Uncategorized

Kishi Da Aljan Chapter 8 Complete Novel

Da ƙyar aka ƙwaƙule ƴar baƙa daga jikin IƳA

Zainab na kallon ƴar baƙa ta gane firgita tayi, akwai abinda ya bata tsoro

In taji tsoro haka take, se tazo ta maƙale ta, taita ɓoye kanta a jikin ta

Maganar da Abie ya tara su ayi bata yiwu ba tunda IYA ta rikice

Abie da kanshi yace ma Abbah ya je gida ya huta zasuyi waya.

Seda Abbah ya ƙara godiya sosai kafin ya tafi,

A nan ya bar muslim da Abdul, ganin Abbah ze tafi muslim yaso ya bishi

Se kuma ya tuna ai Abdul be zo da mota ba, a motar shi suka zo, haka nan ba dan ran shi yaso ba ya zauna

Mama da kanta ta kama Iya ta shigar da ita cikin gida, Zainab kuma ta tsaya ta tattaro zanin ta da kuma takalman ta da suka watse a wajen.

Tunda Abdul ya koma ya zauna ya maida hankalin shi kacokam a kanta,

Allah-Allah yake ta ɗago kanta ko Allah ze sa suyi ido huɗu, amma ina, tana gama kwashe kayan ta tsugunna ta ɗauki ƴar baƙa ta wuce cikin gida abinta.

Duk maganar da Abie ke mishi be ji ba, yana can yana kallon Zainabu

Seda ya bari Zainab ɗin ta shige tukun Abie yace

“Ko akwai abunda kake so a kawo maka ne?”

Da sauri Abdul ya sadda kansa ƙasa, yai murmushi, bece dai komi ba, se kaɗa kai da yayi alamar “a’a”

Murmushi Abbie yayi me ɗan sauti, sannan ya maida kanshi ga yaran shi da har yanzu  basu tafi ba, yace

“Zaku iya tafiya ai, Allah yai muku albarka, ya kuma shiga lamarin ku”

Da “Amin” suka amsa, sannan ɗaya bayan ɗaya suka ba Abdul da Muslim hannu suka gaisa, 

Ko wanne su suna mishi fatan alkairi da kuma wanzuwar zaman lafia a tsakanin shi da auta.

Fuska ɗauke da murmushi Abdul ke amsa musu, 

Har ga Allah baze taɓa iya fasalta yanayin da yake jin shi ba, wani lokacin se yaji sanyi-sanyi a ranshi, wani lokacin kuma kadaran kadahan, wani lokacin kuma hakanan se ɓacin rai ya cika shi.

Palon ya rage daga Abie se Abdul da muslim

Sosai Abie ya zaunar da su yayi musu nasiha akan aure da haƙƙoƙin sa

Ya jima sosai yana basu misalai akan rayuwar manzon Allah, da kuma yarda yake zamantakewa da matan shi

Sosai nasihar Abie ke shigar su, 

A hankali cikin dabara  Abie ya fara gangarowa kan matsalar Abdul.

“In har ka dage da yin waɗannan addu’o’in  da na baka, to ina me tabbatar maka da dukkan wani abokin halitta kafi ƙarfin sharrin shi, kuma ka gwada ka gani

Allah yayi muku albarka, ya ƙara tsareku daga dukkan abin ƙi”

Abie yana kaiwa nan ya miƙe tsaye yace

“Bari in turo maka ita”.

