Uncategorized

Abban Sojoji Page 50 Book 2 Complete Hausa Novel

 

“`The father Of Soldiers“`

 

Story &  Written 

       By 

      Hafsat Bature

 _💋Boss Bature💋_

*SANARWA SANARWA*💃💃💃💃

*ME TAKEN NA AMARYA HUTAA$$*

*MUNA FARIN CIKIN SANAR DAKU CEWA MUNA BADA HAYAR KAYAN AMARYA(WEDDING GOWN), KAYAN BRIDAL SHOWER, KAYAN BIRTHDAY PARTY, KAYAN FITAR SUNA, SANNAN MUNA BADA HEAD AND SHOULDER, MUNA DA POSS, MUNA ALKYABBAR KAI AMARYA KO TARON WALIMAR SAUKA, MUNA DA KAYAN FULANI FARARE NA YARA DANA MANYA MUNA DA NA AMARYA BLUE BLACK, SANNAN MUNA GYARAN JIKIN AMARYA DA UWARGIDA CIKIN KWANA UKU CAKAL ZAKIGA KIN KOMA TAURARUWA MAI WALWALI.  MUNAYIN TURARUKAN WUTA DA HUMRA DA KOLACCAR, KOWANNE KALA KIKE BUKATA AKWAI CIKIN FARASHI MAI SAUKI.*

*LOCATION KANO*

08062073990

🤍💖❤️

dakatar da abra hayaam tayi tare da cewa”ki rabu da ita,wahalar tayi yawa just for to day ta huta,tunda bata da lafiya,” sam ba haka taso ba,bata ji daɗi da Hayaam ta hanata hukunta amal ba,a fusace ta fuce daga ɗakin tana huci

Shiga ciki hayaam tayi tare da samun wuri daga gefen katifar ta zauna,jin muryar Amal tana sambatu  na raɗaɗin ciwo yasa ta kasa kunne tana sauraronta,

   “Ina jin cewa bazan rayu ba,dan Allah ku kaini wurin auntyna,inaso naganta kafin na bar duniya,”

   dariya Hayaam tayi tare da cewa”aikuwa dae ba zaki ta6a ganinta ba adae nan duniyar, ae kin ɗaura aure da wahala tunda kika bari aka haifoki acikin gidan nan,” tayi maganar tana ƙarashe dariyarta,

  Amal kuwa fashewa tayi da kuka mai cin rai, 

  tsawa hayaam ta daka mata tare da cewa”yi mun shiru, kuka baya maganin komai sai ma ya ƙara jaza maki wani ciwon,” shiru Amal tayi tana shassheƙar kuka ƙasa ƙasa

Shigowa abra ta sake yi hannun ta ɗauke da wayar amani iphone 13 sai faman ruri take yi,miƙa mata wayar tayi tare da cewa”Sofwan ne ke kiranki,”

 “ɗan wahala,” ta fadi tare da kai hannu ta amshi wayar,juyawa abra tayi ta kalli Amal dake ƙumshe cikin bargo,guntun tsoki taja tare da cewa”salon ki sakarwa mutane miyan bacci asaman katifarsu,sai kin shanye shi don ubanki,” ta ƙarasa maganar tare da kama hanya ta fuce daga ɗakin,

Kara wayar tayi a kunnanta bayan tayi picking call ɗin,magana suka shiga yi dashi akan tafiyarta,duk wulaƙancin da tayi mashi hakan baisa ya rabu da ita ba, sai ma kiranta da yayi akan cewa gobe yanaso su tafi tare yakaita abujan,

Sun jima suna waya kafin daga bisa ni su kayi sallama,

tana ƙoƙarin ajiye wayar wani kiran ya sake shigowa,tsoki ta ɗanja tare da cewa”wani jarababben ne kuma yake kira na”!?

   Duba screen ɗin wayar tayi Sunan AMANI ne ya bayyana,ɗan juyawa tayi ta saci kallon Amal dake ƙumshe cikin bargo alamu sun nuna cewa bacci yayi awon gaba da ita,hakan ne yasa ta ɗaga kiran tare da karawa a kunnanta tare da yin sallama,

  On the other hand amani tace”wa’alaikum salam,hayam y kk ya gida yasu mammy”?

   yatsina fuska tayi tare da cewa”duk suna lafiya,”

   Amani tace”labarine ya same ni daga wurin aunty laila nacewa zaki koma gidansu Abbas da zama,sam abun bai dace ba wannan abun kunyar har ina?menene alaƙarmu dasu da har zaki koma gidan surukan mu da zama?amatsayin ƙanwar matar yayansu! 

Jin wannan maganar ta Amani yasa ran hayaam 6aci,miƙewa tayi daga zaunen da take saboda tsiwa tamkar zata fasa screen ɗin wayar haka tashiga cewa”Ki tsaya iya matsayinki AMANI!!babu ruwanki dani, iya sa idone kawai naki  kada kice zakiyi mun shisshigi acikin lamarina! Ni ba kamar Aunty laila bace data saba jan ki ajiki har tayi maki sanadin auren Abbas,kina magana ne da HAYAAM!!!yakama ki iya bakin ki!!!!

  jin yarda hayaam ke zazzaga mata rashin mutunci yasa tayi rejecting kiran,

  tsoki hayaam ta saki tare da cewa”matsoraciyar banza!!ae banso kika kashe kiran ba,so nayi na sauke maki kwandon rashin mutunci shashasha kawai,” rai a6ace ta ƙarasa yin maganar tare da yin wurgi da wayar saman katifar,kama hanyar fita ɗakin tayi domin taje ta sanarwa mamaynsu yarda su kayi da Amanin,

 fitarta ke da wuya, Amal ta buɗe idanunta  waɗanda suka kumbura jawur saboda raɗaɗin ciwo, ta samu bacci amma tsiwar hayaam ce tafarkar da ita, gaba ɗaya duk wayar da su kayi da amani tana ji a kunnanta,saboda taji lokacin da hayaam ta ambaci sunan Amani,

Domin Sauke Littafin Sai Ku Dannan inda aka saka Download Now!

   A hankali ta sanya hannunta tare da yaye bargon,a galabaice ta ɗan tashi zaune, hannu takai tare da ɗaukar wayar hayaam wadda tayi wurgi da ita asaman katifar kuma cikin sa’a wayar bata kai ga shiga security ba,

   jiki na kerma ta shiga wurin kiran,sai ga sunan amani ya bayyana a list ɗin farko da tayi waya dasu,cikin sauri Amal ta buɗo numbarta, zuba ma numbar ido tayi tana tunanin yarda zata ɗauki numbar,babu wurin da zatayi copying dinta,tuni hawaye sun soma zarya a fuskanta, wannan shi ake ce ma ga ƙoshi ga kwannan yunwa,

  runtse idonta tayi tare da buɗe su  akan screen ɗin wayar,nan take taji cewa zata iya haddace numbar akanta,muddin taci gaba da bitarta akanta, a hankali take ƙarewa numbers ɗin kallo tana naɗarsu akanta,motsin mutun taji alamar an tunkaro ɗakin cikin sauri  Amal ta fita daga wurin numbar amanin ta danna power ɗin wayar tayi duhu sannan ta ajiyeta,da hanzari tashige cikin bargon ta lullu6e dukkan jikinta, Hayaam ce tashigo  kai tsaye ta ƙarasa inda wayar take tasanya hannu ta ɗauka tare da fucewa daga ɗakin,

  ajiyar zuciya Amal tashiga saukewa,har lokacin tana cigaba da bitar numbar amani akanta,

*******************

Bacci sosai sehrish tasha, har wuraren ƙarfe biyar da wani abu babu alamun zata farka kamar matatta, kusan sau huɗu azmee na leƙowa don taga kota farka saboda ta lallashe ta akan abunda ya faru amma duk in tashigo sai ta same ta tana ta faman shan bacci, 

