Hausa novels

Zakuna Biyar Page 37 By Princess Teema

Tin da ta fara karantawa take murmushi har ta kai karshe, da sauri ta ce. “Manassa come and see something”……… Sauƙowa ƙasa Manassa ta yi, ta zo da gudu dan ta gani. A gaban laptop ɗin ta tsaya ta bayan Angelina, a natse ta fara karantawa.”Assalamu alaikum my flower, kin wuni lafiya? Fatan kina enjoying wannan yanayi na ruwan saman?. Tun daga farkon lokacin da na kalle ki, ban ga kyau kawai ba, na ga ƙarfi, ladabi da jarumta, ga natsuwa dake cikin zuciyar soja na gaskiya, kina ɗaukar jarumtarki da kima, kuma kina cike da kwarin gwiwa, kyanki ba a fuska kaɗai yake ba, yana tattare da muryarki, tsayuwarki, da yadda kike tsayawa daram ko da duniya na ƙoƙarin girgiza ki, ke jaruma ce mai zuciya mai taushi, a rayuwar da aka horar da mu mu fuskanci rikici da hatsari, ke ce nutsuwar dake kwantar min da hankali, kasancewarki kusa da ni ya kawo min salama fiye da duk wani filin daga, idan ina tinanin hutu, kariya da ƙarfin zuciya game da natsuwa, to ke nake gani, dikkanmu mun san nauyin wannan uniform ta soja, mun san ma’anar sadaukarwa, aminci da natsuwa, amma tare da ke, ina jin an fahimce ni ba tare da na yi magana ba, ina jin kariya ba tare da makami ba, kina tuna min cewa ko sojoji ma suna buƙatar peace, soyayya da wuri na numfashi mai kyau, saboda haka yau, na ajiye girman kai na, na furta maki daga zuciyata cewa na kamu da sonki, ba dan rauni ba, sai dan tabbaci, na zaɓe ki ba kawai a matsayin abokiya soja ba, sai dai a matsayin macen dake kwantar min da guguwata kuma ke ƙarfafa ruhina, idan soyayya fagen daga ce, to ke kaɗai ce wacce zan tsaya a gefenta da yardar rai, a zaman lafiya da a lokacin yaƙi”……… To jama’a ga shi nan na fassara maku kalaman na jiya, gaskiya kun sakani dariya jiya, to anyway ga shi nan dai na fassara.Bayan ta gama karantawa ne ta ɗan rungumo Angelina tana murmushi, a sanyayye ta ce. “Angelie ki amince mashi, waye ne ma? Kuma kaman soja ne ko? Ya iya kalamai”……… Kai ta jinjina. “Soja ne, a cikin sojojinmu yake, ina tinanin ma shi ne wanda yake mun magana, ba shi ne wanda ɗazun ya ce zai ɗauka mun V ba”. Ɗan zazzare idanu Manassa ta yi. “Wow he’s so handsome ai, chocolate guy, ya haɗu, look at his eyes, his gorgeous body, ta ko’ina ya haɗu”…… Nisawa Angelina ta yi. “Ni ina da wanda nake so, bawai Unays bai haɗu bane, ya haɗu, but ina da wanda zuciyata ta kamu da sonsa tin farkon mission ɗinmu”. Ƙara rumgumeta Manassa ta yi, tana murmushi ta ce. “Ke wanenen wannan?. Shi ne baki taɓa faɗa mun ba?”….. Murmushi ita ma ta ɗan yi. “Hmmmm ya haɗu over, shi ma fa soja ne, hoooooo Manassa i love him from the button of my heart, everything about him is special, his movement, his speech, his walking, his energy, his looking, the way he’s working, the way he’s praying har yasa na ji ina sha’awar addinin da suke yi, baki ga idan suna addininsu ina fita in tsaya ina ganinsu ba? Everyday shi ne yake tsayawa right side na sir Nirash idan zasu yi addini, i love his natsuwa over”. Kara zazzare idanu Manassa ta yi, tana ɗage gera ta ce. “You mean sir Zaynish?”……….. Gyaɗa kai ta yi sama alamar yeah shi fa……. Manassa ta ce. “Yeah, sir Zaynish karshen haɗuwa ne shi ma, especially his hair, African hair ɗinsa akwai ɗaukar hankali, yana da yawa kuma ya cika kansa”…… Jama’a kunsan gashi buzaye ai, akwai kyau, ashe kalle mana gashin Zaynish namu suke yi.Angelina zata yi magana Arya dake fama da aiki ne ta rigasu da cewa. “Rubbish! Ku ba zaku daina ɓata lokacinku a kan maza ba ko? Ba za ku kama abin dake gabanku ba ko?”…….. Harararta Angelina ta yi. “To tin da ke baki da lokacinsu sai aka ce maki muma haka ne? Mu muna son maza, especially kyawawa, ina son sir Zaynish, a kansa zan iya komai, abeg maintain word and mind your business!”. Ta kai karshe tana murguɗa mata baki. Kunsan Arya da karfin hali, hata ɗaukar raini, aikuwa tana juyowa ta kaiwa bakin Angelina bugu da karfi wanda sai da tasa ta saki karar da bata taɓa zatan zata yi ba. Ai a miliyan ta miƙe ta yi kan Arya, da sauri Arya ma ta miƙe tana faɗin. “Zaki sa hannunki a jikina ne?”