Fentin Zina Page 4 Hausa Novel
Tashi tayi ta nufi madafin ta don samawa cikinta abunda zata ci, cikin kankanin lokaci ta dafa taliya rabi ta dafa kwai guda biyu ta soya manja tana da ruwan zafi a flask ta hada komai ta kai falo a kasan karpet ta zauna ta fasa kwan ta ajiye gefe ta zuba manja a taliyar data debo zata ci ta jawo robar yajinta ta hada tea mai kauri ta soma ci, tana yi tana danna waya har ta gama ta mike ta Kai kayak in kitchen ta dauraye su bata bukatar tayi abincin rana taliyar zata isheta don haka daki ta koma ta kwanta duk da bata jin bacci.******Abdul Yana zaune a office dinshi ya zura wa waje daya ido yana kallon irin rigingimun daya sha tadawa tsakanin shi da Ameena a kan kankanin abu yanajin cewar bai kyauta mata ba domin tunda ya aureta kullum kokarinta ta faranta masa bata kaunar ganin bacin ransa ko kadan amma shi dai har yau ya kasa kwantar da hankali ya manta da komai, a kullum wannan FENTIN ZIN🅰️R, ita ke masa jagoranci wurin saurin fusata da rashin yi mata uzuri ga kullum zuciyarshi cike da waswasin zata iya cin amanar shi, yasha daukar wayarta yayi bincike ba tareda ta sani ba kawai domin ya samu makamar da zata gwada mishi zaman karya takeyi dashi kuma ladabin mage take masa sai dai har rana mai kamar ta yau bai samu hujja komin kashinsa ba.Yana cikin wannan halin sectriyarsa ta turu kofar ganin shi cikin halin tunani ya sanya ta tura kofar ta rufe ta tako zuwa gaban shi ta dafa kafadar shi ta shafo gemunshi tana wani matsiyacin murmushi tace.Sam ba haka nike son ka kasance ba, anyway ta watsa hannu tana komawa kujerar gaban teburin shi ta zauna.Ya sauke numfashi yana kallonta, meke tafe dake yanzu kuma um?Babu kawai so nike ingan ka so nike inji dumin jikin ka domin nayi kewar ka.Haba maryam duk ma yaushe kika bar nan din ne inace bayan sallahr azahar dinnane bakiso inyi aikina cikin salama kwata kwata. Ya fada yana dan daure fuska.Meyasa kwanakin nan duk ka soma canja mun ne? Meyasa yanzu baka so kaga ina rabarka? Kasan radadi da kunar da nike ji akan share ni da ka fara yi a kwanan nan? Dan Allah kada ka mun haka! Kada ka rabani daga gare ka.Ki sani bawai ina share ki bane da wani dalili akwai abunda ke damuna ne shiyasa bana jin dadin mood dina ne so kidan bani space please.Shikenan bazan takuraka ba amma ka sani bawai na rabu dakai bane kanaji.Ya gyada kai domin so yake kawai ta fita ta bashi guri ya cigaba da tunaninsa.Tashi tayi ta fita cikin mintuna kadan aka kuma turo kofar wannan karon abokinsa ne Anas ya shigo.Tun daga kofa yake bin abokin nasa da kallo har ya zauna a inda maryam din ta tashi.Naga kamar baka jin dadi?Bawai bana jin dadi bane wani al’amarine yake son dagula lissafina kuma bansan yadda zan iya shawo kan al’amarin ba.Allah shine Masanin dukkan komai shine wanda zaka kai kukan ka gareshi zai magance maka damuwarka.Anas bazaka gane ba! Wani abun fah yana da bukatar shawara ne nidai kaina ya kulle.Ina jinka! Anas ya fada.Ya gyara zama ya fara bayani, Anas har yanzu na kasa barin komai ya wuce a zuciyata har yanzu na kasa daina kallon Ameena da FENTIN ZIN🅰️ bazawara mai ɗa a waje kafin aure Ameena ta cuceni ta cuci kanta sam hankalina baya kwanciya kullum gani nike kamar zata iya cin amanata da wani.Innalillahi wa inna ilaihi raji’un, me kake fada haka ne Abdul? Anya kana cikin hankalinka kuwa? Meyasa zuciyarka take da dan banzan riko ne? Koba kai ka ganta kace kana sonta ba? Kuma a lokacin wani irin shawara ne ban baka ba amma kayi fatali da ita, sai yanzu kazo kana magana marar dadin ji kada ka cemun