Labarai

Fatalwar Delu Part 11

🤡 FATALWAR DELU 🤡

Part 11

Kingboy Isah 👑

Short story

ZAMANI WRITERS ASSOCIATION

 

Gudu nake ina waiwayan baya tamkar wanda mayunwatan zakuna ke biye da shi, ko da yake a nawa lissafin har gwara ma ace rikakkun zakuna ne wanda sukayi akalla wata guda basu ci ba su biyoni a kan wannan fatalwa da ke biye da ni a cikin iska. Ni dai bansan inda na nufa ba kawai ina gudu ne da nufin yin bakin kokarina kafin karfina ya kare in gaji in tsaya har ta tarar da ni. Ko da yake na tabbata batayi niyar kamani a lokaci guda ba, domin kuwa wanda yake bacewa ai ba a hadashi da bayananne ba. Idan tayi niya yanzu ina iya ganinta a gabana ta cafkeni. Rike nake da fitilar waya duk kuwa da yanzu haka hasken farin wata ya dan bayyana kana iya ganin nesa da kai. A haka nasha wata uwar kwana wacce karfin gudun da nake ya turani gaba, kadan ta hana inyi katantanwa in fadi kasa in mirgina watakil ma har in fasa kai ko baki. Amma duk da haka sai da hannuna ya dafa kasa, ban tsaya sauraren komai ba na sake shekawa a guje na bi yar hanyar da na ga ta mike ta nufi daji, don na tabbata a cikin garin nan babu maboya.

Don har nayi tunanin tsallakawa wani gidan ko ta katanga ne tunda sun rufe gidajensu, amma kuma sai nayi nazarin idan nayi haka ko gidan wa na tsallaka zan jawo masa bala’i ne yana zaman-zamansa. Domin kuwa duk wanda Allah ya hada da wannan fatalwa tabbas ya gamu da masifa. Ganin na fita daga cikin gari na nufi daji, sai na juyo baya domin ganin tazarar dake tsakanina da fatalwa Surayyah da kuma iskar guguwar da suke tafe kusan tare wanda bansan bala’in da ta kunshe a ciki ba. Sai gani nayi tana wani masifaffen gudu wanda na tabbata ba jimawa zata riskeni ta kamoni. Amma duk da haka ban sare ba na juya na kara kaimi a kan wanda nake da shi na cigaba da gudu cikin dajin, ina iya juyo dariyar da take marar dadin saurare. Munyi gudu na a kalla minti 20 nan take naji kafafuna suna neman cirewa saboda gudun da nake ba na wasa bane, ana iya kiransa gudun famfalaki.

A hankali na fara rage gudu daga karshe ma na yanke shawarar tsayawa, zuciyata ce tace da mutuwa a wahalarce gwara mutuwa a saukake don haka na gaji da wahalar da kaina da nake gwara in tsaya ta kasheni kawai. Tsaye nayi na juyo baya ina kallonta ina haki, cikin abun da baifi seconds 20 ba sai gata, ai kuwa tana zuwa na ga wannan iskar guguwa ta zo ta kwasheni tayi sama dani, nan take na fara wulwulani a cikin iska. Ba shiri na fara ihu ina rokonta tayi hakuri ta saukeni muyi magana. Ita kuwa ko saurarena batayi ba, asali ma daga kai sama tayi tana kyalkyala dariya irin wacce ta fi kama da ta mugunta. Na dade ina ihu yayin da iska ke hajijiya da ni a tunanina ko za’ayi katari wasu mutanen su jiyo su kawo min dauki, amma shiru ko tsuntsu banga alamar sa ba, kai ai ko dan adam yayi niyar kawo min dauki yayin da idanunsa sukayi arba da abinda yake faru na tabbata shima juyawa baya zaiyi a guje ya fara neman dauki, don haka na cire rai da zuwan wani domin taimakona na cigaba da bata hakuri.

Zuwa can da ta ga dama dan kanta ta tsayar da iskar, sai gani tsaye cik a cikin iska tamkar wanda aka daure da igiya ina reto. Surayyah na kalla ai kuwa ba shiri na kulle idanuna domin ganin yadda fuskarta ta dawo abun tsoro. Idanunta sun kara zazzarowa sun kuma zama baki kirin, ga wani gashi da ya zubo mata tun daga kai har kusan kasar kafafunta. Hannunta kuwa na hangi wata doguwar wuka da take ta sheki yayin da farin wata ya haskata. Idanuna na rufe ina jiran jin abinda zai biyo baya kwatsam sai ji nayi an dora min wuka makoro, ba shiri na bude idanuna ai kuwa sai ganin Surayyah nayi a gabana rike da wuka itace ta dora min wuka a wuya, tana wani jujuya kai tana dariya jajayen hakoranta na bayyana. Bansan lokacin da gumi ya fara tsatsafo min ba, duk kuwa da iska na kadawa a wajen. Cikin matukar tsoro na fara fadin, “Dan Allah masoyiyata Surayyah ki saurareni ki tsaya muyi magana, idan kika kasheni tabbas kin aikata kuskure mafi girma a rayuwarki wanda zaki kare rayuwa kina nadamarsa”.