A CIKIN GIDA

Tunda suka shigar da Iya cikin gida ta nutsu tai shiru, ko tari ta kasa yi, 

Duk janta da Zainab ke yi dan ta magantu, amma Iya tai mursisi taƙi cewa komi

Suna a haka Abie ya yi sallama ya shigo palon, 

kallon Iya yayi yaga ta kauda kai can gefe, a nutse ya ƙarasa kusa da ita ya ɗan russina yace

“Sannu da gida Iya”  ko uffan bata ce mishi ba, ya ƙara cewa “kizo a maida ki gida, naga dare ya fara yi”

A ƙufule Iya tace

“Ba inda zani, naga alamar kaima ka fara rikiɗewa”

Murmushi Abie yayi ya juya inda zainab ke kwance tana buga game yace

“Auta, kije kuyi sallama da mijin naki zasu tafi wai”

Banbaraƙwai taji maganar Abie, wai “miji na”

Kunya ce soaai ta rufeta a inda take, seda Abie ya sake maimaitawa tukun ta tashi sumi-sumi tai hanyar fita, sannan ta  tsaya tace a shagwaɓe

“Nifa Abie ban iya maganar kurame ba fa”

Dariya Abie yayi yana kallon ta yace

“kije, abokin shi na nan, se ya rinƙa fassara miki abinda yace”

Kallaon Iya tayi tace

“Iya naga ke kin ƙware wajen magana da kurame, dan Allah kizo muje”

Wani zabura da Iya tayi, se kayi tunanin cinnaka ne ko wani abun ne ya cije ta, 

Zainab na ganin hakan ta kwasa da gudu tai waje tana dariyar yarda IYA tai ta ihun a tuna mata addu’ar da aka koya mata

Tunda Zaiinab ta tashi Iya taci gaba da baza idanu, magana take son yi, amma ta kasa.

Ƴar ɓaƙa na farkawa bata ga Zainab ba ta sakko daga kan kujerar da take kai ta yi hanyar ƙofa,

Da  sauri Iya ta janye ƙafafun ta gefe, tace

“Ga wata jarabar can kuma, Allah ya tsayar a kanku dai”

Sosai dariya ke cin Abie da mama, basar wa kawai suke, 

Amma firgice Iya kam ta shige shi, sedai Allah ya kyauta gaba.

Hijabi kawai Zainab ta ɗauka, tai fice

Tafi minti uku tsaye a bakin ƙofar ta kasa shiga

Can dai ta daure tai sallama,

Muslim da gaba ɗaya ya matsu wani ya shigo palon,

 dan ba’a son ranshi yake zaune daga shi se Abdul ɗin ba, ya amsa sallamar da saurin shi

Kanta aƙasa ta ƙaraso palon, 

Tunda ta shigo Abdul ke kallon ta, 

Sosai take jin kallon shi a jikin ta, ƙafafun ta har wani harɗewa suke

Ɗan nesa dasu kaɗan ta zauna

Tana zama,  ana kiran wayar muslim 

Tashi yayi yace

“ina zuwa amarya”

Muslim na fita daga palon ya danƙara da gudu ya fice a gidan gaba ɗaya, yana fita ya shige motar sa yai hanyar gidan su.

Kusan minti goma Abdul be ce mata komi ba, se ƙare mata kallo da yake tun shigowar ta

Tunawa  da tai kurma ne yasa ta ɗago kanta, a cewar ta kar yayi magana bata gani ba

Tana ɗagowa suka haɗa idanu,

Zaro mishi manyan idanunta ta yi waje,  a hankali tace

“Na haɗu da alaƙaƙai ni kam, to ta ina zan fara ma kurman nan magana”

Zaro shima na shi manyan idanun yayi jin ta kira shi da kurma

Abin se yaso bashi dariya ma, wai shine kurma

Basarwa yayi yaci gaba da kallon ta

Da dai ta gaji da kallon da yake mata tace tana magana tana mishi nuni da hannu

“Tunda baka iya magana ba, ka tashi ka tafi gidan ku”

Maƙe kafaɗa yayi, alamar a’a

murmushi tayi da seda kumatun ta gefe ɗaya ya loɓa, tace

“hoooo, ashe dai na iya maganar kurame”

Dariya sosai ke cin Abdul, dakewa yayi kawai dan yaga iya gudun ruwan ta.