musgunawa yarinyar nan kake yi?Ya dafa kai kafin yace, ba haka bane Anas, kasan ina son Ameena nidai zuciyata ce kawai bata jurewa a duk sadda na tuna cewar wani ya rigani keta Ameena kuma ba tare da aure ba sai inji kamar iyi ta ihu ko hakan zai sama mun natsuwa a rayuwata.Anas ya girgiza kai cikin tausayin Ameena yace, yana daga cikin hadarin zinå shiyasa Allah ma yace “walaa taqrabuzzinah, innahu kana fahishatan wa sa’a sabila” duk mace ko na mijin da zai aikata zina hakika baya tareda ko digon imani a lokaci aikatawa, zina alfasha ce mai warware aiki, sannan FENTINSA yana bin mutum har tsufansa kamar yadda dai ya hanaka zaman lafiya da matarka, saidai inaso in fada maka kaji tsoron Allah ita wannan Ameenar amana ce a gareka babu ruwan Allah da uzurinka idan baka rike amanarta ba ka sauke hakkokin da Allah ya daura maka nata ka sani Allah bazai barka ba, tun farko kasan wacece ita kuma kasan tana tare da FENTIN ZIN🅰️ amma kaji ka gani kana so ka aureta bayan kasan ga yadda zuciyarka take? Ameena bata cuce kaba kaine ma ka zalunce ta tunda kasan bazaka iya rungumar kaddara ka zauna da ita cikin rufin asiri da kuma zaman lafiya ba amma ka rabota da gidan su ka ajiye a gidan ka.Dan Allah Kada ka daura mun laifi malam, Abdul ya katse shi cikin fushi, ko ni nace taje tayi zinár har ta samu ciki ta haihu? Allah ma kadai yasan iya mutanen data sallamawa wa kanta, ba zaka tayani jimami ba saidai ma kayi kokarin juyo da laifin kaina? Kodai kaima kana daga cikin tsoppin samarinta ne da kake kokarin saika kareta iye? Mikewa Anas yayi fuskar shi kam murmushin yake yakeyi yace, banga laifinka ba domin ni nazo na same ka a inda kake dole ka wulakanta ni son ranka amma babu komai nidai Allah ya gani babu maganar yaudara ko boye boye tsakanina dakai saidai inaso ka sani, da irin wannan zuciyar taka wata rana saika rasa wannan auren kuma muddin kayi sakacin da zaka rasa Ameena baza ka taba samun makwafin taba ya rage naka kayi amfani da hankalinka ko ka bar shaidan yayi galaba a kanka daga haka yayi waje ya bogo masa kofar cikin tsananin fushi.Zugum yayi yana kallon kofar da Anas ya banko yana son tantance ma’anar abunda yake faruwa dashi amma ya kasa don haka bai iya karasa aikin sa ba ya mike ya tattara abubuwanshi ya saka a jaka ya fita ya rufe office din maryam tana zaune a kujerarta ganin ra fito dauke da jaka kuma ya rufe office din ya tabbatar mata gida zai tafi don haka ta tashi ta isa gare shi tana karairaya da rangwada tasa hannu ta dafa kafadar shi tace, baby sweet wai yau har zaka tafi da wuri?Gyada mata kai kawai yayi amma kasan zuciyarshi ji yake duk ya kosa da tsayuwa a wajen yafi so ya ganshi a dakin shi kwance ya samu damar yin tunani yadda ya kamata.Ka mun magana mana baby nice fa taka maryam kaji, ta fada tana langwabar da kai tana tabe faffadan bakinta wainan zatayi shagwaba saboda ta burge shi.Dan Allah maryam ki barni in tafi gida akwai abunda ya taso mun ne nike so inje in warware idan na samu natsuwa zanyi charting dinki ta WhatsApp please.Alright tunda kace haka amma ka sani indai bakayi chartting dina ba ni zan kiraka kuma bazan karbi uzuri ba.Ya gyada kai, zanma yi ke dai ki jira.Matsawa gefe tayi ta bashi hanya ya wuce tana bin bayan shi da kallo tace a hankali, dole sai ka aure ni mu zuba ni da kai da waccan matar taka.Tana can cikin dakinta daya dawo taji dirin motar shi amma bata fito ba domin tana wanka ne.Tunda yaga bata fito tarbarsa kamar yadda ta sababa ya ayyana ta tafin kenan a ranshi, take wani daci ya ziyarci zuciyar shi, ya fito ya shiga