Haihuwa Da Hanji Page 54 Hausa Novel
“Duk wanda ka ga ya lashi zumar nasara, to tabbas ya ɗanɗani maɗaciyar haƙuri.”Wannan ɗin wani zance ne na masu hikima. Bahaushe ya ce haƙuri gishirin zaman duniya, Yayin da ubangiji ya koya mana cewa duk inda abu ya je ya dawo kayi haƙuri! Duk ƙunci ka yi haƙuri, Duk damuwa ka zama mai haƙuri, Duk mai haƙuri shi ke galaba kuma duk mai haƙuri shi ke cin riba da wannan aya ta;”Ista’eenuu billahi wasbiruu” (Ku nemi taimakon Allah kuma ku yi haƙuri).Haƙiƙa da a shekarun baya za’a iya cewa zata taka wannan matsayi da take kai a yanzu za ta ce karya ne amma dayake Allah mai jin ƙan bayinsa ne da jiɓantar lamuransu gata a cikin ni’imarsa marar yankewa. Hakan ya sa cikin waennan watanni uku da suka biyo bayan tariyarta gidan Sarautar Fombina Bakinta bai taɓa hutawa da godiya ga ubangajinta ba saboda shi ya ce mana ka gode mishi a dukkan ni’imominsa shi kuma zai ƙara maka.”Alhamdulillahil lazee bini’imatihi tatimmus salihaat… Alhamdulillah ala kulli haalin… Alhamdulillah hamdan hamda… Hamdan katsiran dayyiban mubarakan fihi”Sun kasance kaman ruwan sha a Bakinta, ta samu duk wani gata da zata nema ta uwa irin Ammi da uba irin mai martaba. Waenda a yanzu suke tabbatar da cewa bata yi kuka da sunan maraici ba.Ta samu ɗumbin soyayya marar fasaltuwa daga wurin jarumi kuma gwarzon mazanta, a wannan watanni uku ba zata ce ko kallon banza ya taɓa shiga tsakaninsu ba bayan tattali da nuna kulawa, bata taɓa neman wani abu ta rasa ba zata iya cewa rayuwar da tayi a gidan na watannin ukun farko suna daga cikin waenda ba zata taɓa iya shafe su a tarihin rayuwarta ba, Dukda sau biyu yana tafiya akan aikinshi hakan bai dakile mata dukkannin abinda ya saba ba. Jannah ta koma sai dai su yi waya, Abeeha ta yi transfer ta dawo nan Fombina da karatun ta yayinda ta yi kane kane zuciyar Ameer Galadima ta hana shi komawa wurin aiki, a gefe ɗaya kusan duk waenda suke kusanci da Aisha da Saleem sun san cewa sun mato akan son junansu, daga mommy har su Sadiqa har Umman Sulaiman da ma matarshi su kan kira ta su gaisa sa’i da lokaci don yadda suka mayar da ita ɗaya daga cikinsu itama haka ta ɗauke su tamkar yan uwan da ta rasa, abu ɗaya ta kasa shine ƙarasa shirya tsakanin Rayyan da Ammi, yana da taurin zuciya irin na Fulanin Asali iyakancinshi da ita idan sun haɗu gaisuwa ne amma bayan nan baya ƙara komai Ameer yayi, mai martaba ya yi, Yaya Maudo(Galadiman Fombina) shima ya yi itama tana kan yi Dukda duk ranar da tayi maganan sai sun ɗan samu saɓani ya nuna mata baya so bata taɓa dainawa ba lokaci lokaci.A gefe ta kan tuna kawu da su inna Larai don an ce jini ko ya yake ya fi ruwa kauri duk abinda suka yi mata gashi bai katangeta da samun farin ciki ba, sai ma kusanta ta da yayi da farin cikin mai tarin alkhairai, Result ɗinsu na Waec ya fito kuma ta ci sossai tayi ƙoƙari Dukda shi gogan nata bai ce komai a kai ba hakan ya sa ta fara sanyawa zuciyarta cewa ba lallai tayi karatu yadda take so ba, ta sakawa zuciyarta ba komai kake so kake samu ba kila karatun ba alkhairi bane da haka ta danne ranta bata taɓa yi mishi magana a kan makarantar ba.Yau ya kama Friday haka kawai take cikin nishadi tun da ya sauƙe mata zallar madarar ƙauna ya fice da safe sa’i da lokaci ta kan saki murmushin da baya rabo da fuskarta, bayan tayi Sallar la’asar ta gabatar da duk abinda ta saba kowani juma’a a irin lokacin na karatun suratul kahf da adu’o’i ta tashi ta nufi kitchen. Ta ɓata lokaci sossai