Ƙarar jiniyar motocinsu ce tasa sehrish farkawa a gigice, fuskar nan tayi jaga-jaga da ita saboda kukan da tasha,ko da ta farka zuciyarta nata faman bugawa, a kasalance ta tashi zaune saman gadon tana faman sauke ajiyar zuciya, idonta takai kan agogon bangon dake manne, hankalinta ba ƙaramin tashi yayi ba ganin cewa har lokacin sallar magrib yayi, gashi ba tayi la’asar ba, cikin sauri ta sauko daga saman gadon ta wuce cikin toilet donta ɗaura alwala,

Yau da wuri suka dawo, Abbansu tare da marshal Omar da kuma Sgr sai kanal Yousouf, a nan main palour ɗin suka rarrabu, Abbansu tare da kanal yousouf suka wuce bedroom ɗinsu dake a nan down stairs, Omar da Rafayet atare suka haye upstairs, 

Tuni azmee ta kammala jera masu dinner ɗinsu a dining, duk anan suka hallara suka ci abincin, banda sgr da bai fito ba, bayan sun kammala ita tashiga kwashe warmers din da sauran tarkacen da sukayi amfani dashi tana kaiwa kitchen, ganin tana ta faman ɗawainiya ita kaɗae ba sehrish yasa junaid kama mata kayan suna kaiwa kitchen atare ba ƙaramin daɗin hakan taji ba,barin shi tayi a cikin  kitchen ɗin ita kuma ta wuce don ta gyara masu  dining area ɗin, kafin ta dawo har junaid ya kammala yin wanke wanken kayan da sukayi amfani dashi, tare da gyara kitchen ɗin tsaf tamkar ba’ayi amfani dashi ba,

   tsayawa tayi tana kallon shi yana ƙoƙarin haɗama sehrish cornflakes acikin  kofi,

  Juyowa yayi ya kalle ta tare da cewa”aunty azmee irin wannan kallo haka”?

 Murmushi tayi tare da cewa”junaid kai na musamman ne,kana bani mamaki yanzu kai da kanka kayi wanke wanken nan?kuma ka gyara kitchen ɗin nan?

 Murmushi yayi tare da cewa “menene aciki aunty azmee?nifa ba aikin da bazan iya yi ba,kuma aiyukan mata suna burge ni sosai, naji ma ina shawa’ar inga ina wanke wanke girki da shara,”

   dariya sosai azmee tayi tana girgiza kai tace”gsky baka da dama junaid, koda yake abune mai kyau ka koya,yana da amfani hakan saboda wata rana zaka taimaki matarka ne da wasu aiyukan cikin gidan,Ko ba haka ba?” ta tambaya tana kallon shi,.  

  ɗaga mata kai yayi alamar eh, sannan yace”aunty azmee ki tayani da addu’a Allah ya cikamin burina,inaso nayi aure very soon insha Allah end of this year…..’ kasa ƙarasa maganar yayi ganin yarda Azmee ta saki baki galala tana kallon shi,

  fashewa da dariya yayi a lokacin har ya kammala haɗa ma sehrish cornflakes ɗin, 

  “Joking aside pls faɗamun gaskiya amma dae wasa kake mun ko”? 

  girgiza mata kai yayi alamar a’a sannan yace”just keep praying for me, insha Allah soon i wll get marriage,” yana faɗin hakan ya kama hanyar fucewa daga kitchen ɗin hannun  shi ɗauke da Cup sai faman tiriri yake,

Domin Sauke Littafin Sai Ku Dannan inda aka saka Download Now!

  shiru azmee tayi tana kallon bayanshi har ya 6ace mata, lamarin ya ɗaure mata kai tabbas tasan halin junaid tunda harya iya furta mata aure yakeso to kuwa fa auren zaiyi dagaske, kuma duk abunda ya nuna yanaso sai abbansu ya mara mashi baya,

 “Ashe zamu sha biki,” ta faɗi da dariya a fuskarta, 

   Knocking kopar ɗakin sehrish ya shiga yi, a lokacin har wani baccin ya soma ƙoƙarin ɗaukarta asaman sallayar,tana jin bugun ƙopar a firgice ta tashi tana faɗin “Waye”!

   daga waje junaid yace”Mijinki ne insha Allah,” ita kanta batasan lokacin da tasaki murmushi ba,

  “Ka shigo ciki,” ta bashi amsa, tura kopar yayi tare da sa kai yashiga ciki yana faman zabga mata murmushin nan nashi, wuri yasamu kusa da ita anan ƙasa ya lankwashe ƙafarsa ya zauna tare da miƙa mata cup ɗin yace”nasan zaki buƙaci wannan,haɗine na musamman daga mijinki insha Allah,”

 fashewa da dariya tayi tana kallon shi, kafin ta zuro hannayenta daga cikin hijabin jikinta ta kar6a, jikinta har rawa yake yi wurin ɗaukar spoon ɗin dake aciki tashiga ɗebowa tana kaiwa bakinta, ba ƙaramin daɗi yayi mata ba,

  Tun tana sha da cokali har ta tsame cokalin daga cikin kofin ta miƙa mashi tare da cewa”ruƙe mun,” hannu yasa ya kar6a, kafa cup ɗin tayi abakinta tashiga kwankwaɗarshi harta shanye duka,

 tausayi ta bashi saboda ya lura ba ƙaramar yunwa take ji ba, cikin sanyin murya yace”nasan kina jin yunwa sosai,bari naje na kawo maki dinner ɗinki,” yayi maganar tare da yunkurawa zai miƙe cikin sauri tace”a’a nagode da wannan ma,ba yunwa bace damuwata ba, abunda ke damu na shine Har yanzu aunty azmee fushi take dani”? fuskarta ɗauke da damuwa tayi maganar,

   “Kada kisa damuwa aranki, nayi ma aunty azmee magana kuma ta fahimce ki,tun ɗazu ma take ta son tayi magana dake,” 

  Cike da farin ciki tace”dagaske Aunty azmee bata fushi dani kuma nema na take”?

   jinjina mata kai yayi alamar eh, cikin sauri ta miƙe tana naɗe dardumar don taje ta ganta, 

   ɗaukar cup din da ta ajiye yayi sannan yayi mata sallama ya fuce daga ɗakin,

    cire hajib ɗin tayi, sannan ta ɗauko mayafi mai girma ta rufe jikinta dashi, buɗe ƙopan tayi sannan ta fito tare da wuce wa ɗakin azmeen, kwankwasa mata ƙopa tayi, a lokacin azmee bata jima da kammala salla ba, 

  tasowa tayi tare da sanya hannu ta buɗe mata ƙopan, jikinta na sanye da dogon hijabi hannunta na ruƙe da cazbaha,

   Zuba ma sehrish ido tayi tana kallonta, cikin en ina tace”Aunty azmee dama junaid ne yace kina son gani na,” ta ƙarasa maganar tana sunnar dakai cike da fargabar amsar da Azmeen zata bata,

  murmushi azmee tayi tare da cewa”hakane tun ɗazun nake ta son in yi maki magana amma duk in nazo saina same ki kina bacci,” jinjina kai sehrish tayi sannan tace”nasan na 6ata maki rai aunty azmee, ki yafe mun,” 

  hannu azmee tasa tare da shafa gefen fuskarta tace”just forget about the past komai ya wuce ki manta kawai, yanzu ma nake shirin zuwa in shirya maki abinci don nasan kina jin yunwa sosai,

  Murmushi sehrish tayi ba ƙaramin kwanciyar hankali tasamu ba, 

     Sannan tace”bari na barki  ki huta nasan kinyi aiki sosai kin gaji,banji daɗi ba ɗazun da kika hanani tayaki aiki,” cikin sanyin murya ta ƙarasa maganar,

   Azmee tace”ki manta da wannan, yanzu kije ki haɗa abincin ki ci,” amsa mata tayi da toh,sannan ta juya zata fita,

Muryar azmee ce ta sake katse ta da cewa”Au na manta ban sanar dake ba, babban yayan ku fa ya dawo, yau da wuri suka shigo, shi kaɗae ne ma ya rage bai ci abincin shi ba, ki fara kai mashi pls,”

