Mejo Najeeb Page 25 By Autar Alheri
“Kai hannunshi gefen wuyanta yana janye sumarda tazubo awurin. Runtse ido Isseta taƙarayi sosai kafin tace “of course…Humm yasauke numfashi tareda ƙara matseta ajikinshi kawai yana shafar jikinta yana tunanin abubuwa dayawa gameda ita wanda suka zomishi amatsin baƙi nazahiri dakuma na baɗini…Isseta kuwa jin yana neman kauce hanyane yasata kwaɓe fuska tana faɗar “please aikifa nakeyi, taƙarasa faɗa taba turo ɗan ƙaramin bakinta gaba. Buɗe blue eyes ɗinshi yayi yana kallonta kafin yayi murmushin gefe baki yace “Humm bakiso nabarki kiyi aikinba ai tunda baki iya gaisuwaba kuma ina tunanin haruffan sunana sunɓata a ƙwaƙwalwarki inaso nadawo dasune, yafada yana ƙoƙarin tura hannunshi cikin rigarta…dasauri tariƙe hannu tana faɗar “good morning yah najeeb tareda marairaice fuskarta, domin tagano nufinshi sarai…..wani shi’umin murmushi mejo yayi kafin yaɗage gira ɗaya yana faɗar”au ashe haruffan sundawo kenan dawuri haka? Itadai batace mishi komaiba domin taƙagu yafice yabata wuri…Shikuwa sam beda niyyar Hakan hasalima wuri yasamu yazauna a kitchen ɗin yana faɗar “to ƙarasa aikinki nanuna Miki yadda ake gaisuwa domin sam wannan bataminba yana maganar kamar wani yaro ƙarami….itadai Isseta batace mishi komaiba domin kullun sabon mamaki yake ƙara shayar da ita..ahakan taƙarasa juye mishi abuncin kana tashiga gyara wurin, tana gamawa dan karya koma samun damar yin abinda yayi niyya tayi saurin janyo table ɗin dake kitchen ɗin tashiga jeramai nashi abin breakfast ɗin seda Tagama tsabb. Tayi saving ɗinshi tukunna tabar kitchen ɗin tanufi bedroom ɗinta domin tasake yin wanka sabida guminda tayi…Shikuwa hankali kwance yashiga cin abincinshi yanaci yana lumshe blue eyes ɗinshi domin sosai haɗin indomie ɗinnan yayi mishi daɗi seda yagamaci tukunnah yaɗora da black tea ɗin data ajiye mishi.Kana yakwashi kayanshi zefice yamiƙe kenan zehaura gunta general aliyu yakirashi Yana sheda mishi general faruk yasauka yazo su ɗauko shi a airport Hakan yasa yafasa binta yafice daga gidan gaba ɗaya.Gombe StateGidansu IssetaYau laraba shirye shiryen tarewar anty hawwa gidan sabon angonta kawai akeyi agidan, Gabaki ɗaya ƴan uwa da abokan aziki nanesa dana kusa sun bazamo musamman dasukaji cewar mijin nata me hannu dashini ne Hakan yasa kowa zumuɗin wannan bikin yakeyi…abangare mama bintu kuwa Gabaki ɗaya hankalinta atashe yake domin kuwa su sulaiman sun tabbatar mata cewar Maryama bata garinnan domin datana cikin garin doline Zasu ganta sabida yadda suka bazama nemanta amma ba labari…yah Kabir ma Hakance take agunshi domin hankalinshi baze kwantaba tunda na mamarshi ba’akwance yakeba…gida yacika yabatse mutane se ciye ciye akeyi yayinda amarya kecan tana holewarta itada ƙanwarta anty bilki, seda suka gama sheƙe ayarsu tukunnah sukayi wanka suka nufi gidan me makeup.Da misalin ƙarfe 2 Dede ƴan ɗaukar amarya sukazo inda aka fitoda anty hawwa tasha kwalliya kuma tayi kyau Masha allah. gun Abba aka fara Kaita yayimata nasiha sosai kana aka kaita duka inda matan gidan suka yi mata tasu huɗubar ahakan aka fitoda anty hawwa zuwa garin Lagos gidan mijinta su anty bilki sune manyan ƙanen amarya kuma kawayen amarya mamansu yah balah kuwa sune akan gaba wurin kai amarya ɗaki. Semuce Allah yasauke su lpy……motocin ɗaukar amarya na ɗagawa wasu dalla dallan motocin nasawo kai unguwar motocine masu masifar ɗaukar hankali da girma wanda daganinsu kasan nera tayi kuka awurin, abakin ƙofar gidansu