. Angelina bata yi magana ba, tana zuwa ta damketa da faɗa, suka fara kokawa da karfi tamkar basu san juna ba, kome suka samu bugawa juna suke yi, da sauri Manassa ta taso ta fara ƙoƙarin rabasu, amma abin ya ci tura, hakan yasa ta fita da gudu sai ɗakin Leo, ta ce su zo su raba mata su Angelina suna faɗa.A lokacin suna tsaka da tattaunawa kan wannan tafiya da zasu yi. Leo ne ya ce Vash ya je ya rabasu kuma ya kawo mashi su nan. Miƙewa ya yi, Manassa ta yi gaba ya rufa mata baya, har lokacin faɗa suke yi sosai, Arya ta jiwa Angelina ciwo a baki na punch ɗin da ta dinga kai mata.Yana zuwa ya damkesu da hannu ɗaiɗai ya rabasu, sai huci dikkansu biyu suke yi. ……. “Dik ku je sir Nirash yana kiranku”. Vash ya faɗa a dake. Siririn tsaki Arya ta ja tare da wucewa gaba kafin Angelie ta rufa mata baya, V dai tana ta barcinta.Juyawa shi ma ya yi zai fita, a sanyayye V ta ce. “Sir Arvash”……. Tsayawa yai tare da juyowa, kallo ɗaya ya yi mata ya ɗauke kansa…….. Cike da zolaya ta ce. “A ranar da muka fara haɗuwa ka ce kana sona, nai maka kyau, amma yanzu meyasa ko magana baka mun? Ko kallona baka son yi?”. Ƴar ƙaniyar yarinya, tafa san meyasa yake dik wannan, na farko ta ce mashi ita ƴar GAT ne, kunga ko a nan ɓangaren soja tafi karfinsa, na biyu ga aljanar da take mashi, aljanar tasa ta ce in ya kula wata mace sai ta kashe macen, kunga kuwa ba zai so a kasheta ba ai.Amma hakika nin gaskiya Vash yana son Manassa, irin sosai ɗin nan, kawai dai waɗan nan iya shege biyun da ta yi mashi ne yasa ya ja baya.”Da farko da na ce ina sonki ma wasa nike yi, shi ne kawai!”. Ya kai karshe tare da yunkurawa zai juya……. “Ban yarda wasa kake yi ba, dan na ce ni ƴar GAT shi ne zaka gujeni? Ba zaka iya fuskantar kowani haɗari a kan macen da kake so ba? Kai ba soja bane”…….. Dakatawa ya yi, slowly ya ɗago eyes ɗinsa a kanta, lallai tayi gaskiya, yakamata ya fuskanci kowani irin haɗari ne a kan soyayyarsa, bai kamata ya janye dan GAT ba, to amma ita aljannar kuma fa? Idan ya ce zai iya ja da GAT zai iya ja da aljanar da baya kallo ne? To ace shi musulmi ne ya riki ayoyin ALLAH, ita Manassa idan ya fara soyayya da ita aljanar ta zo mata me zata karanta ta tsira tin da ba addini ne da ita ba?.Ganin ya yi shiru ne yasa ta ce. “Kasan ba zaka iya sona da gaske bane kasa na fara sonka? Ka cutar da zuciyata? Haka addinin naka ya koyar ka cutar da mutum?”……… Nisawa ya yi tare da ɗago da idanunsa sosai a kanta. Rasa me zai ce mata ya yi, sai kawai ya juya zai fita. Kukan munafurci ta fashe mashi da shi, har da tsuggunawa ƙasa.Cak ya dakata tare da juyowa, ya ALLAH, zuciyansa na sonta, ba zai iya wucewa ya barta tana kuka ba, dawowa ya yi, a gabanta ya tsugguna tare da sanya hannu ya ɗago haɓarta, suna fuskantar juna, hankey ɗinsu na sojoji ya fitar, a natse ya goge mata hawayen munafurcin da ta ƙaƙalo, cikin sanyin murya ya ce. “Sorry, amma a halin yanzu ba zan iya baki amsoshinki ba, tabbas ba karya bane ina sonki, amma ba zan iya soyayya dake yanzu ba, ba kaina nike jiyewa ba, ke nike jiyewa, so please ki bani lokaci zan nemo mafita”. Yana kai karshe ya miƙe ya fita.Ai yana fita ta miƙe tsaye, ta rike waist ɗinta ta fara tikar rawar da babu kiɗa, haka take so dama, ta yi ta wahalar da shi, ita tana da imanin cewa dik abin da namiji ya same shi a sauƙaƙe baya taɓa ɗaukansa da daraja, shiyasa take son sai ta ganawa zuciyar Vash namu azaba kafin ta bada kai, a zahiri gata Manassa kuma tana sonsa, a baɗini gata aljana da ta haramta mashi son kowa. Kai yaran GAT sai shirin ALLAH.Sai da ta yi rawarta mai isarta, sannan ta ɗauko wayarta, ta hau rubuta mashi saƙon cewa a madubin ganinta na aljanu ta ga ya kula wata yarinya yau, lallai ya sani dik abin da ya faru da wannan yarinya shi ne sila, ya shirya ba zata bar wannan yarinya ba, ai ta faɗa mashi dik macen da ya kula sai ta kasheta. Tana gama rubuta mashi ta tura sai ta hau cigaba da taka rawarta tana nishaɗi.A can kuwa Leo ya baiwa Arya da Angelina punishment na frog jump, saboda baya son irin