Hausa novels

Ruwan Zuma Page 18 Hausa Novel

(18) “Tun yaushe?�? Shine tambayar da Mas’ud ya yiwa Laila yana mik’a mata wayar. Kar6a tayi tana harararsa ranta a 6ace ta koma ta zauna kan kujera tana maida numfashi a hankali. Shima biyota yayi ya zauna kusa da ita ya zuba mata idanunshi masu kama dana Sabrin. “Baki bani amsa ba.�? D’ago ido tayi ta kalleshi kana ta d’aura k’afafunta a kan kujeran tace, “Meyasa ka tambaya?�? “Answer me Kalti.�? “Zai yi sati.�? Ta bashi amsa tana mai kawar da kanta gefe ganin irin kallon da yake wurgo mata na tuhuma. “Meyasa kika fara 6oye mini sirrinki yanzu? A daa duk wani motsinki da kowanne abu daya shafi rayuwarki na sani Kalti kuma nima haka kin san nawa. Meyasa kike son 6oye mini abunda ke tsakaninki dashi? Why?�? Ya tambayeta yana mai juyo da fuskarta ta kalleshi da kyau. Had’e fuskarta tayi tamau kana tace, “Mas’ud bani son irin haka, komai ne na rayuwata sai na fad’a maka?�? “Yes.�? “Sake mini fuska kar ka 6ata mini kwalliya.�? Tace dashi tana harararsa kad’an. Sake mata fuskar yayi kana ya rik’o hannunta duka biyu yanda baza ta juya mishi fuska ba yace, “Ina jinki.�? Ajiyar zuciya ta sauk’e tana dubanshi cikin ido tace, “Baza kayi judging d’ina ba?�? “Na daina.�? Ya amsa mata yana murmushi kad’an. Ganin hakan yasa itama ta sake fuskarta ta fara bashi labarin Haydar da take 6oye mishi. Ta k’arisa da cewa, “I don’t know meyasa na kasa korarsa kamar yanda nake yiwa sauran masu cewa suna son aurena. Ko don idan yayi wasu abubuwan yana tuna mini Aliyu ne? Ko dai haka kawai Allah ya had’a jininmu? Babu maganar wai ko ina sonshi Mas’ud, wallahi babu ita. Haydar ba sa’ana bane sannan ko da auren zanyi ina da zawarawa daidai shekaruna in aura. Ni dariya yake bani don shirmensa yayi yawa, shi da gaske wai aurena zai yi.�? Ta k’arishe maganan tana darawa. Murmushi kawai Mas’ud yayi yana kallon yanda take walwala kamar bata da wata damuwa a rayuwarta wanda hiran Haydar kad’ai da tayi ya jawo hakan. “Sai ki matsa masa ya fito da mata kafin lokacin yayi domin yanzu saura sati biyu biki.�? “Zai yi wuya ayi auren nan dashi amma ko daga baya ne zan masa idan Allah ya nufa.�? “Ko tare da naki za’ayi bikin nashi?�? Fad’in Mas’ud yana karantar yanayinta. Laila tayi d’an jimm kad’an tana tunani sannan tace, “Idan kuma hakane bazan samu damar halartar auren nashi ba, ina dai jira ya fitar mata yayi aure kafin Alhaji Abdul ya gane halin da ake ciki ya koresa a aiki.�? “Da wannan ma don wannan. Amma Kalti daga yau bana son kina 6oye mini wani abu na rayuwarki. Karki manta tun a daa tare muke sirrinmu, kuma har gobe ina son mu kasance haka.�? “I promise bazan sake ba amma kaima you have to trust me cewa bana yiwa Haydar soyayya na aure, Allah ne ya had’a jininmu kuma nake taimakonsa babu gajiyawa.�? “I trust you Kalti.