Hausa novels

Halysaah Page 218 By Khaleesat Haydar

HALYSAAH PAGE 218…Ajay ya bude kofar dakin Hajja ya shigo, Khaleesat ta ɗaga kai ta kallesa feeling so relieved da ganinsa, shi ma kallonta yake ya karaso cikin dakin ya zauna kan kujera ya gaida Hajja, sai kuma ya maida dubansa kan Babyn dake hannun Hajja, Hajja tace “Ko a baka ita ne?” Murmushi yayi ya mika hannu ya amshi Babyn, tun da aka haifeta bai gajiya da kallon yarinyar, he just realized he truly have a soft spot for female babies a zuciyarsa, sosai new born din ta shiga ran sa, ya daga kai ya kalli Khaleesat yaga kallonsa kawai take, alama tayi masa da cewa she is tired da fuskarta, amma sai da ta saci kallon Hajja taga ba kallonsu take ba, after some seconds Ajay ya mike ya nufi crib din babyn ya kwantar da ita bayan yayi pecking cheeks dinta, ita dai Hadiyah idonta a rufe suke duk da ba bacci take ba duk tana jin abinda ake yi a dakin, Ajay ya karasa kusa da Khaleesat ya dagota, yayi ma Hajja sai da safe, Khaleesat dai bata yarda su hada ido da Hajja ba ita ma tayi mata sai da safen, Hajja tace “To Allah ya tashe mu lafiya Jiddah….” Bayan sun koma part din su Khaleesat ta tarar har yayi mata shimfida a kasa inda take kwanciya, tun da ta dena kwanciya saman gado shi ma yanxu a kasa yake kwanciya kusa da ita, wani lkcin tayi occupying duk space din sai dai ya sauka kan carpet, he is always making sure she is fine, yanda yake lallabata yake riritata ta cikin ne kawai ya rage bai mayar jikinsa ba, zaunawa tayi kan shimfidar da yayi mata tana kallonsa a hankali tace “Ko dai Hadiyah bata ji dadi da ban je hospital na dubata da Babynta bane, kaga tun asuba fa ta haihu amma ban je ba, shi yasa nace ka bar ni inje ka ki, yanxu gashi kamar bata ji dadin hakan ba” Ajay ya zauna kusa da ita yace “Haka ta ce maki bata ji dadi ba?” Khaleesat ta girgiza kai tace “A’a kawai dai naga mood dinta wani iri ne” Ajay bai ce mata komai ba ya gyara mata pregnancy pillow dinta yace “Kwanta ki huta wife, this is not worth stressing ur self” da taimakonsa ta kwanta ya gyara mata pillow dinta, yayi making sure she is comfortable before switching off the room’s light. The next 7 days was a very busy one in the Emirate saboda hidimar sunan babyn Hadiyah, yan uwa da abokan arziki duk sun zo daga kusa da nesa domin taya Mami murna da samun first grandchild from her only son, Ummi sai da aka yi haihuwan da kwana hudu sannan ta shigo masarautar, taro na gani na fada aka yi ranan sunan Babyn da aka sa ma sunan Mami wato Aseeyah, irin gifts din da jaririyar nan ta samu ba na wasa bane, Ajay kadai siyayyan da yayi ma yarinyar ba a cewa komai kuma duk designer baby wears ya siya mata, he spent soo much on the baby, ga siyayyan da Mai martaba ya bada ayi mata shi ma, kana gani kasan babyn nan er gata ce from every angle, Nenne da kishiyoyin Umma da Aunty Murja duk sun zo ranan suna da sha tara ta arziki for little Aseeyah, ranan sunan ma dai haka Hadiyah ta yini babu wani walwalan kirki, Khaleesat dai na part dinta all through the naming ceremony don ciwon mara ya sakata gaba fiye da kullum, duk bayan wani lokaci yake tasar mata don ma tana da bala’in dauriya, da ya fara kuma yake lafawa, Mami da kanta ta kai ma su Nenne abinci iri iri da aka yi for the ceremony a nan parlon da aka sauke su cikin girmamawa, kuma iya su kadai ne a babban parlon, Hajiya Shafa’atu ta kawo masu babban Cooler cike da peppered chicken ta ajiye ta fita, ta sake kawo tsire da soyayyen cow meat, ga small chops da sauran kayan makulashe, ga kuma carton carton din lemu da aka ajiye masu, bayan sun fita Nenne ta