Fentin Zina Page 16 Hausa Novel
**Da sauri tasha gaban shi ta kama hannun shi ta manna a kirjinta saitin zuciyarta ta marairaice murya tace abun qaunata bana jin rayuwata zata ci gaba da moruwa muddin aka ce babu kai a cikinta, dan Allah ka daina furta mun irin wannan kalmar da zata iya tarwatsa zuciyata, kaji yanda zuciyata take laguden bugu duk a ta dalilin soyayyar ka, ta fada tana kara matse hannun nashi a kirjinta.Ahmad wata iriyar sha’awa ce ta taso masa lokacin daya ji hannun shi a kirjinta nan da nan ya rasa natsuwarsa sai dai yayi karfin halin boyewa yace yana kama hannun nata ya damke, sweetheart ki sani cewa a duk duniyar nan ban taba son wata diya mace ba kamar yadda nike tsananin son ki dan Allah ki amince dani kinji.Gyada kai tayi suka shige falon.Babu motsin kowa a cikin gidan da alamun babu kowa ina shi abokin naka da matarsa suke?Ta fada tana kallon shi kamar tana son karantar wani abu a tattare dashi.Kiyi hakuri karya na miki cewar matar gidan tana nan amma tayi tafiya tun kwanaki biyu da suka gabata shi kuma abokin nawa ya fita ne kawai domin ya bamu damar sararawa a tsakanin mu.Da mamaki take kallon shi tace amma ai kasan ba jimawa zanyi ba meyasa ka bari ya tafi?.Sweetheart ki gane cewar akwai bukatar sirri tsakanin masoyi da kuma masoyiyarsa ba ko wani zance ne zamu iyayi a gaban saba hakan yasa na barshi ya wuce domin muma mu shana, ya fada yana dariya.Gaskiya ni hankalina bai kwanta da zaman mu iya mu biyu a cikin gidan nan ba kasan cewar babu kyau don idan mace da na miji suka kebe shaidan ne cikon na ukun su hakan yasa gara in tafi kawai kuma dama ga yanayin condition din da nake ciki a gidan mu.Ta karashe tana kokarin mikewa.Zaki iya tafiya sai dai ki sa a ranki muddin kika stepping out without mypermission babu ni babu ke kuma kada ki sake nuna kin sanni koda kin ganni a hanya.Dakatawa tayi daga shirin mikewar ta koma ta zauna ta zuba mai ido, yi yayi tamkar baisan shi take kallo ba sai can ya juyo ya kalleta ya dan saki murmushi yace, kiyi hakuri banyi niyyar in bata miki ranki ba kinsan yadda nike sonki shiyasa naji babu dadi da kika ce zaki tafi kenan baki damu dani da yanayin da nike ciki ba.Na damu akan ka kwarai Ahmad kaine dai baka gane hakan ba amma da gaske na damu da kai fiyeda yadda na damu da kaina.Matsowa yayi har jikinsu na gogan juna ya shafa fuskarta cikin salo yace a cikin kunnenta cikin rada, yanzu kuwa zanga irin damuwar da kika yi dani in dai gaskiya kika fada.Tsigar jikinta ce ta tashi yayinda sha’awa ta kamata bata iya hana shi abubuwan da yake mata ba har saida taji yana kokarin saka hannu cikin rigarta kamin ta yunkura ta ture shi tana haki tace ba daidai bane abunda muke kokarin aikatawa dan Allah kada mu marawa shaidan baya ta hanyar bin hudubar sa.Da jajayen idanunsa da sukayi rinewar sha’awa ya kalleta yace yanzu irin kaunar da kike wakar kina yimun kenan kullum? Meyasa baza ki iya sadaukar mun da kanki ba ashe soyayya ta bata kai ba? Babu damuwa nidai Allah ya gani ina sonki fiyeda yadda kike tsammani amma tunda ke ba haka bane a wajen ki bazan miki dole ba saidai ya zama dole in rabi dake koda kuwa sonki zai kasheni.Ta tsani jin wannan kalmar daga gare shi sai tayi saurin isa gare shi ta duka akan kafafunta tace ka fahimceni Ahmad duk yadda kake tunanin soyayyarka a cikin raina ka wuce hakan amma ba daidai bane mu aikata sabon Allah saboda kawai son zuciyar mu yanzu idan Allah ya dauki ranmu a daidai lokacin da muke aikatawa fa? Ka dai san makomar hakan a gare mu.Nine fa wanda zai aure ki Ameena, koda komai ya faru baza kiyi dana sani ba haba dan Allah yanzu ina kike so inkai sha’awata ko so kike in tsallake ki keda nike tunanin