Hausa novels

Karfe A Wuta Chapter 99 By Ayshercool

99Har zai sake bin Nabila a waya, kawai ya tuna yadda ta ɗaga masa murya, ya ɓata masa rai ƙwarai da gaske, kawai ya fasa kiranta ya kira Walid a waya.Walid ya ɗaga ya ce “Mazaa ka ƙaraso ne?””Ina hanya, yarinyar nan ta kira ni ta ce Abbu yana Asibiti, ka je ka bincika mini”Cikin tashin hankali Walid ya ce “Asibiti kuma? Wane Asibitin? Nabila ce ta gaya maka?”Viper ya ce “Ban san wane asibitin ba ne, ka tambaya mini kawai ka bincika mini, idan ma mutuwa yayi kawai ka gaya mini ba wani abu””Ahh no, in sha Allah yana raye, tambeyata yana wani Asibitin?””Manta da ita, ka duba mini kawai””Ok yanzu kuwa in sha Allah”Allah ya sa yana wurin shayinsu, dan haka ya tashi ya tafi gidansu Viper, ya rasa wa zai aika gidan, Shahida ta fito hannunta riƙe da leda.Gaida Walid tayi, ya amsa. Ya ce “Ya ake ciki, mai zamani ya kirani, ya ce an kwantar da Abbu a asibiti na zo na bincika masa”Ta kalle shi ta ce “Dan Allah da gaske shi ne ya ce ka zo ka bincika masa?””Eh mana, yanzu muka gama waya da shi ma”Ta ce “Damuwar yaƙi zuwa, ya sanya Abbu ya faɗi, Abbu yana ta roƙon ya yafe masa amma yaƙi damuwa da hakan” tayi maganar tana share hawaye.”Kin ga ki daina kuka, ya gaya mini ya zo sun haɗu a gidansu jauhar, har Abbu ya buƙaci ya zo su yi magana, wai wani wuri aka tura shi a Jos, wurin ko network babu, shiyasa bai zo ba, amma wani Asibitin ne?””Can zan je yanzu, in da muke ganin likita ne” suka rankaya suka tafi, yana ta bata haƙuri.Ga mamakinsa a can suka tarar da Nabila da Sumayya, har da Murtala abokin aikin Sumayya.Suka gaisa da Nabila, cikin damuwa Nabila ta ce “Oga walid, Vi ba ya kyautawa ko kaɗan, wane irin abu yayi haka fisabilillahi?””Allah ya baku haƙuri, mun gode sosai da kulawarku a kan babanmu”Nabila ta ce “Ai ba dan shi muka yi ba, dan Allah muke yi, dan kuma ƴar uwata, ayi mutum sai zafin rai, komai ba zai yi a hankali normal kamar kowa ba”Walid ya ce “A’a fa, muna fa kawar miki da kai duk da haka, kar ki ƙure mu Barrister, ba fa haka Jauhar take yi mana ba”Nabila ta ce “Taɓ ai ita wannan, idan ana ganin ɗan aljanna a duniya sai a nunata, ina zan iya, wataran sai baƙin ciki ya kasheni. Kayi ta yi wa mutum magana, amma ya gagara responding ma, ya ƙame yana harararka”Yayi murmushi ya ce “Yanzu yaya mai jikin?””An yi masa alluran bacci ne, an ce mu jira kar wanda ya shiga sai bayan 2hours tukuna, amma jikinsa Alhamdilillah. Nima sumayya ce ta gaya mini ba shi da lafiya, sun yi waya da wannan sistern ta shi” tayi maganar tana nuna Shahida.Tun da Nabila ta fara magana Shahida take kallonta, a nan take ƙara gano bambancin Jauhar da Nabila, Jauhar ba zata taɓa reacting a hasale haka ba, komai girman laifin da ya yi mata kuwa. Wannan kuma a tsaye take, ba ta ɗaukar komai a hankali.Har mamakin yadda take faɗar maganganu a kan yayanta take yi.Viper ya sake kiran Walid a waya, “Ya mutu ne ko kuwa?””A’a lafiyarsa ƙalau, yana samun kulawa ta musamman””Walid, dan Allah kar ka ɓoye mini, ba wani abu ka gaya mini kawai, ba yau na saba ji ba” yayi maganar haɗe da wani irin wahalallen numfashi na