🐅MATAR DAMISA🐅
(The Wife Of Tinger)
Written and story by
Asma’u Muhammad Auwal
(ASMEETAH NOVEL✍️✍️)
*NASARA WRITERS ASSOCIATION*
___________________________________
{{ *_Nasara abin so ga kowa, domin marubuta da cigaban rubutu, alƙalaminmu ƴancinmu._* }}
___________________________________
https://www.facebook.com/103637491942644/
💫💫 *{{N W A}}* 💫💫
بِسْــــــــــــــــــــــمِ اللّهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيْم
*BOOK ONE*
🅿️ ——-> 61 & 62 <——-
___________________________
A razane Junaid ya tashi daga kan Ayush yana faɗin “subhanallah Mom meya kawo ki ɗakina?”
zuba masa ido tayi tana ƙara jinjina kai “aah ƙwarai dole kace mena zo yi ɗakin ka, kana shan sharholiyar ka! marar kunya har kana da bakin magana ka danne ƴer mutane sai faman nishi take…”
shafa suman kansa ya soma yi kai a sunkuye.
ita kuma Ayush tin shugowar Mommy ta danna kanta a cikin pillow tsabar kunya ta kasa ɗagowa, Mommy ce ta kalli yanda take tace “Ayusher kin nuna mun cewa Aure kike so, acikin mutum biyu ki zaɓi ɗaya Junaid ko Doctor Hasheem? zuwa gobe ki fitar da gwani,
kai kuma Junaid idan ta fitar da kai zuwa wani satin za’ayi muku baiko, kar ina zaune naga an ajiye mun jariri…”
Mommy tana kaiwa ƙarshe tayi ficewar ta ga flask na kayan abinci wanda ta ajiye su akan table.
Ayush tana zaune jin abunda mommy ta gaya yasa tayi firgit bata san lokacin da ta tashi zaune ba, tana ta zazzaro ido waje zuciyar ta kuwa kamar wanda ake buga ganga a ciki! “tashin hankali” abunda ta furta kenam a cikin zuciyar ta.
shi kuwa Oga Junaid tinda mommy ta fara maganar Aure yaji kamar an zare masa rai, a hankali yake motsa lips ɗinsa “Aure kuma! ni Junaid? a’a bada ni ba, i can’t marry any girls, bana tunanin zanyi Aure a rayuwata bani da ra’ayin yin Aure..” haka yake ta maganar zuci kansa a ƙasa.
itama Ayush da abunda take faɗi a ranta “taya zan zaɓi ɗaya a cikin Yaya Junaid da Dr Hasheem alhalin ba wanda ya taɓa cewa zai Aure ni, hankali na yafi kwanci da Yaya Junaid sai dai matsala ɗaya shine mahaifina bazai taɓa yadda da al’amarin nan ba, ni kuma bazan taɓa Auran kowa ba inba Yayana Junaid ba domin shine makami na..”
******
*FADAR SARKI RAAMUD*
zaune yake a kan kujerar mulkinsa na alhurma gwanin sha’awa, da wasu ɗirma-ɗirman mutane a ta gefensa suna tsatstsaye da baƙaƙen kaya a jikinsu wanda kana ganinsu kasan ba mutane bane, su kai biyar ga kuma damusa a gefen kujerar sarki!
makeken madubi yasa a gaban sa yana ta kallon abunda ke faruwa ata ɓangaren su Ayush, murmushi yasau mai ƙayatarwa ya lumshe kyawawan idanuwan sa yace “Ɓingel Mayushert na gaya miki Auren ki da Junaid ba mai yuwa bane, duk abunda nace bazai yu ba toh bazan taɓa barin hakan ya yuba domin shi ɗa ga ɗan uwa nane kuma maƙiyi na”
yana kallon cikin mirrow yana kuma furta kalamansa ba tare da su Ayush sun san yana yi ba.
