Hausa novels

Halysaah Page 131 By Khaleesat Haydar

HALYSAAH PAGE 131…Da yamma Khaleesat suka sauka Airport din garin Abuja, Driver din da ya zo daukansu ya saka duk akwatunan ta a booth sannan ya bude mata back seat ta shiga ya kulle motar ya koma gefe yana jiran Ajay dake waya ya shiga motar kafin shi ma ya shiga, ita dai Khaleesat kallon Ajay take don duk da he is not too far from the car amma baka ma jin me yake cewa a wayar, few seconds later ya saka wayar a aljihunsa sannan ya juya, driver ya bude masa bayan motar da sauri, Ajay yace “I will take the front seat….” Yana fadin haka ya bude gaban motar ya shiga, drivern ya zaga ya koma driver seat, suna fita daga Airport din Khaleesat ta dinga baza ido taga inda za su a Abuja, bayan tafiyar minti arba’in da biyar suka iso gidan, tun da suka shiga compound din gidan take kallon gidan, driver yayi parking a lot din dake compound, Ajay ya bude motar ya sauka, ita dai Khaleesat sai bin sa take da ido don tun da suka baro Airport ko kallon bayan motar bai yi ba, driver ya bude mata back seat, sai a sannan ta lura she was still sitted inside the car ashe, ta sauko daga motar a hankali tace ma drivern “Thank you” Ajay ya fara tafiya toward building din gidan don dama jira yake ta gama zaman da take a motar ta sauko, hararansa tayi tana bin sa a baya kamar bata son tafiyar, yana danna bell mai aikin gidan ta bude kofar ta koma gefe tana gaishesa da fara’a fuskarta, yace “Ya kike Aisha” Tace “Lafiya lau Yaya Prince, sannu da zuwa, ya hanya?” Cikin few seconds Khaleesat tayi ma mai aikin kallon sama har kasa sannan ta amsa gaisuwar da take mata ta bi bayan Ajay da ya karasa can cikin parlon, ya nemi kujera ya zauna yana gaida Ammi da ta tashi daga zaunen da take tana welcoming dinsu da fara’a sosai, Khaleesat zata zauna kasan carpet Ammi ta dagota ta zaunar da ita kan kujera tace “A’a yi zaman ki kan kujera daughter, sannun ku da zuwa, kun sha tafiya” Khaleesat ta gaisheta da ladabi, Ammi ta amsa tana murmushi tace “Lafiya lau my dear, ya gajiyan hanya?” Inteesar ce ta fito daga kitchen tana ganin Ajay ta taho da gudu ta zauna gefensa tayi masa side hug cike da farin cikin ganinsa tace “Yaya Prince amma fa kace min sai anjima da daddare za ku sauka, dama wasa kake min?” Ya ɗan yi murmushi yana kallonta yace “Ohh… na zata ai daren yayi yanxu, ashe da saura ko” Inteesar tayi dariya sosai tace “Kai Yaya, even for once ka zama serious mana, yanxu da ban yi girkin da nace zan yi ba fa?” Yace “Sai Ammi tayi min” Khaleesat dai kallo daya tayi ma Inteesar ta sunkuyar da kanta tana wasa da veil dinta, Inteesar na lura da ita lokaci daya ta sake Ajay, ta mike da sauri ta koma kusa da ita ta zauna ta rungumeta cike da fara’a tace “Khaleesat sannu da zuwa, yau dai Allah yayi kin sake dawowa gidanmu, ya hanya?” Khaleesat ta ɗan yi murmushi tace “Alhamdulillah” Inteesar bata sake bin ta kan Ajay ba ta kama hannun Khaleesat tana murmushi tace “Mu je sama ki huta” Ammi tace “Yauwa ki kai ta tayi wanka tayi sallah sai ta huta kafin ayi dishing abinci, she look so tired” Khaleesat dai ta bi Inteesar dake rike da hannunta suka haura sama, Ajay ya bi ta da kallo, Inteesar na haurawa sama da ita ta kai ta har Bedroom dinta tace “Yaya Prince ce min yayi fa sai can da daddare za ku sauka ashe dai wasa yake min, Allah ya so har na gama girkin da nake, let me get you towel ki shiga kiyi wanka, before I dish the food….” Khaleesat tayi murmushi kawai, Inteesar ta dauko mata new towel a wardrobe dinta ta mika mata sannan ta amshi handbag din hannunta ta ajiye kan bedside drawer ta nuna mata bathroom dinta tace “Ki shiga kiyi wanka Khaleesat, i will get ur box now kafin ki fito sai ki canza kaya” Khaleesat tace “Toh nagode” Juyawa