razani.”A’a wallahi da gaske nake yi maka, muna tare da Nabila ma, ko na baka ta tabattar maka””A’a, tura mini adress ɗin, yanzu zan ƙaraso in sha Allah”Shahida dai gefe ta koma ta zauna, tana ta kallon Nabila, babu yadda za ayi ka ce ba Jauhar ba ce ba.”Haryan ƙoƙarin tantancewa ki ke yi ne?” Ta ji maganar Walid unexpected.Ta ce “Eh wallahi, haryanzu na kasa yadda, abin mamaki yake bani”Yayi murmushi ya ce “Haka ne”Sai da aka yi kusan awanni uku, sai ga Viper, tamkar an hankaɗo shi, ya yi duhu sosai da sosai, idanunsa jawur, yana zuwa Walid ya miƙe ya nufe shi.”Walin yana ina?””Yana cikin ɗaki, likitoci sun ce kar a shiga” ai take ya ture Walid, ya nufi ɗakin, ana kar ya shiga, amma ko waiwayowa bai yi ba ya shiga.Wata nurse ya taho ta ce “Ya za ku bari ya shiga, isasshen bacci ake so yayi”Walid ya ce “Dan Allah ki yi haƙuri, yanzu a kan ku hana shi shiga, duk sai ya tayar mana da hankali, ku ƙyale shi dan Allah”.Viper kuwa gaban gadon Abbu yaje ya durƙusa, ya ɗora hannunsa a kan cikinsa, ya tabattar da yana numfashi, sai dai still ya kasa yarda, gani yake kamar Abbun ya mutu ne.Ya cigaba da ta tattaɓa duk wasu sassa a jikin Abbun, domin tabattar da yana raye.Caraf ya ji Abbun ya riƙe hannunsa, ya ce “Al’amin””Na’am, sannu ya jikin naka?””Na ce ka zo, amma kaƙi zuwa, ko dai haryanzu baka yafe minin bane ba, k yi haƙuri, idan baka yafe mini ba na mutu a haka, na san sai Allah ya tambayeni, tun da kana da hakki a kaina””Dan Allah ka daina maganar nan, kaima sai ka tafi ka barni? Ba ƙin zuwa nayi ba, aiki aka tura ni wani daji can jos, shiyasa ba wai ƙi nayi ba”Ya kalli Viper ya ce “Aikin menene haka?””Zan gaya maka amma sai ka warke tukuna in sha Allah” yayi maganar yana shafa saman hannun Abbun.”Matso na rungumeka nima, nayi kewarka sosai”Viper ya gyara zamansa, ya ɗora kansa a ƙirjin Abbu. Ya ɗora hannunsa a kan sumar Viper ya ce “Lallai kana cikin maraici, da jauhar na nan ba zan ganka da wannan sumar ba, Allah ya yi mata rahama” Viper ya yi shiru ya kasa magana.”Al’amin””Na’am””Kana ganin idan muka nemi auren yar uwar jauhar za su bamu? Ina son yarinyar ita ma”Viper ya ɗago ya ce “Ka samu ka koma baccinka, zan je na yi salla”Abbu ya ce “To, ka ci abinci ma, ina ga Shahida ta kawo abinci, sauran yaran nawa duk su ci abinci, na ji daɗi yadda duk suka zo suka tsaya tare da ni, Alhaji Bashir ma bai daɗe da tafiya ba, na ji daɗi sosai da sosai.””Tom, amma ka yi shiru” ya fita.Ya tarar daga Nabila sai Walid, da Shahida, liti ma ya zo duk suna zazzaune.Yana fitowa suka fara tambayar sa, ya jikin Abbun.Fuskarsa babu walwala ya ce “Da sauƙi har ma mun yi magana, bari na je na samu wuri na yi sallar la’asar” Nabila na nan zaune, jira take yi, Alhaji mu’azzam take yi wa kwatance, zai zo ya duba Abbu.Bayan mintuna talatin, liti ya amsa waya, ya kalli Nabila ya ce “Viper ya ce ki je””Ina?””Wallahi ban sani ba, sai dai ki kira shi”Sai da ta ja lokaci kamar ba zata tashi ba, sai kuma ta tashi, tana tunanin ta ina ma za ta ganshi da zai ce ta je, me ma za ta yi masa.Tana tafe tana waige-waige, kawai ta ganshi a can wani wuri yana amsa waya, ƙarasawa