Ƙara zare mishi ido tai tana nuna mishi hanyar fita da hannun

Zungwi zungwi, kamar warce aka ajiye a ƙofar palon ta ƙarasa shigowa

Kai tsaye jikin zainab ta nufa ta lafe akan cinyar ta, kafe Abdul tayi da idanun ta.

Abdul na kallon ƴar baƙa, yaga fuskar ta na rikoɗewa izuwa ta wannan mujiyar, 

Zainab kuma ta haƙura ta maida hankalin ta ga ƴar baƙa tana ta shafa mata kanta har zuwa wajen hancin ta

Yunƙuri Abdul yayi ze ɗauke ƴar baƙa daga jikin ta,

kafin ma ya ƙaraso ta danna hannun Zainab ɗin a baki, ta ganna mata wani mahaukacin cizo

Raɗaɗin azabar da ya ratsa Zainab yasa ta miƙe a gigice tana ambaton

“Innalillahi wa’inna ilaihirraji’un”  Da iya ƙarfin ta

A ruɗe Abdul ya tashi yayi kanta,

Yana miƙewa ya fara jin wannan sarewar dake saka shi manta kowa da komi

A take ya zube a wajen, 

A dai-dai nan kuma Abie da ya jiyo salatin zainab daga ɗakin shi ya shigo palon a sukwane..

Gam Abie ya riƙe ta yana duba hannun da har ya fara zubar da jini

Ta kasa jure azabar da hannun ke mata, a iya rayuwar ta bata taɓa jin raɗaɗi  makamancin wannan ba

Jinin ta da ya ɗiɗiga  a ƙasa ƴar baƙa ta fara lashewa da sauri da sauri

Yatsar Zainab na a hannun Abie, ya fara karanto mata fatiha, yana karantawa iskar bakin shi na taɓa wajen da ciwon yake

A hankali Zainab ta fara jin sanyi na ratsa yatsan nata

Mugun raɗaɗin da take ji a kaso ɗari, befi biyar bane yayi saura 

Sakin hannun ta Abie yayi, yace 

“kije ki wanke jinin, sannan ki kawo min ruwa a kwanon sha se wannan turaren da na baki ajiya ɗazu”

Da “to” Zainab ta amsa, tana tafe tana waiwayen Abdul dake kwance kamar me bacci

Seda ta tsaya bakin famfo ta wanke jinin da ya ɓata hannun nata taa

Ƙare ma yatsan kallo tayi, taga ashe cizon ɗan ƙanƙani ne, 

Be ci ace yayi mata zafi haka ba, ƙara matsawa tayi, amma ba jinin ba alamun shi

Kai tsaye cikin gidan ta nufa, 

Ɗakin ta tafara shiga ta ɗauki turaren sannan ta ɗibo ruwan ta dawo palon

A yarda ta fita ta bar Abdul, a haka ta dawo ta same shi,

Abie na zaune daga gefe.

Zuwa tai ta ajiye ruwan da turaren a gaban Abie, sannan itama ta samu waje ta zauna

Gaba ɗaya tausayin Abdul ya mamaye mata zuciya a cikin ƙanƙanin lokaci.

Kallon ta Abie yayi, yaga yarda ta kafe Abdul da ido, cikin taushin murya Abie yace mata

“Ki tashi ki tafi, ki ce maman ki tazo, ta tawo da buta”

Kanta a ƙasa tace

“Nima in dawo tare da ita Abie?”

Shafa kanta Abie yayi yace

“Kar ki dawo, kiyi alwala ki kwanta kinji ko Auta?”

Ba dan ran zainab ya so ba ta gyaɗa mishi kanta, sannan 

Ta tashi ta nufi ƙofa tana waiwayen  inda Abdul ke kwance.

Mama na shigowa palon Abie yace

“Rufe ƙofar”

Tura ƙofar tayi ta ƙaraso ta zauna a ƙasa 

Abie na ta saitin kan Abdul, mama kuma na ta saitin ƙafafun shi.