gyara yafin tsadadden gyalenta ga sarkan zinari a wuyanta da dankunnensa wanda Aunty Farida ta siya mata, tace “Ko ya za mu yi da wannan abinci haka Maa sha Allah” Su kansu Mama Zubaida da Mama Shatu shiga ta kece raini suka yi ko wacce da zoben gwal a yatsan ta, baza ka taɓa cewa sun taɓa rayuwa a slum din Mariri ba, Aunty Murja ita ma shiga me kyau tayi babu wanda zai renata, Nenne ta debi kaji a plate tayi kasa da murya tana kallon Aunty Murja tace “Cikin Faridah zai yi wata nawa yanxu wai?” Aunty Murja tayi murmushi tace “Gaskiya ban sani ba Nenne, amma dai nasan zata kusa sauka ita ma yanxu” Nenne tace “Amma ina ga Khaleesat zata riga ta, don ta rigata samun cikin” Ita dai Aunty Murja murmushi kawai tayi, Nenne tace “Kuma a can kasar wajen zata haihu?” Aunty Murja tace “Ehh ta ce min can zata haihu” Nenne tace “Atoh, ai da biyu ta koma kasar waje abun ta, ga er ta da ciki, ga ita wannan da ta haihu, sannan ga ta duk a gida daya, kin ga ai bazata zauna cikinsu suna jan ciki tana ja ba ita ma, shi yasa tun cikin bai fito ba ma tayi tafiyarta kasar waje sai dai Sarki yaje ya dubota bayan ɗan lokaci, sannan ga masu kula da ita sun fi biyar ta ce min a can, har da wannan jakadiyar tata mutuniyar kirki suka tafi” Mama Shatu ta marairaice tace “Ba dai mu da rabon zuwa suna idan Farida ta haihu” Nenne ta wani kalleta tace “Ku kuma a su wa? Wannan ma ai don kar yan gidan su ga bamu yi ma facalar Khaleesat kara ba shi sa na taho da ku, amma da ni kadai zan zo abina, Murja ta zo ita ma ta sameni a nan….” Mama Shatu bata sake cewa komai ba, Mama Zubaida tace “To Allah Ubangiji ya sauketa lafiya dai, ita ma Khaleesat Allah ya rabasu lafiya, naga ita haihuwar ma ko yau ko gobe tashi da kyar zama da kyar, Allah dai ya rabata da cikin lafiya” Nenne tace “Ba komai fa ake bude baki a fada ba Zubaida, ina ruwanki da cikinta da har zaki ce haihuwa ko yau ko gobe kamar ke kika bata cikin, wannan da wasu yare kika yi ma haka yau da sai an daure ki idan abu ya samu cikin nan, ai ba a sa ma ciki ido haka, shi ido guba ne” Mama Zubaida bata sake cewa komai ba a parlon, a ranan su Nenne suka bar masarauta, babu yanda ba ayi da su su kwana ba suka ki, Nenne ta gwammace su tafi gidan su Aunty Murja su kwana….. Bayan sati daya da sunan Babyn Hadiyah Khaleesat ta tashi da matsanancin ciwon mara ranan juma’a, duk da it was so intense amma yana yi yana lafa mata ne, ko kadan bata wani nuna ma Ajay halin da take ciki ba don due date dinta is in 5 days time kuma bata yi noticing rupture of membrane ba, sannan bata son tayi ta masa complain din ciwon mara, amma he was very watchful for any sign of distress a tare da ita shi yasa ma baya nisa da ita kwata kwata, tuni Jay ya koma aiki shi kam yaki komawa don bai son barin ta a condition dinta duk da Mami na sa mata ido sosai, a ranan da safe haka ta marairaice masa ita tana son yin aikin da masu aiki ke yi a bangaren nata duk safiya, haka nan ya kyaleta tayi amma duk da haka sai da yayi assisting dinta duk aikin da zai yi stressing dinta bai bari tayi ba, daga karshe with his help tayi wanka tayi breakfast din da ya kawo mata sannan ta kwanta, all through that day yana parlor kuma jifa jifa yake shiga daki ya dubata, da yamma yana tafiya masallaci, ita ma ta daure tayi sallah sannan ta tafi part din Hajja zata je ganin Baby Eeman duk da Ajay kan kawo babyn part dinsu, ko daxu da safe sai da ya kawota bangaren, a takaice Hadiyah ta gaisa da ita sannan ta mika mata babyn ta ci gaba da labarin da suke yi da Hajja, Khaleesat dai na ta zaune tayi shiru tana dauke da Eeman dake ta bacci, ta dade a