Harijin Sarki Page 1 Romantic Hausa Novel
_*ƘASAR MOROCCO*_ Tana Arewacin Afirka, tsakanin tekun Atlantic da Bahariyyar Rum (Mediterranean).Birnin ƙasar shine Rabat, amma Marrakesh, Fes, da Casablanca sune shahararrun birane.Ana magana da Larabci (Arabic) da Berber (Amazigh), sannan Faransanci.Masarautar ta kasance ƙarƙashin Sarki Mohammed VI, wanda yake da masarauta mai dogon tarihi tun ƙarni da dama.Masarautar Morocco ta kasance mai bin tsarin gargajiya da musulunci sosai.Fada ko “Kasr” suna da ginshiƙai masu kyau, marmara, fale-falen zinariya, da zane irin na Andalusian-Arabic (irin wanda kuke gani a cikin masallacin Alhambra).A cikin fada akwai masu hidima, ’yan majalisar sarki, da sarƙin fada (vizier).Sarki yana da mata fiye da ɗaya, amma tana iya zama ɗaya ce ke da matsayi na “Sarauniya ta farko” wacce ake kira Lalla a Morocco.Yanayin Rayuwa da Al’aduMorocco tana cike da al’adu masu haɗa Larabci, Afirka, da Turai.Ana yawan ganin fadar da ke bakin hamada, daji mai ƙyalli, da kasuwannin gargajiya (souks) masu cike da kayan ado, turaruka, da ƙyale ƙyalen fata.Abincinsu shahara da Couscous, Tagine, da Mint Tea.Tufafinsu irin su Kaftan da Djellaba*Mafari**Samha Idrees El Fahreey* matashiyar budurwa me tashen ilimi nutsuwa da ƙwarewa a ɓangarenta, ta kasance Likitar zuciya da jini wato (Cardiologist and neurophysiologist) ƙwararriyar likita da Wannan babban asibiti na Casablanca yake alfahari da ita, bata da tsoro sannan tanada jajircewa matuƙa akan duk abinda ta sanya a gabanta. Ta ɗauki aikinta kamar yanda ta ɗauki ibada bata wasa da aikinta kuma bata son duk wanda zai kawo mata wasa a cikin aikinta.Ma’abociyar bincike ce akan abinda ya shafi sirrikan ɓoye sannan tana yawan bincike akan abinda ya shafi ruhin mutum da tasirin sha’awa a cikin ƙwaƙwalwa, A duk lokacin da mara lafiya ya ziyarceta takan fahimci sirrin ciwonsa ta cikin tambayoyin da take yi masa ba tare da ta auna wani sashi na jikinsa ba, tanada wani sirrin asirin iyali da bata sani ba, sirrin kallon idanunta yana sanya mutum jin sanyi da tsoro lokaci guda. Mace me kamar maza a ɓangarenta.Yau Litinin ce tunda ta tashi da asuba tayi sallah ya zauna domin azkar bayan ta gama ta tashi tayi wanka ta fara shirin tafiya gurin aikinta cike take da walwala kasancewar cikin weekend ɗin tayi bincike matuƙa akan aikin da Dr Rafiq ya bata wanda takeda yaƙinin indai anbi shawararta za’a samu waraka da yardar Allah, “Samha! Yauma sai kin makara kamar yanda kika saba ko?” Saka takalminta tayi ta yafa mayafin Kaftan nata ta fito da sauri tana ɗaura agogo tace “Jaddah kin hanani sakat tun asuba kika tasheni yanzu kuma kina kwalamin kira me zanyi Miki ne, jagwalgwalon abincinki ne banaci zandai iya shan Mint tea idan kin dafamin” dungure mata kai Jadda tayi tace “Ke dama ba’a Miki gwani wannan yarinya mijinki ya shiga uku da gwasala to ban dafa Mint tea ba in zakici abinda na dafa kici in bakici ki kije” bubbuɗa kwanukan dake jere bisa dinning ta ɗauki abinda zata iya ci ta tuttura suna zagaya parlour da kakarta suna dariya, ta maƙale bayan Jadda tayi mata kiss tace “Jaddatu ina sonki kiyimin Shahara yau itane zanci idan na taso a aiki zanje na gaida Ummu da Abih” ɗaure fuska Jadda tayi tace “Zakije ya bato Miki Rai kizo ki hanamin bacci ko? To babu ruwana tunda kince ba zaki iya zaman guri ɗaya ba nikam Nima na fara gajiya da halinki ki fito da miji kawai mu bashi ke kuje ku ƙarasa rayuwarku tare” Remote na motarta ta ɗauka ta rungumi files files