Uncategorized

Wace Ce Ita Chapter 31 Complete Novel

 

WACE CE ITA⁉️ (WHO IS SHE⁉️)

Unique Barakancy

                             THIRTY-ONE📍

       Alhamdulillah Alhamdulillah Allah yasawa wannan aure albarka!…….

Daddy ya juyo muryar mallamin na fadin haka… Sai kuma ya farka firgit daga dan baccin daya kwashesa, ashe mafarki yake har lokacin baa gama daura auren ba, ajiyar zuciya yayi yana jin kamar ya janyo lokaci, burinsa kawai a daura auren a wuce gurin, chan sai yaji gabansa na faduwa kamar wanda yayi tsere, babu wanda ya kula da yanayin da yake ciki aka cigaba da hidindimun daurin aure……

Alhaji habibu na shirin bada shedar an basu ita a matsayinsa na waliyyinta sukaji karar kofa…..

Sai kuma baa shigo ba, tinani sukayi ko iska ne hakan yasa suka cigaba da harkokin gabansu….

Alhaji habibu na shirin kara yin magana kenan sukaga an banko kofar parlourn da karfi……

Kallon juna suka shigayi kowannensu na tinanin waye dan meshi be shigoba har lokacin…….

     “Dama baka rufe kofar ba dazun?”……..

    “Wallahi na manta, ashe ban rufe ba, bari na duba naga waye sai mu cigaba”…….

Daddy ze mike kenan idonsa ya sauka cikin na khaleel da kallo daya zaka masa kasan har lokacin be dawo daidai ba…….

Tsabar rudewa besan sanda yace;

       “Auren ka ake daurawa son”…….

    “Bangane aurena ba? Dad what’s going on here?”

Cewar khaleel idonsa na sauka akan fatima zainab….

      “Wifey what’s happening here?”…..

   “Bansani ba”…

Ta bashi amsa tana mikewa…..

     “Can anyone tell me what’s really going on here?!”

   “It’s nothing serious son”…..

    “Daddy stop telling me it’s not serious, how comes wifey ita kadai a cikinku?”……

     “Nace maka auren ku ake daurawa”…….

     “Wifey is that so?”……

    “No! Ba auren mu ake daurawa ba and I don’t know what’s going on here too, I just found myself here!”…..

     “Dad just know that I’m not ready to listen to you in kasan bazaka fadamin gskyr abinda kuke shiryawa ba! Wifey taso mu tafi”……

Ba musu ta mike tabi bayansa suka fita daga parlourn……….

       “Yanzu kana ganin danka ya fita da ita amma bazaka tsawatarmasa ba? Yanzu wannan shirin shima ya kara rugujewa kenan?! Alhaji Ibrahim you’re playing with your life! Ku tashi mu tafi!”……..

Cewar alhaji habibu rai bace…..

      “Dan Allah ku zauna mu nemo solution, ku bani last chance nayi alkawari ba zaa kara samun matsala ba………. 

     “Bamu da wannan lokacin yanzu, mu hadu a house anjima kawai!”……

          Tinda suka fito daga part din daddy aka rasa me magana a cikinsu, kowanne yayi shiru yana fama da abinda yake tinani….Shi khaleel na tinanin abinda su daddy sukeyi dan haka kawai zuciyarsa taki aminta da abun alkhairi suke kullawa, harda masa karya wai aurensa ake daurawa ya tambayi fatima zainab kuma tace ba haka bane, she even seem so lost kamar batasan abinda ake ba tanadai zaune ne a gurin……. 

Ita kuma tinanin irin ramar da taga khaleel yayi take, tabbas taso taje ta dubasa dukda batayi tinanin ciwon nasa yakai har yayi rama haka ba……. 

       “Ya jiki?”….

Tasamu kanta da fadin haka……

Surprisingly yace;

    “Dama kinsan banida lafiya?”….

   “Nasani! Koda bansani ba your look said it all”….

    “Shine ko kizo ki dubani wifey? I was sick because of you, kinsani kikayi kamar baki sani ba”…..

    “I don’t know if you would believe this but I intended coming to check on you, bansan abinda yasha min kai ba”…..

    “Wow for real? Am I dreaming? Anya fatima zainab din danasani ce kuwa?”…..