Kallon ta Abie yayi yace

“sun fara bugar da shi fa nike jin, bari muga ta inda zamu fara”

A nan inda Abdul ke kwance Abie ya ɗaura mishi alwala, mama na zuba mishi har ya gama

Sannan suka ɗaga shi da ƙyar suka jingina shi da jikin kujera, Babu wani abinda na jikin shi da yake a lanƙwashe, komi da komi sun miƙar da shi

Bismillah Abie yayi ya fara karanto ayoyin da mussamman zakuji masu ruƙiya na yawan karanta su

Suna nan a haka kusan rabin awa, suka fara jin iska,

Iska ce me ƙarfin gaske, ji suke kamar rufin ɗakin se kwaye tsabar tsananin iskar nan

Abie beyi shiru ba, yaci gaba da karatun shi

Mama kuma na a gefe, tana ma ruwan da zainab ta kawo ɗazu addu’a

Da ƙarfin gaske sarauniya Aziza ta sakko palon nan, tana gunji tana ƙoƙarin ƙwacewa 

Amma ina, Abie ya kamo ta ya riƙota da ƙarfin ayar Allah

Gunjin da take yi irin wanda dole in ka jishi tsiga jikin ka ta tashi, 

Tafi minti goma tana gurnani, kafin daga baya suka fara jin haki kamar wanda yayi gudun kilomitoci a ƙafa

Cikin muryar haki, Aziza tace

“TSAYA! TSAYA!!, WANNAN WANI IRIN KIRA NE?, KO CUTAR DA ABDULAZIZ NAYI AI SE HAKA MALAM”

Ta ƙarashe maganar hakin da take na daɗa yawa

Fuska ɗaure Abie yace

“Ƙaryar rashin kunya kike yi ai, kwana nawa a jere ina miki gargaɗi amma kikai kunnen uwar shegu dani?”

Shiru tayi, amma gurnanin muryar ta na nan, alamun tana kusa bata tafi ba kenan.

Tsawa me ƙarfi Abie ya daka mata yace

“Au ba zaki magana ba?”

Be jira cewar ta ba yaci gaba da karatun shi yai banza da ita

Ihu take sosai, tana faɗin ya dakata, zata gaya mishi komi, amma Abie yayi banza da ita

Bata da hanyar guduwa daga palon nan, dolenta ta tsaya tunda har ta bari Abie yayi mata wannan kiran da bata isa ta ƙi zuwan shi ba.

Seda Abie yayi karatu sosai ya haɗa zufa ta ko’ina tukun ya tsaya yace

“Ehum, ina jin ki, ki gaya min miye manufar ki na hana bawan Allah sukuni? sannan miye haɗin aljani da kuma mutum?”

Cikin kuka sarauniya Aziza ta basu labarin kaf, ta yarda akayi haɗuwa ta kawo su yanzu.

Shiru Abie yayi, ya ƙura ma saitin inda suke jin muryar ta ido, mama kuwa kuka riris take na tsabar tsananin tausayin Abdul na halin ƙaƙanikayi da ya shiga

Bayan sarauniya Aziza ta kai ƙarshen labarin ta, ta ƙara cewa

“Bawani wanda ya cancanci zama da shi in ba ni ba, ina son shi, bazan taɓa cutar da shi ba malam”

Abie be nuna karayar shi da wuri ba, yace

“Ban taɓa ganin inda jinsin ku ya auri jinsin mu ba, sannan duk abinda kikayi mishi ki barshi a matsayin temako, se kiga ranar gobe ƙiyama kin samu rabauta a wajen ubangijin mu.

Banyi niyar lallashin ki ba, amma jin wannan magana taki, 

duk da dai ku aljanu maƙarya ta ne na gaske, kun iya shirya labarin ƙanzon kurege, ki bar jikin shi cikin lalama daga yau karki ƙara dawowa na gaya miki.”