�? Kwana biyu da haka Haydar ya iso gidan Laila kamar yanda ta umarcesa. Ganin Mas’ud zaune kusa da ita yasa yaji kamar yaje ya bashi naushi, amma tunawa da yayi cewa k’aninta ne sai ya samu sauk’i a zuciyarsa. Zama yayi a k’asa kamar kullum ya gaishesu tana tambayarshi jikin Ammi yace, “Ta samu sauk’i sosai.�? Sai dai Laila ta lura da wani kallon soyayya da yake mata idan Mas’ud baya gani wanda hakan yaso ya bata dariya amma ta tamke fuska tamkar bata gani ba. “Ka fitar da mata?�? Tambayar farko kenan da ta fara masa. Gyad’a kai yayi ya had’a da cewa, “Na samu.�? “Wacece kuma a ina take?�? Tayi masa tambayar tana rik’e numfashinta. Kallon Mas’ud yayi yaga shima jiran amsarsa yake yi. Haydar ya had’iye yawu yace, “Sunanta Minat a unguwarmu take amma iyayenta basu shirya aurenta nan da sati biyu ba.�? Ajiyar zuciya Laila ta sauk’e wacce bata ma san ta rik’e ba, Mas’ud ya bita da ido yayi d’an murmushi ta gefen bakinsa. “Sai yaushe kenan?�? “Zuwa wata biyar ko sama da haka, saboda basu shirya ba kuma basu da k’arfi.�? Ya amsa mata cikin sauri kamar wanda ya haddace maganan tun ba yau ba. Kallon Mas’ud tayi suka yi magana ta ido kana ta juyo da dubanta ga Haydar tace, “Shikenan, da zarar anyi auren Sabrin hankalina ya dawo jikina za’a fara naka sai ka yiwa dangin mahaifinka magana a je nemo maka aurenta.�? Shiru yayi ya sadda kanshi k’asa fuskarsa ta canja zuwa bak’in ciki, kallon juna Mas’ud da Laila suka yi kana ta maida dubanta ga Haydar tace, “Haydar lafiya dai ko?�? “Ban san su waye dangin mahaifina ba haka kuma ban san na mahaifiyata ba. Ammi kad’ai na tashi na gani a matsayin zuri’ata.�? Ya k’arishe maganan yana runtse idonshi kad’an domin hawayen da suka taru su koma. Mas’ud ya mik’e tsaye yace, “If you need me ina side d’ina.�? Kana ya fice ya bar musu falon. Cikin tausayawa Laila ta dubi Haydar itama taji hawaye na taruwa a nata idon tace, “Baka ta6a fad’a mini ba.�? “Bana son yin maganar da kowa ne.�? “Ka tambayi Ammi ita zata sani Haydar, duk tsawon wannan lokacin me ya hanaka tambayarta?�? “Tambayarta da nayi yasa ciwonta ya tashi har ta kwanta a asibiti. Idan kuma na k’ara matsa mata zan iya rasata alhali she is all a have.�? “Ko ni zata iya fad’a mini idan naje mata da maganar aurenka?�? “Baza ta fad’a miki komai ba k’arshe ma hakan kan iya tayar mata da ciwonta. Idan ba ita taso yin maganar ba don Allah kar ki kawo mata shi.�? Gyad’a kai Laila tayi tana jin zafi a k’irjinta, ashe shine dalilin da yasa bai ta6a kawo mata hiran ‘yan uwanshi ba? Itama kuma sai tayi nauyin baki duk tsawon wannan lokacin bata ta6a tambayarshi ba. Ganin har lokacin Haydar baya cikin walwala yasa Laila taji babu dad’i domin tafi sabawa da barkwancinsa ko da kuwa wani lokacin yana wuce gona da iri. Sallamarshi tayi ya fita jiki babu kwari sannan ko d’an tsokananta da yake yi na maganar soyayyar yau bai mata ba. A nan ta gane hakan ba k’aramin cinsa yake yi a ciki ba. Waye ba zai so sanin tsatsonsa ba? Bayan tafiyar Haydar ta kira Mas’ud ya dawo take fad’a masa wasu abubuwa da ta gani game dashi wanda a daa bata d’aukeshi a komai ba. “Sai yanzu na gane dalilin da yasa har Ammi ta kwanta a asibiti amma babu wani d’an uwansu da yazo dubata.