“Hummm! zanga ta yanda za’ayi baikon nan, ni na yadda ki zaɓi kowa a matsayin mijin ki amma banda Junaid, idan kuwa ba haka ba zanyi maganin shi…”
******
wata kyakykyawar mata ne black beauty ga hanci kamar zai shige baki tsabar tsayi, idanuwan ta manya-manya farare tass ga zara-zaran gashin ido! girar ta kuwa har sun haɗe biyu, da ƙaton mayafi a kanta ta rufe duk ilahirin jikin ta,
a hankali take motsa ɗan ƙaramin bakinta ta ɗaga hannu sama idonuwanta suna kallon sama tana roƙon Allah (S.W.T)
“Yaa Allah ka dube ni da idon rahma kaji ƙaina ka tausaya mun ka dubi maraici na yaa Allah ka gafarta mun, ka yafe mun! a baya ni christal ce amma a yanzu ni tubabbiya ce na riƙe addinin musulunci hannu bibbiyu Allah ka kankare mun zunubai na,
ya Allah bansan a wani hali ƴata take ciki ba, Allah ka taimake ta ka bata nasara akan JUNAID! ka bata ikon aiwatar da aikin ta akan Junaid waran samar masa da lafiya, Allah ka kuɓutar da Junaid daga halin da yake ciki duk da nasan ni na jefa shi cikin mawuyancin halin nan yaaa Allah……” lokaci guda ta fashe da matsanancin kuka mai cin rai
“Yaa Allah ka haɗa zuciyoyin mutum biyu JUNAID DA AYUSHERT kasa su zamo ma’aurata……
“Ba Ameen ba..”
jin anyi magana ta bayan ta yasa ta tsayar da addu’ar ta shafe jikinta,
tana zaune akan sallaya
a hankali ta waigo bayan ta tana fuskantar wanda ya shugo cikin room ɗin, samun guri ya yi ya zauna a bakin katafaren gado mai laushin gaske wanda aka ƙera da gwal, ɗakin sai canza haske yake kala-kala ga wasu mahaukatan labulaye masu tsadar bala’i, capet kuwa kana takawa ƙafarka tana lotsewa cikin carpet..
“Shugaba ya kamata ka dakata haka, wai shin mai Junaid ya yi maka ne? yaron da bai san komai ba, hatta mahaifinsa bai san laifin da ya yi maka ba har ka tsane shi balle shi Junaid da bai taɓa sakaka a ido ba,
yanda Ayush take a gurinka a shima Junaid yake jininka ne…..”
bata ƙarisa maganar ba ya daka mata wani gigitaccen tsawa yana faɗin “ki kiyayi bakin ki kina shiga gonar da ba taki ba, ki tsaya a iya matsayinki na matata kuma uwar ɗiyata, domin idan ba haka ba zansa Manya-manyan aljiin ɗina su ƙarƙameki a cikin kurkuku na ina ɗaga miki ƙafa ne saboda ke sarauniya ce..”
taso wa tayi daga inda take zaune tana tafa hannayen ta tana dariya ta zauna itama a bakin gado daf da sarki ta kafeshi da ido tana murmushin takaici tace “shugaba dan Allah kada ka fasa sa a ƙarƙame ni nayi zaman daji da yake da sauraye da ƙwaruna da macije da kunamu ga kuma sanyin duniya duk wahalar nan anan nayi rayuwa tare da ɗiyata mun riga mun saba da wahalar ai balle kurkukun ka da yafi ɗakin governor tsaruwa,
shi daman gaskiya ɗaci gareta kuma bazan fasa gaya maka gaskiya ba…”
“Hahahaha! Sarauniya Bara’at shikenam mu zuba tsakani na da ke wazai ci galaba akan yaran nan, ni sarki Raamud bazan taɓa barin Junaid ya Auri ɗiyata ba sai dai mu mutu tare ni da shi, ko kuma shi ya mutu”
ya ƙarisa maganar yana nuna ta da yatsa.
itama murmushi tayi sannan tace “toh mu zuba mana insha Allahu sai Ayusher ta Auri Junaid ko bayan rai na…”
jinjina kai ya yi sannan yace “mai kike taƙama da shi?”
buɗar bakinta tace “Allah shine abun dogaro na,
kai kanada tsafi ni kuma inada Allah…..”
tin kafin ta ƙarasa maganar ya ɗauketa da zazzafar mari sai data faɗo daga saman bed ta kama fuskar ta a gigice ta ɗago da kanta tana kallonsa tace “ni ka mara?..”