  Amsa mata tayi da toh sannan tasa kai ta fuce daga ɗakin nata,

  *SGR*

gaba ɗaya hankalin shi na akan Laptop dinsa da yake dannawa, yana a hakimce saman royal sofa mai mazaunin mutun biyu, jikin shi na sanye da kimono robe ta cotton,green colour jikinta akwai zane zane masu kyan gaske, rigar bata rufe faffaɗan ƙijinshi ba,hakan ba ƙaramin kyau ya ƙara mashi ba,ya ɗaure igiyar rigar adai dae saitin shafafen cikin sa, a natse yake danna laptop din da zira ziran yatsun hannun shi, ƙamshi ta ko’ina 

  da sallama sehrish  ta shiga falon nashi, batare da ya ɗago ba ya amsa mata sallamar,

    Shiga ciki tayi hannunta na ɗauke da ƙaramin tray mai ɗauke da fruits tare da coffee, 

  koda ta ƙarasa dab dashi murya na rawa tace”sannu  da aiki,fatan kana lafiya,” 

 “Alhmdllh,” ya amsa mata har time ɗin bai ɗago ba, ajiye mashi tray ɗin tayi daga gefen laptop ɗinsa, sannan tace”kana buƙatar wani abu”? hannu yasa ya ɗauki cup of coffee ɗin yakai bakinsa ya ɗan kur6a, janye shi yayi daga bakin shi sannan anatse yace”na manta phone ɗina asaman pillow a ɗaukomin ita,” juyawa sehrish tayi da sauri zata kama hanyar zuwa bedroom ɗin nashi kamar daga sama taji gaba ɗaya mayafin jikinta ya sulale ƙasa daga jikinta, cikin sauri ta juya tare da kai hannu zata ɗauki mayafin daya faɗi ƙasa, ganin ƙafar sgr tayi asaman mayafin ya take shi da farar ƙafarshi, kasa ɗaukar mayafin tayi saboda fargabar da tashi ga, ranta ne ya bata cewa ba dagangan yayi hakan ba, da alama baisan ya take mata mayafin ba, 

 A ɗan tsorace tace”mayafi na” batare da ya ɗago ya kalle ta ba yace “ina Sane,” jiki asanyaye ta juya tare da nufar ɗakin nashi, tsoranta kar ace alluran nan ta jiya bata sake shi ba, 

  faɗawa cikin ɗakin nashi tayi tare da nufar saman pillow ɗinsa wayar na ajiye asama,hannu takai zata ɗauki wayar kwatsam taji motsin mutun abayanta hakan ya sanyata juyowa a firgice gaba ɗaya sumar kanta ta watso harta gaban fuskarta, tsananin tsoro ne yakamata ganin mutumin da tabaro yana shan coffee tsaye agabanta, a wani irin yanayi yake bin jikinta da kallo tundaga kan ƙafarta har izuwa saman ƙirjinta, ganin haka yasa sehrish ta soma ja da baya a tsananin tsorace saboda tunawa da abunda ya faru jiya atsakaninsu hakan na nufin cewa Allurar bata sake shi bane, har yanzu akwai saura ajikin shi, 

Domin Sauke Littafin Sai Ku Dannan inda aka saka Download Now!

   tuni zufa tasoma tsatstsafo mata a fuskarta, takawa sgr yayi yana matsawa kusa da ita, ja da bayan da zata ƙara yi ke da wuya , gaba ɗaya ta faɗa asaman gadon shi, bin ta saman gadon yayi gadan gadan ya tunkareta, hakan yasa ta fashe da matsanancin kuka atsorace ta dinga girgiza mashi kai tana cewa”wlh bani bace na ɗauko allurar ba ! Bani ita akayi….ba zan iya cutar dakai ba…….!!” sai faman sambatu takeyi ita kanta batasan me take cewa ba saboda ya ƙureta sosai ta runtse idanunta zuciyarta nata faman harbawa, sam batasan cewa sgr yana cikin hayyacin shi ba,da gangan yayi mata haka saboda akwai abunda yakeson ganowa game da daren jiya da kuma abubuwan da ya gani na canji a bedroom ɗinshi da kuma body ɗinshi, yasan cewa itace last person daya kasance tare da ita, 

     jin shiru baice komai ba yasa ta ɗan buɗe idonta, ba komai yake kallo ba face doguwar sumar kanta, sai yanzu ya gane inda ya samu siraran gashi guda uku masu tsayi, hakan na nufin gashin kan Yarinyar ne ya tsinta asaman gadon shi ɗazu da safe, acikin sambatun da tayi mashi ta ambaci cewa ba ita bace ta ɗauko allurar ba, ba ta ita akayi, nan ma ya gane cewa kwa6a tayi mashi jiya har ya ɗirka ma kanshi allura, that’s why omar ya tambaye shi akan cewa shi ya dauko allurar, natsuwa yayi a hankali yana ƙare ma fuskar sehrish kallo, ita kuwa sai faman haɗiyar yawu take yi saboda tsoro ga zufa dake gangarowa ta cikin gashin kanta kamar mara gaskiya, duk da sanyin A.c dake gudana aciki,

   rufe idanuwanta tayi tana faman karanta addu’oi’ acikin bakinta,

   for the first time daya ƙarewa wata ƴa mace kallo irin wannan aduniyar nan, yana kallon kyakkyawar fuskarta ne aƙoƙarin shi na ya tuna abunda ya faru jiya,amma yarda take motsi da siraran la66anta tana karanta addu’oi’n neman tsari hakan ba ƙaramin burge shi yayi ba, sai ya samu kan shi da shagala wurin kallon bakinta, tunanowa yayi da ranar daya turketa amatsayin mace yarda ta tsorata har ta sume mashi, shi kuma rayuwarshi mace mai shegen tsoro ba ƙaramin burgeshi takeyi ba,ba don komai ba sai don ya ruƙa tsorata ta don ya samu nishaɗi,

    ɗan gyara muryarshi yayi tare da cewa”jiya kin ban allura nayi ma kaina har nayi ƙoƙarin yin raping ɗinki, ko ba haka akayi ba? ya tambaya fuskarshi a ɗaure,. 

   hankali tashe sehrish ta shiga furta”innalallahi wa’inna ilaihirraji’un. Nashiga uku, kasan Allah ni bani bace na ɗauko allurar ba  bansan komai akai ba,. 

   shiru sgr yayi yana kallonta har lokacin taƙi buɗe idanunta, abunda bata sani ba shi guessing yayi bai tuna komai ba, amma yayi mata rijiya ta faɗa,

   cigaba da magana yayi anatse”then tell me who brought it to u”?

    shiru tayi lamo saboda tasan ba zata iya furta sunan haroon ba, ganin taƙi magana yasa shi daka mata tsawa tare da cewa”ba magana nake maki ba!!,” wannan tsawar da yayi mata ne yasa ta sume mashi, dama sai da ranshi ya bashi,

  Saukowa daga saman gadon yayi tare da fucewa izuwa palour dinshi, kai tsaye ya wuce wurin fridge ɗinsa tare da buɗewa ya ɗauko bottle water mai sanyi, sannan ya koma cikin bedroom ɗin nashi,zama yayi daga gefen gadon tare da sanya hannu ya buɗe roban rubar saida ya fara sha sannan ya ɗebo a hannun shi ya yayyafa mata a fuskarta, a gigice ta ware idanunta kai tsaye suka shiga cikin nashi a lokacin ya mayar da  bottle din abakin shi yana ƙara shan ruwan, tamkar a mafarki take ganin abun har lokacin jikinta bai daina kerma ba, cire roban ruwan yayi daga bakin shi sannan ya mayar da murfin ya rufeta tare da ajiyewa saman side drawer ɗinshi,

    sannan yayi mata nuni da hanyar fita yace”zaki iya tafiya,” cikin sauri ta sauko daga saman gadon nashi, hanyar fita ta nufa da sauri da sauri, jinkirtawa tayi tare da ɗan juyawa don ta saci kallon shi, samun shi tayi a kashingiɗe saman gadon ya aza head dinsa asaman pillow, eyes dinshi a lumshe tamkat zasu rufe amma hasken kwayar idonshi blue ya ɗan fito alamar bai runtse idanun duka ba,