Murmushi me kyau ta masa tace;

    “Itace mana, I hope you’re better now?”….

    “Even if I’m not better ganinki da maganganunki sun sani na warke rass and I still can’t believe it’s you”…..

    “Come on it’s me mana!”…..

Kawai saita ganshi ya duka kasa yayi sujuda yana godewa Allah…..

Dariya tashigayi sosai…..

    “Sujudush-shukur nakeyi, you won’t understand how I’m happy having a nice conversation with you”.

   “Ya isa haka toh tashi”….

Ta fada still dariya dauke akan fuskarta……

 Dagowa yayi yana kallon yanda dimples dinta yake lotsawa a yayinda take dariyar, be taba sanin tanada dimples ba sai yau, toh ta ina ze sani shida be taba ganinta tana dariya ba?…. It felt like a dream come true, yanzu addu’ar shi daya Allah ya dasa mata koda rabin son da yake mata ne, har imagining suna soyayya me zafi ya farayi……..

     ““Your beautiful laugh makes my heart melt; I can’t imagine a life without you. I love you dearly.”

Dauke kai tayi tana juya masa baya….

Dariya yayi sosai yace;

     “Wai kunya kike ji? Wayaga wifey da jin kunya”..

   “Kunya? Naaah, you’re kidding man!”….

 “This is the fatima zainab I know!”….

       “Hmmm”….

  “Whenever I see you, I feel like I’m looking at the most beautiful angel on earth. You are loved. You are wonderfully made wifey!”……

      “You’re so sweet khal!”….

Tafada murmushi dauke akan kyakkyawar fuskarta, sannan tashige part din momma da sauri…. 

Wani melting yaji zuciyarsa nayi, sai kuma ya shiga bubbuga kansa da hannunsa yana fadin;

   “Wake up khaleel! Wake up! You’re dreaming!”……

Sai kuma ya Girgiza kai yace;

      “It’s real!  Kamar fa I’m not dreaming”…..

Chan kuma saiya bita ciki……

    “Shine muna hirarmu me dadi kika gudu ko?”….

  “You talk too much, my head is aching already”….

    “Oh sorry love! Kin ki yarda muje a duba kannan naki?”…..

     “It’s not serious! Can you excuse me?”……

    “Of course yes! Take care love”……

Harya fara tafiya ta dawo dashi da fadin;

    “Ina momma?”…..

“She has travelled, kamar sun dan samu issue da daddy”…..

    “Ban tambayeka wannan ba”….

  “Allah ya baki hakuri sarauniyata, yauwa I heard you guys are starting exam tomorrow, hope you’re prepared?”……..

     “No!”…

   “Why?”….

 “Hakanan!”…..

  “No pls, let’s go get the materials, I’ll assist you muyi karatun tare”….

    “Babu inda zani!”….

Ta fada tana bata rai….. 

     “Toh let me get the material sai muyikaratun?”…..

    “Bafa zan karanta komai ba, dan Allah ka fita ka bani guri, why do you talk too much?”…..

     “Sorry, sorry, yanzu zan fita”….

Ya fada yana stammering ganin yanda ta fara zuciya daga magana kadan, kamar ba itace harda ce mishi he’s so sweet dazu ba, well koma menene shiya janyo daya sata surutu kuma yasan bataso saboda yaga ta kulashi yau…… 

Fita yayi da niyar yaje ya siyo mata handouts din koda bazatayi karatun ba kamar yanda ta fada, sannan ya kamata ya binciko mata time table dan yasan kila batasani ba…….

     Yafi awa daya yana tafiya batareda yasan inda ya dosa ba, tsabar bacin rai ko gajiya beyiba saima wani karfi daya keji na karuwan masa, burinsa kawai ya samu abinda ze buga ko zeji sanyi a ransa, haka ya taka da kafa harya karasa gidansa… Knocking ya shigayi da karfi me gadi ya taso ya bude yana fadin “waye haka?” 

     “Ubanka ne!” …..