Isseta sukayi Perking, kamin kosuwaye aciki sufito kuwa tuni yara da manya sukayiwa motocin ƙawanya..Gimbiya mardiyaTsaye take agaban yayar tata tana kora mata bayani kamar Hakan. “Anty laweesat kisani nibazan lamunci wannan zaluncinba wannan ciwon da najeebullah keyi wata rana ze iya rasa rayuwarsa sanadinshi, sanin kankine wannan aljaninda suke sakawa yana sakar mishi wannan jiyon watarana ze iya hallakashi to kafin akaiga yin Hakan nakamashi kuma nasaka an daureshi sekuma abu nagaba wlh tunda waccan matar bata tsoron Allah nima Sena nuna mata kalar nawa rashin imanin, tana gama faɗar Hakan Takoma ƙatuwar macijiya tare da yankan jeji ahasale cikin mugun gudu….ajiyar zuciya Maah tasauka tana kallo umaima kaminta girgiza kanta cikin damuwa tace “ƙawata kina ganin abinda mardiya keshirin aikatawa dedene kuwa? Ninaso ace tabarsu su fallasa kansu dakansu domin nasan zalunci baze taɓa dorewaba…. “Hakane kam amma nima tunfarko dakinbi sharawata laweesat datuni anwuceda wannan matsalar amma kikaƙi gimbiya minene anfanin tausayin wanda basa tausayin kansu? Minene anfanin rufawa wanda baya rufawa kansa asiri? Haba kema kiyi tunani mana wlh hukuncinda gimbiya mardiya taɗauka shine Dede kuma itace Dede da kowanne taƙadari wlh, cewar umaima cikin Jin haushin su….tunda tafara magana maah tazuba mata ido kawai tana kallonta hartakai ƙarshe, ajiyar zuciya kawai tasauke kana tace”shikenan tunda Hakan kuka zaɓa amma ni naso ace abikomai asannu wata ƙila masu shiryuwane base ambayya nasuba… “Shiryuwa laweesat wacce irin shiryuwace zasuyi ayanzu wanda basuyiba tun shekaru 27 baya wannan ai sedai arakasu da halinsa, umaima tafaɗa cikin fishi… “To shikenan Allah yakyauta. Cewar maah tana komawarta cikin ruwa……murmushi umaima tayi kawai tajuya tanufi cikin gari kaitsaye gidansu Halima tanufa inda tasameta ita kaɗai tsakiyar gidansu tana shara, sallama tayi Halima ta amsa kana tashigo gidan yadda bazata tsorotarda itaba…kallonta Halima tayi kana tace “inawuni. “Lpy qalau Ina mamarki? “Batanan kishigo kizauna yanzu zata dawo. “Aa bazama nazoyiba Maah ɗinku ce ta aikoni wirinki Maah ɗin Isseta tace nagaya miki gobe kishirya zuwa asibiti zata ɗauko miki Isseta kuhaɗu acan asibitin. Ihun murna Halima tasaka tana faɗar in sha Allah kuwa gobe zataje Allah yakaimu darai da lpy tafaɗa cikin zumuɗi sam ƙwaƙwalwarta bata tsaya yimata tunanin to wacece wannan Maah ta aikoba kotayi tunanin a,Ina Ita wannan matar Taga maah dahar zata sikota sam ita bata kawo komai aranranta ba burinta kawai gobe tayi domin Taga aminiyar tata.. ahakan umaima Tayi mata sallama tatafi.Lagos”Ummi ummi kina inane? Cewar mama data fito daga ɗakinta fuska ba walwala. Cikin sauri ummi dake bedroom ɗinta itada juwaira tafito tana amsa kiran mahaifiyar tata inda suka haɗu a Perlor part ɗin mamar. “Ummi jiya yayanki ba’agidannan yakwana ba kuma koda yafita dare yayi sosai jeki duba pert ɗinshi kigani koya shigo domin tinɗazu nake jiran dawowarshi naji ko lafiya amma bedawoba. “innalillahi barana duba to amma gaskiya bana tunanin yadawo sabida koda asuba naji dady natambayar Hajiya Umma shi akan beje masallaci ba kuma nemanshi yakeyi. “Tofa iKon Allah amma abinnan da mamaki kuma nakira capital Jameel yacemun basa tare domin Shima seda yazo bega motarshi ɗaya ba yasan baya gidan. Mama tafaɗa cikin damuwa….ummi zatayi magana kenan baba inno tashigo parlor me aikin Hajiya Umma kenan. Gaisarda Hajiya mama tayi kana tace Alhaji nakiranta yana general