   Muryarshi ce ta ratsa kunnanta da cewa”akwai wani abu ne”? Cikin sauri ta girgiza kai alamar a’a sannan ta fuce daga ɗakin, sai da tafara ɗaukar mayafinta dake zube a ƙasa, ta yafa shi akanta sannan ta fuce daga part ɗin nashi, tafiya take anatse fuskarta ɗauke da ƙayataccen murmushi tayi mamakin yarda akai Sgr bai tuhumeta ba,bayan ya tuna duk abunda ya faru atsakaninsu jiya, tayi tunanin zata sha mari ne a wurin shi amma sai gashi abun yazo mata da sauƙi, har yau tana mamakin sauƙin kai irin nashi da ba kowa zai fahimta ba, amma tabbas bai da girman kai ko kaɗan, jan ajine kawai dake gare shi ko jinin sarauta bazai nuna mashi wannan ba, Domin kuwa shi kanshi Sarki ne mai cike da ƙarfin iko👑

  a hankali take taka steps ɗin down stairs zata sauko, jin alamar shigowar mutun cikin babban falon yasa ta tsagaitawa da tafiyar tana kallon shi, jahan ne ya shigo cikin falon hannun shi ruƙe da jakar kuɗin da zasu ba haroon, ganin yarda yake tafiya cikin sanɗa yasa ta gane cewa bai son wani ya ganshi cikin sauri ta ja da baya tare da samun wuri ta la6e,

   sai faman ƴan waige waige yake yi yaga ko akwai mutun amma wayaam ba kowa hakan yasa cikin sauri ya wuce bedroom ɗinsu, ajiyar zuciya sehrish ta sauke tare da lalla6awa ta fito kai tsaye ta nufi kitchen tana zullumin ko menene Jahan ya ɗauko acikin jakar hannunshi, da alama dae wani mugun abunne tunda har yake sanɗa don kar aganshi, ta faɗi acikin ranta a lokacin da take ƙarasawa cikin kitchen ɗin don ta zuba ma kanta abincin da zata ci,

   turo ƙopar yayi a hankali yashiga daga cikin ɗakin nasu, jin alamar shigowar mutun yasa ayaan dakatawa daga zirga zirgan da yake yi acikin ɗakin,

  Cikin sauri ya nufe shi yana cewa”Jahan ka tabbata babu wanda ya ganka”? Amsa mashi yayi da cewa”eh babu da alama duk sunyi bacci, kazo yanzu mu hanzarta mu kai mashi kuɗin,” 

  Atare suka fito daga bedroom ɗin nasu,  duka suna sanye cikin jallabiya, ɗakin haroon suka nufa, koda suka ƙaraso ƙopar ɗakin a rufe take, kwankwasawa Jahan yashiga yi a hankali,

  “Su waye ne”? Ya tambaya daga ciki,

Har suna haɗa baki wurin cewa “twins ne “,

   kwance yake daga saman gadonshi,daga shi sai shorts ajikinshi ba riga, tasowa yayi tare da nufar kofan yasa hannu ya buɗe masu tare da cewa”ku shigo daga ciki,” kallon juna su kayi kafin daga bisani suka shiga daga ciki,

  tunda haroon yayi arba da jakar kuɗin dake hannun jahan yashiga sakin murmushin nan na shu’umanci yana cewa”ince dae kuɗina ne acikin jakar nan ko”? yayi maganar tare da miƙa hannu zai kar6i jakar,janye ta jahan yayi tare da cewa”ka fara goge  video ɗin tukunna mu damƙa maka su,” 

  ta6e baki yayi yana kallon su,kafin ya juya ya nufi saman gadonshi inda wayar shi ke ajiye ya ɗaukota, yatsan shi yasa ta buɗe sannan ya shiga wurin videos ɗinshi ya lalubo nasu daya ɗauka sannan ya miƙa masu tare da cewa”Gashi nan ku goge da kan ku,ina ga hakan zai fi ko”?  Kallon juna suka sake yi duk jikinsu yayi sanyin, tsoransu karya cuce su,ayaan ne ya kar6i wayar tashi yayi deleting ɗinsa gaba ɗaya, sannan ya kalli haroon ɗin dake ta faman sakin murmushi yace”ka  tabbata babu wani videon namu dake gare ka bayan wannan!? 

 ɗaga mashi gira yayi alamar eh, jahan yace’laptop ɗinka fa babu wani aciki”? nan ma ya sake cewa”babu wannan ne kawai gare ni,” 

  ajiyar zuciya suka saki gaba ɗayansu,

 Miƙa mashi wayar Ayaan yayi, sannan jahan ya damƙa mashi jakar kuɗin, kar6a yayi yana cewa”kun tabbatar  cewa miliyan 80 ɗinne”?

  ayaan yace”ka ƙirga su mana sai kaga in sun cika,” 

Domin Sauke Littafin Sai Ku Dannan inda aka saka Download Now!

Zuƙunnawa haroon yayi tare da zuge zeep ɗin jakar, sai ga bandir bandir ɗin ƴan dubu dubu, dami dami shaƙe acikinta, hannu yasa tare da curo bandir guɗa ɗaya yakai a saitin hancin shi yana shinshinasu yace”Anya wannan ba kuɗin ganye bane?harara suka watsa mashi jahan yace”a’a na bishiya ne,” dariya haroon yayi yana faman shaƙa kuɗin a hancin shi,

  gaba ɗaya ransu ya gama 6aci burinsu ya ƙirga kuɗin yaga in sun cika, amma ya tsaya yi masu shegantaka,

   tass ya fiddo da kuɗin ya ƙirga su, duk dami ɗaya na dubu ɗari ne, a haka yayi counting ɗinsu 80 millions ne bayan ya kammala ƙirgasu, ya shiga cusa su acikin jakar kaf ya kwashe su, sai da ya zuge zeep ɗin sannan ya ɗago ya kalle s u cike da shaƙiyanci yace”Au na manta ban baku la’ada ba,” 

  atare suka haɗa baki wurin cewa”mun fi ƙarfinsu,kai ke buƙatarsu kai daga ganin mu kasancewa ba matsiyata bane,” 

  “Wow,” ya furta yana tafa hannunshi “abu yayi kyau ƴa’ƴan billionaire,karfa kuce zaku gayamin magana!ku fuce mun daga ɗaki cikin salama,” 

  Jahan yace”ba sai ka kore mu ba, mukan mu aƙagare muke da mu fita mubar maka wannan ƙazamin ɗakin naka wanda ko numfashi mutun daƙyar yake iya fitarwa!!kuma inaso ka sani Haroon baka ci bulus ba, zamu rama duk wani wulaƙancin da kayi mana!!

  yana kai ƙarshen maganar tashi ya ruƙe hannun ayaan suka juya zasu fita daga ɗakin karaf idonsu ya sauka akan mutumin dake shigowa cikin ɗakin, A wani irin firgice suka ja da baya gaba ɗayansu, shi kanshi Haroon ya sha jinin jikin shi saboda basu son da mutun ba, gaba ɗaya duk abunda suka tattauna acikin kunnanshi kaf ya gama naɗar komai, 

  hankali tashe suke kallon shi,kamar yarda shima hankali atashe yake kallon su 

Follow my tiktok acct 👇

https://www.tiktok.com/@boss_bature?_t=8WKx0lm4jaP&_r=1

Atare suka sauke ajiyar zuciya lokacin da suka shaida cewa junaid ne,sai faman murza idanunshi yake yi da hannunshi,da alama magagin bacci ne ya shigo dashi,hakan ya basu tabbacin ba lallai in ya fahimci komae ba,

    cikin sauri Jahan yace”junaid tun yaushe kake anan?me kake yi har yanzu baka yi bacci ba”? 