Ya fada yana hankadashi gefe, Allah ya taimakesa beji ciwo ba, ko bi takansu Deen beyiba ya shiga ya dauko mukullin daya daga cikin motocin dake gidan ya fito ya shiga yaja ya bar gidan…… 

Driving ya shigayi recklessly kamar wanda yake a cikin maye, duk inda yabi saidai a kauce masa tsabar yanda yake sharara gudu, a haka yayita tuki har Allah ya taimakesa ya isa kano, shida be taba driving daga abuja zuwa kano ba, sai gashi bacin rai yasasa yayi be sani ba…….

           “Ya mukayi da kai akan Hamida last time?…….

Dad daya keta zazzaga masa masifa tun bayan sun hadu a parking space har suka shigo parlournsa ya tamabaya…..

      “Nace naji!”….

   “Kace kaji kamar wani sa’anka? Rashin da’ar da aka sake koya maka kenan achan? Wani kalan irresponsible man kakeson maida kanka ne? Toh a yau basai gobe ba ka tabbatar kaje kun daidaita da Hamida!”……

     “I’m not ready for marriage!”…..

   “Na gaji da jin wannan zancen banzan! Whether you’re ready or not aure saika yishi very soon! Sannan banaso kafarka ta kara takawa abuja, don’t try me!”……

     “Naji”…..

    “Karma kaji! Daidai nake dakai, now out!!!”…..

Tashi yayi ya fita yanajin kamar duka damuwar duniya akansa aka tara, Fisabilillahi mezeyi da wata Hamida? Aiko a kafa aka daura masa ita sai ya kwance kuma yafi karfin yaje gidansu su wani daidaita, ai saita raina shi ma…. 

     “Keep dreaming ba inda zanje wallahi!”….

Ya fada kamar Dad na gurin……

       Ko zama beyiba bayan ya shiga part dinshi yaji anturo kofar tare dayin sallama…..

Dagowa yayi ya kalleta yana kara daure fuska kamar itace ta gama masa masifa……

      “My son!”…..

    “Kiyiwa mijinki magana ya fita sabgata!”…..

Ya fada yana kallonta ido cikin ido…..

Sosai ta dan tsoratata da yanayin fuskarta tadai dake tace;

     “Haba kyakkyawan dana sam fuskarka bata dace da bacin rai ba, tell me what’s your problem I promise to help”……..

Shiru yayi yana kokarin saita zuciyarsa, besan ya akayi ya mata masifa ba……

      “Wai Hamida yakeso na aura!”….

    “Kai kuma bakaso?”….

    “Inyi me da ita mom! Allah ya kiyaye”……

  “Toh karka damu zan shawo maka kansa a fasa, amma wa kakeso, ko choice din hajiya fatima kakeso?”…….

    “Wai mami?”….

     “Ita!”…..

    “Bamuyi wannan maganar da ita ba, daddy ne kawai problem dina!”…

   “Are you sure?”…..

  “Yes!”…

Dan jim tayi tana tinanin kila mami batariga ta fadamasa ba amma tasan tunda dad yayi maganar toh anyi hakanne, for that it’s a good opportunity tinda besani ba, and she’ll make sure she use the opportunity wisely”…….. 

Murmushi tayi kamar ko yaushe tace;

       “Karka damu babu me maka auren dole, ka kwantar da hankalinka kaji?”……

    “Ok”…..

   “Akawo maka abinci nan ko zaka zo kaci?”….

Ta fada hoping zeci abincin dan tarasa gane meyasa baya cin abincinta, idan ta fara tinanin ko yana zarginta ne sai kuma yayi abunda zesa ta dena wannan tinanin……

      “A kawo min”…..

     “Alright, bari na kawo maka da kaina son”….

     “Okay”…..

Fita tayi daga part din dan tayi sauri ta hadomasa abincin, da kanta ta dawo ta kawo masa abincin ta kuma zauna har saida taga ya cinye tass sannan ta kwashe kwanukan ta mayar dasu kitchen dukda tarin masu aikin dake gidan, sake dawowa tayi a lokacin yana kokarin barin parlour ta tsaida shi…..

      “Zauna magana zamuyi”…..

Ta fada ba alamun wasa…..

    “Ina jinki mom”…..

  “Meyasa bakason auren Hamida?”

“Bata da qualities din da nakeso a mace”

Ya bata amsa yana gyara zama….

      “Dole fah saika auri Hamida!”……

     “Why?”….

   “Saboda zabina ce, kuma dole kamin biyayya!”….

    “Ok”…..

