Hausa novels

Wace ce ita (Who is she) Chapter 71 Complete Novel

WACECE ITA⁉️(WHO IS SHE⁉️)

Unique Barakancy🌹

SEVENTY-ONE📍

Jin abun sukayi tamkar saukar dalma kadama mami taji labari da take tinanin babu ita a zancen, umm ko wani tashin hankali ne ya saukar mata taji dama bappan bezo ba, gabadaya shock suka shiga aka rasa wanda zecewa bappa wani abu, babban tashin hankalinsu shine bappa kaifi dayane, da wuya ya fadi abu ya chanza, su da girmansu ma basu tabaji bappa ya yanke tsattsauran decision akansu irin haka ba, tabbas ya barsu sunyi rayuwar yanci, ya kuma yiwa ko wacce uzuri akan sake yin aure saboda trauma din aurensu na farko, sai hakan yasa suka sakankance har suka cire maganar aure daga tsarinsu, kwatsam kawai sai bappa yace nan da sati ze hadasu da yayansu a musu aure, wannan wani kalan abun kunya ne?…
Tashi bappa yayi ya fita ya barsu a gurin tinda ya gama isar da sakonsa, masaukinsa na gidan ya koma yayi kwanciyarsa hankali kwance…..
Sai da bappa ya fita sannan mami ta samu kwarin gwiwar yin magana, kallon umm tayi cikin tashin hankali tace;
“Innalillahi wa inna ilaihi raji’un, kinga abinda kika janyo mana ko? Hankalinki ya kwanta yanzu? Wannan wani kalan masifa ne muna zaman zamanmu, sai da nace miki mubi abunnan a hankali kika ki, yanzu ya kikeso muyi jamila”……
A rude umm tace;
“Amma yaya daga yin magana da muhammad shikenan sai ya kwasa ya fadawa bappa, cewa fa nayi mu fara shawara a tsakaninmu, wallahi be kyauta min ba”…..
“Toh ya akayi bappa yasan bana daga wayar abubakar, wani munafukin ne ya min wannan, ko shi ya fadamasa da kansa?”…..
“Waya sani ma? Tinda muhammad ya iya kiran bappa ai abubakar zeyi, wallahi muhammad ya bani mamaki”…
“Kinga duk wannan zancen naki baze fisshemu ba, ni yanzu solution nake nema, bari in kira anna”….
Mami ta fada tana daukan wayarta dake kusa da ita, wayar bata jima tana ringing ba anna ta dauka, a speaker tasa wayar ko gaisawa mami bata bari sunyi ba tace;
“Anna muna cikin tashin hankali, anna mun shiga uku, dan allah dan annabi ki taimaka ki rufa mana asiri ki shawo mana kan bappa”….