  Cikin shagwa6a yace”nima bansan ya akai na shigo ba,dan Allah kutaimaka mun ku kaini ɗakin abbanmu in kwanta,wurin shi nake son zuwa,”

 Shu’umin Murmushi haroon yasaki yana kallon shi,

  ganin yarda yake binshi da kallo yasa su twins saurin ruƙe hannun junaid suka fuce dashi daga ɗakin,

    “Ayaan kaje kawai ka kwanta,ni bari nakai shi ɗakin Abban namu,”

Amsa mashi yayi da toh,sannan ya wuce bedroom ɗinsu,

  Shi kuma jahan zuƙunnawa yayi tare da ce mashi”ka hau na goya ka karka faɗi,”

   daddagewa junaid yayi ya haye bayanshi tare da ƙanƙame shi,sannan jahan ya miƙe ɗauke dashi abayansa ya wuce bedroom ɗin Abban nasu,

   A hankali ya tura ƙopar bedroom ɗin Abban nasu,yana kwance sai faman sharar bacci yake yi asaman royal bed ɗinshi,shiga da junaid ciki yayi a hankali ya sauke junaid saman gadon daga gefen abban nasu,

     gyara kwanciya junaid yayi tare da rungumo Abban nasu da hannunshi sannan yace ma Jahan”thank u,”

  murmushi jahan yayi ba ƙaramin burge shi yayi ba,sam junaid bashi da wata damuwa,sai yaji dama shine ke irin rayuwar shi,

   “Sleep well,” ya furta tare da juyawa ya fuce daga bedroom ɗin yana sauke ajiyar zuciya,ɗakinsu ya koma lokacin daya shiga a kwance ya samu Ayaan har bacci yayi awon gaba da shi,shima wucewa yayi tare da haurawa saman gadon ya kwanta daga gefenshi,

Yaushe rabon da suyi bacci irin na daren nan harsun manta,saboda fargabar haroon kullum da damuwarshi suke kwana,yau dae sun huta ma rayuwarsu tunda sun sallame shi,

A 6angaren haroon kuwa tun bayan da suka fita ranshi ya raya mashi cewa tabbas akwai alamar tambaya game da zuwan junaid bedroom ɗinshi,saboda tun da yake junaid bai ta6a faɗowa ɗakinshi ba irin haka,duk irin magagin baccin da junaid yake yi bai ta6a zuwa ɗakin shi ba,amma sai yau kwatsam zai faɗo mashi ɗakin shi adai² lokacin da suke tattaunawa dasu twins kuma? Anya ba turo shi akayi ba❓

   zama yayi daga gefen gadon nashi yana tunani,dakyar ya iya tashi yakai hannu ya kinkimi jibgegiyar jakar kuɗin,wuri yayi mata acan cikin ɗakin nashi ya 6oyeta,

   Sannan ya koma tare da hayewa saman gadonshi ya kwanta,

     *********************

Washe gari 

A hankali ya buɗe idanunshi da su kayi mashi nauyi saboda bacci,hannu yasa tare da yaye blanket ɗin daya lullu6a dashi,miƙa hannu yayi tare da ɗaukar wayarshi dake ajiye saman bedside drawer dinshi,missed calls ya gani nasu hossana da jahad,tashi yayi daga zaune yana kallon screen ɗin wayar tashi,jiya yaso yaje ya duba su amma bai samu time ba,

   danna musu kira yayi tuni tashi ga ringing,

  A lokacin Jahad ce acikin falon zaune saman 2 seater tana ta jiran kiranshi,hossana kuwa tana can tana sharar bacci,

    har ta fidda ran cewa zai kirasu saiga kiran nashi ya shigo,cikin sauri ta miƙe ta nufi telephone ɗin tasa hannu ta dauka tare da karata a kunnanta,

   Cikin sanyin murya tace”Assalamu Alaikum ya Omar an tashi lafiya,”

  murmushi yasaki tamkar yana agabanta yace”lafiya lou Alhmdlh,nayi laifi ko?jiya banzo na duba ku ba,ayi mun afwa ina busy sosai,amma kuna araina,”

   “Babu komai ya Omar,dama mun damune akan rashin zuwan naka,kuma mun kira wayarka jiya da safe,baka a kusa sai dai matarka Aunty zainab ta ɗaga kiran,” 

   “What!matata kuma? Wacece kuma aunty zainab?pls explain to me ni bangane me kike cewa ba,”

   murmushi jahad tayi tare da cewa”Ya omar meyasa ba ka sanar damu cewa kana da aure ba?baka so mu sani ne?

  Sam Omar baisan inda zanjen nata ya dosa ba,

   “Jahad nifa bansan me kike cewa ba! Wacece kuma matata?

  kafin jahad tace wani abu,sai ga hossana ta fito da saurin gaske jikinta sanye da kayan bacci,tana ƙarasowa tasa hannu ta kar6i telephone ɗin tare da karata a kunnanta cikin shagwa6a tace”eh mana ya omar ashe kana da aure,jiya da safe mun kira wayarka,mace ta ɗaga kiran tace mana kai mijinta ne kuma baka a kusa,sannan kuma tace mana tana ɗauke da juna biyu,kuma sunanta zainab amma kana kiranta da Hayaty,”

   tunkan ta ƙarasa maganar Omar yashiga 6a66aka dariya,natsuwa su kayi gaba dayansu suna sauraron sautin dariyarshi,

  “Ya omar kayi shiru baka ce komai ba,” muryar hossana ce ta katse mashi dariyar tashi,daƙyar ya tsagaita tare da cewa”Am sorry na fahimci abunda kuke cewa,bazan iya yi maku bayani anan ba,insha Allah bayan na kammala breakfast dina zan shigo sai muyi magana ta fahimta ko? 

  Atare suka haɗa baki wurin cewa”Eh muna jiran zuwanka,sannan in ka tashi zuwa kazo mana tare da Hayati ɗinka muganta,”

   murmushi kawai yayi tare da rejecting call ɗin,sai lokacin ya duba kiran nasu da sukayi mashi jiya acikin wayarshi,cike da mamaki yaga kiran da sukayi mashi jiyan da safen kuma already an ɗaga kiran,natsuwa yayi yana tunanin wanene ya daga mashi kira harya tsara wannan ƙaryar,tabbas junaid zai iya yi mashi wannan aikin,.  

  Miƙewa yayi tare da saukowa daga saman gadon nashi,ya wuce cikin toilet dinshi,within 15 mins ya fito ya wuce wurin closet ɗinshi,tsaf ya kammala shiryawa cikin shadda purple colour ba ƙaramin kyau tayi mashi ba yabi jikinshi duka ya feshe shi da turare,

  Bayan ya ɗauki wayar shi ya fito tare da wuce wa part ɗin Rafayet,da sallama ya shiga ciki,baya acikin falon shi don haka ya wuce cikin bedroom ɗin shi,

  Yayi mamakin ganin shi a kwance saman shimfiɗeɗen gadonshi,jikin shi na’a sanye da bathrobe da alama bai jima da fitowa daga wanka ba,

   Shiga ciki omar yayi tare da samun wuri daga gefen gadon ya zauna sannan ya ambaci sunan shi a hankali”Rafayet wai haryanzu bacci kake yi?

   Yamutsa fuska yayi alamar idonshi biyu sannan yace”Omar,yau lalaci nake ji ajikina,duba fa ka gani tun ɗazu nayi wanka amma nagaza tashi in shirya kaina,”

   sakin baki Omar yayi yana kallon shi tare da jinjina kai yace”nasan meye matsalarka,wato har yanzu abun nan bai bar jikinka ba ko?

Domin Sauke Littafin Sai Ku Dannan inda aka saka Download Now!

   “Mekenan”? Sgr ya tambaya yana kallon shi daga kwancen da yake,

   Murmushi Omar yasaki batare da yace komai ba,

   Miƙewa Sgr yayi tare da tashi daga zaune suna fuskantar juna shi da Omar yace”Na fa tuna duk abunda ya faru jiya a tsakanina da yarinyar nan,”!

