Halysaah Page 185 By Khaleesat Haydar
HALYSAAH PAGE 185…HALYSAAH…Har bayan la’asar Khaleesat na zaune dakin da aka sauke su tana zuba ido taga Mami ta shigo amma shiru shiru, tun daxu ta shigo dakin ta tarar Mami bata nan, kamar ance ta duba wajen akwatin Mami taga babu handbag dinta a wajen, kasa daurewa tayi ta mike ta fita zuwa wajen Hadiyah, nan wata kawar Inteesar ke gaya mata Hadiyah tayi baƙo ta fita gun sa, Khaleesat ta fita daga dakin ta sauka downstairs, a compound din gidan ta tarar da Hadiyah tare da Khalil da ya zo wajenta, ta karasa har inda suke zaune, ta gaida Khalil ya amsa mata da fara’a yace “Yanxu nake tambayar Hadiyah ina kike tace kina sama” Khaleesat ta ɗan yi murmushi ta gyada masa kai sannan ta kalli Hadiyah tace “Mami ta ce maki zata fita wani waje ne?” Hadiyah ta girgiza kai tace “A’a, nima na shiga daki daxu ban ganta ba nayi tunanin tana wajen Ammin su Inteesar” Khaleesat tace “To ki bani wayar ki sai in kirata, kilan fita tayi…” Hadiyah ta mika ma Khaleesat wayar hannunta, sannan Khaleesat tayi ma Khalil sai anjima ta juya ta bar wajen ta koma cikin gida, dialing number Mami tayi bayan ta koma daki, sai da ya kusa katsewa sannan Mami ta daga kiran, Mami na jin sallaman Khaleesat ta amsa cikin sanyin murya tace “Halysaah” Khaleesat tace “Na’am, Mami kin je unguwa ne? Naga ban gan ki ba” a hankali Mami tace “Eh na fita Halysaah, kina wajen su Inteesar lkcn da na fita” Khaleesat ta ɗan yi shiru, sai kuma a sanyaye tace “To amma yanxu zaki dawo ai ko?” Mami ta sauke wani ajiyar zuciya tace “Ba lallai ba Halysaah, na je wajen wata kawata ne, kuma da nisa daga cikin gari, i probably won’t make it back today” Nan da nan mood din Khaleesat ya canza, cikin sanyin murya tace “To Mami kin ce fa gobe za mu koma Bauchi” Tana fadin haka hawaye suka cicciko idon ta, Mami ta lumshe ido ta bude tace “In sha Allah, idan na dawo za mu koma Halysaah” Halysaah dai bata ce komai ba ta goge hawayen dake makale idonta, Mami tace “Take care kin ji?” Kai Khaleesat ta gyada mata sannan Mami ta katse wayar ta sauke ajiyar zuciya, Allah Allah kawai take ta ganta a Benue, bata taɓa jin ta kagu ta isa waje ba irin yau…. Likitan dake shiga now and then duba Ajay ya kalli Jay da ya taso ya nufosa yana kallonsa, cikin sanyin murya Jay yace “Har yanxu bazan iya shiga wajensa ba Dr?” Likitan ya sauke ajiyar zuciya yace “Kayi hakuri abokina, we want him to be stable first, he is still semi conscious up till now, kasan har yanxu akwai bullets fragments a jikinsa wanda yayi causing various complications da za mu yi figuring daya bayan daya, we are afraid he might be suffering from lead poisoning also, Kai likita ne kasan abinda hakan ke nufi, we have to check his Blood lead level if he is stable, and also check for sepsis if any, so we are still monitoring him for now, har sai ya dawo fully conscious….” Jay was completely short of words, lokaci daya jikinsa yayi sanyi ya kasa ce ma likitan komai, kana kallonsa zaka ga damuwar da ya bayyana sosai a fuskarsa, likitan ya dafa shoulder dinsa calmly yace “All will be fine in sha Allah, kai ma kana bukatar kaje ka huta wani yayi takeover, you are stressed already, Kilan ko abinci baka ci ba duk yau ma” Jay bai iya yace ma likitan komai ba har likitan ya bar wajen, ya koma cikin sanyin jiki ya zauna ya dafe kansa, a hankali ya dago kansa after a while, ya ciro wayarsa yana duba agogo yaga karfe bakwai har da rabi na dare, har sannan Mai martaba bai biyo kiran sa ba yasan he might definitely be busy today, bayan Mai martaba babu wanda yayi attempting ya kira a masarautar don tsoron gaya ma kowa yake, kiran Mami ne ya shigo wayarsa a lokacin, rabonsa da waya da ita tun la’asar da ta kira tana kara tambayarsa jikin Ajay ta kuma tambayi asibitin da aka yi admitting dinsa, daga nan basu sake waya ba sai yanxu da ta kirasa, daga kiran yayi ya kai kunne cikin sanyin murya yace “Mami….” Mami tace “Ka fito ina haraban asibitin Jawwad” Jawwad was very shock, ya mike tsaye da mamaki sosai yace “Kina waje kuma Mami? How did you get here?” Mami tace “Ina compound Jawwad, i just arrived, motar haya na biyo tun sanda muka yi waya da rana….” Da sauri Jay ya nufi hanyar da zai sada shi da compound din asibitin, ai ko nan yaga Maminsa a tsaye daga ita sai Handbag, ya tsaya yana kallonta ya kasa karasawa inda take, ji yayi kamar ya fara yi mata kuka, har cikin ransa yaji dadin zuwan ta da yanda ta ba Ajay muhimmanci har ta biyo motar haya abinda bai taɓa gani ba tun tasowar sa, he felt so emotional at this point, Mami ta nufesa ganin ya kasa karasowa tana kallonsa a hankali tace “Jawwad ina Junaid din?” side hug yayi mata ya kasa ce mata komai trying hard to control his emotions, amma