Matar Makaho Complete Hausa Novel Document

“Nitsu fatimatu, nitsu ki fadamin meya faru, me bappan naku yayi?”…..
Tass mami ta kwashe komai ta fadamata, tindaga batan da baby tee har zuwan bappa yanzu da abinda tace musu, da kuma tabbacin da umm take dashi na cewa abby ne ya kira bappa saboda dashi kadai tayi magana…….
Sai da anna ta gama sauraranta tsap sannan tace;
“Matsalarku ba kwa yin shawara sai abu ya kwabe muku, wannan ai duk ba abun tashin hankali bane, bansan meyasa kuka daga hankalinku haka ba, na farko jamila tana da gaskiya akan auren da tace ayiwa ita zara’u saboda babu uwar da zataga yarta ta fara irin wannan halin hankalinta ya kwanta inba aurar da ita tayi ba, na biyu menene abun tashin hankali dan yace ku koma dakinku?, kun dauka jindadin ganinku a haka muke? Ni kaina kawai zuba muku ido nayi inga gudun ruwanku, wace irin ni’ima ta rayuwace ubangiji be muku ba? Toh saboda me bazakuyi aure ku cike wannan ni’imar ba?, Shikenan kun fiso ayita zaginmu a gari ana cewa mun zuba muku ido kunki aure sai dai kadarori da kuke tarawa? Yau a ganku a wannan motar gobe a ganku a wannan? Yau kune kun gina wannan gdan kun gina wanchan? Su kansu ya’yan naku sai sun fi jindadi idan suka ganku tare da mahaifansu, so this is the right time da zakuyiwa kanku fada kuyi abinda ya dace”…..
Karap umm tace;
“Eh anna munji zamuyi amma dan allah dan annabi ki rokar mana bappa ya bamu time”….
“Time na menene kenan jam?”….
Dake itama sometimes tana kiranta haka…
“Wallahi anna komai ya kachame min, gani da uban patients a duka hospitals dina, ga wani research work da nakeyi akan wata cuta, ayyuka kota ina sun min yawa, rabona da samun cikekken nitsuwa har na manta anna, ga lamarin baby tee yana matukar damuna, wallahi I’m mentally derailed, bazan boye miki ba idan kukayi forcing dina nayi aure bangama clearing abinda ke kaina ba bazamu taba zaman lafiya ba, I just need time I promise koba gidan muhammad ba zanyi aure”…

Surbajo Complete Document

“Eh wallahi anna nima I’ve been in series of critical cases, tambayi jam ko zaman gidannan banayi in banda jiya zuwa yau da abinnan ya faru, ki taimakemu kiyiwa bappa magana ya sassauta mana dan Allah, gwarama jam zata iya komawa gidan muhammad, ni kuwa bansan ta inda zan fara ba”…..
Da sauri umm ta katse mami..
“Ah ah ya zakice haka, just speak for yourself please, haka na gayamiki zan iya komawa gidan nasa”…
Dakatar dasu anna tayi da fadin;
“Ya isa haka, duk ku kwantar da hankalinku, duk naji uzurirrikanku kuma insha allahu zanyi iya bakin kokarina gurin ganin ya kara muku lokaci, kunsan halinsa idan yayi magana da wuya ya chanza amma wannan karan zan dage har sai naga ya daga muku kafa ko yayane, kar dai ku sake sakankancewa”…..
Cikin farinciki kamar ance musu bappa ya yarda ne mami tace;
“Insha Allah bazamu sakankance ba, mungode sosai annan mu, allah ya kara lafiya ya bar mana ke”…..
“Thank you so much mother, allah ya kara girma”…
Cewar umm cikin farinciki itama….
“Ameen, ke jam abinda nakeso dake shine kija yarki a jiki sosai, yaran zamani ba’a hukuntasu da duka saidai nasiha bare ita da bata taso damu ba, dole sai ana mata uzuri a wasu abubuwan, bance kar a tsawatar mata ba amma duka yayi tsauri, sannan kar kice zakiyi fushi da ita dan nasan halinki, ki jata a jiki ki mata nasiha ki karanta mata rayuwa yanda zata gane, nima kinga da kuka kirani aina saurareku dukda bappa ya fiku gaskiya, toh kema ki kasancewa yarki wacce zata fara nema in abun farinciki ko akasinta ya sameta”….