�? “A yanda na samu labari basu da kowa sai junansu, and he was 23 suka zo wannan unguwar suka zauna. Mutanen unguwan sun ce basu san daga ina suke ba amma basu da wani mummunan hali ko wani abun kushewa.�? Laila ta yiwa Mas’ud kallon tambaya ya kuma gane ya bata amsa da cewa, “Kalti a yanda kike ji dashi I won’t let him hurt you idan ya gama shiga jikinki ba, shiyasa nayi bincike a kanshi sosai. Sai dai Haydar bashi da wani mummunan hali illa rashin sanin daga ina suka fito. A nan garin yayi University har ya gama tare da abokinsa Nasir. Ina ga sauran tarihinsa na baya zai iya fad’a miki idan kika tambayeshi.�? “Kana tunanin zai fad’a mini?�? “Zai fad’a miki tunda yace yana sonki.�? “Mas’ud kenan. Yau kuma kaine kake fad’an hakan da bakinka?�? Tayi ‘yar murmushi da iyakarta fatar baki. “Ya zan yi? Idan ma kince zaki aureshi ni bazan hanaki ba domin kuwa hakan ba haramun bane Kalti.�? “You are joking right?�? Ta tambayeshi cikin mamaki don bata tsammaci jin hakan daga gareshi ba. “Komai kika yi a rayuwa zaki samu wani hakan bai mishi ba, komai da kika sani.�? “Wannan ba amsa bace.�? “Sannan zai yi wuya a bashi auren yarinya a garin nan matuk’ar ba’a san asalinsa ba. Kamar abun da wuya.�? Da haka ya tashi ya shiga d’akinta ya d’auko mata hijabi yana cewa, “Ki tashi mu tafi.�? “Laffaya zan saka.�? Ta bashi amsa tana mai kar6an hijabin ta koma d’akinta dashi. Minti biyar da haka ta fito sanye da laffaya green wanda yayi mata kyau bana wasa ba. “Kyau kam sosai amma hijabin yafi rufe miki jiki Kalti.�? “Kaima kasan nafi son laffaya akan hijabi.�? Bai k’ara cewa komai ba yayi gaba ta bishi a baya suka bi Laila Beauty suka d’auki Sabrin. Daga nan kuma kasuwa suka tafi sayayyan kayan biki. Bayan sun dawo da dare Laila ta shiga d’akin Abul ta sameshi kwance a kan gado ya rufe idonsa yana bacci. Murmushi tayi tana ganin yanda kowacce rana yake k’ara kama da Babansa tamkar an tsaga kara. Har zata tafi ta jiyo muryarsa ya kira sunanta. “Mama.�? “Dama baka yi bacci bane?�? Ta iso gaban gadonshi ta zauna tana k’ara godewa Allah da ya bata su. “Yanzu nake shirin yi.�? Ya tashi zaune shima yana kallonta. “Kwana biyu baka son cin abinci har ka rame, dubi yanda idonka ya fad’a fa. Ko dai baka da lafiya ne?�? Ta ta6a goshinsa amma bata ji alamar zazza6i ba. Cire hannun nata yayi daga goshinsa ya rik’e a nasa yace, “Mama me ya dawo dashi gidan nan yau?�? “Ya Allah!�? Ta runtse idonta kana ta bud’esu ta kalli Abul, cikin gajiyawa da maganar tace, “Abul ba auren Haydar zan yi ba, zuwan da kaga yayi Mas’ud ne yasa in kirashi yaji ko ya tsayar da mata dalilin naso na had’a aurensa da Sabrin, amma hakan bai yiwu ba saboda iyayen yarinyar basu shirya ba. Haydar mutumin kirki ne Abul, sannan wancan abun da yayi ya bamu hak’uri ni da Mas’ud.