tayi, ta tsaya ya gama wayar, da alama wayar ta shafi aiki ne, yayi ya kammala sannan ya waiwayo ya kalleta.Yanayin kallon da yake yi mata, sai da ta tsorata kamar zai kai mata duka, ya tsuke fuska sosai ya fuskanceta, sannan ya ce “Daga rana mai kamar irin ta yau, ko a waya, ko a zahiri idan ki ka kuma yi mini shouting, ko gaya mini duk maganar da ta zo bakinki, i will mercilessly deal with you, i am not your mate” motsa baki tayi za ta yi magana, amma ta kasa, ya juye mata ya koma mata Vipernsa sak, fuskar nan sam babu annuri.Amma ta sake tattaro jarumtarta ta ce “Ba shouting na yi maka ba, gani nayi idan ba haka nayi maka ba ba zaka zo ba, kuma…”Keep quiet malama, idan ma na zo idan ban zo ba ina ruwanki?” Ta ɗago ta kalleshi, ya sake tsareta da idonsa, dolenta tayi ƙasa da kanta.Ya nuna ta da yatsansa ya ce “This is my last warnin, idan ki ka sake zaki sha mamaki, wuce mu je” zungui-zungui tayi gaba, ya biyo bayanta, zuciyarta kamar ta fashe dan haushi, deep down kuwa a zuciyarsa kewarta yake yi, yanayin yadda tayi masa magana, da yadda ta daina kiransa ne ya ƙara tunzura shi, amma ya ji daɗin ganinta a wurin mahaifinsa da yadda ta nuna damuwarta.Tun daga nesa liti ya hango su, ya san babu arziki faɗa suka yi, ya zo ya zauna Shahida ta zuba masa abinci ta bashi.Liti sai tambayar ƙwaƙwa yakw yi wa Viper, a kan aikin me yaje yi.Suna zazzaune sai ga Alhaji mu’azzam ya zo ya duba baban Al’amin, aka yi sa’a ya ɗan sakar masa fuska, suka yi magana a kan rashin lafiyar Abbu.Har suka keɓe suka yi magana, a kan aikin da yaje yi, tare da shi Viper aka kai ɗan mama can kudancin Najeriya, in da zai karɓi nasa horon na musamman, sai dai bai kai na Al’amin tsauri da takura da kuma daɗewa ba, shi shekara guda kawai zai yi.Suka gama maganar, Kankarofi yayi musu sallama zai tafi, Nabila ta ce “Honorable dan Allah ku ajiyeni a hanya, na samu abin hawa”Kankarofi ya ce “Babu damuwa, ina motarki ne?””Ta lalace ta zama gwangwani”Ya ce “To Allah ya mayar da sabon alkhairi, amma babu risk a a hawanki public vehicles, ina masu fita da ke?””Ai na gama aikina, ba wani abu da zai same ni in sha Allah” sai ya lura kamar tana sane, basarwa yayi ya ce “Shikenan muje” yayi musu sallama amma Viper bai sake cewa komai ba.Wami abu mai zafi ya tsayawa Viper, ganin sun jera ita da Alhaji mu’zzam sun yi gaba, amma ya dake ya shanye, yayi shiru ya maze, dan idan ya ce zai tanka ɓatacciya za ayi.Yana Asibiti har dare, Liti ya ce “Boss ka koma gida, mu sai mu kwana da Abbun, ka je ka samu ka huta”Viper ya ce “Ba zan iya tafiya ba, gani nake idan na tafi komai zai iya faruwa, gara na kwana da shi kawai”.Walid ya ce “Ba gamu ba, babu abin da zai faru in sha Allah””I am sorry, ka bar ni kawai”Walid ya ce “To shikenan, na ga dare ya fara yi, bari na raka Shahida gida, sai na dawo”Viper ya ce “To a sauka lafiya”A hanya Shahida take ƙara bawa Walid labarin yadda aka kashe Abba, ya jajanta masa sosai da sosai, saboda abin gwanin ban tausayi, sa’ar da aka yi shi ne an kama yaran da suka kashe shi ɗin.Bayan ya dawo tare suka kwana su uku tare da Abba, yana kan gado, suka