wurin gasa mishi kifi da yake matuƙar jin daaɗin gashin nata ta soya plantain da irish ta shirya table ɗinta tsaf kan taje tayi wanka, kananun kaya ta saka wando ne da bai kai ma gwiwa ba rabin cinya Black sai White Shirt da ta saka tayi wani irin kyau kaman ka sace ta.A kwanakin ita kanta ta san ta sake chanzawa ta yi kubul kubul fatarta yayi fresh kaman mai wanka da madara, ita kaɗai ce don tun gama taya ta aiki ta tura su Sa’ade sashen baya da ya sa aka gyara musu na cikin ɓangaren nata saboda shi ba mutum bane da yake son takura a sadda yake tare da iyalinshi, Abeeha ta jima da komawa wurin Ammi wai in ta cigaba da zama za su iya makantata cikin ko wani dakika don haka tayi ta kanta. fitowa tayi kai tsaye zuwa kitchen tana tuna wani haɗi na musamman da aka koya mata tun kafin aurenta dashi yau kam ta yi niyyar gwadawa, ayaba ta ɓare guda huɗu ta dauki tafarnuwa guda ɗaya ɗan daidai ta haɗa ta zuba a blender ta markade ta juye a cup, zumarta na asali ta zuba a kai tana jin haushin rashin kankanrar matar da bata dashi amma ko a haka ta san emergency ne mai kyau kaman yadda matar ta yabe shi, shanye wa tayi a tsaye a kitchen ɗin kan ta koma ɗakinta tayi ruf da ciki tana danna waya.Shigowar shi gidan jin bai ji motsinta ba yasa ya nufi ɗakin nata, sanye yake da khakinshi full don wani aiki ya fita akan tsaro tun safiyar yana tafiya yana ɓalle botiran ji yake kayan sun ishe shi, tura kofar ɗakin da kafewarshi a wurin lokaci ɗaya don ji yayi ruwan jikinshi na neman tsiyayewa, surar jikinta na neman zauta shi kafafunta zuwa cinyar ta dake a bayyane suka tasar da mazan dake jikinshi a lokaci guda, harshenshi ya fidda ya ɗan jiƙa lebanshi da yake ji sun bushe kan ya nufi gadon, ya ajiye kayan hannunshi ya kai zaune bakin gadon ya ɗora hannunshi kan cinyarta, tun shigowanshi kamshin turarenshi ya gaya mata wanene da gayya ta ƙi juyawan, ganin har lokacin bata juya ba ya sa ya saki murmushi mai sauti.Hannun ya ɗago ya kai kan rigan ta ya yaye ya kai fuskarshi yayi kissing fatar bayan yana shafawa a hankali, kan ya ɗan kwantar da kanshi yana jin yadda ta sauƙe ajiyar zuciya, bai yi magana ba ya cigaba da goga mata gashin gemunshi a bayan yana shafawa da hannunshi tuni ta kasa natsuwa ta juyo sai yayi mata rumfa yana haɗe goshinta da nashi ya lumshe idanu yana shakar daddadan kamshin turarenta dake ƙara hautsina shi.”Debbo boɗɗo am! Fushi kika yi?” (Kyakyawar matata)Yayi magana yana dan hura mata iska a idanun da ta rufe.”Shi ne ka je kayi zamanka ka manta da ni tun safe ko waya baka yi min ba.. Kuma ai ka ce za ka dawo da wuri amma sai yanzu? Kwalliyana har ya goge””Ya subhallah…!”Ya ambata a chan ƙasan makogoronshin, peck yayiwa bakin Shagwaɓar ta sanya hannu akan dantsenshi dake bayyane don daga shi sai vest ya zame rigar ta riƙe shi da kyau.”Na isa in manta da bugun zuciyata? Ko kin san mintuna biyu a nesa dake kaman shekara biyu ne a gareni yayinda shekara biyu a tare da ke zai zama tamkar mintuna biyu? Sam bana sanin gudun lokaci idan ina kusa dake Matar masu sarauta”Murmushi mai sauti kaɗan ta sake da ta sake motsa zuciyarshi.”Ni ce addiction ɗinka yanzu kenan?”Tayi maganan tana ɗan yawo da hannunta slowly a kan damtsenshi zuwa ƙirjinshi, ya ɗan taune lip.”Yes you really are my dear.. Craving ɗinki nake kaman mai ciki”Dariya ta ɗan yi, ya kama lips ɗin da nashi yana kissing slowly kan ya saki ta ɗan yi murmushi “Always remember that zan iya gajiya da komai a wannan duniyar amma