parlor. “Okay Ina zuwa yanzu. “to Hajiya baba inno tafaɗa tana barin perlor…mama kuwa seda Tagama alhinin rashin kwanan najeeb agidan tukunnah tanufi general parlor.Anan tasamu Hajiya Umma Itama zama tayi tana gaida megidan nasu. Amsa mata yayi kana yafara magana kamar Hakan. “Hajiya jamila, yakira asalin Sunan Hajiya Umma. Na’am Alhaji ta,amsa tana bashi ankalinta gaba ɗaya domin tasan maganar dazeyi me mahimmanci ce.. “Hajiya safiyya. Yasake Kiran Hajiya mama, Itama amsa mishin tayi cikin kulawa. Nisawa yayi kana yace “abinda yasa nace akiraku akwai wani baƙon al’amari daze faru agidannan inaso ku karɓeshi hannu biyu kuma kar wadda tanuna gazawa ko ɓacin ranta akan abin ba lalle Sena gayamuku ko minene ba ayanzu amma gobe idan Allah yakaimu zan sanar muku inaso ku ɗauki abin amatsin ƙaddara ce wadda tariga fata kusani Hakan Allah yatsara babu mahani, ɗan shiru yayi yana kallonsu kamin yaci gabada faɗar anjima idan Allah yakaimu zamuyi baƙi masu mahimmanci agidannan inaso kuduba kayan abincin damuke dasu idan akwai abinda babu kugayamin akawo domin ashirya musu wadataccen abinci sabida banaso sunemi wani abin surasa agidannan ina Fatar Kun fahimceni banaso Asamu wata matsalar daga gare ku. Yaƙarasa zancen cikin bada umurni tare da haɗe fuska domin karsu kawo mishi wargi azancenshi…..ajiyar zuciya Hajiya Umma tasauke kana tace “shikenan Alhaji Za’ayi yadda kace. “Yayi kyau Hakan jamila daman nasan baza’asamu matsala daga garekiba. Hajiya mama kuwa murmushin gefen baki tayi kana tace “Allah yakawosu lafiya sedai bamuda wada taccen Nama agidan domin baze wadaci baƙi ba. “Okay badamuwa safiyya za’akawo daga Hakan yatashi yayi ficewarshi. Dukkansu miƙewa sukayi kowacce tanufi ɗakinta zuciyoyinsu fall tunanin wannan wanne irin al’amarine Alhaji Khamis yace zefaru agidan?🤔AirportTsaye suke su ukku atsakiyar filin jirgin kamar wasu taurari dariya sukeyi suna fira cikin nishaɗi dafarin cikin ganin junansu yayinda gogan kemurmushi kawai yana kallonsu. Mejo Najeeb kenan se general aliyu dakuma general faruk tareda zugar yaransu dasuke take musu baya abin gwanin birgewa… motocin su suka shiga inda ilahirin airport ɗin yaɗauke da jiniyarsu atake suka halba kwalta sukabar mutane da kallon bayan motocinsu🤩 sabida sun haska airport ɗin baƙarya💃Kaitsaye gidansu general aliyu suka wuce kaitsaye bayan sunyi Perking motocinsu sukafito tare da nufar cikin gidan….a Perlor suka samu habbey da mufeedah zaune sunacin kwaɗon zugale, cikin sauri mufeedah tataso tana faɗar oyoyo yah najeeb yadawo shine jiya bakazoba kabarni inata jiranka. Shiru tayi ganinsu da baƙuwar fuska wadda batasaniba, tana binsu da kallo…ɗan murmushi mejo Najeeb yayi kafin yabuɗe baki cikin cool voice ɗinshi yace “ayya sorry my little sis namantane shiyasa but I promise you yau zankaiki kinji, yaƙarasa zancen suna karasa shigowa cikin perlor. “Yee yah najeeb ngd sosai zanshirya idan zaka fita zanbika domin idan katafi badawowa zakayiba. “To sarkin fitina Zaki bari muhuta ko Sena make bakinki kinwani dame mutane sekace wata jinjira cewar general aliyu.Murmushi general faruk yayi cikin sanyin halinshi yace “ah,ah bazaka dukar muna ƙanwaba daga tafaɗi gaskiya. “Allah yaya gaskiya nafaɗa amma zedukeni tayi zancen tana komawa bayan general faruk ɗin. “Hakane kam koda yakema baruwana ai damuka shigo mejo kawai kika kula kogaidamu bakiyiba namafasa tare Miki faɗan yafaɗa cikin tsokana.. “ayya sorry Yaya wlh sabida inata jiran yah najeeb ne