yi shimfiɗa a ƙasa, suna hirarrakin su ƙasa-ƙasa dan kar su takura masa, har aka jima kuma su ka yi bacci.Viper kuwa idonsa biyu, ransa a matuƙar ɓace da abin da Nabila ta yi masa, ga kuma kewarta da take ta addabar ruhinsa.Abbu kuwa kallonsu yayi, yadda suka jere su uku a ƙasa a kwance, ya sake jinjina girman ikon Allah. Dukkannin su, kowanne gidansu daban, ba su haɗa wata alaƙa ta jini ba, sai ta rashin jin su, amma sun riƙe juna da tsantsar amana, da ƙauna.Da ya motsa dukkaninsu ƙoƙarin su, su ji meye damuwarsa me za su yi masa, sai ya ji ina ma ace duka nasa ne.Da haka gari ya waye, suka takura Viper ya je gida ya yi wanka sai ya dawo su ma su tafi.Haka aka yi, ya tafi ya je yayi wanka, ya ɗan huta, ya ga message ɗin Nabila “Assalamu alaikum, ya mai jiki? Ba zan samu zuwa yau ba, daga wurin aiki zan je ganin likita, idan kuma na kammala da wuri zan zo in sha Allah, ayi masa sannu” guntun tsaki ya ja, ko arzikin gaisuwa ma bai samu daga gareta ba sai surutu.Lokacin da ya koma, Shahida ta kawo abincin rana, suna zaune a ɗakin Abbu, ya samu har ya tashi zaune ya yi wanka, ya ci abinci.”Ka dawo?””Eh ya jikin””Alhamdilillah”Shahida ta gaishe shi ya amsa, liti kamar wanda aka matsa sai cewa yayi “Wai babarku ba ta san an kwantar da Abbu bane, naga tun jiya ba ta zo ba”Shahida ta ce “Ai tun da aka kashe Yaya Abba, ita ma ba ta da lafiya, shiyasa ba ta zo ba”Walid kamar ya zabga wa Liti mari, ko ina ruwansa oho.Viper ya ce “Muhsin yakamata kuma ku je ku huta”.”Eh bari mu ci abinci tukuna, ko a gidan ka bar mana abin da zamu ci?”Viper ya harare shi, ya ce “In dawo jiya, yau kuma na hau yi muku girki””Dama can ma ai mu muke yi, bayar da order kawai ka ke yi, sai ma idan an yi kai ta cewa bai yi daɗi ba”Walid ya ce “Yaushe ma ya fara cin abincin, sai da Nabila ta shigo rayuwarsa, yanzu carryover wanda bai ci ba yake yi”. Abbu kallonsu kawai yake yi yana murmushi, yana mamakin yadda suka iya zama da Al’amin, gashi dai ba dolensu ba, amma da shi da halinsa suke iya zaune da shi. Suka ci abincin suka tashi suka fita.Viper ya ce “Shahida ta tashi ta tafi gida, tun da akwai wata mara lafiyar a gida, ba ta yi musu ba, ta tashi ta tafi.Abbu ya kalli Al’amin ya ce “Aminu yaran nan suna matuƙar ƙaunarka, sai suka ƙara shiga raina, Allah ya ƙara muku haɗin kai””Amin, amma meye ya kashe wa Shahida aure? Ina fatan ba wani rashin kyautawar tayi ba”Abbu ya girgiza kai ya ce “Nima ban san ainihin abin da yake faruwa ba sai yanzu, uwatta ce ta bawa mai kuɗi, da akwai wanda take so, ta ce ita ba shi take so ba, mai kuɗin zata aura”.”Abbu kuma ka bari?””Ya zan yi mata, ta dage tana nuna mini ‘yar ta ce, sai kwanan nan Shahidan ta same ni, wai ita ta kai shi kotu, Khul’i za su yi, ya sauwwaƙe mata, na tambayeta dalili ta ƙi faɗa, na kira shi mijin nata ya ce shi ma bai san dalilin ta ba, sai da na ritsa uwarta, sannan take gaya mini wai ba shi da lafiya, tsawon shekaru ukun da suke zaune” guntun tsaki ya ja, ya ce “Da ina nan gaskiya ba zan bari ayi wannan abin ba, yanzu shikenan ta zama bazawara””To yaya zan yi, makaranta dai nake so ta zo ta koma, gaba