wannan ɗabia, ace suna ƴan uwa kuma suna faɗa, ba zai ɗauki wannan iskaci a team ɗinsa ba. Abin ku da soja a cikin ruwan sama ya sanyasu tsallen kwaɗon fa, ga dukan ruwa ga wahala.Dikkansu sai da suka yi frog jump 100 suna kewaye tantunansu su sake dawowa, abinku da renon AZURE basu nuna wahala ko gajiya ba, amma sun ji a jikinsu kasancewar a cikin ruwan sama ne hakan ta faru. Dalilin wannan wahalar da Angelina da ya Leo ya yi ne yasa Unays ya ƙara ƙullatansa, ya ce ba zai kyalesa ba sai ya ɗauka mata fansa.After some hours, garin ya yi shiru, iska mai sanyi ya sauƙa saboda ruwan da aka sha, dajin ya ƙara kyau da zama kore shar, ruwan sama ya ɗauke ɗiff, matasan sojojin da suka yi sallar magrib da ishai sun hura wuta suna zaune ƙarƙashin bishiya suna hira suna shan ɗumi, dik suna sanye da army jacket da takalmar aikinsu, while team 1 suna cikin ɗaki a zaune suna tsara yadda komai zai tafi, suna tsara a daren nan zasu saci jiki akwai in da zasu je su duba wani abu. Sojojin dake masu girki sun girka sun gama, sun zubawa kowa a plate, sojojin dake kewaye da wutan da suka kunna suna cin abincinsu.While su Arya ma suna cin nasu abincin a ɗaki, amma V kwance take saman gado, ta yi wanka tana sanye da sleeping dress ɗinta masu kyau, taki cin abinci, idanunta har sun kumbura saboda kuka, tana kudundune a cikin army blanket ɗinsu. Sai rarrashinta Angelina take yi, amma taki tasowa ta ci abincin.Daga karshe dole suka kyaleta, dan sun san hali. Fitowa Angelina ta yi hannunta rike da abincinta, ta nufi in da matasan sojojin nan suke zazzaune, daidai lokacin Zaynish and Vash suka iso wajen. Sai kallon Zaynish Angelina take yi, amma shi bai san da zamanta ma a wajen ba, yana zuwa yai zamansa a kusa da wutar tare da fito da wayansa, take sojojin wajen dik suka miƙe suka sara mashi har ita Angelina ɗin, sai da ya jinjina masu kai sannan suka koma suka zauna.Wayansa Zaynish ya ya ɗan fara latsawa, da alama shi fa su Angelina basu mashi bama, ba ruwansa da su.Ya mayar da hankali kan abinda yake yi kawai, a daidai lokacin Aunty Ummi ta kirasa, miƙewa yai ya bar wajen, bayansa Angelina ta bi da kallo, sai magana Unays yake yi mata amma bata tanka ba, cikin sanyin murya ya ce. “Nai maki message baki mun reply ba”. Ƙasa ta yi da kai, a ɗan daƙike ta amsa da. “Banga saƙon bane”…… Nisawa ya yi tare da ƙara matsawa kusa da ita, ya fara janta da hira, ƙasa ta yi da kai, bata ƙara bi ta kansa ba ta hau cin abincinta a natse.A can gefe kuwa, Leo da Noor ne zaune a cikin ɗakinsu suna cin abinci, Noor ya ce. “Bro zan je in ɗauki Juliet ɗita, ba zan iya cigaba da fushi ba”…….. Abinci Leo ya ɗebo a spoon mai zafi sosai ya dannawa Noor ɗin a cikin baki ba tare da ya yi magana. Da sauri Noor ya fito da abincin yana buɗe bakin ta sha iska saboda zafi, akwai zafi sosai, ta ƙona mashi baki matuƙa.A ƙule ya ce. “Yau mugunta kake ji da shi ne?”……. Ɗebo wani abincin Leo ya sake yi, ya shammacesa yana magana ya sake danna mashi a baki. Ai a miliyan Noor ya miƙe yana tufo da abincin waje saboda zafi. Da sauri ya dunƙule hannu zai kai wa Leo ɗin punch a kumatu Leo ya damki hannun nasa tare da ture plate na abincin gabansa, ya jawosa Noor ya faɗo jikinsa, yana ƙoƙarin damke wuyan Noor ɗin.Noor ya juya ya rungumesa yana faɗin. “Wai ni yau me nai maka ne?”. Shiru Leo bai yi magana ba, ya janye Noor daga jikinsa kawai yana ja mashi coily hair ɗin nan nasa. Wasa suka ɗan taɓa gwanin burgewa kafin Noor ya kwanto da kansa a kan laps na Leo yana faɗin. “Bro me na yi maka yau kuma?”