 “Ka amince?”….

 Murmushi yayi yace;

     “Na amince mom!”…..

Murmushin ta maida masa itama tace;

    “That’s why I’m always proud of you, yanzu dai kashirya kaje kaganta yau”……

     “I’m exhausted, saidai ko gobe”….

   “Ba matsala tinda ka amince zakaje”……

      “Yeah I need some rest now!”

      “Take care!”….

Ta fada tana fita daga parlourn…

Mikewa yayi ya shiga ciki yana jinjina wautarta, shi be taba sanin rashin wayenta yakai har haka ba, me take tinanin tayi masa da kai tsaye zatace masa dole saiya auri wata hameeda, yana sane yayi playing along don kawai ya gane abinda yake san ganewa, and alhamdulillah ya gane kuma saiya nuna mata bata da wayo…..

        “Ko ina take yanzu?”…..

Ya tambayi kansa jin tinaninta kawai is making him feel reckless, zeso ya koma abuja yanzu kodan ya nemeta amma yasan kome zeyi baze iya fita daga gidan ba yanzu dan idon dad nakan duk wani motsinsa, gwara ma ya bari da asuba idan ya fita sallah daganan ya kara gaba……

Wani dan murmushi yayi tunowa da gobe zaa fara exam a school dinsu so probably yasan dole zatabar duk inda take taje tayi exam, sannan kuma course din dayayi lecturing dinsu ne he needs to be there….. A take yayi booking flight na karfe shidan safe…..

          Sanye take cikin lilac lifaya me ratsin pusher pink, sosai take san lifaya dan tanajin dadin sasu dukda yanda takeshan kallo idan tasusu dan ba karamin kyau suke mata ba da kuma fitar da shape dinta me daukan hankali…..

      “Zaka bude motarnan mu tafi ko inyi tafiya ta!”..

Khaleel da tun dazu ya kafeta da ido ko kiftawa bayayi ya cigaba da kallonta be kulata ba, ana ganin sonda yake mata yayi yawa amma waye baze haukace akan wannan flawless creature din ba?….

     “I have seen beauty but this is a discovery? I need to see your mom, dan Allah a gurinwa kika kwaso wannan kyan?”…….

      “Hand me the key bansan shirme”……

       “I’m sorry you’ve got me hooked with your beauty!”….

Ya fada yana bude mata motar, shiga tayi shikuma ya zagaya driver seat har lokacin be dena santinta ba……

Har gaban hall din da zasuyi exam ya rakata, saida yaga tashiga sannan ya koma inda yayi parking nan kusa da hall din yana binta da addu’ar samun nasara, shiga mota yayi ya hau danne danne a waya yana jiran fitowarta.

     Sai karfe tara ya shigo school din kamar yanda ya tsara sai sun fara exam din sannan ze shigo…. Direct hall din da suke exam ya nufa dan saida yasa aka turo masa duka venues din exam dinsu……..

Tun kafin ya karasa ya hango invigilators din idonsu kur a guri daya ko zagayawa basayi kamar yanda ya kamata ace sunayi…. Ko kula da shigowarsa basuyi ba tsabar yanda suka bawa guri daya mahimmanci da kallo, kallon inda suke kallo yayi nan yayi tozali da ita looking as beautiful as ever, take ransa ya baci yaji kamar ya shake duka masu kallonta, wato da gangan suka sata a gaba saboda su kare mata kallo gasu yan iska ko? Amma bega laifinsu ba tana sane taki sa hijabi dan su kalleta, bama hijabi ba har niqab yaci ace tasa…. 

    “Get up!”….

Taji an daka mata wani mugun tsawa…..

Kin tashi tayi kuma bata dago ba, bata gansa ba amma zuciyarta tagama tabbatar da shine, tayaya zata kasa gane masifaffiyar muryarnan?”……

Kawai ji tayi ana yaga abu, da sauri ta dago ta ganshi yana yaga booklet dinta kamar wacce aka kama da examination malpractice, kasa motsi tayi tsabar shock din data shiga, an dade baa mata abinda ya mata ciwo irin wannan ba, take taji wani tsanarsa ya ninku a ranta……

Sai kuma taji ya kamo hannunta yana janta, kokarin fizge hannunta tayi amma ta kasa, janta ya cigaba dayi harya fita da ita daga class din ta daya kofar, a take hall din ya hargitse da hayaniya kamar ba exam akeyi ba kowa sai mamakin metayi yake……. 