ɗaya tausayinta nake ji, halinta ya sha bamban da na uwatta da yar uwatta, ba yadda muka iya da ƙaddara”.Viper ya yi shiru bai sake cewa komai ba.Abbu ya sake numfasawa ya ce “Yakamata na gaya maka abin da nake son na gaya maka, kar lokaci ya ƙure mini”Al’amin ya tattara hankalinsa a kan Abbu.”Zuwa yanzu Al’amin babu wani wanda ya san kan kasuwancina sosai, duk wanda na janyo sai yayi ƙoƙarin cutar da ni. Sannan akwai gadonka na mahaifiyarka da kuma ɗan uwanka, sun zama manyan kadarori, kar karɓi abinka ka tallafi rayuwarka, kuma ina son ko bayan babu raina, ka cigaba da jujjuya harkar kasuwancin nan, kar abun da zan bar maka ya ƙare ba tare da ka tsaya da ƙafarka ba”Viper ya gyara zamansa ya ce “Babu in da zaka mutu ka je”Abbu ya yi murmushi ya ce “Faɗa kawai ka ke kaima”Ya rausayar da kai ya ce “Abbu already ina aiki, ni ba zan iya kasuwanci ba””Aikin me?””Sojoji nake yi wa aiki, ba zan iya haɗawa ba, ko zan haɗa ma, sai dai wani ya riƙe mini, wasu alfarma nake nema ka yi mini”Cikin sauri Abbu ya ce “Na menene?””Na farko, ina so ka taimaka ka jagoranci Abdallah, liti ka mayar da shi wurin mahaifinsa, a nema masa afuwa, dan na san nine silar barinsa gida baki daya, ko ba ni bane, na taka muhimmiyar rawa a hakan.Abu na gaba kuma, a yanzu Walid ba shi da kowa sai Allah sai ni, maraya ne, yan uwansa ba sa ta tashi, duk masu ƙaramin ƙarfi ne. Ina roƙonka ka sanya mini shi a harkar kasuwancinka, ka bashi babban gurbi, sannan ka aura masa Shahida” shiru Abbu yayi yana kallon Viper.Ya cigaba da cewa “Na san zaka ga abin wani iri, amma bana zaɓen tumun dare, daga ni har su muna ta ƙoƙarin gyara kura-kuranmu, mu sake sabuwar rayuwa ne. Kuma Walid mutum ne mai amana, ba zai taɓa ci maka amana ba, duk rintsi duk wahala, Walid ba ya cin amana, ni na yarda idan ma ba zaka saka shi a kan naka kasuwancin ba, ka bashi gidana ɗaya, a sayar da sauran kayana, a koya masa harkar kasuwancin katakon, sannan ka aura masa Shahida. Ba kuma dan na cutar da ita ko rayuwarta ba, zan iya yi maka rantsuwa da Allah, ko Walid ba shi da komai, Shahida ba zata wahala ba, ina ƙara tabattar maka da mai amana ne. Shi liti shagon shayinmu yake so, ya ce ko na mutu shi zai gajeta tun da shi ne ya rayata ba ni ba, ya je ya ƙarata da ita, Walid ko duk wani abu da na gada za a ƙarar, dan Allah a bashi ba zan iya biyan bawan Allah nan ba”.Abba ya jinjina kai ya ce “Na ga alama, shikenan babu damuwa idan ma ya fi hakan za ayi masa, sai dai ita Shahidan ka yi magana da ita idan ta amince, ka san halin mata kar ayi abu, azo a ji kunya”Viper ya ce “In sha Allah ba za a ji kunya ba, Walid mutum ne mai haƙuri da kawaici, kuma mai amana””To shikenan, ba zan taɓa maka kayan gadonka ba, amma zan ɗauke shi a kasuwa, zan bashi auren Shahida muddin ta amince, ni ma na shaida ɗawainiyar da yake yi da kai, Allah ya tabattar mana da alkhairi”.Likita ne ya shigo yayi musu bayanin jikin Abbu da sauƙi, jininsa ne ya hau sosai, kuma an samu ya sauka, zuwa washegari za a iya sallamarsa.Maƙwabta da abokanan kasuwancin Abbu suna ta zuwa duba Abbu, suna ta so su magantu da ganinsa tare da Viper, ya ƙara girma, da kwarjini sannan akwai alamun ƙarin nutsuwa a tattare da shi.