  “dagaske”? Omar ya faɗi da ɗan mamaki a fuskarshi,

  “yeah,amma bakomai na tuna ba,so nake ka faɗamun gaskiyar abunda ya faru,time ɗin da ka tarar damu asaman gadon nan,shin na cire shorts ɗin jikina ko ban cire ba”?

   tunkan ya ƙarasa maganar omar ya soma sakin dariya,

  Ɗaure fuska sgr yayi tare da cewa”pls Omar banason wasa,just tell me the truth,cos banaso yarinya ta raina ni,”

    tsagaitawa omar yayi sannan ya zayyana mashi dukkan abunda ya faru tsakanin shi da Sehrish,

   hannu sgr yasa tare da dafe forehead ɗinshi yace”OMG!Omar ashe kaine ka katse mun jin daɗina a wannan lokacin!meyasa baka bari na ƙarasa aikina ba”? ya ƙarasa maganar yana jifar shi da harara,

   dariya omar ya kuma yi kafin yace”nifa taimakonka nayi,kisan kai fa zakayi,”

   tsuke fuska yayi tare da cewa”babu wani nan,ni narasa meyasa kake mun haka,”

  Yayi maganar tare da kai hannu ya dauki pillow ya wurga mashi shi a fuskarshi,tarbe pillow ɗin Omar yayi a hannunshi tare da cewa”Am sorry bro,bansan abun yayi hurting ɗinka ba,amma ae ko yanzu bata 6aci ba,kasan inason farin cikin ka,bari natashi naje na kira maka yarinyar sai ka ƙarasa aikin naka,”

  Yana kai ƙarshen maganar tashi ya mike tare da nufar  hanyar fita daga bedroom ɗin  yana  karashe dariyar shi,yana jiyo muryar sgr cike da zolaya yana cewa”Am waiting,”

Kai tsaye bayan Omar ya fito daga sashen sgr down stairs ya sauko tare da fuce wa daga main palour din,ko breakfast din bai tsaya yayi ba ya wuce wurinsu hossana,

Wuraren ƙarfe tara kiran Amrish ya tashe ta daga dogon baccin daya ɗauke ta tun bayan sallar asuba,dakyar ta iya buɗe idanunta da sukayi nauyi saboda bacci,hannu takai tare da daukar wayar dake ajiye asaman side drawer ɗinta,picking call ɗin tayi tare da kara wayar a kunnanta a kasalance tace”Assalamu alaikum Amrish irin wannan kira haka tunda sanyin safiya”?

   daga can 6angaren Amrish tace”Sleeping sickness wai kina nufin har zuwa yanzu baki tashi daga bacci ba?duba time ki gani kusan 9 fa yanzu,”

  Jin haka yasa sehrish sa hannu tare da janye blanket ɗin jikinta ta tashi daga zaune tana kallon clock, ɗan xaro ido tayi tare da cewa”subhanallahi wai har 9 tayi?meyasa aunty azmee bata tashe ni ba,ya ilahi,” 

  dariya amrish tayi tare da cewa”kin cika bacci reeshi yakama kije kiga psychiatric doctor ya duba brain ɗinki,”

   ɗaure fuska sehrish tayi kamar tana agabanta tace”oh ashe dama kallon da kike mun kenan ko?

     muryarta cike da dariya tace”no ba haka bane inason lafiyarki ne shiyasa na baki shawarar kije aduba ki,”

   “Okey thanks for ur advise amma fa ni ba inda zanje,da raina da lafiyata bazan kwasa na tafi asibiti ba,salon su ja man bala’e,” 

ƙarasa maganar tayi tare da cewa”pls inason zan shiga kitchen yanzu,i wll call u later bye,” 

   sallama su kayi da amrish sannan ta mayar da wayar saman side drawer ta ajiyeta,

saukowa tayi daga saman gadon cikin sauri ta wuce cikin toilet, brush tayi tare da wanko fuskarta sannan ta fito ta wuce wurin wardrobe ɗinta,buɗewa tayi tare da ɗauko mayafi ta daure shi akanta kamar ɗan kwali,

Lokacin da fito har azmee ta kammala jera masu breakfast ɗin asaman dining,junaid ta samu tare da fawan zaune suna yin breakfast dinsu,kamar waɗanda yunwa ta koro sai faman turawa suke yi abakinsu suna ci,

   dagowa junaid yayi tare da kallonta nan take ya sakar mata murmushi tare da kiran sunanta”sehrish,” 

  Juyowa fawan yayi tare da kallonta yace”ke zo nan,” 

  nan da nan taji gabanta ya faɗi dama basu ta6a magana dashi ba,

  jiki asanyaye ta ƙarasa inda suke dai dai kusa dashi sannan ta tsaya tana faman ƴan kame kame,

   cikin sanyin murya yace”jira kike na fara gaishe ki ne”?

  cikin sauri sehrish tace”ina kwana,ka tashi lafiya,”

  fashewa da dariya junaid yayi yana kallonsu,harara fawan ya watsa mashi tare da mayar da idonshi kan sehrish yace”lafiya lou,haka yadace daga yanxu basai nace ki gaishe ni ba,daga zarar kin ganni kiyi hanzarin gaidani amatsayina na yayanki,”

  Murmushi sehrish tayi tare da amsa mashi da”toh,”

    junaid yace”bismillah ki zauna muyi breakfast atare mana,” girgiza kai tayi tare da cewa”a’a inaso zan shiga kitchen ne wurin aunty azmee,”

  Amsa mata yayi da”okey,”

  Sannan cikin sauri ta juya tare da nufar kitchen din,

   time din da taƙarasa kitchen ɗin azmee ta kammala gyare kitchen din tsaf, dakyar ta iya cewa”ina kwana aunty azmee,”

   sai lokacin ta lura da ita,murmushi tasakar mata tare da cewa”lafiya lou babyn junaid,sai yanzu kika tashi daga baccin naki?dazu nashiga ɗakin naki na sameki kina bacci,

   ciki sehrish ta shiga tana cewa”Aunty azmee ae da kinsani kin tashe ni,nikaina banasan yawan baccin nan da nake yawan yi,”

  Azmee tace”ai baida amfani atlease yakamata ace duk in kika kammala sallar asuba ki daure kina karanta al’qur’ani, sannan ki dinga yawaita yin azhkar,insha Allah duk wani abu dake damunki Allah zai yaye maki shi,”

  “Insha Allah zan yawaita yinsu kamar yarda kikace,yanzu inaso in kaima babban yaya breakfast ɗinshi,bansani ba ko kin kai mashi,

   Azmee tace”a’a ban kai mashi ba,bari na haɗa maki sai ki kai mashi,”

   Tsayawa sehrish tayi tana jiranta,

  Bayan azmee ta kammala shirya mata breakfast din nashi acikin tray ta miƙa mata,hannu biyu tasa ta kar6a tare da kama hanya ta fuce daga kitchen ɗin,

  Da sallama abakinta tashiga part din nashi,

    har time din bai fito ba,yana acikin bedroom ɗinshi,ƙarasawa ciki tayi tare da ajiye mashi tray din asaman table,sannan ta wuce izuwa bedroom ɗinshi daga bakin kopar ta tsaya tare da maimaita sallamar,

   daga cikin bedroom ɗin tajiyo muryarshi yana cewa”wanene nan”

  tuni tasha jinin jikinta,musamman data tuna abunda ya faru jiya ba ƙaramin tsoro ya bata ba,

   murya na rawa tace”Ni ce,breakfast nakawo maka,”

   “Okey,come in,”

a hankali tasa ƙafa tare da shiga ciki zuciyarta nata faman ɗar ɗar,

  tsayawa tayi daga bakin ƙopan tana kallon shi,har lokacin yana kishingiɗe kamar yarda Omar ya barshi,

   ganin ta tsaya abakin ƙopar yasa shi cewa”lafiya?

   cikin sauri tace”bakomai,”

“Okey shigo ciki,ki fara gyara min toilet ɗina,” 

  ƙarasawa ciki tayi a hankali take tafiya tana satar kallon shi,eyes ɗinshi na’a rufe tamkar mai jin bacci,duk wani motsinta acikin kunnanshi yake jinshi,tura ƙopar toilet ɗin tayi tare da shigewa ciki,

   Sai bayan da ta shiga ciki sannan ya buɗe idanun shi tare da bin ƙopar toilet ɗin da kallo,tunawa da abunda ya faru jiya tsakaninsu yayi,mayar da idonshi yayi tare da lumshe su,

   ba da jimawa ba sehrish tafito daga cikin toilet tare da cewa”na kammala gyarawa,saura bedroom din,”

   buɗe idanunshi yayi ba tare da ya kalleta ba yace “okey,ki duba cikin closet ɗina,ki ciro mun kayan da zan sanya,”

  Cike da mamaki ido waje sehrish tace”dani kake”? 

