Uncategorized

Application din da zaku iya karanta ko wane irin littafin da shi cikin sauki (Wps Office)

Assalamu alaikum jama’a barkanku da wannan lokaci da fatan kuna cikin koshin lafiya kasancewar muna dora litattafan hausa wato Hausa Novel Document a wannan site namu na Aihausanovels.com to mutane da dama suna sha wahala wajen sauke littattafan da muke dorawa hakan yasa muka yi bincike wajen saukaka wa mabiyan mu ta hanyar lalubo masu wani Application wanda zai saukaka masu wajen karanta duk littafin da muka ɗora.

Domin Sauke Application Din Sai Ku Dannan inda aka saka Download Now!

Bayan kun suke shi cikin wayoyinku kai tsaye sai ku shiga cikin Application ɗin ,inda nan take zaku fara ganin duk wani littafi da kuka sauke kama daga Txt. Documents, Pdf. Docx. Da dai sauransu.
Wani abin sha’awa ga wannan Application shine yana yana taimaka wa marubuta wajen lissafa adadin yawan kalmomin da mutum ya rubuta musamman ga masu shiga gasa.
Sannan wannan Application ɗin yana taimakawa dalibai da da suke rubuta project zasu iya yinsa a nan sai dai kawai sukai ayi masu printing out wanda shima wannan ba karamin sauki gane.
Sannan Mutum zai iya hada Invitation
Card wato I.V da da dai sauransu.
Note: Wasu za su iya cewa ai muna da wannan Application ɗin to ku sani wannan sabon Update ne ma’ana wannan akwai abubuwan burgewa da babu a wancan alal misali zaku iya ganin Novel an saka masa Password to da wannan Application ɗin zaku iya karanta Novel ko yana da password ɗin.

Back to top button