“na mareki ko kin manta ni wanene? idan kin manta bari na tunatar da ke ni nine *Sarki Raamud* kuma *Sarkin matsafar duniya* ina da magoyan bayan manya-manyar aljanu, ki kiyayi tsayawa a gabana kina faɗa mun maganganu son ranki, kada ki mayar ni ƙaton arne kamar iyayenki da suka mutu a banza da wofi, ni cikakken musulmi ne,
kin koyawa ɗiyata taurin kai itama bata jin magana ta kamar ke,
Junaid kuma zan kashe shi naga iya shegenku, mttsswww!!!”
tashi yayi ya bar mata ɗakin
kifar da kanta tayi ta soma rera kuka……
*****
“Bros wai dan Allah wacece wannan Ayushert daka damu akan ta ko abinci ka kasa ci kullum sai ambatar sunanta kake, kai ka daina damuwa akan dukan da Oga Junaid ya yi maka ma..”
turɓune fuska tayi tana kallon Dr Hasheem wanda yasa abinci a gaba ya kasa ci sai labarin sufar Ayush yake ta badawa.
Alhamdulillahi Dr ya fara samun lafiya, ya dawo gida ƙanwarsa ce take temaka masa da wasu abubuwa sai ƙannensa biyu maza,
ƙanwarsa wacce ake kira da Lailah ƴer shekara 18 tana zaune a gaban Yayanta Dr Hasheem tana son jin ƙarin bayani akan Ayushert, domin ta fahimci ba ƙaramin so yayanta yake yi mata ba, hatta fuskar wayarsa photon Ayush ce a jiki.
murmushi ya yi sannan ya kalli ƙanwarsa Lailah yace “ita ɗin rayuwata ce, kuma mutuwa ta domin idan babu ita zuciyata bugawa zata yi”
zaro ido waje Lailah tayi ta jinjina kai sannan tace “tab al’amarin babba ne, amma dan Allah Bros kar ka mutu ka barmu kaga bamu da kowa, iyayen mu basa raye, kaine mai kula da mu karka mutu akan wata mace…”
murmusawa ya yi sannan yace “Hummm ƙanwata kenam! muga wayarki”
miƙa masa wayar hannunta tayi mai ƙirar iphone ya kunna fuskar wayar yace “wannan photon waye akan screen ɗin wayar ki” ya juyar mata da wayar yana nuna mata,
sunkuyar da kanta ƙasi tayi a hankali tace motsi da leɓɓen ta tace “Oga Junaid ne..”
yace “meye matsayinsa a gurinki?”
still kanta a ƙasa tace “Bros kaima fa ka sani ina masifar son Oga Junaid”
short laught ya yi sannan yace “ke masifar son Junaid kike ni kuma bala’in son Ayush nake,
ni bazance kada ki so Junaid ba sai dai kisa a ranki cewa Junaid bazai Aure ki ba domin shi babu maganar Aure a story book ɗinsa, shine abunda zan gaya miki, ki maida hankali wajen karatunki duk da nasan Junaid ba wani kiranki yake a waya ba….”
turɓune fuska tayi
sannan ta fisgi wayarta ta tashi da gudu tana kuka ta nufi ɗakinta, ita a rayuwa ta tsani taji ance Junaid ba Aurenta zaiyi ba..
itama Lailah ba’a barta a baya ba wajen kyau, chaculat colour ce ita ba baƙa ba ita ba fara ba kyakykyawa ce ga gashi sai dai ita tanada ƙiba dirin jikine da ita ko ina a cike yake ɓul-ɓul.
iyayensu su huɗu suka haifa Allah ya yi musu rasuwa a tafiyarsu ƙasar saudi jirginsu ya faɗo,
Dr Hasheem shine babba sai second born wato Muzaffar shi yana karatu a ƙasar egyph, sai Haydar shi kuma yana karatu anan nigeria day yake yi a gida, sai Autar su Lailah…
Domin sauke CikakkenLittafin Sai Ku Danna bulun Rubutun dake kasa
Matar Damisa Book 1 Complete Novel Document
*MASHA ALLAH*
Follow me on my whatsApp
09065443871
More comments more more read more😘
*SHARING*