zekaini shopping shiyasa Amma zan gaidaku ai, inawuni kunzo lafiya? Dariya dukkansu sukayi general aliyu nafaɗar munafuka kamar gaske. “iKon Allah wai mufeedah bazaki bari mugaisa da yaran nawaba kinsakasu agaba da rigimarki? habbey tafaɗa tana murmushi. “Allah kuwa habbey wannan Autar taki ko aku albarka a gun surutu, cewar general aliyu. Yayinda su general faruk da mejo suka shiga gaidata…ta amsa musu kuwa cikin sakin fuska domin matar nada kirki sosai, sunɗan taɓa fira awurinta kamin suwuce pert ɗin general aliyu inda suka bawa general faruk wani bedroom domin yayi wanka yahuta…hakako akayi bayan yayi wanka yahuta yafito anan perlorn general aliyu inda mufeedah tacika bagansu fall dakayan ciye,ciye Dana abunci abisa umurnin habbey…seda sukaci abincinsu suka ƙoshi kana suka shiga tattauna yadda tafiyarsu South Africa zata kasance cikin kwanakinnan.Gombe StateGidansu IssetaSecurity ne suka fito daga cikin wasu motocin kusan su 8 dukkansu sojojin ƙasar Niger ne dubada yanayin shigarsu, cikin sauri ɗaya daga cikinsu yazo yabuɗe marfin motar tsakiya…ahakanli tasauko daƙafarta akasa kana tafito gaba ɗayanta Hajiya Hannah kenan cikakkiyar buzuwar asali mece me cikar haiba da Kamala…da kallo tabi mutanen dake wurin kamar yadda suma ɗin ita suke kallo, ahankali tashigabin uguwar da kallo yadda Gabaki ɗaya tajanca mata tana tunanin marabarta da garin kusan shekaru sha Biyar kenan, ajiyar zuciya tasauke tana share ƙwallar idonta kafin tafara tafiya ahankali tanufi cikin gidan yayinda ƴaƴanta ketake mata baya sapwan da nazeer. Abakin soron gidan tahaɗu da iyya hassi domin tuni tabazamo jin yadda yara ke ihu suna Koɗa motocin dasuke ciki atinaninta wasu dangin angon ƴarta ne setaga saɓanin Hakan. Baki tawashe tana faɗar “sannu da zuwa Hajiya sannunku dai maraba lale lale. “Murmushi Hajiya Hannah tayi tana amsa mata gaisuwar datake mata, lokacinda suka ƙarasa cikin gidan….iyya hassi kuwa hafizu takira ƙanen yah balah kenan tabashi kuɗi jikina rawa tace yaje maza bakin layi yakarɓo musu Lemun roba da ruwa aibaza’abar baƙi ahakanba tabashi jikina kaɗi kamar mazari. Yakarɓa yafice daga gidan… Itadai Hajiya Hannah kallonta kawai takeyi tanabin gidan dakallo ranta namata ƙuna idan kuma tatuno wani abin setaji sanyi aranta. Mama salmu ce tafito tanabin su Hajiya Hannah da kallo itada yaranta ganin dai basuda alamun reni yasa tasaki ranta suka gaisa dajuna cikin mutunci….itadai Hajiya Hannah gidan kawai takebi da kallo ganin bataga wadda takeson gani bane yasa tabuɗe baki ahankali tace “dan Allah ina bintu kotana gidannan? Hajiya Hannah ta tambaya…ido suka zuba mata kaɗan lokaci kafin mama salmu tace “tana cikin ɗakinta zogata nan tayi gaba suka mara mata baya zuwa ɗakin mama bintu…itako mama bintun tana zaune abin duniya duk ya ishe ta taji muryarda bazata taɓa mantawaba arayuwarta tasauka acikin dodon kunnenta wanda yasa gabanta mummunar faɗuwa, azabure tamiƙe zata fito sukayi karo dasu a Perlor ta su Zasu shigo itakuma zata fita. Kallon kallo aka tsayi tsakaninsu kafin mama bintu tabuɗe bakinta dake rawa tace Hajiya Hannah.. “na’am Hajiya bintu tafaɗa cikin murmushi kafin tadubi bayan mama bintu ganin bataga kowaba tace “Hajiya bintu ina letteiy ne? *INA ƳATA*?? Tatambaya cikin ɗaukin son ganin ƴar tata. Ido su mama salmu da iyya hassi suka zuba musu sunason ganin inda ƴar tata take…mama bintu kuwa ƙwallar data ciki idonta tashare kana tabuɗe baki cikin kuka tace “kiyi haƙuri Hajiya Hannah nakasa cika