ɗinta tayi waje, inda sabo ta saba wannan surutun a kowanne ɓangare idan tace zata rayu, ta rasa sau yaushe zasu daina mata maganar abinda ba ita zatayiwa kanta ba, aure dai aure dai, shin wai ita zata auri kanta ne ko kuwa aurenta za’ayi? Numfasawa tayi tana ci gaba da driving ɗinta koda suke nuna damuwarsu da aurenta tafisu damuwa shekaru 25 ko ba’a faɗa mata ba ya kamata tayi aure don samawa rayuwarta makoma me kyau, to saidai shin wai ma wa zata aura ne? Meyesa kowa baya fahimtarta? Meyesa idan taso baasonta kuma Meyesa idan aka sota ta yarda taso ake yaudarar ta? Meyesa duk wanda ta ɗauki amanar rayuwa ta bashi sai yaci? Mene yasa ta kasa samun mahaɗi?.Waɗannan tunane tunanen ne fal zuciyarta a haka ta isa babban asibitin Fes Zuciyarta cunkushe da tunanin abinda yake cire mata walwala a ko yaushe, yau ɗin ma babu wata cikakkiyar walwala ta tayi parking ta fito tare da ɗiban files nata da system nata ta nufi hanyar da zata sadata da office ɗinta, lokacin kusan dukkanin likitocin sun samu isowa saboda babban taron da zasuyi da Ministan lafiya na ƙasar yau ɗin da misalin ƙarfe goma na safiya wanda ya kasance shine taro mafi girma da suke gudanarwa duk shekara, a gurguje suka gaisa da Wasu daga cikin abokan aikinta ta shiga office ɗin, komai need kamar yanda akasan tana buƙata, jan kujera tayi ta zauna tana daidaita zaman takardun dake saman table na gabanta ta ɗago cikin son sanin waye ke shigowa office ɗin nata a daidai wannan lokacin, idanunta ne ya sauka kan daya daga cikin abokan aikinta Dr Lamir, ta gyara zaman tabarau ɗin idanunta ta na saita system ɗin gabanta, inda ya ja kujera ya zauna, cikin Yarensu na Berber ya gaisheta ta amsa da gajerar walwala tace “banyi tunanin zan tarar da kowa kamar yanda na tarar yau ba Dr Lamir wannan taron yanada muhimmanci gareku bisa alamu” Cikin ido yake Kallonta yace “Taron yanada muhimmanci gareki kema Dr Samha a wannan taron za’ayi gwajin fasaha don ƙarawa juna sani da kuma ɗaga matsayin wasu daga cikinmu, bana raba dayan biyu kina cikin waɗanda zasu samu wannan karramawar sannan akwai wani shiri na ɗiban wasu daga cikinmu a tura su Casablanca wasu Rabat domin ci gaba da taimakon al’ummarmu, ban cika son canjin wajen aiki ba amma naji ina sha’awar daga Fes na tafi Rabat tabbas nasan na samu daidaitacciyar ɗaukaka da kuma dama ta zama wani a cikin Aikina zanyi amfani da damar yanda ya dace” tunda ya fara maganar take kallonsa tare da kallon abinda yake zanawa akan abinda yake zanawa game da gobensa, ƙasa tayi da kanta tana buɗe wani File a system ɗinta tana dubawa tace “Ba komai nakeso ya ritsa dani ba Dr Lamir banawa kaina fatan zama cikin waɗanda government zata zaɓa yanzu burina kawai shine na daidaita rayuwata ta samu makoma idan hakan ta samu zanyi farin ciki fiye da tafiya Casablanca ko Rabat a matsayin da zanje” tashi tayi tace “Zanje na duba petiant ɗina” daga haka ta fice ta fara zaga inda marasa lafiyarta suke tana duba files ɗin kowa tana ganin abinda ya dace dashi, da ɗaiɗai Saida ta gama duba waɗanda suke kwance domin karɓar agajin gaggawa sannan ta juya ta koma ta zauna a office nata ta fara ganin masu shan magani, misalin ƙarfe goma aka danna bell da take umarni ga kowa ya halarta don fara taro, rufe files na gabanta tayi ta miƙe tare da duban agogon ta 10:03am tayi ajiyar zuciya jikinta cike da sanyi Zuciyarta cike da rauni karon farko a rayuwarta da taji bata buƙatar zuwa wajen taron saidai kashhh…. Ta makara domin tarone da dole kowa