group : Writers Association

The Book is not free

Back to top button