*****Bunkure ta kasa zaune ta kasa tsaye, saboda rashin sanin abin yi, dan tun bayan da Nabila ta damƙa mata kundin ƙorafe-ƙorafen da zata kai ma’aikatar Shari’a a kanta, ta rasa yadda zata yi. Gashi ma’aikatar shari’ar duk waɗanda ta sani yanzu ba sa nan, an yi musu canjin wurin aiki, tana ta kasa kunne ta ji ta ina za a nemeta. Tsananin damuwa ya sanya ko baccin kirki ba ta iya yi, sai ta sha tayi mankas tukuna.Duk da abokan aikinta, na ta ƙarfafa mata gwiwa, da nuna mata cewa za ta iya fuskantar ƙalubalen da yake gabanta. Ga mutane duk sun dawo daga rakiyar Foundation ɗin ta, kuɗaɗen da suke tallafawa ƙungiyar domin taimakon mutane, duk sun daina saboda sun gano cewa cuta ce.A dalilin Nabila, mutane da yawa suka samu ‘yancin yin magana, tare da sanarwa duniya tallafin da aka nema da sunansu, ko aka basu, ana dawowa a karɓa, wasu kuma ma ba a basu.Sosai social media da gidajen rediyo, maganar bunkure ta yamutsa hazo, ko ina zancen ake yi.****Washegari aka sallami Abbu daga asibiti, suka koma gida.Shahida na ɗakinta, tana kwance tana karatun Alqur’ani, Viper ya ƙwanƙwasa mata ƙofa, ta yi masa iznin shiga, ya shiga ya zauna, ya dube ta ya ce “Kin gama idda ko?”Ta jinjina masa kai, ba tare da ta ɗago ba.”Magana nake son mu yi, shawara ce, ba dole zan yi miki ba, zaki iya cewa a’a idan abin bai yi miki ba”Ta jinjina masa kai.”Na san zaki ji abin wani banbarakwai, amma ba zan yi miki zaɓen tumun dare ba, kuma ba dole zan yi miki ba, ina son Abbu ya haɗa aurenki da Muhsin ne, abokina Walid. Na san zaki yi mamaki, ko ki ji babu daɗi, saboda duba da yanayin mummunar rayuwar da muka yi a baya. Dama kowane mutum tara yake bai cika goma ba, duk wani halin kirki na mutum, sai an tarar da shi da wani hali da ba a so, kuma yanzu muna ta ƙoƙarin gyara ɓarnar da muka yi ne a baya. Ina baki tabbacin Muhsin mutumin kirki ne, kuma zaki ji daɗin zama da shi, ya fi ni nagarta da halacci, da zunzurutun haƙuri. Kema kuma na san mutuniyar kirki ce, a dalilinki ina fatan ya ƙara shiryuwa, amma ina baki tabbacin zaki iya dukan ƙirji a gaba, ki ce kin yi dacen mijin aure. Amma ba dole nake yi miki ba, na tuntuɓe ki ne dai da maganar, kafin nayi masa, idan kuma ba kya son sa babu wani abu shikenan shawara ce”.Sai da Shahida ta ji dummm, tabbas Walid ma tsohon ɗan sara suka ne, kuma bata san shi da wata sana’a ba, amma kwana biyun nan da take zuwa asibiti, suka ɗan zauna tare, akwai nutsuwa da dattaku a tattare da shi, kuma karo na farko kenan, da Al’amin ya yi ƙoƙarin yin wani abu a kan rayuwarta, ta san ba zai cutar da ita ba, dan haka ta numfasa ta ce “To yaya duk yadda ka yi dai-dai ne, in dai ka amince, nima na yarda”.”A’a kar ki yi mini haka, ki gaya mini abin da yake zuciyarki, ko kuma dai na fara turo shi ya nemi yardar ki da kansa, amma magana ta domin Allah bamu iya soyayya irin wadda ku ke so ba, sai dai ki koya masa, kin san mazaje we are always serious” yayi maganar yana ɗan murmushi.Ita ma murmushin ta yi tana sunkuyar da kai.Nan ya cigaba da koɗa mata nagartar