Murya cikin kuka Aziza tace

“wallahi ban shiga jikin AZIZ ba, ina nan a tare da shi ne ko yaushe, nasan in na huda shi na shige shi nayi mishi illa dole ta wani fannin, amma abinda nake so ne shiyasa na haƙura nake bibiyar shi”

Ganin zaƙewar ta na neman wuce gona da iri yasa Abie yace

“Ba kiji lallashi ba ko?”

Shiru ba amsa, ba kuma alamun tana wajen

Sosai Abie ya sauke ajiyar zuciya yana kallon Abdul da ya buɗe idon shi tarwai yana kallon sirikan nashi

Da sauri mama ta share hawayen dake fuskar ta tana maye su da murmushin yaƙe

A kasalance Adul ya gyara zaman shi ya tanƙwashe kafafun shi, murya a ƙasa yace

“Ba dai taji mata ciwo ba ko Abie”?

Abie yace

“Wa ke nan?”

Da zuciya ɗaya yake maganar shi yace

“Na ganta a cinyar ta Abie, ka raba ta da ita kar ta cutar da ita dan Allah”

Se asan nan Abie ya gane maganar zainab Abdul yake mishi

Murmushi Abie yayi ya shafa kan Abdul yace

“Ba abunda zata iya mata da izinin ubangiji, nasan zainab ba baya ba wajen azkhar da karatun ƙur’ani,

In da kaima zaka daure ka riƙe azkhar se kaga wani labarin ake ba wannan ba”

Shiru Abdul yayi yana sadda kanshi ƙasa, a ƙasan zuciyar shi yana ji ina ma ace mantuwa bata aure shi ba, inama ace ze iya da yafi kowa murna.

Abie be ƙara cewa komi ba, sema kwanon da mama ta gama tofi a ciki da ya miƙa mishi

Ba musu Abdul ya karɓa yayi bisimillah ya kafa kai sha fiye da rabin ruwan.

Nan da nan zufa ta fara karyo mishi tun daga cikin shi har ta fito waje.

Sake kallon shi Abie yayi yace

“Tashi muje in sauke ka a gida, dare yayi sosai”

Ba musu Abdul ya miƙe, dan yasan fitar da muslim yayi ɗazu ba dawowa zeyi ba.

Rissinawa yayi yai wa mama sallama sannan yayi gaba

Abie yace “ki koma cikin gida sarauniyar kuka, duk ke kika ɓata min yarinya da saurin kuka”

Murmuahi mama tayi, tana miƙewa, a ranta tace  “Mijina baya tsufa”

(JAMA’A SOYAYYA HALAL CE, KOMIN TSUFAN KU, KUYI TA, KAR KU CUCI KANKU)😎😎

Tana shiga ta iske IYA nata zuba gyangyaɗi a zaune

Zainab kuma na kwance kan kujera bacci ya ɗauke ta

Sallamar da maman ta ƙara ce ya farkar da IYA a ɗan tsorace, 

Seda ta saita idanun ta tukun ta ga mama ce sannan tai ajiyar zuciya ta gyara zaman ta

Tashin Zainab tayi, tana tashi tace 

“Mama, ya farfaɗo kuwa?”

Cikin kulawa tace

“eh, har Abie ya tafi kaishi gida”

Kafib Zainab tai magana IYA tace

“Munafuka kishiyar aljana”

Mama bata ce komi ba, sema waje data samu ta zauna tana ƙara tunano maganar da AZIZA tayi

A hanjali, yarda mama bazata ji ba zainab tace ma Iya

“Kuma a kan gado ɗaya zaku kwana da kishiyar tawa ba, se inga wanda ze tuna miki addu’o’in da zaki yi dan ki koreta, ai ni na godr ma Allah ma da baki riƙe su ba”

Zabura Iya tayi tai baya, tana salati da tafa hannaye

Can ta fashebda kuka tace

“Binta, dama tun ɗazu nake faɗa miki ba zainabun da na sani bace wannan, wallahi ta rikiɗe ta zama dangin kishiyoyin ta, ni Salamatu jikar Dije”

Mama da tai nisa a tunani, kukan Iya ta fargar da ita, da azama maman tayi kanta tana tambayar “menene kuma?”

