Daga Amina Yusuf Gwamna.
Turaren ɗaki na ruwa mai daɗin ƙamshi, yana sa ɗakunanmu su zama na Musamman.
Babu shakka ɗakunanmu na da buƙatar kulawa ta Musamman, Domin su zama wajen hutawarmu tare da mazajenmu. Mu dinga tsaftace su, kuma mu dinga yawan sa turaren ɗaki na Musamman akai-akai.
Haɗin wannan turare, yana da sauƙin haɗawa. Kuma da kuɗinki ɗan kaɗan za ki haɗa shi.
KAYAN HAƊA TURAREN ƊAKI NA BAKHUR:
- Ruwan Bakhur
- Ambur
- Turaruka Madarori: Sk, Nasis, Sultan.
Za ki juye ambur a roba. Sai ki dake ambur shi ma ki zuba a ciki. Sai ki juye madarorin turaren Sk , Nasis , sultan. A dinga yarfashi a kafet , dardumar sallah da shimfidar gado.
KAYAN HAƊA TURAREN ƊAKI NA RUWAN SS:
- Turaren ruwa na SS
- Turaren kafi-kafi
- Madarar ambur
- Ambur dakakke
- Itacen Demask niƙaƙƙe
- Kafur
Idan kika haɗa su, sauran sai ki zuba cikin ruwan turaren SS. Ki juya su haɗe sosai. Sai ki zuba madarar ambur. Sai ki rufe su cikin mazubi. Ki dinga yarfawa a shimfidun falonki da ɗaki. Dardumar sallah, harma da jikin kujerunki.
Domin karanta yadda ake turaren wuta danna koren rubutu nan