  “Ni da waye” ya tambaya a ataƙaice,d’an murmushi tayi tare da wuce wa can ciki wurin wardrobe ɗinshi,mai girma da faɗin gaske gaba ɗaya glass ne ta gabanta,daga waje kana iya hango kayan sawarshi dake aciki gasunan abun kamar a company jeri jeri komai a tsare,tana ɗauke da sliding doors ajikinta,

  Hannu sehrish takai ajikin wardrobe ɗin nan take ƙopar ta zuge da kanta,abun ba ƙaramin burgeta yayi ba,ruwan ido ta tsaya yi tama rasa wanne zata ɗauko mashi,saboda kowanne acikin kayan sawar nashi kyau suke yi mata,wata ƙopar ta zuge anan taga jerin kayan hausawa ta jima tana mamakin ashe yana dasu amma bai ta6a sanyawa ba,hannu tasa tare da ɗauko mashi haɗaɗɗiyar shadda gezna sky blue mai ɗaukar ido,

   ruƙowa tayi a hannunta tare da dawowa wurin gadon Shi a lokacin harya gaji da jiranta ya sauko da ƙafafunshi ƙasa yana ƙoƙarin tashi,jin takon tafiyarta yasa shi ɗagowa yana kallon kayan data ruƙo a hannunta,

  tsayawa tayi dab dashi sannan ta miƙa mashi,

    ƙin kar6a yayi saima nuna mata hanya da yayi tare da cewa”basu nakeso ba,ki canza mun wasu bana sa kalar wannan,” 

     Jiki asanyaye sehrish ta koma ta maida shaddar sannan ta ɗauko mashi jeans da t shirt baƙa,

   

  Komawa tayi tare da miƙa mashi,hannu yasa ya kar6a tare da furta”thanks” a gefen shi ya ajiye kayan sannan ya miƙe tare da kai hannu ya zame bathrobe ɗin jikin shi,cikin sauri sehrish tayi hanzarin barin bedroom ɗin takoma daga waje tana faman sauke ajiyar zuciya,ƙiris ya rage sgr ya saki murmushi don ba ƙaramin dariya ta bashi ba,ita duk atunaninta babu shorts ajikinshi shiyasa tayi saurin guduwa daga ɗakin nashi,

  Tsaf ya kammala zura kayan ajikinshi bayan ya gama ya koma gaban dressing mirror ɗinshi tare da kai hannu ya ɗauki kwalbar turarennan nashi shumukh yabi ko’ina na jikinshi ya feshe shi da shi,sannan ya koma wurin shoe rack ɗin shi tare da zaro takalma ya zura a ƙafarshi,

   tana atsaye tana jiran fitowarshi muryarshi ta ratsa kunnanta da cewa”ki shiga ciki ki gyara mun,”

  Sannan ya wuce ta izuwa cikin falon nashi,

   Shiga ciki sehrish tayi anatse ta soma gyara mashi bedroom ɗin nashi,

    **************

A hankali motarsu tashiga cikin gidan abusufyan major ne ke driving ɗinshi yayin da yake zaune a back seat na motar,

  Bayan yayi parking ɗin motar omar ya fito tare da wuce wa ciki,

  Koda yashiga cikin falon samun su yayi azune saman 3seater sun haɗa kai sun kurawa plasma tv ɗin dake manne abango suna kallon tashar bollywood,

   ba ƙaramin burgeshi su kayi ba,gyara muryar yayi tare da yi masu sallama,atare suka dago tare da kallon shi,hossana na ganin shi ta miƙe da gudun gaske ta tunkare shi,dakatar da ita yashiga yi da hannun shi amma ina sai da ta faɗa mashi,sosai ta rumgume shi tare da kwantar da kanta a saman wide chest ɗinshi,lokaci guda yaji wani irin yanayi atattare dashi,

  Jahad kuwa a fusace tace”hossana menene haka wai?ba zaki bari ya ƙaraso ciki ba?

   tamkar bata jita ba,haka ta ƙara ƙanƙame shi tana cewa”ya Omar nayi missing ɗinka sosai,jiya ko isasshen bacci bansamu ba saboda ban saka a idona ba,

  hannu omar yasa tare da janyeta daga jikinshi suna kallon juna ido cikin ido yace”Am sorry pls,amma yanzu ae gashi nan nazo ko?

  daga mashi kai tayi alamar eh,sannan tasanya hannunta cikin nashi suka ƙarasa ciki atare suka zauna kusa da Jahad saman 3 seater ɗin da take,

  Cikin sanyin murya tace”sannu da zuwa ya omar,yasu abba da sauran mutanen gidan,

  Fuskarshi dauke da murmushi yace”yawwa jahad,duk suna lafiya,ina fata kuma nasame ku cikin ƙoshin lafiya,” 

  Amsa mashi tayi da eh,sannan tace”namanta ban tambayeka ba,yasu Aunty zainab,”?

   kafin yace wani abu hossana tace”ya Omar wai dagaske kana da aure”?a shagawa6e tayi maganar tamkar zatayi kuka,

   cikin natsuwa ya soma kora masu jawabi”Ni banta6a aure ba,saurayi ne ni,ko budurwa ban ta6a ajiyewa ba,”

  Jahad tace”amma ya Omar wacece ta ɗaga kiran wayarka da mukayi a lokacin?

    shiru ya danyi kafin yace”ina tunanin younger brother ɗina ne Junaid,ya cika zolaya sosai,”

Domin Sauke Littafin Sai Ku Dannan inda aka saka Download Now!

  maimaita sunan Jahad tayi “JUNAID!ya omar ƙaninka ne shima?

  kallonta yayi tare da cewa”eh ƙanina ne,yana da kyau sosai ga kyan hali sannan ya iya kyakkyawan murmushi kuma shagwa6a66e,”

  Murmushi su kayi jin yadda Omar ke zayyana musu ƙanin nashi da alama dae ba ƙaramin sonshi yake ba,

   “Ya omar ka nuna mana hotonshi mu gani mana,” acewar hossana,

  Batare da 6ata lokaci ba Omar ya zura hannu a ajihun wandonshi ya ciro wayarshi tare da shiga gallery ɗinshi,hoton junaid ya buɗo tare da miƙa ma Hossana,hannu tasa ta kar6a tana kallon hoton cike da mamaki tace”wow! yaya Omar wai dagaske ƙaninka ne?wlh yana da kyau sosai dan Allah ka kaimu gidanku wata rana mu ganshi,”

  Jin yarda hossana keta santin hoton junaid yasa Jahad sa hannu tare da kar6ar wayar,

  Lokaci guda taji gabanta yayi wani irin bugu,tunda ta aza idonta akan kyakkyawar fuskar junaid bata ƙara cewa uffan ba,sam tagaza janye idanunta akan fuskarshi,bakomai take furtawa acikin zuciyarta ba face”Tabarakallahu Ahsanul khaliqin,”

   Muryar omar ce ta katse ta da cewa”jahad naji kinyi shiru”?

  jiki asanyaye ta ɗago tare da kallon shi tace”ya omar pls zan iya tafiya da wayarka cikin ɗakinmu?yanzu zan dawo,”

  murmushi ya saki tare da cewa”ba damuwa zaki iya zuwa,”

  cikin sauri ta miƙe tare da nufar bedroom ɗin nasu ta shige ciki,

     “Ya omar bari nakawo maka breakfast nasan baka ci komai ba,” hossana ce tayi maganar yayin da take miƙewa daga saman kujerar,” 

Ruƙo hannunta yayi tare da cewa”dawo ki zauna,idan kika tafi wa zai tayani fira,”

   ƙayataccen murmushi tasaki tare da komawa ta zauna daga gefenshi sannan tace”Ya Omar yaushe zakayi aure ne?