Jinin Sarauta Complete Novel Document

“Insha allah anna, dama banyi fushi da ita ba, ina tashi yanzu gurinta zanje ma, nagode sosai”….
“Shikenan sai kun jini”….
Suna gama magana da anna umm ta tafi dakin baby tee kamar yanda tayi alkawari, hangota tayi a cikin bargo tana kwance, sosai taji babu dadi hango abun drip daga sama means saida aka mata karin ruwa, karasawa tayi ta dan yaye bargon ta dora hannunta a wuyarta, bude ido baby tee da farkawarta kenan tayi, tana ganin umm ce tayi saurin maida idon ta rufe, tunowa tayi da hakurin da deen yace ta bata, sai kuma taji tsoron karta kara dukanta gwara tayi sauri ta bata hakurin, bude idonta ta sakeyi daidai umm na sake dora hannuta a goshinta, cikin tsoro tace;
“Umm kiyi hakuri bazan kara ba, karki sake dukana dan Allah”….
Murmushi umm tayi ta dagota tace;
“Bazan kara dukanki ba my princess, wannan ma ba a san raina bane”….
Sai kuma ta ruko hannunta tace;
“Yanzu fadamin gaskiya meyasa kika je gidan? Karki boyemin komai, ”….
Sunkuyar da kai baby tee tayi ta bata exact labarin abinda ya faru, ta karashe da fadin;
“Ai be kamata ya bada number ba ko?”….
Shiru umm tayi tana mamakin abinda yasa deen be basu wannan labarin ba, koda be basu exact labarin ba atleast sai yace suna tare da baby tee din kafin ya nemeta ya rasa, wato shiyasa ya dinga cewa su kwantar da hankalinsu kenan, sai ta girgiza kai tace;
“No! You’re very wrong, koda ya bada number baki da right din da zakiyi tafiyarki tinda ba sa’anki bane, infact wannan highest form of raini ne saboda yana gaba dake, abinda kikayi is very very unnecessary, ko kinada wani dalilin ne bayan haka?”….
A sanyaye tace;
“A’a”….
“Toh karki sake and koda wasa banaso wani abu ya kara kaiki gidansu khaleel kome ya faru kuwa, infact kwata kwata babu tarbiyya a hakan, ko kinfiso kita dagamin hankali ne?”….
Da sauri ta kada kai alamar a’a….
“Good, should I tell you something daughter?”…
“Yes umm”…

TAKARI… Complete Document By Aihausanovels.com.ng

“You’re my happiness and the best gift Allah had given me! Allah ya bani ke a lokacin dana fidda rai fatima, sai kuma Allah ya jarabceni ya rabani da ke a lokacin da ban taba tsammani ba but I still never give up saboda nasan komai yayi farko zeyi karshe, kuma shi ubangiji yana jarabtarka da abinda kafiso ne but despite bana tare dake I’ve never failed to pray for you even for once, kullum sai na cewa Allah ya karemin ke a duk inda kike, yanzu da nake tinanin na cinye jarabawata shine kike yin abinda be dace? Ko kinaso hawan jini ya kamani ne? Don’t you know your mother is a very weak person when it comes to you?”….
“Noo umm, kiyi hakuri bazan kara ba”…..
Baby tee ta fada jiki a mace…..
Sosai umm ta mata nasiha me ratsa jiki ta kuma bata wasu labarai akan wahalar datasha na rabasu da akayi, ba karamin mutuwa jikin baby tee yayi ba sai gata harda kuka…..
Sai da umm taga jikinta ya mutu murus sannan ta tashi ta tafi ta barta…..
Baby tee nata so ta tambayeta kota fasa mata auren da tace amma ina bata da kwarin gwiwar tambaya, dole ta hadiye zancenta har umm ta fita…

A kofar gidansu me mashin din ya saukesa bayan yayi shawara da zuciyarsa yaga gwara ya fara zuwa gida kafin yaje gidansu baby tee, shiga ciki yayi ya dauko kudi me yawa ya basa, sosai yayi masa godiya sannan sukayi sallama khaleel ya shiga cika….
Direct part dinsa ya wuce, be tsaya a ko ina ba sai toilet, ya dade a tsaye a gaban shower ruwa na dukansa kafin ya fara wanka, haka kawai tinanin momma ya fadomasa, maganganun da sukayi da bappa na dawo masa, ranar yaje gurin baby tee sai ya nemi ya fara gaisawa da bappa, sai bappan yake tambayarsa ya gurin mahaifiyarsa sai yayi shiru, anan ne bappa yace ya daukesa kamar mahaifinsa da ze iya sharing duk wata matsalarsa dashi, haka kawai yaji mutumin ya kwanta masa yaji yanaso ya fadamasa, cemasa yayi sun dan samu sabani ne da ita sannan bata garin yanzu…..
Fada sosai bappa ya masa ya kuma nunamasa lallai yaje ya shirya da mahaifiyarsa inba haka ba baze taba ganin daidai a alamuransa ba, tindaga wannan ranar yake kiran wayarta amma amsar dayace a kashe, har na abdul ya kira so babu adadi dan ya tambayesa labarin mahaifiyarsu amma baya samunsa shima, sai yanzu yake tabbatar da maganar bappa dan baya sati cikin kwanciyar hankali wani abun be taso ba, ko yanda deen yake tarwatsa lamarinsa da baby tee kadai ta ishesa, sai ya kudirta aransa a yau dinnan ze tafi gurin mahaifiyarsa yaje ya bata hakuri, gwara ya fuskanceta ya nemi yafiyarta ko zega daidai a lamarinsa…..