Da hannu biyu Iya ke nuna zainab da tai mirsisi kamar ba itace tai maganar ba

Da zainab ɗin aka haɗu ana tambayar Iya da lafia

Dariya ke son ƙwace mata, amma ta daure, ta kalli mama da fuakar tausayi tace

“Anya mama ba se an haɗa ma Iya da addu’a ba?

Naga ta firgita da yawa wallahi”

Kallon Zainab mama tayi taga har ga Allah da gaake take magana, bata ga alamar tayi mata wani abun ba, tace

“Gaskiya, bari malam ya dawo kam”

Ƙara fashewa da kuka iya tayi tace

“Haba koda naji, wallahi zainabu ta bata da munafurci, Binta daure ki duba min ƙafar ta ki gani ko akwai kofato daga nan se in ƙara tabbatarwa”

Mama batace komi ba, sema tofi data fara tofa ma Iya, ita duk a tunanin ta firgicin ɗazu ne be sake ta ba.

Mama ta juya baya tana ma iya tofi, zainab kuma na daga bayan maman tana zare ma Iya idanu, tana zaro harshe waje kamar wata mayya.

Rikicewa sosai IYA ta sake yi, har seda mama takai ga kiran Abie a waya.

**********

Haka Allah ke al’amarin shi Asiya, kuma maganar sauya gida da kike magana, to ki sani wallahi tallahi ba wani gidan da zan sauya.

Banda ma bana son tashin tashana,  duk wahalar da Abdul ke a ciki waye sabab ɗin ta?

Nace waye sabab ɗin ta?

Ummie bata ce komi ba se kumbure-kumbure da ta ke tayi.

A fusace Abbah ya tashi ya bata waje, yana ƙara gargaɗin ta da kar ta kuskura ta biyo shi ta ƙara mishi ciwon kai akan wanda ya shigo da shi gidan..

Raya daren ranar Abbah yayi da nafiloli na nuna godiyar shi ga ubangiji.

Duk da ɓacin ran da ya shiga ciki da shi, be  hana shi nitsuwa wajen roƙa ma Abdul lafia da kuma zama lafia da matar shi ba.

Ta ɓangaren Abdul kuwa zamu iya cewa rabon da ya ta shi yayi sallar tsakar dare, tun Ammah na raye bata mutu ba

A daren ranar, tun da ya sallame sallar yaji wata nutsuwa na ratsa shi ta ko’ina a jikin shi

Salin alin ba wani tunani ko takura bacci yayi awon gaba da shi, 

Cikin hukuncin ubangiji kuma ana kiran asubah ya tashi.

BAYAN SATI ƊAYA DA  ƊAURA AUREN ABDUL DA ZAINAB.

Da yamma, Abbah na zaune a palon shi bayan ya dawo daga aiki, ya ɗaga waya ya kira Abdul da shima yana wajen aiki be kai ga dawowa ba, bugu biyu ya ɗaga, bakin shi ɗauke da sallama.

Abbah yace

“what time zaka dawo?”

A ladabce kamar yarda ya saba amsa ma Abbahn nashi yace

“zuwa five zan tashi Abbah”

Abbah yace “ka same ni bayan sallar magriba, akwai inda zaka rakani”

Da “to” ya amsa mishi, sannan suka aje wayar.

Abdul na tashi daga office kai tsaye gida ya wuce

Seda ya gama abubuwan da ya saba yi sannan ya wuce masallaci sallar magrib

Ana idarwa ya samu Abbah dake jiran shi suka wuce,

motar tayi shiru, baka jin komi se sautin radio dake aiki

Ɗan waigowa Abbah yayi ya kalli Abdul da yai shiru yana kallon waje, yace

“Ya matar ka, tana lafia?”