Miki burinki nakasa cikamiki mafalkinki nakasa kulada amanar dakika bani dan Allah kiyafemun, taƙarasa zancen tana rushewa da wani irin matsanancin kuka memasifar tashin hankali wanda dajinshi kasan daga zuciyarta yake fita…cikin tashin hankali ruɗu firgici Hajiya Hannah tariƙo hannun mama bintu duka biyu cikin rawar murya take cewa “please aminiyata kiyamun miyake faruwane?? Kigayamin abinda kunnena ze iya ɗauka dan girman Allah karki manta yadda da amana tasa nabaki ƴata mace ƙwaya ɗaya tall dana mallaka aduniya karkicemun kinci amanar dana baki please kigayamin ina *MARYAMA* take??? ina letteiy??? Bintu ina kika kaimun ƴata?? Taƙarasa zancen tana rushewada kuka itama wanda yasa sapwan saurin rungumota ajikinshi karta faɗi….ido mama salmu da iyya hassi suka zaro atare suka haɗa baki wurin fadar Maryama kuma?? Kafin su samu damaryin magana suka tsinkayo muryar nazeer dayazo kusan mama bintu yatsaya agabanta idonshi babu amalar wasa yace “mama bintu ina ƙanwarmu take?? Nasani cewar bazaki taɓa cutadda babinmu ba bazaki yadda murasa letteiy ba kigayamin gaskiyar abinda yafaru da ƙanwata ƙarki ɓoyemun komai? Yaƙarasa zancen yana kafeta da manyan idanuwanshi. “Sosai mama bintu kekuka metsima zuciya tajima tana yinshi kafin ta shiga sauke ajiyar zuciya kusan minti 4 sa’anan tafara bashi labarin zaman Isseta agidan tindaga farko harƙarshe da aka ƙullah mata makirci abbansu yakoreta tare da Auren daya ɗaura mata wanda yamaida akan anty hawwa yanzu…tunda mama bintu tafara magana Hajiya Hannah tanemi kukanda takeyi tarasa wani irin ƙanƙancewa idonta suka yi wanda kallo ɗaya zakayi mata kasan cewar ceke suke tabb da bala’i….hakama sapwan da nazeer wanda zuciyarsu ketafasa har acikin rigunan jikinsuBabu wanda yasamu damar cewa komai acikinsu har mlm Musa yafaɗo gidan kamar anjefoshi saka makon danƙara danƙaran motocin dayagani awaje gakuma sojojin Niger tsaye kamar dogarawa kowannensu babu alamun rahama ataredashi, aiko yana shigowa sukayi ido huɗu shida Hajiya Hannah wanda yasaka cikinshi muguwar mirɗawa aguje yasure buta yayi ban ɗaki ko sallama babu ɓalle gaisuwa, Yajima aciki kafin yafito yana raba idon kamar anturke shege lahira…wani mugun kallo Hajiya Hannah tawatsa mishi irin kallonnan wanda babu sassauci ko kaɗan acikinshi,,kallon kazalunceni ka tarwatsamin farin cikina dana daɗe ina mafalki,,kallon duk abinda kayi bashine Kaci wanda dolinka zaka biya….Hakan yatabbatar masa dacewar tasan komai kenan, salati yafara acikin ranshi babu ƙaƙƙautawa wanda indan yaɗauko wannan yasuɓuce masa yakamo wancan kuma duk shi atunaninshi cikin ranshi yakeyi besan cewar afili yakeyinshiba…..wani wulakaccen kallo sapwan wa watsa mishi kafin yace “wlh indai salatine yanzuma kafara, tareda janyo wayarshi yashiga Kiran sojojin dake waje, suna shigowa kafin sapwan yayi magana Hajiya Hannah tarigashi ta hanyar faɗar “kukama matarnan kujeda ita, tafaɗa tana nuna iyya hassi, kana tace wasu daga cikinku zasuje garin Lagos suzonin da ɗayar domin wlh wlh wlh kunji rantsuwar musulmi sekusan cewar kun cutarda ƴa ɗaya tilo mace agun shugaban kasar Niger. Kana tajuya gun mlm Musa tace bazansaka akamaka yanzuba sabida ina buƙatar kafitomun da ƴata aduk inda take cikin 24 hours wlh idan bahakaba Sena saka antada ilahirin zuri’arka dake garin gombe, tana gama faɗar Hakan tajuya tafice daga gidan ƴaƴanta suka mara mata baya yayinda sojojinnan suka tasa ƙeyar iyya hassi agaba tana ihu tana kururuwa tana ƙarawa….!