Yar Harka Page 1-10 Hot Romantic Hausa Novel

 

Fitowarsa parlour kenan bayan ya gama shiri, ga mamakinsa yaji ana knocking kofa, tsoro ne ya kamasa duk a tinaninsa deen ne ya dawo, zaro ido yayi jin an turo kofar dan besan a bude ya barta ba, kawai yaga momma tashigo abinda ko a mafarki be taba tinanin ze ganta yanzu ba, abu na lamarin ubangiji kuma kamar ba yanzu ya gama tinaninta ba….
Kallonshi tayi daga sama har kasa sannan ta tabe baki tace;
“Sai yanzu uwartaka ta sakoka kenan?”…..
Zubewa a kasa yayi ya hade hannayensa alamun roko yace;
“Momma nasan ni me lefi ne a gurinki, rashin samunki a waya kuma yasa na kasa tunkararki badan wani abu, ina rokonki dan darajar Allah da annabi ki yafemin”….
Sakin baki momma tayi tana kallon khaleel, wai khaleel ne yake neman yafiyarta? Is she dreaming or what? Wannan ya tabbatr mata da asirin da aka masa ne ya karye, ita dama tasan ba haka danta yake ba, dagosa tayi tace;
“Ni ban rikeka da komai ba son, dama nasan bayin kanka bane, duk aikin asirine amma alhamdulillah tinda Allah yasa ka dawo hanya, burina kawai ka rabu da tsinanniyar yarinyar nan”….
“No momma this has nothing to do with her please, wallahi duk abinda nakeyi ba ruwan wifey”….
“Au abinda zakace ma kenan?”…..
Saurin chanza zancen yayi da fadin;
“Meya samu wayarki inata kira bana samu keda abdul”…..
Tsaki taja tace;
“Cire layin nayi saboda ubanka da yayita damuna da kira bayan nayi nayi ya bani takardata yaki tinda yace ze auri mayyar yarinyar da kake yiwa naci, abdul kuma baya kasar”….
Rintse ido khaleel yayi har bayasan tuno abinda daddy yaso aikatawa….
“Ina abdul ya tafi?”…
Ya tambaya batareda yabi takan wanchan maganar ba….
“Yana Russia, ina mahaifin naka yake ya bani takardata dan banga alamun yana gidannan ba?”…
“Bashi da lafiya yana asibiti, muje in kai ki”….