ita sai da hawayen suka taru idonta da kyar tace “Yana ina” Still ya kasa ce mata komai ya kama hannunta kawai suka shiga cikin asibitin, Mami na kallonsa tace “Amma baka kira Mai martaba ba har yanxu, don naga bai kira ni ba, har a gida ma babu wanda ya kirani alamar basu samu labarin nan ba….” Da kyar Jay yace “Naga miss calls din Sarki bayan Dsp ya bani wayata, sai na kirasa har sau biyu bai daga ba, i still called him after Asr no response, and he is still yet to call me back i think he might be busy today, I am afraid ban sanar ma kowa a masarauta ba tukun, bana son wani abu ya sake samun Ajay, he needs to be protected till he regain his strength Mami….” Mami tace “Mai martaba yana tare da jama’a sosai yau saboda daurin auren nan nasa, sai ya samu nutsuwa zai biyo ka, gwara kuma da baka sanar ma kowa a gidan Sarki ba tukun, da Mai martaba ya kamata ka fara magana” Jay dai a hankali yake tafiya tare da Mami, kwata kwata ya mance da wani daurin auren Mai martaba, shi duk yau tsabar yanayi na farin ciki da godiyar Allah da yake ciki babu abinda ya iya ci, ji yake baya ma jin yunwan kwata kwata, sai ruwa kawai da yake sha cause he is weak, a haka suka iso ward din da Ajay yake, Jay ya kalli Mami cikin sanyin murya yace “Ba a bari a shiga wajen sa Mami” a hankali Mami tace “Har ni baza a bari in shiga ba Jawwad?” Jay yayi shiru ya sauke idonsa, Mami tace “Yanxu baka shiga ka gansa ba kenan har yanxu?” Jay yace “Na shiga, but he was sleeping a lokacin, har yanxu kuma ba a bari na kara shiga ba” Mami zata yi magana sai ga Dr din dake shiga wajen Ajay tare da wata nurse, Mami ta gaida likitan, ya amsa mata, Jay na kallonsa yace “She is his mother Doctor, tana son shiga ta gansa ne if possible, ku taimaka” Likitan ya sake kallon Mami yayi mata sannu da zuwa sannan yace “Mu shiga Hajiya, but you won’t stay long” Mami ta gyada masa kai kawai tana jin gabanta na faduwa don bata san a halin da zata shiga ta ga Ajay ba, a hankali take biye da likitan har suka shiga ward din, dai dai nan wayar Jay ya fara ringing ya duba yaga Mai martaba ke kiran sa, juyawa yayi cikin sanyin jiki ya nufi kujeran da ke wajen ya zauna sannan ya ɗaga kiran ya kai kunne a hankali yace “Barka da dare ranka shi dade….” Mai martaba yace “How are you Jawwad, ina ka shiga yau?” Jay yayi shiru ya ma rasa ta inda zai fara, he can’t believe he is going to break this precious news to the king himself kamar yanda shi ne ya fara breaking masa news din abinda ya samu Ajay, tuna hakan da yayi got him really emotional at this moment, and he couldn’t hold back his tears, Mai martaba yace “Ahmad….” Jay ya kasa amsawa ya kai hannu yana goge tears dinsa still trying to control his emotions, Mai martaba yaji hankalinsa ya tashi yace “Is everything alright Ahmad? Are you there?” Shi kansa Sarki babu abinda ya fado masa sai ranan da aka kirasa aka gaya masa abinda ya samu Junaid, duk da damuwar da ya shiga yanxu haka ya dake yace “Ahmad are you there?” Jay ya gyada masa kai da kyar yace “Ina jin ka Mai martaba” Mai martaba yace “Speak to me Ahmad, me ya faru? Kana ina yanxu?” Jay ya dake cike da karfin hali yace “Abba…. I found Ajay, he is alive Abba”Mikewa Mai martaba yayi ba tare da yasan yayi hakan ba jin abinda Jay yace….. Mami na zaune gefen Ajay sai goge hawayen da yaki tsaya mata take duk ta jika gyalen jikinta da hawaye, she can’t believe this is Ajay by her side, rabonta da shiga irin wannan farin cikin a rayuwa har ta manta, kallonsa kawai take hawaye na zuba idonta, in ta tuna irin tashin hankalin da kowa a masarauta ya shiga akan rashinsa sai taji zuciyarta ya kara karaya, babu wanda rashin Ajay bai taɓa ba duk da yanda suka dinga nuna basa sonsa ashe bai kai zuci ba rashin son nasa, ga kuma halin da matarsa ta shiga wanda har yau bata dawo dai dai ba kullum cewa take zai dawo sai gashi ya dawo din a sanda babu wanda yayi zato don duk an cire rai da dadewa, kuka Mami ta dinga yi a hankali don ta kasa controlling kanta, tasan a yanxu dai babu wanda zai sake bakin ciki da Ajay a gidan nan ko matarsa, shi dai likitan na ta kokarin zuba wasu allurai cikin drip ga nurse tsaye kusa da shi da alluran, Motsin da Mami taga Ajay yana yi da hannunsa yasa ta kai hannunta cikin nasa tana kara matsawa kusa da shi, ya bude ido a hankali yana kallonta, rufe idon yayi as if trying to be sure of who he is seeing, ita dai kallonsa kawai take hawaye na bin kuncinta tsabar farin ciki ta kasa bude baki tace komai, ya sake bude idon ya kalleta, kara rufe idon yayi sannan ya sake budewa still dai yaga ita din ce, murya can kasa yace “Mami….” Mami ta kai hannu Gashin kansa da kyar tace “Junaid” ya fara kokarin mikewa zaune kawai Mami ta rungumosa ta fashe Da kuka.