Be saketa ba har saida ya sadata da office dinsa sannan ya wurgata kan couch ya koma ya rufe kofa ya dawo ya zauna yana kallonta……

Sosai ta galabaita dama batajin karfin jikinta kwanannan gashi kamar wacce akayiwa baki takasa zuwa asibiti…….

Daurewa tayi ta mike tana haderai ta nufi kofa da niyar ta bude ta gudu, da sauri ya taso ransa na kara baci da taurin kanta gashi zuciyarsa a kusa take dama dan idan ya fara irin wannan fushin sai yafi sati a haka…….

 Hannunsa yayi maza ya daura akan nata datake kokarin murda mukullin…..

Cikin kokarin calming kansa yace;

      “Meyasa bakyajin magana ne?!”…..

     “And why are you so wicked and stupid?!”……

Shaketa yayi yana manneta da kofar cikin masifa yace;

     “Don’t you dare abuse me again!, kika kara zagina kasheki zanyi a gurinnan in wuta!”……

Hannunta tasa tana kokarin zare nasa dake wuyarta at the same time fighting for her breath dan ji take kamar numfashinta ze dauke…….

      “Tell me who the hell are you or I kill you here! Nace WACECE KE?!”…

Kakarin amai ta farayi amma yaki sakinta, saida yaga kamar numfashinta na janyewa sannan ya zare hannunsa daga wuyanta da sauri still yana manne da ita a bakin kofar, yana sakinta ta sulale a kasa, haka shima ya bita suka zube kasa tare yana tareta akan cinyarsa…….

Hannun yasa a hancinta yaji bata numfashi, da sauri ya dagota yana jijjigata, sai a lokacin yayi realizing stupidity din dayayi, just like she said he’s indeed stupid, meya kaishi shaketa, ya akayi ya kasa controlling kansa? Yanzu idan da mutu ya zeyi da ransa?…. 

    “Dan Allah karki mutu, in kika mutu nima binki zanyi, Forgive me please, ki taimakeni ki tashi, I can’t live without you!!”…….

Yayita sambatu da karfi yanajin kamar ya fashe da kuka, tinda yake be taba feeling remorseful akan abinda yayiwa wani irin haka ba, sosai yake nadama da danasani akan abinda ya aikata, da ze iya dawoda hannun agogo baya da tabbas ya goge wannan abun daya faru, addu’a kawai yake kar wani abu yasameta if not he’ll never forgive himself…..

Da sauri ya dauketa ya fita daga office din dauke da ita a hannunsa, cikin motarsa ya sata ya nufi asibitinsa direct….

Ma’aikatan asibitin na ganinsa dauke da unconscious patient suka fito da gado da sauri, ko kulasu beyiba ya shige emergency da ita yana fadin kar kowa ya biyosa dan duka available doctors din maza ne…..

Yafi awa daya kafin ya samu ya daidaita numfashinta da yanayin bugun zuciyarta, gumi ya sharce yana godewa Allah daya taimakesa be kashe yar mutane ba da tashi ta kare yau, har lokacin kuma hankalinsa be kwanta ba, sai  yayi taking blood sample dinta yayi distributing a kowani lab dan general checkup yakeso a mata, dama beyarda da health status dinta ba musamman yawan suman dayaga tanayi a baya..

Har aka kowa masa duka result din bata farka ba, budesu yayi daya bayan daya yana karanta content din ciki yanayi yana dagowa ya kalleta………

      A hankali ta bude ido, ba wanda idonta ya sauka a ciki sai nasa, tun bayan ya gama karance duka result dinta yake tsaye a kanta yana mata kallon mamaki… Dauke idonta tayi tana kokarin tashi zaune……

      “A ina kika kwaso HIV?!”…..

Taji muryarsa ta daki kwanyarta…….

Domin samun cikakken Littafin sai ku dannan Bulun Rubutun dake kasa ko kuma hoton 👇👇

https://www.aihausanovels.com.ng/2023/01/wace-ce-ita-chapter-27-28-complete-novel.html

     

Hmmmm🤐

Back to top button