Dumm, haka gaban Abdul ya bada sound, a ranshi yace

“Ya akai Abbah yasan ita nake tunani?”

Seda Abbah ya ƙara maimaita tambayar shi, tukun Abdul ya ɗan sosa ƙeyar shi yana inda inda, can dai yace

“Nima ban sani ba Abbah”

Kallon shi sosai Abbah yayi yace

“kamar ya baka sani ba?”

Kanshi a ƙasa yace

“Kusan sati kenan indai naje bana gane gidan Abbah”

Shiru Abbah yayi, ya na nazartar maganar shi, a ranshi ya maimaita “baya gane gidan”

Kaɗa kai kawai Abbah yayi yace

“Ka ci gaba da sakaci da addu’a ko, ka daure ka jajirce Abdul, in bakai ma kanka ba, ba wanda ze tsaya yai maka, kasani sarai”.

Insha Allah zan ƙara dagewa”

Shiru ne ya ƙara biyo baya, se amsa calls da Abdul keyi sama-sama, in wani call ɗin ya shigo yaƙi ɗagawa, a haka har suka ƙarasa unguwar G R A dake ta bayan anguwar su kaɗan.

Can ciki sosai Abbah ya nausa motar shi,

 ƙofar wani ɗan madedecin gida me kyau da ƙayatar wa yayi parcking

Waigowa yayi ya kalli Abdul dake ƙare ma gidan kallo, yace

“Ka tuna gidan ne?”

Murmushi Abdul yayi yace

“Se inga kamar mun taɓa zuwa gidan nan da Ammah lokacin nan”

Murmushi me sauti Abbah yayi, fita yayi daga motar bayan ya ɗauki keys daga pigionhole

Da kan shi ya buɗe ƙaramar ƙofar ya shiga, sannan ya buɗo gate ɗin ta ciki

Abdul na ganin hakan shima ya fita, komawa yayi mazaunin driver sannan ya saka hancin motar ciki,

Bayan ya shige, Abbah ya sakaya ƙofar.

“fito mana” Abbah yace, yana ƙoƙarin lalubar makullin da ze buɗe ƙofar palon.

Fitowa Abdul yayi yana ƙara kallon gidan da ya shiga ranshi farat ɗaya, kuma yana ɗan tuna wani lokaci can baya

Inda wutar gidan gaba ɗaya take Abbah ya laluba ya kunna,

farin haske ƙar ya haske ko ina na cikin gidan

Bakomai a gidan, kwanɓar haka yake, sema ƙura da yanar gizo-gizo da suka rufe ko ina na gidan

Gida ne hawa ɗaya, ɗaki biyu da ɗan madedecin palo a sama, 

se ɗaki ɗaya a ƙasa da babban palo, dinning se kitchen babba da store,

 se harabar gidan zata iya ɗaukan motoci uku.

Hannu Abbah ya saka a aljihun shi ya zaro takardu,

Seda ya ƙara duba su, sannan ya miƙa ma Abdul da duk ƙyanƙyamin gidan ya kama shi saboda ƙurar da yayi.

Hannu biyu Abdul yasa ya karɓa, idon shi akan Abbah yana neman ƙarin bayani.

Kama hannun shi Abbah yayi suka fito waje, bayan ya kashe wutar gidan, sannan ya kulle ƙofar palon

Seda suka fita a gidan gaba ɗaya, sannan Abbah ya kalli Abdul, muryar shi na rawa, yace

“Saƙon Murjanatu ne da ta bani na aje maka, 

wai in kayi aure ka zauna a ciki”

Shiru Abdul yayi ya rungume takardun a ƙirjin shi, yana jin idanun shi na ciccikowa da ƙwalla

Murya ƙasa-ƙasa yace

“AMMAH!”