Walid, da ƙoƙarin da ya din ga yi wa rayuwarsa.Za ta iya cewa, ba ta taɓa zama sun yi hirar kirki mai tsawo da yayan nata ba sai yau.Da daddare ya bar gidan, ya tafi can gidan da suke zama, Walid suna ta faɗa da liti, a kan liti yayi musu wanki, ya ce ba zai yi ba, ya saka Viper ya dawo da ɗan mama yayi, tun da ya fi jin maganar sa, dama ɗan mama ne yake yi musu.Viper ya ce “Rabu da shi mai laya, kai ka kusa shiga daga ciki, a din ga haɗa kayan ka masu datti a bayar wanki, ka bar Liti””Wace zata aure shi, bai iya komai ba sai saka aiki, daga kai har shi?”Viper ya ce “Seriously, Walid Abbu zai baka auren Shahida, abin da ya rage maka kawai ka nemi yardarta” waro ido Walid yayi ya ce “Wane Walid ɗin?”Liti ya yi shewa ya ce “Sai dai kai maigida, Allah ya ja zamaninka ka daɗe ka yi ƙarko irin na dabino, Allah dai ya saka da alkhairi”Walid ya ce “Kai fa mahaukaci ne wasu lokutan, uban waye zai bamu aure a haka? Mai zamani ka daina wannan wasan”Viper ya kwanta ya ce “Ba wasa nake yi ba, da gaske nake, ka nemi soyayyarta kawai, aure zan yi muku, Abbu ma ya san zancen. Kai kuma liti sai dai ka nemo da kanka, tun da na san kai ba gwaninta ake yi maka ba”Walid ya ce “Dan Allah a daina wannan wasan, wai waye ma zai bani wani aure? Dan Allah ka bari ta samu mutumin kirki ta aura”Viper ya tashi zaune, ya dafa kafaɗar Walid ya ce “Kai ma mutumin kirki ne, shiyasa ba zan so wata ta samu ba, alhalin ga ƙanwata, ku daidaita kawai sai da safe” yana gama maganar ya kwanta.Walid ya zauna kamar soko yana rarraba ido, Liti kuwa dariya ya din ga tuntsirawa, saboda har gara Viper ma da Walid, dan shi kamar ma tsoron mata yake ji, shi ko da wasa bai taɓa tare budurwa ba.Liti ya din ga tsokanarsa, yayi masa banza ya kwanta, hango Shahida yake yi, yarinya nutsatsiya yar gayu, wai kuma ta aure shi shi dai abin bai yi masa tsari ba.Washegari za su je duba Abbu da yamma, kamar ya fasa zuwa, saboda gaba ɗaya kunya ce ta kama shi.Kasancewar Viper ya riga su tafiya, ya sanar wa Shahida, su Walid za su zo duba Abbu, dan haka ta shirya, za su yi magana ita da Walid ɗin.Duk abin nan, rahila ba ta san me ake shiryawa ba.Sai bayan la’asar, su Walid suka zo, duk yadda yake ɗan sakin jiki da Abbu su yi hira kasa yayi, ya din ga mutsu-mutsu, kamar ya nutse a ƙasa, liti yana ankare da shi, kamar ya yi dariya.Liti ya ce zai je ya dawo, ya fita ya yi nasa wuri, bayan sun yi wa Abbu sallama, a ƙofar gida Viper ya ce “Na yi mata magana, za ta fito ku yi magana, mu haɗe a jungle””Dan Allah Viper ka ce da wasa ka ke yi, ni wallahi ban san me zan ce mata ba, wallahi kunya nake ji””Malam yakamata ka girma, ka yi mata tatsuniya if you like” zai sake magana, suka yi ido huɗu da Shahida, ta fito cikin doguwar rigar abaya maroon.Viper ya yi gaba yana murmushi, Walid ya ɗan diririce.Ta ƙaraso tayi masa sallama ya amsa, ta saci kallonsa, dogo ne shi ma, sai dai bai kai Viper jiki da tsawo ba, kuma yana da haske sosai, sai dai laɓɓansa baƙi ƙirin, idanunsa kuma jajaye, yana da dogon hanci da gemu kaɗan ba mai yawa ba.”Sannu ya jikin Abbu?””Da sauƙi Alhamdilillah””Amm na san wataƙila mai