  “Ranar dana samu maisona,” ya bata amsa yayin da idonshi ke akan agogon hannunshi,

  cikin shagwa6a tace”ya omar ni nasan cewa kana da ƴan mata dayawa da suke sonka,kawai dae kaine baka shirya yin auren ba,”

  “haryanzu bansamu kalar wadda nakeso ba hossana,” 

ɗan turo baki tayi tare da cewa”ka faɗamun kalar matar da kakeso ka aura,zan tayaka da addu’a insha Allah,”

  murmushi ya ɗanyi tare da kwantar da bayanshi ajikin sofa ɗin yadda zai samu damar kallonta sosai sannan yace”Inason mace natsastsiya kamila,miskila mai ilmin addini dana zamani,mai ladabi da biyayya,idan Allah ya bani mace mai irin wannan suffar tuni zanyi wuff da ita,” 

  tunkan ya ƙarasa maganar hossana ta ɗaure mashi fuska,sunnar dakai ƙasa tayi tamkar zata zubar da hawaye,

  “Meya faru ne”? Ya tambaya yana kallon ta,

  Cikin shessheƙar kuka tace”ya omar ba dole sai mace nutsastsiya ba,ko miskila,in dai tana sonka tsakani Allah kawai ka aureta,”

   kawar da fuskarshi gefe guda yayi yana murmushi,

  Sanya hannunta tayi acikin nashi tare da kwantar da kanta asaman kafaɗarshi,

…sun jima a haka batare da wani yace ƙala ba,kusan 30 mins sai ga jahad tafito hannunta ɗauke da wayarshi,tsayawa tayi tana kallonsu shi ya lumshe ido,hossana kuma har ta fara bacci,

  murmushi ta saki tare da samun wuri ta zauna daga gefen shi sannan ta ambaci sunan shi “ya Omar,”

  Buɗe donshi yayi a hankali yana kallonta,miƙa mashi wayar tayi tare da cewa”thanks,”hannu yasa ya kar6i Wayar sannan ya mayar da idonshi tare da rufe su,.  

  Ajiyar zuciya tasaki tare da miƙewa ta koma cikin bedroom ɗinsu,saman gadonsu ta haye a inda ta ajiye drawing book ɗinta,ashe lokacin da ta kar6i wayar omar ta shigo dashi bedroom ɗin nasu,zama tayi tare da ɗauko kayan zanen ta acikin school bag ɗinta,a natse ta zauna tare da zana fuskar,ba ƙaramin kyau zanen yayi ba,fuskar ta fito raɗau dauke da wannan murmushin nashi,zuba ma zanen ido tayi tana kallon shi,lokaci guda taji tana son taganshi face to face~~~~

  

************************

Yau tunda ta farka da kewarsu jahad ta tashi saboda mafarkinsu da tayi,fitowa tayi daga cikin bedroom ɗinta jikinta na sanye da riga bubu ta material,

  tsayawa tayi daga tsaye tana sauraron wayar da Aunty babba keyi,da alama da hayaam suke magana saboda taji ta ambaci sunanta sai faman 6a66aka dariya take yi,

   “wlh ba kiji irin farin cikin da nake ji ba,yau burina zai cika na ganin kin koma gidan da zama,hayaam bana so ki raga ma yarinyar nan!so nake acikin one week ki ƙuntata ma rayuwarta har taji ta tsani zama acikin gidan,maƙirci kawai zaki cigaba da haɗa mata ae nasan kin ƙware a wannan 6angaren shiyasa nake yin ki,”

   girgiza kai hafsat tayi tare da ƙarasawa ciki ta samu wuri saman 2 seater ta zauna tana sauraronta,sun jima suna wayar kafin daga bisa ni su kayi sallamar,mayar da wayar tayi tare da ajiyewa agefenta,sannan ta ɗago tare da kallon hafsat tace”gulmawuya halan kin fito don kiji abunda muke tattaunawa ne?

  Murmushi hafsat tayi tace”mommy kenan ashe haryanzu kina akan bakanki na ganin cewa hayaam ta koma gidansu Abbana da zama hmmmm whatever ni wannan ba damuwa ta bane,kawai akwai shawarar da nakeso na baki in ba damuwa,”

  zuba mata ido aunty babba tayi tana sauraronta,. 

  Ci gaba da magana hafsat tayi”Mommy aunty hayam zata koma gidan da zama wannan ba laifi bane Amma zai iya zama abun kunya,amma maganar a ƙuntata ma rayuwar yarinyar dake acikin gidan sam wannan bai taso ba,in ba haka ba wlh zaku yi danasanin yin hakan,”

  wata uwar harara aunty babba ta watsa mata kafin tace”ke tashi ki ban wuri!tun kafin ranki ya 6aci,”

  Maƙe kafaɗa hafsat tayi tare da cewa”mommy dama ita gaskiya ɗaci gare ta,kullum ina faɗa maki kiji tsoran Allah,ki daina biye ma ruɗin duniya…..’

  Katse ta aunty babba tayi tare da cewa”karfa kice zakiyi mun nasiha,ko iyayen da suka tsugunna suka haife ni ban ta6a sauraran nasiharsu ba balle ke ƴar cikina dana haifa,

  tana kai ƙarshen maganarta,takai hannu tare da ɗaukar wayarta sannan ta miƙe tare da wuce wa ciki,

  “Mommy ae da alama basu  yi maki nasihar ma,don da ace suna yi maki da duk ba haka ba,nibansan ma ya akai abba ya auroki ba anya ba rufa ido kukayi mashi ba,”

   “Hafsat! Me kike cewa”?

A ɗan firgice hafsat ta juya tana kallonta duk a tunaninta ta jima da barin falon ashe bata ƙarasa fita ba,

  Cikin sauri tace “haka nace ni dae na gode ma Allah daya bani uwa tagari kamar ki,”

   ba don ta yarda da maganarta ba ta juya tare da wuce wa upstairs,

  Ajiyar zuciya hafsat ta saki tana faman tiƙar dariya,

Domin Sauke Littafin Sai Ku Dannan inda aka saka Download Now!

(Wannan kenan)

Na yanke shawarar takaita littafin nan saboda yanayin da nake ciki, kamar labarinsu jahad zaiyi tsayi don haka na taƙaita zanyi labarin ataƙaice yarda kowa zai fahimta, pls kada a haɗa mun document!!saboda ba full story ɗin bane,yanxu wurare masu mahimmanci kawai zan dinga tsayawa bayyanawa amma sauraron abubuwan zan gajarce su ne, bayan na kammala littafin gaba ɗaya insha Allah, in komai ya warware mun nan gaba zan faɗaɗa labarin saboda inason littafin sosai❤️🥰 masoyan littafina ina matuƙar godiya sosai da addu’o’inku da kuma soyayyar da kuka nuna ma littafin nan nawa, har ga Allah naci buri sosai akan littafin nan amma abubuwa dayawa basu tafiyarmun dai dai😔Dan Allah idan har akwai wanda na 6ata ma rai,to ya yafe mun, kada mutun ya ƙullace ni a zuciyarsu ko yayi magana akaina wadda bata dace ba,yawancin irin hakan suke jefa ni cikin matsala, kowa da yanayin bakinsa,zan sake maimaitawa duk wanda na 6ata ma rai batare da sani na ba,yayi hkr mu yafe ma juna,nasan na 6ata masu rai sosai,nima kuma wasu sun 6ata mun rai duk akan littafin nan👏🤝Pls komai ya wuce wa ne, wata rana ma mai bada labarin ma babu shi🥲just ya kasance tsakanina daku addu’ace kawai, Allah yabar zumunci🥰😍

Allah ya kare mu daga aikata aikin danasani,yasa mu cika da kyau da imani, waɗanda basu da lafiya kuma na gida dana asibiti Allah ya basu lafiya,ya tashi kafaɗasun,ƴan uwan mu dake cikin wani hali na rayuwa ya Allah ka yaye masu ka kawo masu mafita,Alfarmar annabi muhammad (SAW)

  Ku ƙara gyara zama,ynx hot episodes zasu fara🔥🔥🔥

Back to top button