zaki rufa mun asiri inkai wa na banza a waje idan kika mun haka meye ribarki?.Dan Allah Ahmad na rokeka mu bar wannan maganar ba mai yiwuwa bace zan tafi gida.Zaki iya tafiya kamar yadda na fada miki a farko, yace yana kawar da kai daga barin kallon ta.Dan Allah kayi hakuri.Dakata, ya daga mata hannu ya kara da cewa zaki iya tafiya, ya nuna mata kofar fita.Taya zan tafi alhalin kana a halin fushi dani sannan ma idan na tafi bansan yaushe zan sake ganinka ba nafiso muyi sallama mai kyau kafin tafiyata wacce zata dinga sanyani nishadi idan na tuna.Baki nemi hakan ba Ameena, wannan abunfa mintuna biyar sunyi yawa an gama kum babu wanda zai sani daga ni sai ke kuma na miki alkawarin zanyi jajircewa sosai gurin neman aurenki.Yanzu kana nufin bazaka yi hakuriba har saina aminta da kudurinka.Bafa tilas na miki ba, kina iya tafiya idan hakan bai miki ba ni sai in nemi wata nasan bazan rasa ba.Wani mololon abu ta hadiya saboda jin ya ambaci wata kuma wai zai kwanta da ita sai taji a ranta gara ta bashi kanta akan dai yaje ya nema din kamar yanda ya fada.Shikenan na amince da abunda kake so, bazan iya bari ka rabi wata ba alhalin ni ina nan.Rungume ta yayi suka mike a hakan har ya kaisu bedroom ya tureta ta fadi kan gado shima ya bita.Bayan wasu mintuna.Ameena tana zaune saman tsakiyar gadon tana risgar kuka kamar ranta zai fita, Ahmad ya fito daga ban daki ya bitta daa kallo yae har yanzu kukan kike? Kiyi shiru kinji babu komai.Daga ido tayi ta kalleshi tace babu komai fa kace, bayan kai kasanme muka aikata wayyo Allah kaico na, ta cigaba da kukanta shi kuma ya shirya warshi, saida ya gama ya dubeta yace zaki iya shiga kiyi wanka ki fito in mayar dake.Mikewa tayi ta nufi kofar tana dingisa kafarta har ta shige ban dakin yana kallonta ya lashi lebenshi na kasa yace yaro man kaza.Bata jima ba ta fito ta mayar da kayanta lokacin ya fita falo, nan taje ta same shi yana ganinta ya mike ya sauki wayarsa da keys dinshi yaje sorry sweetheart muje ko, ya fada yana jefa mata kallo mai cike da ma’anoni.A mota sai bata hakuri yakeyi tare da mata alkawarin hakan bazata sake faruwa a tsakaninsu ba kuma yana kan bakan shi na aurenta kuma zai jajirce wurin ganin ba’a dauki lokaci ba.Ta danji sanyi a ranta saidai hakan bazai goge tabon data yiwa kanta ba a zuciyarta, wai yau ita ce da aikata zina? Kazanta ta dauketa da duk mai akatawa sai gashi itama ta samu kanta a irin wannan.Daga nesa da gidansu ya parka motar ya dauko kudi masu yawa ya bata yace ko zaki bukaci wani abu sai ki siya ba sai kin tambaya ba a gida.Karba tayi tace nagode amma ina mai kara rokon ka akan ka rike mun alkawari kada ka juya mun baya don ka samu abunda kake so idan ka mun haka baka mun adalci ba sannan Allah zai mana hisabi dani da kai.Kada kice haka sweetheart ki bar ma tunanin ire iren abubuwan nan ni naki ne har abada domin wannan abun daya faru ma ya kara kusanta kine da zuciyata na miki alkawari.Daga haka sukayi sallama ta sauka shi kuma ya tafi, wani shago ta biya ta siyi sanitry pad ta boye kudaden daya bata a cikin aljihunta ta cigaba da tafiya tana kokarin daidaita kanta don kada a gane yanayin tafiyar tata a tambayeta abunda ya same ta.Da inna taci karo a tsakar gida tashinta kenan daga bacci don lokacin karfe shabiyu da rabi ne, kallon kallo suka shiga yi, inna tana jifanta da kallon tuhuma ita kuma Ameena tsorone fal ya shigeta gabanta ya shiga bugu.Inna ta jefo mata tambaya, daga ina kike kuma waya baki izinin fita?.Inna uzurin fitan ne ya kamani kuma fateema tana bacci bana son tashinta shiyasa nace barin fita in siyo da kaina kingan shi nan, ta nuna mata ledan pad din data siya. *EESHERT ADAMU* *MATAR* *MAJEEDADI* ✍️