banda ke, even when am tired all i want is you..”Hannayenta ta mayar bayan ƙeyarshi tana mishi susa ita kanta ta san tana yin hakan ta gama kunnashi, tuni hannunshi ya kai ga kwankwasonta yana yin sama da rigar bakinshi is kissing her like his life depend on that, ba zai iya haƙuri sai dare ba he just want to feel her bukatarta kullum sabo yake zama mishi, kaman yadda mutum ba zai iya rayuwa babu iska ba haka yake jin ba zai iya rayuwa babu ita a gangarshi ba.Ya kuwa ɗanɗani abin da ba zai iya janyewa cikin lokaci kankani ba, rikice mata yayi sai da ta fara dana sanin shan abinda ta sha da yamman don bai barta ba sai da ta fara mishi kukan gaske, ya rungumeta yana sanya mata albarka.Tayi lub a ƙirjinshi suna sauƙe numfashi a hankali hankali, wayanshi ya duba sai ya ga dab ake da kiran sallah dole ya miƙe da ita zuwa bayi suka yi wanka duk jikinta a mace suka fito daure da alwala, bai iya ya je masallaci ba don an fara kiraye kiraye kan ya isa ma za’a iya idar wa jallabiya ya saka ya ja su suka idar, ya waigo yaga sai ɓata fuska take ya janyota jikinshi ta kwanta suka yi azkar a haka kan yana shafa fuskarta yace “Raguwata zan ga ranar da zaki gama sabo da jaruminki”A Shagwaɓe tace “Ni dai a’a na yi fushi!”Murmushi ya saki ta kalleshi “Murmushi na yi maka kyau kar ka daina kwata kwata ka ji Ya Saraki?”Yana shafa girarta yace “Yau jinki nake na musamman Boɗɗi garɗinki wane zuma farar saƙa don haka dole ma in yi ta miki har sai kin gaji. Tashi ki ga wani abu”Miƙewa tayi ya tashi yaje ya dawo manyan paper bags da ya shigo da su ya ajiye ya koma ya zauna, buɗewa yayi ya ɗauko wasu papers ya miƙa mata.”Congratulations wannan admission naki ne”Hannu ta sa ta rufe bakinta tana zaro idanu fuskarta cike da wani irin tarin expression tace “No..No you can’t be Serious! Don Allah da gaske kake ko wasa? It can’t be…”Ta ma rasa me zata faɗa tsabar farin ciki and ganin irin wannan tarin farin cikin da shine sanadin ya saka ya ji shima zuciyarshi ta yalwata da farin ciki, ta ajiye papers ɗin ta rungumeshi tana hawaye “Ban zaci za ka barni nayi karatu ba, har na cire rai ashe kana chan kana nema min thank you My love! Thank you so so much rabin raina”Ya rungumeta shima har ta gama farin cikin kan ya ɗago ta ya riƙe hannunta.”Maganan gaskiya Afeefah ina matuƙar kishinki, ina jin zafi idan na ga idanun wani namiji ya kalleki ko da da second guda ne, don ke ɗin tawa ce! don ni kaɗai aka halliceki kaman yadda aka halliceni don ke! At First ban yi niyyar bari kiyi karatu ba ko ba don kishi na ba sai don kasancewarki Matar Ciroma mai jiran gado, ba Girmanki bane chakuduwa da maza don neman ilimi hakan yasa na nema miki Open university”Sakin hannunta yayi ya buɗe jakar Apple Mac book ne da Apple Ipad ya fiddosu a kwali ya miƙa mata “za ki yi amfani da waennan kiyi karatunki daga kan gado i promise to help you in all the process exams kaɗai zai kai ki makaranta. Ina fata hakan bai ɓata miki ba?”Ts saki murmushi hawaye na zuba mata tace “Har wacece ni da zan ce hakan bai min ba? Ciroma ne fa gabana kuma Sarakin Fombina..! Ni din ban kai wannan matsayi ba kuma ko da na kai ba zan taɓa kin amincewa ba don ni’imace hakan da ban tsammata ba Allah ya bani, wasu na chan ma suna neman yadda za su yi karatun bai samu ba, wasu na chan suna yawo lectures cikin rana, zafi da ruwa ai ni daaɗina ma na samu miji mai gatanta ni… Allah ya saka maka da alkhairi na gode sossai na gode kwarai, na….”Bakinta yayi saurin rufewa