�? Tayi masa wannan k’aryar don kawai hankalinsa ya kwanta. Wani irin farin ciki ta gani kwance a fuskar Abul wanda ya sakata nishad’i har sai da hakwaranta duka bayyana. “Mama da gaske?�? Tsaki taja cikin wasa tace, “Ban sani ba.�? Saisaita fuskarsa yayi ya zama babu wannan wasan yace, “Ki mini alk’awarin cewa bazaki ta6a aurenshi ba.�? “Abul…�? Zata yi magana ya dakatar da ita da cewa, “Just promise me Mama. Ina son hankalina ya kwanta yanda ko da gaba na ganshi a gidan nan bazan nemi karyashi ba.�? “Baza ka iya fad’a da Haydar kaci nasara ba Abul.�? Tayi dariya kad’an cikin ganin wautarsa. Shima d’aga kai yayi sama yana tuno siffar Haydar, yaga kuwa idan har aka bari suka yi fad’a ba k’aramin kashi zai sha ba, sai dai ko rundunar sojoji ne zai iya taransu in dai akan mamanshi ne. “Sai yanzu nake mamakin ya aka yi ya bari Uncle Mas’ud yaja kwalar rigarsa har waje bai kwace ko yayi fighting d’inshi back ba.�? Murmusawa kawai tayi bata ce kanzil ba, Abul yaci gaba da magana. “Now promise me.�? Ya jefar da wancan maganan yana mik’a mata hannu don ayi sealing promise d’in. Itama mik’a mishi nata hannun tayi tana cewa, “I promise, amma kai har yanzu in mutum zai maka alk’awari sai yayi shaking hannunka?�? A cikin sati biyun nan Laila na yawan kiran Haydar idan wani aika ya tashi da take son ya mata. K’arshe ma motarta ta dawo hannunsa duk inda zata je shi zai kaita wanda hakan ya faru ne da sa hannun Alhaji Abdul wanda ya bawa Haydar damar barin Office matuk’ar Gimbiya Laila ce ta kirashi. (Rashin sani yafi dare duhu) Sabrin, wacce bata son bidi’a walima kad’ai aka yi a bakinta. Komai da akayi Haydar na ciki, sannan minti kad’an Laila zata kirashi har falo zai shigo ta bashi wani aikan ya tafi. Sai dai duk inda ya had’a ido da Sabrin ko Abul harararsa kawai suke yi, Sabrin kuwa har da jan tsaki da ya mata fatan alkhairi a aurenta. K’awayen Laila wato Hajiya Maryam da Hajiya Shatu kuwa sai da suka tambayeta waye Haydar ganin yanda yake shiga da fice a bikin kamar na k’anwarsa, wanda hatta Abul bai kaishi hidima ba. “Wallahi wani maraya ne wanda yake da nitsuwa sosai gashi zai miki aiki tsakani da Allah babu cuwa-cuwa. Halinsa na kwarai yasa na sama masa aiki a k’ark’ashin Alhaji Abdul.�? “Allah ya biyaki uwar kwashe-kwashe.�? Fad’in Hajiya Maryam tana jinjina halin k’awar tata na tausayi. “Baki da dama.�? Shine kawai abunda Laila ta fad’a tana murmushi ba tare data sanar dasu ainihin meya faru tsakaninta da Haydar ba. Bayan an gama walima aka fara d’aukan hoto wanda Sabrin ne da kanta ta za6i a kira Damo photography saboda yasan makamar aikinsa. Ana cikin d’aukan hoto Laila taji kamar mutum na kallonta ta juya ta fara duba a ina ne. Haydar ta gani tsaye a bakin mashigar hall d’in hannayensa sanye cikin aljihun wandonsa yana mata murmushi. Sosai yayi kyau cikin maroon d’in shadda wacce ta tsufa kad’an amma hakan bai hanashi haskawa a cikin jama’a ba. Magana ya mata da baki wanda bata gane ba, d’aukar wayarsa yayi yana kad’a mata alamar ta duba tata. “Haydar matsala.