. “Babu abin da ka mun, kawai ina son gwada maka ne, yadda ka ji wannan zafin abincin nan haka mace take, ka kiyaye”…….. Awwa sai yanzu Noor ya gane karatun, ya ALLAH, watau Leo ba zai canza ba, halinsa ɗaya da yayansa Lion, wai a haka ma fa Leo bai san tarihin iyayensu da irin cin amanar da ya faru ba, da ya sani kam ban dan me zai faru ba.Miƙewa Noor ya yi yana faɗin. “Sauran mata ne suke saka mutu a zafi tamkar wuta, but my Juliet daban take da sauran mata, bari ma in je in ganta, goodnight bro”……. Da ido kawai Leo ya bisa ba tare da ya yi magana ba, miƙewa tsaye ya yi, har zai fita kuma sai ya ɗan dakata tare da juyowa.A kusa da Leo ya tsaya, a kunne ya raɗa mashi cewa. “Kada ku nemeni, kuma kada ku zo mun ɗauki, yau ni da matata zamu kwana, yau zan yi dis virgin ɗinta, bye bro”. Yana kai karshe ya miƙe da sauri yana ja baya, dan yasan sai Leo ya kai mashi duka ko damƙa. Harara Leo ya bisa da shi, sai kuma ya sauke idanunsa ƙasa bai yi magana ba. Wucewa Noor ya yi ya fice waje. Kai tsaye tantinsu Arya ya shiga, yana shiga V dake kwance ta ɗago kai, ta ji kamshin perfume ɗinsa, Arya na zaune gaban laptop tana cin abinci. Tabbatarwa da cewa shi ne yasa ta miƙe zaune a tsakiyar mattress ɗin. Muryarta a dishashe ta ce. “My Romeo”. Bai yi magana ba, ya iso dab ita, hannu yasa ya ɗauketa cak, da sauri ta saƙalo wuyansa tana kwantar da kanta a gefen kirjinsa. Bai ce da Arya ko uppan ba ya fito waje da V, kai tsaye cikin tantinsa ya shige da ita. Bai direta a ko’ina ba sai a saman mattress ɗinsa, ya sauƙeta game da yunkurawa zai miƙe ya sauƙa.Da sauri ta riko damtsen hannunsa, muryarta a raunace ta ce. “I’m so so sorry my Romeo, ba zan sake ba, na tuba”…….. Dogon numfashi ya ja tare da sauƙewa a hankali. Can ƙasa kamar mai raɗa ya ce. “To sakeni”……… Sake shi ɗin ta yi tare da kwanciya a saman mattress ɗin, ta fashe da sabon kuka. Miƙewa ya yi, ya cire uniform ɗinsa, ya rage daga shi sai shorts guntu wanda bai kai tsakiyar cinya ba, ga shi short ɗin ta matse shi sosai………. Saman gadon ya dawo, yasa hannu ya ɗagota gabaɗaya ya rungume, sosai take ta faman shessheƙa, in a cool way sosai ya ce. “Ke baki san ke matata bace da zaki ce voice na wani is so sweet? Baki san cewa voice ɗina kawai zaki ji ki yaba ba? Kin manta ina sonki ne? Kin manta zan ji zafin in kika yabi wani ne?”. Cikin muryan kuka ta rungumesa taigtly kafin ta ce. “Sorry my Romeo it was a mistake, ba zan sake ba”……. Kai ya jinjina. “Is okay to, for now I forgive you, but in kika sake, you will lose my control and my happiness”…… Ƙara ƙanƙame shi ta yi tana ƙara ce mashi sorry. Ɗago face ɗinta ya yi, ya haɗe fuskokinsu kafin ya haɗe bakinsu, ya fara bata hot kiss mai narka zuciya, ai ƙara shigewa jikinsa ta yi, ta fara shafesa tana turo mashi kirjinta, a gefe guda tana shessheƙa. Ai kwantar da ita ya yi, ya mata runfa da buɗaɗɗiyar kirjinsa, ya fara moving hands ɗinsa a jikinta, cikin salo ya fara ɓalle mata botiran sleeping dress ɗinta.Ita kuwa ta ɗaura hannayenta a saman bayansa, tana yin sama da su, slowly ta dawo da shi ta gaba, kai tsaye ta damki magicstick ɗinsa. Ƴar ƙara ya saka mata kafin ya fara bata komai cikin zafa, dan ta kunna shi ne……… Romancing ɗinta sosai ya yi, ya rabata da kayanta dikka, daga ita har shi suka manta da a filin daga fa suke, yaki suka fito, ko da yake dama su basu ɗauki rayukansu a bakin komai ba, already sun sa a ransu mutuwa zasu yi anytime.In a romantic way ya dinga binta da love and sexy words, ya ɗauke mata hankali kafin ya yi yunkurin shigarta, ko me ya tina kuma sai ya fasa, ya kwanto jikinta yana mayar da numfashi, yana jin tamkar ana buga mashi guduma a tsakiyar kai. Hannu tasa tana ɗan bubbuga bayansa kamar mai rarrashinsa, tana jin bugun zuciyansa na tsanantawa. Shiru ya kwanta a jikinta, after like 10 mins, slowly ya miƙe, ya sauƙo ƙasa, kayansa ya mayar jikinsa tare da matsowa bakin mattress ɗin, ya tsuguna a gabanta, in a cool way ya ce. “I’m coming, ki yi barci, yau a tare zamu kwana”. Yana kai karshe ya miƙe ya fita. Yana fita bai zame ko’ina ba sai ta bayan tantunansu, a nan ya isko Leo, Zaynish, Vash suna tsaye, wayar hannunsa ya duba time 11 na dare ya yi, gaba Leo ya yi, suka rufa mashi baya, dik cikinsu Vash ne kawai yake rike da bindiga, su kam banda ƙananan wuƙaƙen dake jikin takalmarsu na aiki babu abin da suka ɗauka sai torchlight ɗinsu mai bala’in hasken nan.Cikin tsakiyar dokar daji suka kutsa ba tare da sanin kowa ba, suna tafiya suna tattaunawa kan aikin da zasu je yi, ma’ana aikin da ya fitar dasu a daren nan. A can kuwa sauran sojojinsu