Suna tafe Abbah na mishi bayanin yarda yasa a shekarun baya akayi renovating gidan, aka maida shi yarda yake a yanzu

Abdul na jin shi, be dai ce komi ba, sema tunanin rayuwar can baya da ya tafi, duk da dai ba wani girma yayi ba a lokacin, Amma yana iya tuna abubuwa da dama

A haka har suka dawo gida,

Da Abbahn yaga kamar hankalin Abdul gaba ɗaya baya a kanshi yace

“Gobe in Allah ya kaimu ma ƙarasa maganar da naso muyi  ɗin”

“To” yace mishi, daga nan ya wuce ɗakin shi rungume da takardun gidan.

Yana shiga ɗakin ya zauna gefen gadon shi ya ƙura ma takardun idanu yana tuna every single moments da sukai tare da Ammah

Kafin kace me, ya fashe da kuka me taɓa zuciya, yana kiran sunan “Ammah”

“Nayi kewar ki Ammah, 

ashe da gaske kike lokacin da nace miki gidan nan ya burge ni, kikace se nayi aure zaki bani!

Ammah ashe kin aje wannan alƙawarin? Ammah kin ce se na zaɓi mata na darje kafin ki bari a aura min, 

har nake gaya miki kalar matar da nake so,

Wayyo Ammah na, naso ace kina a raye ki ga matar da ban sha wahala ba na same ta, 

Albishirin ki Ammah?, kalar wannan matar da na gaya miki ita ɗince na samu albarkacin addu’ar da kikai min a wannan lokacin

Ammah itama me kyauce kuma ƴar fara,   muryar ta me daɗin gaske, 

Ina ta so in baki labarin ta Ammah, amman ban san ta inda zan fara ba, 

sam yanzu na dena gane ƙabarin ki Ammah na,

Shedar da na saka dan na rinƙa ganewa, wataran Abbah da kan shi yaje ya cire, lokacin da naje na gama shan wahala ta ban gane ba, 

daga baya na haƙura!

Ammah akwai labarai a baki na da yawa, wanda ke kaɗai zan iya gaya ma, 

Ammah ina buƙatar kafaɗar da zan kwanta nayi kuka ko na samu nauyin dake cikin zuciya ta ya ragu”

Ɓurum Abbah ya turo ƙofar ɗakin ya shigo, shima fuskar shi shaɓe shaɓe da hawaye

Rungume Abdul yayi ƙam a jikin shi yana shafa bayan shi, alamun lallashi, dan gaba ɗaya ya kasa magana ma

Tunda yaga yanayin yarda Abdul ya fita daga motar yasha jinin jikin shi, 

shiyasa ya biyo bayan shi, 

Kafin ya kai ga shiga ɗakin, 

kunnuwan shi suka fara jiyo mishi kalamun Abdul masu taɓa zuciyar me saurare

Cikin raunin murya Abbah yace

“Haba Abdul, 

gani a memakon murjanatu, 

ga kafaɗa ta ka kwanta kayi kukan ka har se kaji zuciyar ka ta maka yarda kake so, 

bana ƙaunar in ga kana kukan rashin mutuniyar kirki murjanatu,  addu’ar mu tafi buƙata a yanzu

ni kaina kana daɗa tayar min da mikin dake kwance can cikin zuciya ta”

Uffan Abdul be ce ba, se ajiyar zuciya da yai ta yi akai-akai.

Sosai Abbah ya daɗe a wajen Abdul yana lallashin shi da bashi baki, 

hada tsokanar shi ya fara cikin ƴar fara’a yace

“Kace kalar matar da kake so ce ka samu? amma ka kasa gane ƙofar gidan su ballanta na ka ɗakko mana ita”

Murmushi kawai Abdul yayi, yana ɗan sunkuyar da kan shi ƙasa.

Seda Abbah ya tabbatar da ya samar ma ɗan nashi nutsuwa na wannan lokacin, sannan yayi mishi sallama yana ayyana yarda za’ai ayi a bashi matar shi nan kusa.

ALLAH KASA ANNABI YA CECE MU.

Back to top button