sai ya halarta kuma tana cikin waɗanda zasu gabatar da jawabin taron, ta gama tattara duk wani statement nata ta fito gabanta na faɗuwa zuciyarta na bugawa fiye da bugunta na yau da kullum. Hall na taron ta nufa cike da ƙarfin hali daidai zata shiga taji an kirata ta baya ta tsaya cak tare da juyowa ta sauke ajiyar zuciya ganin shugaban asibitin Dr Junaid ya miƙa mata hannu cike da mutumtawa ta ɗora hannunta bisa ƙirjinta, tayi ƙasa da kanta tare da furta kalmar gaisuwa da take nuna tsananin girmamawarka ga wanda ke gabanka. Numfasawa yayi wannan ɗabi’ar ta Dr Samha tana burgeshi gata matashiya me lokaci wadda zamani yake yayinta mutane suke rububinta saidai hakan baisa tayi watsi da Al’adarta ba a matsayinta Na ƙabilar Berber ta usul kuma musulma ɗiya ga babban Malamin Addini Shaikh Idrees El Fahreey, sanannen mutum zamanin rayuwarsa sannan ɗiya ga Dr Binaya sananniyar Likitar gargajiya kuma shugabar Majami’ar Nasayaƙ. Katse masa tunani tayi ta hanyar cewa “Yallaɓai na gama aikin daka sanyani saidai lokacin nuni ya ƙure muna iya bari sai bayan taro?” Jinjina mata kai yayi yace “Hakan yayi Dr Samha mu shiga domin fara gabatarwa” shiga sukayi Hall ɗin kowa ya nutsu cif ya hallara ta zagaya gurin da aka tanada domin ta kasancewar kowacce kujera da mazauninta bayan tayi Gaisuwa irin ta al’adar Berber ta zauna tana me buɗe wani File dake hannunta tana dubawa. Ji tayi idanun na yawo a jikinta tabbas tasan akwai sashen da suke Kallonta wannan ta sanyata ɗagowa daidai lokacin da Mai girma ministan lafiya ya shigo ya samu rakiyar rukunin kariya na IV12 kowa ya miƙe tare da miƙa gaisuwa cikin girmamawa ladabi da kuma sallamawa kamar yanda al’adar taron take aka fara buɗeshi da addu’a sannan akayi taken ƙasa da kuma taken ma’aikatar lafiya ta ƙasar sannan kowa ya zauna, masu gabatarwa suka fara gabatarwa ɗaya bayan ɗaya, ta shagala da duba abu mai muhimmanci a tattare da ita ta fara jiyo amon sauti na ambaton sunanta, faɗuwar gaban data fara da ita ta dawo mata sabuwa daidai lokacin da take Miƙewa ta fara takawa a hankali tanajin idanun mutum ɗaya na yawo bisa duk wani motsinta, haka ta daure ta ƙarasa ta rusuna a ladabce ta ƙara kwasar gaisuwa gurin manyan ƙasar da suka samu halartar wannan taro da yake faruwa duk watan shida na kowacce shekara. Bayan gabatar da kanta ne ta fara bayani akan abinda ya shafi sashin da take jagoranta da irin nasarorin da suke samu da kuma irin abubuwan da suke damunsu da tallafin da suke buƙata a ɓangaren gwamnatin ƙasarsu me adalci. Ɗagowa tayi don fuskantar yanayin da masu sauraronta suke kasancewa da jin bayaninta, idanunta ya sauka cikin idanun wani mutum me cike da kwarjini da fuskar jarumta sanye cikin kayan da suke nuna shiɗin mutum ne mai girma a wannan ƙasa. Saurin janye idanunta tayi lokacin da saƙo biyu suka gauraya jarumta biyu ta haɗu sirri ya shiga cikin sirri sai ya haifarwa da gangar jikin kowanne kasala mara misali, tabbas Dr Samha ta firgita da abinda ta gani a idanun wannan mutumin da batasan waye shi ba kuma ta razana da ƙarfin ikon tsafin data gani a cikin ƙwayar idanunsa, rawar jikinta ta tsananta wadda ta sabbaba mata bada abin magana ba tare data gama furuci ba ta koma mazauninta ta zauna, cike da zullumi tare da tunanin “to shi wannan sihirtaccen bawan wanene?” Ɗagowa ta kumayi suka kuma haɗa idanu ƙirjinta ya kuma bugawa da ƙarfin gaske ta furta “Hasbunallahu wani’imal wakil” abinda ya sanya waɗanda suke kusa da ita Kallonta, Dr Lamir ya riƙo