Inteesar tayi ta fita daga dakin ta kullo kofar, Khaleesat ta fi minti biyar tsaye inda take, can ta fara unrolling din veil dinta a hankali sannan ta shiga bandakin, ko da ta fito ta tarar Inteesar har ta kawo mata akwatinta ta ajiye a dakin, bayan ta ɗan yi shafe shafenta ta bude akwatin ta cire doguwar riga da hijab dinta ta saka, tana idar da sallah ko tashi bata yi saman darduman ba sai ga Inteesar ta shigo dakin tana kallonta tace “Yauwa taso mu je parlor, anyi dishing abinci a dinning ke ake jira” Khaleesat ta kalleta tace “Bana jin yunwa yanxu” Inteesar ta hade rai tace “Don Allah ki taso, in ma baza ki ci a dinning ba sai kiyi zaman ki a parlor ki ci abincin” Bata jira cewar Khaleesat ba ta tafi ta kamo hannunta tace “Mu je plss” Ba yanda Khaleesat ta iya haka ta mike ta bi ta suka fita daga dakin suka sauka downstairs, Ajay na zaune dinning area yana cin white rice and stew din gabansa, sai Umar yayan Inteesar dake cin tuwo da miyar vegetable yana zaune daga kusa da Ajay, Ammi ma na dining din zaune da nata abincin a gabanta, Inteesar ta ja Khaleesat har zuwa gun dining din sannan ta ja mata kujeran dake kallon inda Ajay ke zaune, gaida Umar Khaleesat tayi ganin yana kama da Ammi sosai, ya amsa da fara’a yana tambayarta ya hanya, tace “Alhamdulillah” zaunawa tayi ta ɗan kalli Ajay dake cin abincinsa without looking at her, Ammi tace “Tuwon za ki ci ko shinkafa daughter?” Khaleesat ta ɗan yi murmushin karfin hali tace “Shinkafa” Ammi tayi dishing mata shinkafa da miya da nama sai coslow a wani bowl ta ajiye mata abincin a gabanta tace “Ga shi daughter, ki saki jiki ki ci abinci kin ji” a hankali Khaleesat tace “Toh Nagode Ammi” Inteesar da ta fara cin nata abincin ta kalli Ajay tace “Yaya abincin yayi dadi?” Ajay ya ɗan kalleta yace “I am still trying to figure out” Dariya tayi sosai tace “Ai na san abinda zaka ce kenan, da na sani da ban dafa shinkafar ba in ga yanda zaka yi da tuwo” Ita dai Khaleesat juya abincin gabanta kawai take a hankali kanta a kasa, Umar yayi ma Inteesar wani kallo yace “Ke wai bakin ki bazai iya shiru for good 10 mins bane, kin cika mutane da surutu wajen cin abinci” Inteesar bata ce komai ba ta ci gaba da cin abincinta, Ajay ne ya fara tashi daga dinning din bayan ya gama cin abincinsa don dama ba da yawa yasa Inteesar tayi masa dishing ba, Ammi na kallonsa tace “Wai har ka koshi?” Yace “Na koshi” Tace “Ko dai shayi zaka sha?” Yace “A’a, sai anjima” Khaleesat ta daga kai ta kallesa suka hada ido a karo na farko, barin dinning area din yayi ya tafi sama…. Ajay na zaune Bedroom din da yake sauka always a duk sanda ya zo gidan Ammi, wanda wannan daki ya fi zame masa comfort zone akan masarautarsu, he is more comfortable and have rest of mind a gidan nan akan Bauchi, don in dai ya dawo daga Amurka ya kan yi kwanaki biyar wani lokacin har sati a gidan Ammi kafin ya tafi Kano, a Kano kuma yayi kwana uku ko hudu before leaving for Bauchi, kuma yana haka ne duk don ya ja lokacin da ya zo yi a Nigeria ta yanda few days zai yi a Bauchi ya koma Amurka, Umar da ya shigo dakin not long ago ya gama wayar da yake sannan ya kalli Ajay yace “Hope an samu canji tsakanin ka da Jay zuwa yanxu?” Ajay ya dauke idonsa daga football da yake kallo a dakin ya kalli Umar yace “Not when i am still together with the girl he has in mind as a wife” Umar yayi shiru na wasu sakwanni yana kallonsa, sai kuma ya sauke ajiyar zuciya yace “Ajay nasan ka a mutumin da baya keeping malice no matter what, bar ka dai da saurin hawa wani lokacin amma fa baka da wuyan saukowa, to don me zaka biye ma Jawwad har zuwa wannan lokacin baku magana duba da irin closeness dinku kai da shi?” Ajay yace “I am not keeping Malice with him, jira yake in sakar masa yarinyar