�? Ta furta a hankali tana ciro wayarta daga cikin pos d’inta. Sai dai kafin ta bud’e wayar aka ce su tsaya d’aukan wani hoton, ana d’auka taji shigowar sak’o a wayarta ta matsa gefe tana ce musu, “Carry on ina zuwa zan yi waya ne.�? Kana ta bud’e sak’on wanda ta karanta kamar haka; ‘Kamar yau muma ranarmu zata zo and I’ll be the happiest man on earth. I love you Hajiyata.�? Wani irin abu taji daga k’afarta har tsakar kanta wanda ta jima bata ji hakan ba tun bayan rasuwar mijinta. Haydar na neman wargaza mata lissafi yana neman jawo mata lik’i. ‘Ka daina turo mini irin wannan messages d’in.�? Ta tura masa kana ta koma aka cigaba da d’aukan hoto amma tunaninta kaff na kan sak’on Haydar. Juyawa tayi inda yake taga baya gurin sai taji zuciyarta babu dad’i, seconds goma da haka taji k’arar shigowar wani sak’on. ‘Miss me yet? And no, I won’t stop har sai ranar dana ganki a d’akina.�? Tana karantawa ta kashe wayar tata gabad’aya ta k’ara dubawa bata ganshi ba, k’arshe ta tabbatar ya koma gida don tun safe ya zo gidanta gashi har magriba ta kunno kai bai koma ba, ita kanta tasan ya gaji kuma ya kamata ya huta. Wani lokacin maganarshi kunya had’e da takaici yake bata, wai bai san cewa ita d’in ba yarinya bace da zai yi amfani da wad’annan kalaman don ya sayi zuciyarta ba? Washe gari asabar aka d’aura auren Sabrin da Salman, sai a lokacin kuma Laila ta yarda da gaske zata rabu da d’iyarta wacce ko sau d’aya basu ta6a rabuwa ko na kwana d’aya ba, dalilin sakasu a ranta da tayi yasa bata son abunda zaisa tayi nesa dasu. Mas’ud ne ya kirata a waya kan tazo falonta tayi bak’i. Minti biyar da haka Laila ta isa falon Mas’ud inda wasu maza hud’u ke zaune suna hira. Alhaji Abdul, Nazifi, Haruna (abokin marigayi Aliyu na kut da kut) da kuma Alhaji Mukhtar abokin Mas’ud. Guri ta samu ta zauna tana musu sannu da zuwa, yanda kowa ya zuba mata ido yana k’ok’arin yanda zai yi tayi noticing d’insa. Kwatsam sai ga Haydar ya shigo wanda Mas’ud ya aika ya sayo musu ruwa saboda na gida ya k’are. Da kanshi ya ajiye musu ruwan a gabansu yana gaishesu cikin girmamawa wanda gaisuwar ubangidansa Alhaji Abdul tafi ta kowa. Mas’ud dai na tsaye a bakin k’ofa yana kallon masu neman auren yayarshi. Nazifi daya bayar da auren Sabrin ne ya fara magana, “Alhamdulillah. Hajiya an d’aura aure lafiya a bisa sadaki dubu hamsin gashi nan. Kai yaro zo ka mik’a mata.�? Ya kira Haydar wanda Mas’ud ya tsayar dashi haka kurum ba tare da ya fad’a masa me zai yi ba. Haydar yaje ya kar6i kud’in ya bawa Laila tare da kanne mata ido d’aya yana cewa, “Watarana haka zan damk’a miki naki a hannunki.�? Wannan magana ta bawa Laila kunya ba kad’an ba, ya bar gurin tana cewa, “Mara kunyan yaro kawai.