Ruwa ta watsa bayan fitar umm daga dakin, ba lefi ta dan ji karfin jikinta, kwanciya tayi tana janyo wayarta, kunna wayar tayi ta kure wayar da ido tana jiran wayar ta kawo, direct WhatsApp ta fada bayan wayar ta kunnu, kamar wacce ake zugawa tashiga chat dinsu da deen, da hotonsa data turo ta fara cin karo a chat din kuma dama shi take nema, saving hoton tayi ta kashe data, gallery ta koma ta kure hoton nasa da kallo, batasan me take nema ba amma haka kawai taji batasan dena kallon hoton sannan duk yanda zuciyarta kesan complimenting dinsa ta ki, ita dai kawai tasan tana jindadin kallon hoton..
Kiran eesha ne ya katse mata jindadi, gajeran tsaki taja kafin ta daga wayar…
Daga dayan barin eesha tace;
“Hi teema”….
“Hello eesha”…
“Ya kike? Tun jiya nake kiran wayarki a kashe”…..
“I was sick eesha amma naji sauki yanzu”….
“Subhanallah wallahi bansani ba, zanzo in dubaki anjima Insha Allah”…
“Ok sai kin zo”…
Da haka sukayi sallama ta kashe wayar…
Tana ajye wayar twins suka shigo, nan suka bige da hira…

Sosai jikin momma ya mutu bayan taga halin da daddy yake ciki, a haka ma da kyansa ba kamar sanda brain dinsa ya tabu baya gane kowa ba, yanzu ko tsap yake gane mutane sai dai wata uwar rama dayayi, dole ta hadiye duk wani maganganu data tanadar masa saboda tausayinsa daya kamata lokaci guda abunka da miji da mata, shiyasa ake cewa miji da mata sai Allah kuma ba’a shiga fadansu….
Daddy da kansa ya bata labarin duk wata barna da suka shuka shida alhaji habibu, da yanda suka dinga neman budurcin marainiyar Allah, da kuma irin halaccin da familynta suka masa dan a halin yanzu ma sune a tsaye akan lafiyarsu, asibitin nan ma kakanta ne yasa aka dawo dasu dan sufi samun kulawa, cikin ikon Allah kuwa hankalinsu ya dawo, amma shi yasan baze kai labari ba saboda koda ya samu lafiya yasan yan kungiyarsu ta asiri bazasu barsu ba saboda doka ce duk wanda ya tona musu asiri toh tabbas sai ya bakunci lahira, mamaki ma suke yanda suke zaune da ransu haryanzu…..
Ya karashe da fadin;
“In kinga khaleel be auri yarinyar nan ba toh su suka ki bashi, kuma bama fatan hakan”…..
Wata muguwar kunya ce ta kama momma tuno da irin maganganun data gayawa deen jiya ashe mijinta ne babban me lefe, tsakani da Allah suma kuma sun cutar da rayuwar baiwar allah, sun bada gudunmawa mara kyau sosai a rayuwarta, suka dauki tsanan duniya suka dorawa yarinya batareda wani kwakkwaran dalili ba, sai gashi Allah ya fara mata sakayya tin a duniya, ga dai daddy a kwance sai jinya yake cike da danasani, abun kunyan kuma bappa ne ke tsaye akan lafiyarsa, ita kuma ko yanda Allah ya jarabci khaleel da son yarinyar kadai ya isheta ishara, gabadaya ya koma mata kamar ba dan data haifa ba, bata isa ta fada yaji ba sai abinda wifey tace, ita kuwa meyasa bazata yiwa kanta karatun tanitsu ba tin kafin duniyar ta juya mata gabadaya kamar su daddy?…
Khaleel kawai ganinta yayi ta fito tana kuka, hankali tashe yace;
“Momma lafiya?”…
“Khaleel kai ni gidansu fatima na nemi yafiyarta dana iyayenta, kaini dan Allah”…..
Ji yayi kamar an zuba masa wani abu me sanyi a zuciyarsa, tabbas wannan rana will be the most memorable day of his life, wai momma ce ke cewa ya kaita gidansu wifey? Unbelievable!….
Basu wani tsaya neman permission daga cikin gidan ba aka barsu su shiga saboda securities din sun san khaleel, an dade da basu umarnin barinsa ya shigo duk sanda yazo….
Sai da aka musu iso main parlor din gidan sannan suka shiga da sallama, mami kadai ce a parlourn sai tv daketa aiki…..
“Chief Justice?”….
Cewar momma tana kallon mami da mamaki…

Back to top button