ciki, ya zarce dakin shi domin rage zafin dake tare dashi, wanka ya shiga bai jima ba ya fito yabi lafiyar gado ya kwanta.Data fito daure da alwala don bata bukatar zama babu alwala a jikinta domin ita kanta alwalar zama da ita kariyace daga shaidanu.Gaban mirror taja kujera ta zauna tana shafa mai kana ta shafa turarukanta kala uku ta hada nan kamshi ya soma bazuwa zuwa cikin gidan.Tasa atamfarta ruwan kasa ya zauna a jikinta tayi daurin ture kaga tsiya dinnan da ake sa marko a ciki ya zauna yadda ake so, tasa sarkanta golden colour mai kyau da dan kunne da awarwaron sa tayi kyau sosai masha Allah.Falo ta fita ta zauna already akwai ma’ajin sallaya da hijabinta na sallah a falon koda bata son yin sallah a daki sai tayi a falon haka take yi.Zama tayi bayan ta kunna t.v ta dauki remote ta daura kafa daya kan daya.Yana kwance yaji kamshi na kawo masa ziyara a duka kofofin hancin sa, mikewa yayi zaune yana dada shakowa ta ko ina, a hankali cikin sanyin jiki ya saura ya zura slippers dinshi yayo waje.Daga ta inda yake tsaye ya folding hannu yana kallonta, bata masan yanayi ba har saida ya matso kusa ya zauna a gefenta ya kamo hannunta ya rike.Ta juyo ta kalleshi kadaran kadahan a hankali tace, sannu da zuwa ya aikin?Alhamdulillah aiki mun gode Allah kuma babu dadi.Hmm…..Tace ta tsuke bakinta daga nan.Kiyi hakuri da dukkan abunda ya faru nayi kuskure nasan na cancanci dukkan hukunci daga gare ki ki yafe mun.Ajiyan zuciya kawai ta sauke amma ta kasa magana domin tana bude baki tasan kuka zatayi, wannan abun yana kona ranta.Kimun magana dan Allah kice wani abu.Toh me kake so ince?Kice kinyi hakuri komai ya wuce.Murmushi tayi kadan, kada ka yaudari kanka, tabbas hakurin da nayi shine ma dalilin da har ka dawo ka tarar dani ban tafi din ba amma hakan ba yana nufin na manta ko zan manta abunda kayi mun bane.Ina rokon Allah ya mantar dake abunda ya faru din.Ameen tace bata sake magana ba shi kadai yayita zuban shi ita dai daga um sai um-um.Ko a office ma duk na kasa tabuka komai saboda damuwa da kuma halin da muke ciki, ina sonki da yawa kece baza ki gane hakan ba domin tsananin soyayyar da nike miki itace take ruru wutar kishinki a raina, dan Allah ki dinga mun uzuri kan dabi’una insha Allah zanyi kokarin gyarawa.Allah yasa Allah ya taimaka, ji take kamar ta shage shi tayita bugu amma babu hali.Ya kamata kaje masallaci kaji an fara kiran sallah kada ka rasa jam’i.Ya mike ya Shiga dakinsa ya sawo jallabiya ya fito ya mata sallama ya nufi masallacin itama ta shimfida sallaya tayi nata sallahn.Bayan isha suka zauna a dining suka ci abinci bayan sun gama suka komo falo ta kwanta a doguwar kujera shi kuma ya zauna daga ta kafafunta yana mata tafiyar tsutsa duk don ta saki ranta suyi hira amma bai ci nasara ba domin taki ta sake jiki tayi dariya da wasa kamar yadda ta saba sai dai eh a’a takeyi, bai damu ba saboda yasan shiya taba ta kuma zai biyeta a hakan harta warware.Koda sukaje kwanciya ya bukaceta bata nuna masa komai ba ta biye mai harya samu natsuwa ya bigire gefe ya juya baya, tabi bayan shi da kallo hawaye na tsiyayo mata daga idanunta tana ayyana aranta, wannan wace iriyar rayuwace? Shi hankalin shi ya kwanta ita kenan in zata mutu ta mutu bai damu ba? Ta sauke ajiyan zuciya ta sauka ta nufi ban daki tayi wankan tsarki ta fito ta tsane jikinta ta hau ta kwanta tana mai jin babu dadi gameda abubuwa, ta rasa ya zatayi ita ba kawa ba balle ta nemi shawara, da wannan tunanin har bacci ya dauketa.
LIKE….COMMENT…SHARE……FISABILILLAHI😍EESHERT ADAMUMATAR MAJEEDADI✍️