�? Wanda kowa yaji a falon. Duk sai ido ya dawo kanta ana jiran aji meya faru. Haydar kuwa komawa yayi gefen Mas’ud ya tsaya anan yana dariya k’asa-k’asa tunda ya lura aikinsa a falon mik’a abu ne. Nazifi daya kasa hak’uri ya dubi Laila wacce har lokacin bata bar murmushi ba yace, “Lafiya dai Hajiya? Meya miki na rashin kunya?�? Laila ta d’an rage murmushin ta kawar da zancen tace, “Allah ya sanya albarka a auren.�? “Ameen Ameen.�? Dukansu suka amsa. “Yanzu kam sai na Maman Sabrin ko?�? Alhaji Mukhtar ne yayi wannan magana tun bayan gaisawar da yayi da Laila, kana ya shafi gemunsa yana mata kallon k’auna. Sunkuyar da kanta tayi k’asa ganin yanda mutanen falon suka zuba mata ido kowa bakinshi d’auke da murmushi a zuciyarsa kuma yana fatan ta za6eshi. Haydar dai gimtse fuskarsa yayi domin ya lura Mas’ud na karantarshi tun lokacin daya saka Laila dariya. Alhaji Abdul ne ya fara magana cikin barkwanci yace, “Ai tak’i ne amma da tuni kunji komai ya kankama.�? Wannan magana yasa kowa ya maida dubansa kansa, Haruna daya san da zancen tun zamanin daa ya bishi kallon tausayi. Haydar da bai gane kan zancen ba shima yayi tasa dariyar Mas’ud na kallonshi ta wutsiyar ido. Daga nan suka d’anyi hira na minti biyar cikin raha sai dai kowannensu na ciki na ciki. Daga baya suka mata sallama ta koma gurin bak’i masu shirin d’aukan Amarya. Ko da aka zo tafiya da Sabrin Laila sai da tayi hawaye, k’arshe barin falon tayi ta koma d’akinta aka fita da Sabrin gurin motoci itama tana kuka tana kiran sunan mamanta. Gidan Laila ya watse biki ya koma gidan su Salman. Mutane kalilan da basu bi tawagar Amarya bane suka fara gyara gidan da taimakon masu aikin Laila. Tana kwance a d’aki tana tunanin Sabrin d’inta taji an bud’e k’ofa an shigo. K’amshin turaren Mas’ud data shak’a a k’ofofin hancinta yasa ta gane waye ne. “Wai an ce kina kuka, da gaske ne?�? Ya fad’a yana takowa zuwa bakin gadon nata. Tashi tayi zaune wasu hawayen na d’iga a fuskarta tace, “Ban shirya rabuwa da ita ba yanzu Mas’ud.�? Murmushi yayi yana kiran sunanta, “Kalti, Kalti.�? “Bana son rashin kunya, idan ba rarrashina zaka yi ba ka fita mini a d’aki.�? Ta share hawayen tana murmusawa kad’an. Zama yayi akan kujeran mirror bayan ya daina dariyar yace, “Sabrin zata iya kula da kanta domin tana da sauk’in kai da hankali. Sannan kin yaba da hankalin Salman ne yasa kika d’auki ‘yarki tilo kika bashi aurenta. Ki gyara fuskarki, ga can Umma ta zo.�? Dafa k’irji Laila tayi ta zaro ido tace, “Umman marigayi?�? Ya gyad’a mata kai yana tashi tsaye. “Sai da aka kai yarinyar sannan zata zo?�? Ta fad’a tana shafawa fuskarta powder. A falo suka samu Umma ta hana masu aikin shara wai zasu tayar mata da k’ura kamar a filin yak’i take. Laila ta samu guri ta zauna tana musu sannu da zuwa da fara’arta, Mas’ud kuma ya bar falon yana hararar Umma ita kuma ta bishi da kallon banza, domin har yau basa ko ga maciji. Laila ta gaishe da Umma kana ta dubi Muna wacce tun k’ar6an kayan aure bata k’ara zuwa ba tace, “Sai yau?