suna zaune bakin wuta suna ta hira, while Arya na ta kokarin ganin ta yi aiki tuƙuru, Angelina ma ta dawo ta kunna laptop ɗinta tana duba gabas da dajin, dik da cikin duhu ne tana sauraran sauti da motsi, while Manassa na kwance rike da waya tana zubawa Vash tsiya, dan shi ma suna tafiya yana dannar waya ne, sai hakuri yake baiwa aljanarsa da ta ce zata kashe Manassa da ya kula.Dik ya tashi hankalinsa, ya dinga bata hakuri, har da cewa shi tai mashi dik abin da zata yi mashi, amma ta kyale Manassa bata san komai ba, ita kuwa ta kafe lallai sai ta nakasa Manassa. V dai tana tantin Romeo ɗinta kwance tana tinanin love moment da suka sha, dik ya tashi kanta da salonsa, idan ta tina his soft lips, his romance, his sexy words, ya rabb, sai ta jita a wata duniya na daban. Shi kuwa Unays ya zage sai ya kafa gwamnatinsa a zuciyar Angelina, sai tashin kanta da love words yake yi, ita kuwa tana can tana tinanin yadda zata samu even contact ɗin Zaynish ne. Uhm akwai dirama. CRYSTAL PALACE.4:30 na washegarin ranar da Abba ya kai sadaki, ranar Alhamis kenan.Zaune familyn Khaiza’an’s suke a parlo, Faryan, Harleen, sai kuma Rimsha dake zaune kusa da Faryan ta tada kai da cinyansa tana chatting da Seraphina, suna ta hira kan school, yau sun mayar da hankali kan hirar karatu ne ba hirar shirme ba, Rimsha tana son jan Seraphima ta musulunta, tana bata tarihin Annabi Muhammad (SAW) Faryan yana latsa nashi wayan shi ma suna chat da Seraphina, dan bai hakura ba kuma ba zai hakura ba, while Harleen yana aiki a laptop ɗinsa, kun san Harleen pilot ne, matuƙin jirgin sama. Abba baya nan, sun fita da Aryan, ƙafa ta matsawa Abba sosai, kun san yana da problem na kafa, sai da aka dasa mashi karafuna, to dama dik karshen wata ana zuwa asibitin ƙashi a duba mashi, wannan wata bai je da wuri ba, kafar ta dame shi shiyasa ya kira Aryan a gaggauce suka tafi, dalilin kenan da yasa kuka gansa yana dogara sanda, matsalar kafa ce.Knocking na door aka yi, hakan yasa Rimsha ta mike, a tinaninta su Abba ne ya dawo, ta nufi jikin door ɗin, ba tare da ta duba camerar door ɗin ba ta sanya fingerprint ɗinta, kofar ta buɗe. Tana buɗewa sai ga kaki sun shigo cikin parlon, ƴan sanda ne su biyar, a gaba ACP ne da sauran yaransa.Razana Rimsha ta yi, da gudu ta juya ta koma ciki tana faɗin. “Uncle Faryan police”. Wannan magana da ta yi karaf a kan kunnen Ammie dake ɗaki tana shan americano, tana zaune saman sofa. Jin Rimsha ta yi kukan sunan ƴan sanda yasata ajiye americanon ta miƙe tsaye, tana sanye cikin arabian dress, ta yi rolling veil a kanta. Ƙasa ta nufi tana ɗan sauri dan ta zo ta gani. Police a gudan Khaiza’an? Abin da ko a mafarki bai taɓa faruwa ba. A tsakiyar parlo ƴan sandan suka tsaya, ACP yana kallonsu Faryan ya ce. “Kai ina Muhammad Khaiza’an yake?”……. Dik cikin parlon babu wanda ya amsa mashi, saboda rashin yi masu sallama da basu yi ba. Cigaba da abin da suke yi suka yi tamkar basu san da halittar ƴan sanda a wajen ba. Wani irin ƙasƙantaccen kallo ACP yai masu kafin ya ce. “Wai ba daku muke magana bane?”……. Ɗago kai Faryan ya yi, ya kalli TV dake magana, a ɗan natse ya ce. “Rimsha rage volume na TV ɗin nan, karen ciki na mana haushi dayawa”. Kuma da gaske wani bakin ƙare na haushi a cikin TV ɗin. A tsorace ta miƙe ta je ta rage volume ɗin, shi kuwa Harleen ya ajiye laptop ɗinsa a gefe ya jawo waya ya fara latsawa. Daidai lokacin Ammie ta sauƙo ƙasa. Kallo ɗaya tai wa ƴan sandan ta ɗauke kanta tare da ƙarisawa in da su Faryan suke, ta zauna a saman sofa tana mai da kallonta a kan Rimsha da jikinta ke ta faman kermar tsoro.”Ku wasu irin dabbobi ne? Baku ji ana magana ne? Kuna wasa da wuta ko? Hukuma ce a gabanku!!”. ACP ya faɗa a kadarance. Ɗaura kafa ɗaya kan ɗaya Faryan ya yi, ya jawo Rimsha jikinsa yana faɗin. “Baby zo ki ga me kawarki ta rubuta mun, wai tana sona saboda ina kama da daddynta”. Ya faɗa yana murmushi. Rimsha dai hankalinta sam bai kwanta ba, tana tsorace da ƴan sandan nan, kallon wayar kawai take yi, amma hankalinta baya jikinta, hasalima bata ga me Seraphina ɗin ta rubuta ba. Wani irin tsawa ACP ya daka masu. “Ku dabbobin ina ne nace? Kun san zan iya jefaku a cell ko?”