zamani ne ya takura miki, idan ba kya so na, ki rabu da shi kawai, Allah ya zaɓa miki miji nagari, rigimarsa ce kawai ta saka ya ce wai zai aura mini ke” yadda duk yake a rikice ne ya sanyata murmushi ta ce “Yaya Muhsin, mu yi addu’a mana, bamu san me Allah ya ɓoye ba, mu nemi zaɓin Allah, in dai nima zaka kula da ni, ka din ga lallaɓa ni kamar yadda ka ke yi masa ai ba wani abu” sunkuyar da kai ya yi yana murmushi, sai dai kamar ya zuba da gudu dan kunya. Bai fi mintuna goma ba, yayi mata sallama.Da ya koma can gidan da suke, kamar wanda ya aikata zunubi, liti ya saka shi a gaba, ko murmushi yayi, sai ya ce tunanin Shahida yake yi, ya hana shi sakat.Da daddare Shahida ta kira Viper, ta tambaye shi ya suka je gida. Maimakon ya bata amsa, sai ya miƙa wa Walid wayar.Tayi masa ya yaje gida, sannan ya ce zai ɗauki lambarta a wurin Viper.Washegari da sassafe, Viper ya shirya ya fice ya bar su, dan yai zai koma wurin likitan ƙwaƙwalwa, kuma yana son ya ga Nabila.***Ƙarfe tara na safe, Nabila ta fito falon madam Halima, hannunta riƙe da jakarta, da court ɗin ta, kawai ta ga Viper a falo, suna magana da Madam.”Mummy good morning””Morning sweetheart, kin fito?””Eh, Good morning” tayi maganar tana kallon in da Viper yake, bai amsa ba, ya ci gaba da magana da Madam.Kitchen ta nufa, kusan mintuna biyar, madam ta tashi ta shiga ɗakinta, Viper ya bi bayan Nabila.Sai da ta tsorata da ganinsa unexpected.Wuri-wuri ta yi da ido tana kallonsa.Ya sauke ajiyar zuciya ya yi ya ce “Abin da ki ka yi mana kina ganin kin kyauta ko? Nayi tafiya mai hatsari, ya na je ya na dawo, bai dame ki ba? Kin yi mini laifi amma ba ki iya bani haƙuri ba, yau zamu koma asibiti you don’t even care to call me. And a gabana ki ka bi kankarofi, duk dan ki tura mini takaici”.Tayi shiru ta ɗan kalle shi ta ce “Ba faɗa ka ke yi mini ba, komai ka yi ta hantarata”Ya ce “Ke ki ke yin abin da zan hantarekin ai. Akwai muhimman batutuwa da yakamata muyi discussing, kawai kina wani fushi mara dalili.Ana ta matsa mini lamba, za ayi posting ɗina wurin aiki, da zarar na kammala aikin da nake yi a kan Indabo, ina son ayi aurenmu dai-dai lokacin da zan tafi aiki””Kai da wa?””Ni da waye a nan wurin?” Yayi maganar yana tsareta da idanunsa.”Allah ya baka madadin matarka da ka rasa, ba zan iya aurenka ba Vi, i fulfill my work on you, amma mu bar wannan maganar Please”Sai da ya nazarceta sannan ya ce “Ƙarya ki ke yi mini da ki ka ce ki na so na kenan?”Ta ɗan ja da baya, saboda tsoron yadda idanunsa suka fara sauyawa ta ce “Ko ma ya ne, kai ka fara discouraging ɗina, a lokacin da ka yi fatali da tayina, ka ce mini ba wannan maganar, bayan jauhar baka kallon kowace mace. Nima kuma na gamsu da hakan ba zan iya auren mijin ‘yar uwata ba. Amma Alhamdilillah na cimma burina a kanka, tun da ka dawo yadda take fata kafin ta mutu”.”Ba kya so na kenan? Ba zaki aure ni ba?” Ta jinjina masa kai, tana kawar da kanta gefe alamar eh.Juyawa ya yi, ya fara takawa, wayarsa ta fara ringing, ya cirota ya saka a kunnensa ya ce “Na’am”A razane ya ce “What Walid ɗin? How?”

Ayshercool 08081012143

Back to top button