�? Umma ta kar6e kamar dama jira take yi. “Yanzu ma don Nazifi ya matsa ne amma yaushe zaka zo gidan da za’a wulak’antaka?�? Wannan magana ya yiwa Laila zafi don tasan har Muna ta tafi bata mata abun wulak’anci ba sai ma entertaining tawagarta da tayi suka tafi suna saka mata albarka. “Tace me aka mata?�? Laila ta tambaya tana murmusawa don tasan da gayya suke mata haka kuma baza ta basu wannan daman na 6ata mata rai ba. “Ina mai sunan uwar taki?�? Umma tayi kamar bata ji ba. “D’azu aka kaita Umma.�? “Kinga rashin sanin darajar mutum ko? Yanzu a aurar da jikata amma har a kaita d’akin miji baki yi tunanin ki aiketa gidana ta mini sallama ba?�? K’arshe dai Umma tayi ta fad’a Laila na jinta kawai, Muna kuma na gefe tana tsoma baki tana k’ara harzuk’ata. “Yanzu kam tunda kin aurar da ita ai zaki yi auren ko?�? Laila ta kalli Muna taga yanda take jindad’in wannan cin mutuncin da Umma take mata kana tayi kwafa tace, “Nima nawa ya kusa.�? Basu tsammaci wannan amsar ba amma Umma taji dad’in wannan zancen saboda ko don Abul ya koma gurinta zata so Laila tayi aure. “To Alhamdulillah. Yaushe kuma waye?�? Laila ta gyara zamanta tace, “Tukunna dai ina yin shawara domin masu son auren nawa da yawa. A cikin Alhaji Abdul da Alhaji Mukhtar ko Baffan yaran zan za6a.�? Wani irin zabura Muna tayi ta mik’e tsaye jikinta har kyarma yake yi ta nuna Laila da yatsa tana cewa, “Don cin amana mijin nawa zaki aura? Yayan mijin naki?!�? “To menene a ciki? Naga dani dake duk cigabanmu ne.�? Umma kuma shiru tayi tana tunani, domin ko da Laila ta auri Nazifi ita ba damuwarta bane muddin Abul zai dawo hannunta. “Tashi mu tafi.�? Shine abunda Umma ta fad’a. Muna ta kwaye baki zata yi magana Umma tayi gaba ta barta a gurin tana cewa, “Ga saitin samiru guda biyu ki aikawa ‘yar taki.�? Wani mugun kallo Muna ta yiwa Laila, takaici kamar ya kasheta har hawaye na taruwa a idonta tace, “Mijina yafi k’arfin karya irinki mai bin maza, wallahi sai dai wani can ya kwasa amma ba mutum mai mutunci irinshi ba.�? “Kije ki fad’i hakan a gabanshi kiji me zai ce. Idan kuma bakya son in aurar miki miji ki hanashi da kanki in zaki iya.�? Wannan magana ba k’aramin k’onawa Muna rai yayi ba, a zuciye ta fita daga gidan kamar zata tashi sama tabi bayan Umma wacce hakan bai bata mamaki ba, saboda tun ba yau ba take son Nazifi ya auri Laila saboda Abul ya dawo k’ark’ashin ikonta. Domin kuwa gadon su Abul sun hanata a tunaninsu zata dawo da yaran idan basu bata ba. Duk wannan abun da suka mata har yau Laila bata ta6a tambayarsu batun gadon ba, wanda ta sani Aliyu ya bar gida da kuma wasu kud’ad’e wanda ita kanta Umma bata ci ba domin Nazifi yace ya sakasu a wata harkar kasuwanci kud’in sun watse. Suna fita Laila ta dafe kanta tana nanata lahaula a ranta. Tasan zata had’a fad’a tsakanin Muna da Nazifi amma ya zata yi? Muna tana yawan