………. Jikin Rimsha ne ya tsananta kerma, ta ƙara ƙanƙame Farya. Ammie ce ta ce. “Faryan naga alamar wannan Seraphina ɗin tana burgeka, ka fara biyewa Rimsha ko?”. Murmushi Faryan ya yi. “Ammie yarinyar ta haɗu fa, kin ganta kuwa, kamar ki sace ki ajiye ki yi ta kallo, kyakkyawar gaske ce”…….. Cikin zolaya Ammie ta ce. “To ya tsaya a iya haka dai, kada ka bari Abbanka ya jika”…… Gabaɗaya Khaiza’an’s family sun mance da wasu ƴan sanda, sun baiwa banza ajiyarsu.A fusace ACP ya sake cewa. “Lallai dikkanku sai kun yi danasanin wannan abin fa kuka aikata!”……… Miƙewa Faryan ya yi, ya nufi kitchen yana faɗin. “Ammie bari in duba idan waɗan nan robot ɗin sun kammala abinci”. “Faryan zo mun da ruwa mai sanyi”. Harleen ya faɗa yana ɗaura kafa ɗaya bisa ɗaya ya cigaba da dannar waya. Watau idan kana neman shahararrun ƴan rainin wayau to ka zo gidan Abba, takaici ne zai kasheka. “Rimsha je ki ɗauki mun Americano na da na baro a ɗaki in karisa shanyewa”. Ammie ta faɗa tana kallon Rimsha da tsoro ya gama cikata, dan dik family Abba ita kaɗai ce matsoraciya. Gagara miƙewa ta yi, ta kankame Faryan da ya dawo ya zauna a kusa da ita yanzu yana miƙawa Harleen ruwan da ya ɗauko mashi. Riko hannunta Faryan ya yi, tamkar zata yi kuka can ƙasa ta ce. “Uncle, I’m very scared”……… Ƙasa sosai yai da murya wajen cewa. “Don’t fear anyone except ALLAH, get up and go bring what Ammie sent you to get”. Da gudu ta miƙe ta nufi sama tana waigo ƴan’sandan da suka yi kasaƙe suna ganin ikon God…… Harleen ne ya ce. “Kai Faryan kara gudun Ac ɗin nan ka zo mun da small chop”.Ai a ƙule ACP ya ce. “Me kuka ɗauki kanku ne ahalin Khaiza’an? Dame kuke taƙama ne?”……. Dik cikin parlon babu wanda ya ɗago ya kallesu bare su tankasu, sai ma cewa Harleen yai. “Faryan zo mun da bluetooth”. Watau ya toshe kunne kada su dame shi. Ɗaya daga cikin ƴan’sandan dake baya ACP ne ya ce. “Kufito mana da Muhammad Khaiza’an, shi muka zo tafiya da, in kuma baku fito da shi ba zamu bincike gidan gabaɗaya, kuma ba zamu ragawa kowannenku ba, dik zaku tsinci kanku a bayan kanta!”. In a harsh way ya faɗa yana wani zazzare masu ido, bai san nan gidan dik tantirancinka sun fika iyawa ba, kuma su ba duka ba zagi, kai bama magana zasu sanya zuciyarka bugawa ne.”Wai ba daku muke magana bane?!!”. ACP ya faɗa cikin ɗaga murya wanda ya sanya Rimsha dake sauƙowa yanzu ta razana ta saki plate and cup na hannunta ya faɗi ƙasa ya tarwatse, Americanon ya malale a ƙasa. Jikinta na rawa ta ɗago da kai ta sauke kallonta a kan mugun watau Harleen, dan tasan ko kowa bai yi mata magana ba shi sai ya yi saboda bala’insa daban ne a gidan nan bayan Aryan. Ga mamakinta sai ta ga ya harareta ya ɗauke kai bai yi magana ba, take ta haɗiyi yawu gwad jikinta na ɗan kerma. Tana ƙoƙarin raɓawa gefen glass ɗin ta isa wajen Faryan ACP ya damki hannunta tare da sanya mata pistol gun ɗinsa a forehead ɗinta, a dake ya ce. “Ku fito da Khaiza’an ko in fasa kanta!!”. Wai irin zai razanasun nan.Miƙewa Ammie ta yi tana faɗin. “Ku kawo mopper a goge Americanon nan, sannan ku zo da tsintsiya dan kwashe glass ɗin, Faryan bari in ɗan kwanta in huta”. Ta kai karshen maganar tare da nufar sama, ta raɓa gefen ACP ta yi wucewarta……….. Saura kaɗan Rimsha ta saki fitsari a wando saboda tashin hankali, jikinta ya tsananta kerma, kallonta a kan Uncle Faryan dake girgiza mata kai alamar kada ta tsorata. Harleen kuwa ko a jikinsa yana cigaba da cin small shop da Faryan ya shigo mashi da shi, suka baiwa bansa ajiyar su ACP, kuma ga shi su ACP ɗin suna shakkar shiga cikin ɗakunan gidan su duba ko Abba yana nan, su da kansu sun san da wuya idan Abba yana gidan, amma sun jajirce sai Khaiza’an’s family sun kulasu. Ganin babu sarki sai ALLAH ne yasa suka ce zasu tafi da Rimsha, idan har suna sonta Khaiza’an ya kawo kansa station. Still dai babu wanda ya kulasu, ACP ya kamata suka nufi waje. Take ta fara kuka hawaye bibbiyu. Suna fitowa harabar side ɗinsu