da nashi ya bata deep Kiss da ya sa take jin sanyin na sauka har cikin zuciyarta.”Babu wannan tsakaninmu girmanki ne Sarauniyata”Tayi murmushi tana sake godewa Allah.Janshi tayi suka je ya ci abinci yana bata cike da kulawa har suka gama suka zo suka gabatar da isha kan suka shige cikin bargo yana yi mata setting na system da ipad ɗin yana koya mata yadda zata yi amfani da su tana daga kwance nashe nashe akan kirjinshi.Washegari da misalin ƙarfe goma ta fito cikin wani Apiligue lace peach da yayi mugun amsarta ta ɗora gyale mai girma a kai tare da alkyabba marar nauyi ta nufi sashen Ammi don miƙa gaisuwa, ta isa parlorn babu kowa don haka kai tsaye ɗakin Ammin ta nufa ta saka hannu zata bude ta ji Ammin na cewa “Yaya Maudo ni dai ban goyi bayan wani auren Zarah da Sameer ba Dukda na san alkawari ne amma Meyasa Mai martaba zai fara matsawa a yi shi yanzu? Shi kanshi Sameer ɗin ba son maganan yake ba sai kwana- kwana yake ya fi sati biyu mai martaba na Binshi da wannan magana… Ba wai bana son zarah bane amma yaushe har suka dawo suka gama sabo da nan ɗin? Kwata kwata aurenshi ma da Afeefar bai fi watanni takwas ba don Allah ka bashi shawarar a jinkirta ba dai sati biyu masu zuwa kaman yadda yace ba…”Wani irin faɗuwa gabanta yayi har tana ganin jiri, Dukda tana jin Ammin na cigaba da magana bata iya ta tsaya sauraronta ba don mugun jin da tayi ya daki zuciyarta fiye da zato ko tsammani, a gigice ta juya ta nufi sashensu don gaisuwar ba zata iya shi ba cikin wannan hali ta tabbatar da za’a bincika jininta yayi mugun hawa ko ya zuƙe tas yayi ƙasa tsabar tashin hankali Yana zaune kawai ya ga faɗowarta don yau din Asabar ne bai fita ko ina ba da kyar ma ya kyaleta ta fita gaisuwar, ganin halin da ta shigo ya sa yayi saurin Miƙewa yana rike kafaɗunta.”Afeefah! Afeefah menene? Me ya faru?”Ta kasa magana ma, girgizata yayi “Me ya sameki? Afeefah!!!”Da ƙarfi yayi maganan yana bin jikinta da kallo sai dai bai ga komai ba.”A wurin Ammie ne aka ɓata miki rai? Ko wurin Mama ne? Me ya faru kika shiga cikin wannan yanayin? Ki yi min magana mana!”Kuka mai sauti ta fashe dashi kaman wacce aka rufe da duka sai ta sake ɗaga mishi hankali ya juya da sauri zai fita ya tambayo uban da ya taɓa ta tayi saurin riƙo hannunshi tana kukan sossai duk ta ruɗa shi.”Sakeni in ba zaki faɗa min abinda aka yi miki ba Afeefah, Sakeni nace in je in ji dalilin da kaina…!”Da tsawa yayi maganan yana kokarin fusge hannunshi tayi saurin rungumeshi kamkam tana cigaba da kukan da ya ƙarasa cire mishi natsuwa.”I thought ina da muhimmanci a rayuwarka, a zatona duk wani abu da ya shafeka ya shafe ni Meyasa zaka min hakan? Meyasa Ya Saraki?”Sakinta yayi yana riƙo fuskarta idanunshi cikin nata “wa yace miki ba ki da muhimmanci a rayuwata? Kin kuwa san yadda nake jinki Afeefah? Meyasa za ki yi irin wannan tunanin?””Ba gashi ba, idan har ka daukeni da muhimmanci ba zaka binne ni ba, ashe aure zaka yi nan da sati biyu? Aure Ya Saraki irin wannan baka iya ka sanar min ba?”Kukan da take na shaketa ta ƙarasa, sossai fuskarshi yayi Red ainun jijiyoyin kanshi duk suka miƙe kukanta tamkar saukar tafasashen ruwa ne a zuciyarshi shi kadai ya san irin abinda yake ji, a ina ta ji? Zai yi magana ta ture hannayenshi ta nufi ɗaki da gudu tana cigaba da kukan ya riƙe kanshi yana ambaton sunan Allah, bayanta ya bi da sauri sai dai ya tarar ta rufe kofan da makulli hankalinshi ya sake tashi ya shiga bubbugawa yana kiran sunanta cikin damuwa…