hannunta cikin mamaki yace “Kina lfy Dr?” Wata ajiyar zuciya ta sauke ta kuma ɗago idanunta a tsorace saidai ga mamakinta yanzu babu kowa, a gurin da wannan mutumin yake, ta sauke ajiyar zuciya me ƙarfi ta miƙe tace “Inada uzuri Dr zan koma office” daga haka ya fice Dr Lamir ya bita da kallon mamaki, bai taɓa ganin bayyannannen firgici a tare da ita ba sai yau. Koda ta fita tayi nufin komawa office ɗinta ne amma sai ta rinƙajin wani sauti a cikin kunnuwanta yana mata kuwwa da cewa, “ki tafi gida don samun daidaiton tunani” da wannan ta yanke shawarar tafiya gida tanajin yanda ƙarfin dukan zuciyarta ke ƙaruwa tana shiga mota da nufin kunnawa wayar dake cikin aljihun rigar dake jikinta ta fara neman agaji, a ɗan firgice takai hannu ta ɗauki wayar ta sauke ajiyar zuciya ganin number Shugabansu Dr Junaid ta latsa accept ta tare da makala Bluetooth a kunnnenta kafin tayi magana yace “Ki sameni a office yanzu” ji tayi wani abu ya caki zuciyarta ta cika da kunci da tarin zullumi wanda bata taɓa shiga irinsa ba haka ta fito jikinta babu ƙwari ta nufi hanyar da zata sadata da babban Ofishin asibitin ta danna bell aka bata izinin shiga ta shiga tare da maida ƙofar ta rufe ta juyo tana mai furta sallamar data maƙale a maƙoshinta ta tsaya cik jikinta na ci gaba da ɗaukar rawa, kasa ko motsa ƙafarta tayi duk kuwa da bata gama tantance wanda ta gudarwa sake gani ne a ɗakin taro ko kuma wanine daban ba amma taji bata buƙatar ganin mutum makamancinsa. “set down mana Dr Samha” cikin rashin laka ta fara jan kyawawan ƙafafunta ta isa inda aka Umarceta da zaman ta zauna tana me ƙoƙarin arowa kanta jarumta ta buɗe baki cikin muryarta me dukan zuciya tace “Yallaɓai?” Saurin tarar numfashinta yayi da cewa “Naga kina shirin fita Dr gashi ba’a gama taron ba shin hakan na nufin wani uzuri me muhimmancin da yafi tsayawa kiji makomar ƙoƙarinki ya taso Miki ne ko kuwa baki buƙatar karɓar sakamakon aikinki tuƙuru?” Ƙasa tayi da kanta tace “Sorry Sir” Numfasawa yayi yace “Ina sakamakon binciken da na sakaki” hannunta na rawa ta ta buɗe system ɗinta ta buɗe files na binciken da tayi ta tura masa gabansa tace “Yallaɓai wannan shine abinda na gano game da bincikenka na ɗauke komai a modern na adana maka kuma ina shirin sake zurfafa bincike game da Alaƙar Sha’awa da ƙwaƙwalwa, ciwon yanada tasiri ne da jinin dake zagawa a jikin ɗan adam, ƙwaƙwalwa ce ke fara karɓar saƙon tana turawa zuciya sai jini ya amsa ya bawa dukkan gangar jikin ɗan adam aiki, amma ranka shi daɗe akwai nau’in sha’awar da take zama daga ɗarsawa zuciya ne sai ita zuciya ta aikawa ƙwaƙwalwa, kuma yawanci shine ciwon da yafi damun mutanenmu saɓanin wancan kashin na farko akwai abinda karantawa da faɗaɗa bincike akai shine zai iya fitar da sakamakon, naso tsawaita binciken saidai…..” Shiru tayi tana wasa da yatsunta, inda dukkansu suka zuba mata idanu musamman *VIZIER Rayyan Hamad ZIRKAN* da tun shigowarta sai yanzun ya ɗago ya zuba sihirtattun idanunsa akanta “Uhmm! ina sauraronki Dr Samha saidai me?” Ɗagowa tayi tace “Bansan ta ina zan fara ba yallaɓai dole binciken yana buƙatar kusanci da me irin wannan lalurar ta hanyar hakan ne za’a iya samun sakamako me kyau” murmushi yayi dama yasan ƙarshen maganar kenan, yace “wannan bazai zama abu me damuwa ba Dr kamar yanda aka tsara manyan ma’aikata zasu samu ninkin matsayi daga wanda suke zuwa samansa to kema kin samu Hukumar gudanarwa ta ƙasa ta ɗaukeki daga wannan asibitin ta mayar dake Babban Asibitin ƙasa dake Rabat”