sai ga motar Aryan ya danno kai, sun dawo da Abba, an je an gyarawa Abban karafunan kafafun nasa. Tin Aryan bai gama parking ba Abba yasa hannu zai buɗe kofar motar saboda ganin Rimsha a hannun ƴan’sanda ya ɗaga mashi hankali. “Abbaaaaaa……” Aryan ya faɗa yan jan sunan. Harara Abba ya dalla mashi kafin ya buɗe mota ya fita, da alama har yanzu bai huce ba, Aryan kuma babu alamar zai karɓi wannan umarni, ba zai yarda ya auri Aunty Lusi ba. Fitowa Abba ya yi, yana dogara sandarsa ya isa gaban ACP. Da karfi Rimsha ta fara ƙoƙarin kwatar kanta ta nufi Abba, amma ACP ya ƙanƙameta, bai saketa ba.Lokaci guda kuma ya saketa a razane yana kallon Aryan dake tinkarosu tamkar wani zaki, gabaɗayansu babu wanda hantar cikinsa bai kaɗa ba, ACP har da haɗiyar wani yawu da karfi gwad. Da gudu Rimsha ta nufi Abba, tana zuwa ta faɗa jikinsa, riketa ya yi yana cigaba da kallon ƴan sandan.”Me haɗinku da jikata? Me tai maku zaku kamata?”. Abba ya tambaya…… Da kyar ACP ya saita natsuwansa game da ɗauke kallonsa daga kan Aryan dake gab da ƙarisosu kafin ya ce. “Lush family ne suka shigar da ƙara a kan Khaiza’an, batu ne na cin zarafin ɗan adam, ka tilasta masu yin abin da basa so, ka kawo kuɗi ka basu dan kasayesu, cin hanci kenan, kasan kuma corruption haramun ne a ƙasar nan”..….. Abba ya gane karatun, watau grandpa ɗinsu Noor ne da wannan ɗanyen aiki.A daidai lokacin Aryan ya ƙariso wajen, fuskansan nan tamau babu alamar wasa, a dake ya ce. “A yaushe CRYSTAL PALACE ta yi lalacewar da ƴan sanda zasu iya shigowa cikinta?!”…… Shiru ƴan sandan suka yi, dan sun san ba kai tsaye suka shigo da nufin kama wasu ba, sun yi wa jami’an dake bakin main gate karyar cewa ziyara zasu kaiwa ɗan uwansu a Lush family, shi ne suka samu hanyar shigowa, dan jami’an bakin gate sun duba number Lush family dake jikin littafin CRYSTAL PALACE ɗin, sun kira table phone nasu, suna tambayi cewa suna da baƙi kala kaza ne? Dama grandpa ne ya ɗauki wayan, sai ya ce e suna da baki, shi ne fa suka basu hanya bayan sun cajesu basu ɗauke da komai sai bindigar aiki.A tsarin CRYSTAL PALACE da yanayin tsaronta babu wani jami’in da ya isa shiga cikinta ya kama wani, babu wannan mahaluƙin, idan akwai mai laifi a cikinta to sai dai a tuntuɓi jami’an dake tsaron CRYSTAL PALACE ɗin, su da kansu zasu yi bincike, idan ya tabbata mai laifi ne, da kansu zaku kama shi, idan kotu ne su miƙa shi kotun dake cikin CRYSTAL PALACE ɗin, idan hukunci ya dace da shi su zasu yanke mashi, shiyasa na ce maku manyan kai ne ke zama a cikin CRYSTAL PALACE, akwai tsaro, dokoki da ƙaidoji, babu wani abin da ya isa zama barazana ga mutanen ciki, karfin ikon CRYSTAL PALACE ya zarce yadda kuke tinani.Tsuru-tsuru ƴan sandan suka yi. Aryan ya daka masu tsawa, hakan yasa ACP ya ce. “Dama Lush family ne suka shigar da ƙasa kan Khaiza’an, shi ne muka zo tafiya da shi…….”. Bai iya ƙarisa maganar ba sakamakon gigitaccen marin da Aryan ya ɗaukesa da shi, wai Abba aka zo kamawa. In a harsh way Aryan ya ce. “Ba’ayi mahaluƙin da zai iya taka gidan Khaiza’an da suna kama shi ba!”. Da farko Aryan ya so nuna masu ID card ɗinsa na SSO, sai kuma ya fasa, dan basu kai ya tsaya nuna masu waye shi ba, gara ya jibgesu ba’a matsayi nagaba da su a wajen aiki ba, su rubuta a tarihinsu farin kaya ya jibgesu.Abba sarkin izza, aikuwa ya ce Aryan ya ƙara masu, dan shi an walaƙanta shi da har ƴan sanda suka shiga gidansa. Kallon Abba Aryan ya yi. “Abba ka je ciki kawai”. A tausashe ya faɗa…… Hannun Rimsha Abba ya riko suna nufi elevator yana faɗin kada Aryan ya raga masu, ya masu hukuncin da gobe ko sunan Khaiza’an suka ji sai sun saki fitsari a wando. Shi kuwa Aryan Abba na shiga ciki ya ɗauki waya da nufin ya kira jami’an SSO dake benensu, sai ya ga wayar Lion ce a hannunsa, ya ɗan yi mamaki, sai can ya tina ashe ɗazun da ya kwanta jikin Lion suna hira wayoyinsu na haɗe waje guda, da ya tashi ne ya manta ya ɗauki na Lion kenan, dama wayoyin iri ɗaya babu abin da ya rabasu, sai ka kunna hasken wayar zaka ga wallpaper kowa da kalar tasa.Kiran jami’an ya yi, ya ce