cakalarta da fad’a saboda taga bata tanka mata. A ranta kuma taji kwarin guiwan yin aure domin ta lura duk wani mai son bak’anta mata rai maganar aure zai kawo kuma ya samu nasara. Bayan angama biki kowa ya watse ya rage daga Laila, Mas’ud da Abul kad’ai a gidan. Laila tuni ta fara kewar Sabrin wacce ta bawa hutun sati hud’u kafin ta fara zuwa shago. A yammacin wata jumma’a sati kenan da biki, Sabrin ta kira Laila wacce ke shago suka yi hira kamar yanda suka saba, domin kuwa a rana zata kirata sau bakwai ko sama da haka. Ganin abun ya fara yawa ne yasa Laila ta hanata tace ta rage kuma ta kula da mijinta. Bayan sun gama wayar Laila ta tashi daga shago da niyyar zuwa gidanta amma sai ta canja akalar motarta zuwa gidansu Haydar domin gaishe da Amminsa. Sai da ta tsaya a wani super market ta mata sayayya kad’an sannan ta isa gidan. Da sallamarta ta shiga ta samu Ammi zaune ta mik’e k’afafunta yayinda Haydar kuma kanshi ke kan cinyarta tana shafa mishi man zaitun a gashinsa. Ganinta da yayi bai sa ya tashi ba illa ma k’ara lafewa da yayi har da rufe ido saboda fushi yake mata na k’in amsa wayarsa da kuma messages d’insa tun bayan auren Sabrin. “Sannu da zuwa Hajiya, ha’ah Ali tashi mana.�? Ta fad’a tana zungurin kanshi amma ko motsi bai yi ba. “Ammi barshi d’an auta ne ai.�? “D’an auta ko katon banza. Kin zo lafiya Hajiya?�? Ta fad’a murmushi kwance a fuskarta don ba k’aramin dad’i taji ba data ganta, wai mai sonka shine naka. “Ina wuni Ammi?�? Ta gaisheta amma hankalinta na kan Haydar wanda har lokacin bai bud’e idonshi ba. “Lafiya kalau Hajiya, kun gama biki lafiya?�? “Hamdallah Ammi, Haydar ya kawo gudumawarki na turaren wuta, baki ji dad’in da naji ba wallahi nagode sosai, Allah ya bar zumunci.�? Bayan sun gama gaisawa Ammi ta k’ara zungurin kan Haydar tana cewa, “Ali ba magana nake maka ba? Baka jin Hajiya Laila ta zo ne?�? “Naji mana.�? Ya bata amsa amma kuma bai motsa ba illa ma kumburo da fuska da yayi. Dariya Laila tayi wanda hakan na d’aya daga cikin abunda yasa ta kasa rabuwa da Haydar, domin shi d’in yana sakata nishad’i. “Barni da d’an d’akin nan nawa, kullum muna kan yin fad’a muna shiryawa.�? “Ke da Haydar ai sai Allah. Kwanakin baya yazo mini da maganan shirme wanda nayi masa fad’a sosai a kai, da fatan dai bai 6ata miki rai ba?�? Laila ta zaro ido waje tana kallon Ammi wacce ke murd’e kunnen Haydar shi kuma yana yin k’ara yana cewa ta sake masa kunne. “Oh…umm babu komai ai, maganar ta wuce.�? “Ammi bai wuce ba.�? Fad’in Haydar yana tashi zaune ya gyara zamanshi yana k’urawa Laila ido wacce take dana sanin zuwanta gidan. Yaushe ya fad’awa mahaifiyarsa wannan maganan? Ta yaya ya iya tunkararta ya fad’a mata wannan zancen? “Ammi, Hajiya Laila tana sona. Amma gudun maganan mutane da kuma naki yasa tak’i amincewa dani. Yau gaki ga ita ki fad’a mata maganan da muka yi kwanakin baya da nazo miki da zancen.

Mum Fateey👌

Back to top button