dakin har sai da Ajay ya zo dubata ya ganta normal sannan hankalinsa ya kwanta ya fita, wajen karfe shidda Khaleesat ta kwantar da babyn tayi masu sallama ta koma part dinta ta tarar da Ajay a parlor, ya mike with his help ta zauna kan kujera sannan ya zauna kusa da ita yace “Are you okay Jeeddah?” Ta langwabar da kai tace “I am fine, kawai na gaji ne, da wuri zan yi bacci yau” Ya kamo hannunta a hankali yace “If you are feeling pain anywhere ki gaya min fa wife, under water birth za mu yi in sha Allah, I guess ur labor is starting either tomorrow or next in sha Allah, za mu je hospital gobe” Ita dai murmushi kawai tayi, a daddafe Khaleesat ta jira har aka yi sallan isha’i duk da ba bacci take ji ba, she just want to lie down, da kansa ya kai ta har inda take kwanciya, ta kwanta sannan tace ya kashe mata wutan dakin, ya kashe wutan ya fita parlor ya canza channel zuwa na kwallo, can wajen karfe goma Khaleesat na jin sa ya shigo ya zauna kusa da ita, ya gyara mata kwanciyarta a cikin pregnancy pillow dinta, sannan ya kwanta gefenta, ba a wani dau lokaci sosai ba taji alamar yayi bacci, da kyar ta mike zaune ta yanda bazata tashe sa ba ta dau pillow a saman gado ta fita zuwa parlor don yau ji tayi bata son jin sa a kusa da ita, tana kwanciya a parlor bacci ya dauketa, amma ko minti sha biyar bata yi tana baccin ba ta farka. Cikin bacci Ajay ya ji kamar Khaleesat na kiransa, lokaci daya ya bude ido yayi saurin tashi zaune yana duba gefensa yaji babu ita a nan, mikewa yayi da sauri ya kunna wutan dakin yana nemanta a dakin, yaji ta kara kiransa daga cikin parlor tace “Ya Junaid” Although she was calm while calling him amma haka nan ya fita da hanzari zuwa parlon, ya kunna switch din wuta ya ganta a duke ta dafa kujera duk ta hada zufa a goshinta, da sauri ya nufeta ya duka kusa da ita ya rikota cikin kidimewa yace “Are you okay Jeeddah? Let me get my car key” Runtse ido tayi ta kasa ce masa komai, within few seconds har ya shiga daki ya dauko makullin motarsa ya fito, zai ɗagata ta girgiza masa kai tace “I can feel the baby….” Zaro ido yayi ya duka da sauri yana dubata yaji ƙan baby, bai gama recovering daga shock ba sai ga babyn gaba daya ya fito ya saurin tallabosa da hannu biyu, lokaci daya kukan new born ya cika parlon, Ajay ya ƙasa motsi a wajen kamar dai ba likita ba, shortly after sai ga mahaifa ya fado…..*This particular special page goes to all mutanen Ethiopia wato dangin Ajay, iyayen Ajay, yau dai kun yi jika😍💖, Su Aunty Zahrah Mai gari, Mom twins, Maman Janan, Mamata Zeenaru, Maman Faruk, Aunty Maryam, Oum Aayan tawa💖, Aunty Amzaj, Mrs Muhammad, Hajjaju Sumy, Hajiya Rukky Bjw, Ma’ani, our mother Maman Zahrah, Aunty Fattu, My Admin Rabi’ah, Hajiya Kulthum, Namecy Jeeddah, My lovely fan from Bauchi wato kawar Bafillatanar Conversation😂, Moon, Soffys cake and more, Maryam Ibrahim😍, Naimaatuu, sis Naphsat Sanda, Autar Yaya, da ma duk dangin Ajay dake cikin Conversation da bata ga sunanta a nan ba doo Allah tayi hakuri ita ma pejin nata ne, i can’t recall all names, gaba daya na mallaka maku Pejin yau halak malak, ina kuma yi maku fatan alkhairi a duk inda ku ke, Allah ya raya maku zuri’a ya kara maku zaman lafiya da kwanciyar hankali a gidajen ku…😍💖🥰 Au ashe fa har da Meenah parrot dita, uwar Aseeyah er Jawwad😂, to duk mu hade Emirate Ajay na gayyatar mu Suna* _Ex team Jay, su Deejah me lamurje, Maman Manal, Oum Noor, Chamo, Saleey, Oum Nabila, Zero zero, Sis Rukky, duk an baku contract din fito da ankon sunan Babyn Ajay, kala uku za ku fiddo mana, wanda za mu sa da safe, rana, da yamma_ 😂😜

Back to top button