su zo su wuce mashi da ƴan sandan nan, su ajiyesu zuwa dare zai nemesu. Bai faɗawa jami’an SSO ga in da yake ba, ƙasa da minti biyu sai gasu sun yi diran mikiya a wajen, suka wuce da su, su ACP idanu ya raina fata, ga shi yana tsoron ɗaga murya kada ya jawa kansa, dan jami’an dake tsaron CRYSTAL PALACE gabaɗaya jami’an SSO ne, amma ba kowa yasan hakan ba, saboda kada ku manta jami’an sirri ne. And yasan dokar CRYSTAL PALACE, ya yi wa jami’an karya ya samu ketowa ciki, idan ya ɗaga murya zai ji a jikinsa ne.Gara ya yi shiru kawai…… A yayin da dikka wannan abin yake faruwa ita kuwa Seraphina tana can cikin ɗakin Mom ɗinta, ta tada kai da cinyar Madam, Madam ɗin tana gyara mata kyakkyawan silky ash hair ɗinta, tana rike da waya, suna hira da Madam tana ɗan dube-dube a wayar.Madam ta ce mata. “Baby daddy baki jin magana, kullum sai na ja maki kunne a kan kada ki dinga irin waɗan nan maganganu da daddynki amma baki ji ko?”…… Ta faɗawa Madam dik yadda suka yi da Aryan jiya ne, shi ne Madam take mata faɗa, ta nuna mata illar maganganun, ta kuma gwada mata cewa da kunya aka san mace, tai mata faɗa sosai fa, kuma ta yi alkawarin ba zata sake ba.Cikin shagwaɓa ta ce. “Yauwa mom, kin tina mun, yau tin safe ma daddy bai zo ba, har na je school na dawo, sai wani katon mutumi ya turo wai ya kaimu schy, ga shi na dawo bai zo ba, bari in kirasa video call”. Ta faɗa tana turo baki, yau Aryan bai zo ya kaita asibiti ba, ya je amsa kiran Abba har suka tafi hospital, sai dai ya turo ɗaya daga cikin jami’an SSO ya zo ya kaita, kuma ya dawo da ita a lokacin tashi.Madam zata yi magana sai ta ga Seraphina ta danna video call tana murmushi, ɗan kawar da fuskarta Madam ta yi tana faɗin. “Ki dai natsu, kada ki yi wa daddy shirme, ki mashi magana a kame cikin natsuwa”. Da okey ta amsa…….. A daidai lokacin kiran ya shigo wayan Aryan, jawo wayar Lion dake kwance saman bed ya yi, a tinaninsa wayansa ne, ganin video call yasa ya ɗan yi mamaki, sai kuma ya zaci ko Leo ne, amma sai ya ga an yi saving sunan da Cherry bloom, shi dai yasan da boy ya yi saving number Leo, kuma Leo ne kawai zai kirasa video call sai kuma Vir or Aryan, guru ma yana gida.Ɗan jujjuya wayar ya yi yana son tabbatarwa da wayansa ne kuwa? Daidai lokacin kiran ta katse, yana ƙoƙarin kunne wutar ya duba wayar waye sai ga wani kiran ya shigo, wayoyinsu fa idan basu da numberka kiranka ba zata shigo ba, sanin haka ne yasa ya ce dole na gida ne yake kira, dan haka bari ya ɗaga ya ga wanene dik da bai san wayan waye bane a tsakanin su ukun, nasa ne ko na Aryan or guru?.Picking ya yi a daidai lokacin da ta ɗaga kai tana kallon Madam tana cewa. “Mom daddy baya ɗaukan kiran, kila ya bar wayan a wani waje ne”…….. Ta kai karshen maganar tare da dawo da kallonta a kan screen ɗin. Ai wani irin razana ta yi ganin jade sexy eyes na Lion yana kallonta. Ihu ta kurma tana miƙewa zaune, ta saki wayar a ƙasa tana faɗin. “He’s the one! He’s the one who killed my mom! Haka idanunsa yake, with this nose mask ya zo gidanmu, this is his eyes, mom he’s the one!”. Muryanta na rawa kirjinta na bugawa da karfi take maganar, lokaci guda kuma ta ɗauke wuta ɗiff, ta sulale ƙasa zata faɗi Madam ta rikota da sauri.Kit Lion ya katse kiran yana jan siririn tsaki, ya janye nose mask na fuskansa ƙasa yana mamakin yarinyar yadda aka yi ta rike kamanninsa, wai da wannan nose mask ɗin ya je gidansu, da yake su IRON FIST nose mask ɗinsu kala ɗaya ne, dik duniya kuma su kaɗai ke da irinsa, su suka zaɓi design da suke so Company ta buga masu, shiyasa Seraphina ta ce da wannan nose mask ya je gidansu, hakika da irinsa ne sak ba banbanci.Lallai yau akwai rikici tsakanin Aryan da Seraphina idan ta farfaɗo, sai ya faɗa mata dama yasan wanda ya kashe mammynta kenan, a gefe guda kuma akwai rikici tsakanin Aryan da Lion, sai ya faɗa mashi dama yana tare da Seraphina, sai ya faɗa mashi ma’anar Cherry Bloom, e kam akwai case!! Yau dai na ce bari in barku ku ɗan shana ba sai mun leƙa WS-HOSPITAL ba, ku huta da tashin hankalin na yau kam.

Back to top button