Fatalwar Delu Part 7

 

Cikin tsawa wanda yasa ni zabura ta ce, “Barazana kake yi min”. Ai kuwa da sauri na ce, “Ba barazana nake miki ba, amma ba makawa idan kika kasheni kin kashe masoyinki na hakika wanda ke sonki matuka gaya, ina mai tabbatar miki zan iya bada zuciyata a saka miki ki rayu ni na yarda na mutu”. Gani nayi ta saki baki kamar sakara tana kallona, hakan yasa na fahimci yan kalaman da na fara fadi zasu iya tasiri a gareta, watakil ma in nayi sa’a su tseratar dani daga mutuwa a hannunta. Don haka na sunkuyar da kaina kasa kadan ina mai ajiyar zuciya kana na dago na kalleta duk da kallon fuskarta na matukar tsoratani amma a haka na daure domin tsarin nawa ya tafi dai-dai cikin sanyin murya na ce, “Amma ba komai ko na mutu yanzu ni ba zanyi nadama ba, na tabbata mutane kadan ne sukayi sa’a da nasara a rayuwa kamar ni. Domin kuwa mutuwa a hannun kyakykyawar mace wacce ta zarce zinari daraja ta fi tauraruwa haska kamar ke babban dace ne a duniya ni kuwa na dace domin kuwa ga hakan nan yana shirin faruwa a gareni”.

Na danyi murmushi wanda bansan daga gidan uwar wa na samo karfin gwiwar yinsa ba, kana na dora da cewa, “To wai ni a rayuwa me ya rage mini? Shin me yayi saura a cikin burika da muradin da nake son cimmawa a rayuwa? Ai dukkansu sun cika tun ranar farko da nayi arba da kyakkyawar fuskarki. A kalla zakin muryarki ya kore damuwar duk wani abu marar dadi da na taba saurara a rayuwata, furta kalmar so da kikayi a gareni kuwa shine abu mafi kololuwar dadi da na taba ji tunda aka haifeni kawo yanzu. Na kasance mutum mafi sa’a a duniya tunda har soyayyata ta sama gurbi a cikin zuciyarki Surayyah ta. Ko kinsan cewa ke daya ce tamkar dubu, ke tauraruwa ce a cikin taurari. Ma’ana haskenki ya shallake na saura. Don haka ko da zaki kasheni yau, ina so in tabbatar miki da cewa ke daya ce a cikin zuciyata, dake zuciyata ta aminta. Domin ke kadai nake kallo a matsayin mace, ni dai da sonki zan tafi kabarina. Wannan itace a matsayin sallama kuma bankwana a gareki kafin in tafi kabari Surayyata ina sonki sosai”.

Idanuna a kanta, har yanzu ta tsaya cik ta kafeni da kwala-kwalan idanunta, ta saki baki tana kallona. Kallon da na gaza gane na shauki ne ko na mamaki, don haka na sake sauke ajiyar zuciya, game da cewa, “Bismillah yanzu zaki iya yanka wuyana ki kasheni Alhamdulillah ko ba komai ni a hannun masoyiyata na mutu, nafi wanda suke mutuwa a hannun yan ta’adda”. Da gama fadin haka na rufe idanuna alamun ta aiwatar da abinda take shirin aikatawa, amma a karkashin zuciyata dukan tara-tara take yi. Hala ma a dai-dai wannan lokacin idan ka yanka jikina ba lalai ka sama jini ba, ko ba komai dai nasan yanzu na raba kafafuna biyu ne, daya a duniya daya a lahira, musamman da nake jin wuka daf da makogorona. Jin an kusa minti guda Fatalwa Surayyah batayi wani yunkuri ba, yasa na bude ido daya a hankali ina kallonta, ai kuwa sai gani nayi ta rikede ta canza daga fuskar abin tsoro zuwa fuskar kyakyawar yarinya da na fara ganinta da shi. Bisa mamaki kuma sai gani nayi ta janye wukar daga wuyana ta daga kai sama ta bushe da wata mahaukaciyar dariya irin dai wacce ta saba yi.

Zuwa can kuma sai gani nayi ta tsuke fuska ta daina dariyar, “Bude ido ka kalleni”. Abinda ta fada kenan, ai kuwa da sauri na bude idanu ina kallonta. “Ka tabbata abinda ka fada haka ne babu karya a ciki?”. Nan take na daga kai sama ina girgizawa alamun eh. Kana na kara da cewa, “Eh kwarai da gaske nake har cikin zuciyata”. Kara bushewa tayi da dariya, nan take kuma sai naji an fara yin kasa dani har sai da na zo kasa kafafuna suka dira a kasa ita kuma tana sama cikin iska tana dariya, ni kuwa na daga kai ina kallonta, tsuke fuska tayi ta kalleni fuskarta ba alamar wasa tamkarma bata taba yin dariya ba ta ce, “Yau dai ka ci darajar so na yafe maka, amma ina gargadinka karka kuskura ka sake ko da kallon wannan yarinyar, kai bama ita ba ko da wasa naga kana kallon wasu matan da wata manufa sai na kwakule maka ido. Sannan itama kaje ka sameta ka yanke duk wata alaka da ka kulla da ita, in ba haka ba hatta ita kanta sai nayi maganinta. Sannan shima wannan Bukar din ina so ka isar masa da sako, lalai-lalai gobe idan baka kai shi inda na ce mu hadu ba yau zai dandana kudarsa a wajena da kanina da mahaifiyarmu”. Tana gama fadin haka naga ta sake kyalkyalewa da dariya ta fara tafiya cikin iska, har ta danyi nisa ta juyo ta kalleni ta ce, “Ka kula da kanka masoyina ni kadai ina sonka sosai”. Tana fadar haka ta juya, ni kuwa ina tsaye kallonta kawai nake kamar sakarai, har tayi nisa sannan hankalina ya dawo jikina na tuna ashe fa a dokar daji nake, don haka na fara kwalla mata kira a kan ta zo ta taimaka ta daukeni ta mayar da ni gida, amma shegiyar fatalwar nan tayi banza dani.

Yanzu ma dai ba na ce nepa ta dawo ba 😂 dan mu bata tsaya mana ba, rashin typing dina yana da alaka da rashin caji

Back to top button