before we get back together and I understand that, but he is only not being patient….” Umar ya katse sa da sauri yace “I don’t understand he is not being patient? What are you insinuating?” Ajay yace “Eh mana, ba shi da hakuri, da yayi hakuri yayi calm down we will get there in sha Allah” Umar yayi masa wani kallo yace “Are you kidding me? Kana nufin sakar masa yarinyar zaka yi ya aura??” Ajay yace “Idan zai iya ba, balle na ma san zai iya, kuma abinda yake jira kenan, so hakan ne zai faru i told him to calm down” Umar ya girgiza kai yace “This is abhorrent, very disgusting, kuna nufin da ran Mai martaban za ku yi wannan rashin hankalin ko kun mance wani irin gida ku ka fito ne? Kuma ka ban mamaki Ajay don ko ba da consent dinka aka aura maka yarinyar nan ba a sunan matarka take a yanxu dai kuma duk cikakken namiji dole zai yi kishin matarsa ko da kuwa baya sonta aka aura masa ita, balle you can’t just tell me you have no feelings for ur wife Ajay, I am not surprise at Jay’s action don ba a yi masa komai ba ma ya share mutum yayi ignoring calls dinsa yaki replying Whatsapp messenges balle yana tunanin an masa laifi, shi kaga halinsa ne shariya da banzatar da mutum amma kai ba halin ka bane, kuma bana son ka koyi sabon halin da ba naka ba idan har ba hali ne me kyau ba, i know Jay is hurt but he took the issue to another level, yaki yi maka uxuri, ni kaina nayi kokarin fahimtar da shi daga karshe he stopped replying my chat, I called him once bai daga ba, so nima sai ban sake masa magana ba har yau” Ajay dai bai sake cewa komai ba ya maida idonsa kan football da yake kallo, Umar yace “Ni sai yanxu ma na sake tabbatar da cewar shakkan Jay din nan kake, dama na taɓa gaya maka haka da dadewa, banda kana shakkarsa shi har ya isa yasa ka bijire ma hukuncin da Mai martaba ya zartar a kanka? So kana nufin gwara kayi pleasing Jay kayi displeasing Mai martaba, tunda gashi har kana da burin sakin yarinyar da aka aura maka saboda Jay, to sai kace ma Mai martaba me idan ka saki yarinyar?? I promise you he is going to disown you wallahi, shi Jay yayi ma mahaifiyarsa biyayya kai kuma bari ka bijire ma naka mahaifin saboda ka faranta masa, to ko sakin yarinyar nan kayi sorry to say ai ba masarautar taɓaɓɓu bane masarautar taku da za su amince Jay ya sake aurenta tunda shi Jay din ba shi da tunani” Ajay ya ɗan yi murmushi yace “Ba lallai ka fahimta ba, but i know how to go about everything, just watch and see” Yana kai wa nan yayi concentrating akan football din da yake kallo, Umar dai yayi shiru yana kallonsa, can ya mike ya nufi kofa zai fita dai dai sanda aka yi knocking kofar dakin, bude kofar yayi yaga Inteesar tsaye bakin kofar, ya hade rai yace “Me ya faru? Ko dai baki da hankali ne? kina ganin matarsa a gidan kike shisshige masa, ko kina hauka ne?” Inteesar ta koma baya tana kallon yayan nata, Ajay ya daga kai ya kalli Umar yace “I don’t understand Umar?” Umar yace “To ai kasan mata da kishi, is better ku ajiye wani brother and sister things dinku aside don ita matarka ba fahimtar closeness dinku zata yi ba cikin kankanin lokaci” Juyawa Inteesar tayi ta bar bakin kofar bayan ta hade rai ta koma dakinta, tana shiga dakin ta samu Khaleesat zaune kan darduma ta idar da sallah, Inteesar tace “In kawo maki fruit din ne Khaleesat? Or should I make fruit salad for you” Khaleesat bata kalleta ba ta girgiza kai tace “A’a Nagode” Inteesar ta tafi gefen gado ta zauna ta kunna laptop dinta, knocking din kofar dakin aka yi, ta kalli kofar sai kuma ta mike ta tafi ta bude, Ajay ta gani tsaye bakin kofar, yana kallonta yace “Fushi kika yi kika tafi?” Khaleesat ta daga kai tana kallonsu, Inteesar ta jingina da kofar tace “Not at all, just that he reads meaning into nothing” Yace “To mu je” Ta langwabe kai Tace “Ohk” Juyawa yayi ya bar bakin kofar, Inteesar ta koma ta zauna gefen gado tana kallon Khaleesat da murmushi fuskarta tace “Taso mu je dakinsa Khaleesat, tsaraban da ya kawo min zai bani….” Khaleesat ta ɗaga kai ta kalleta tace “Ki je ki dawo, zan fara azkar ne yanxu” Inteesar tace “Ohk” Mikewa tayi ta nufi kofa ta fita, nan kan darduma Khaleesat tayi kwanciyarta, har karfe goma Inteesar bata dawo dakin ba, sai da goma da rabi yayi ta shigo rike da ledan kayayyakin da Ajay ya bata, Khaleesat ta rufe ido kamar me bacci, bayan Inteesar ta ajiye ledan hannunta ta tafi kusa da ita ta durkusa tana tashinta tace “Khaleesat me yasa baki kwanta kan gado ba, why will you lie down here” Juya mata baya Khaleesat tayi tace “Zan hau anjima” Inteesar tace “To baza ki kara abinci ba?” Khaleesat ta girgiza mata kai kawai, mikewa Inteesar tayi ta bar wajen ta tafi ta bude press ta ciro kayan baccin ta zata shiga wanka…. A haka Khaleesat suka yi kwanaki hudu a gidan Ammi, wanda a kwanaki hudun nan jin ta take kamar a ƙaya, bata taɓa jin ta matsu ta bar waje kamar wannan gidan ba, infact bata taɓa zama guri da ta zama uncomfortable kamar zaman da tayi a gidan ba, ko magana bata fiye yi ba sai dai idan yi mata aka yi, she is always pressing her phone, hakan kuma bai sa ta canza ma kowa fuska ba ko ta nuna da wani abu a ranta, cikin dare kuma ta sha kukan da bata san dalilinsa ba, gaba daya ta ma rasa me ke damunta, throughout this 4 days ko kallon inda Ajay yake bata yi a gidan, idan abinci ne ya kai ta downstairs iyaka ta cakalkali abinda zata cakalkala ta wuce sama don appetite din cin abincin ma bata da shi, sanda Inteesar ta shigo wajen karfe biyar da rabi ta sanar mata Ajay yace ta shirya they are leaving, cikin minti goma Khaleesat ta gama shiryawa kamar dama jira take, a haka suka bar gidan bayan Ammi ta hada mata sha tara ta arziki, Inteesar ma ta bata wasu tsadaddun turarruka, har suka yi nisa bayan sun baro gidan Ammi Khaleesat taki kallon Ajay dake zaune gaban mota, shi kuwa lokaci lokaci yake kallonta ta madubi, ita dai idonta na outside of the car, suna isa airport ta sauka daga motar, shi ma ya sauka yana kallonta, still dai taki kallonsa tayi tafiyarta cikin airport din, bin bayanta yayi bayan an shiga da luggages dinta ciki. Karfe bakwai da rabi suka sauka garin kano kuma all through the flight to Kano taki yarda ta kalli Ajay duk da waje daya suka zauna, motar da zai daukesu har ya iso airport yana jiransu a wajen parking, Khaleesat ta ɗan ji dama daman abinda take ji a zuciyarta for 4 days ganinsu a cikin garin kano, yau dai tasan gidansu zata kwana zata ga Ummanta da Babanta da twin sibling dinta da step sibling, tunanin hakan yasa ta farin ciki sosai a ranta, taji har ta kagu su isa Tudun Yola, amma bayan tafiyar minti talatin da biyar a mota ta ga sun iso wani babban hotel, ta dinga kallon drivern motar babu ko kiftawa, shi dai driver yayi parking cikin hotel din, sai a sannan ta juya ta kalli Ajay da ya bude motar ya sauka, nan da nan farin cikin zuciyarta ya gushe ta ji kamar ta rushe da kukan takaici, still dai babu abinda tace ta bude motar ta sauka fuskarta babu yabo babu fallasa ta bi bayan Ajay zuwa cikin hotel din. Bayan sun yi lodging hotel din Khaleesat dai ta zauna gefen gado ta ciro wayarta tana dannawa fuskarta a daure, yana kallonta ta madubi ya gama cire wristwatch din hannunsa ya ajiye gaban madubin sannan ya shiga wanka, bayan ya fito ya shirya ya dau wayarsa ya nufi kofa zai fita daga dakin zuwa masallacin hotel din yayi sallah, ko da wasa Khaleesat taki yarda su yi eye contact da shi har yanxu, after 20 mins sai gashi ya dawo dakin ya ajiye ledan abincin da ya siyo mata yana kallonta, sai a sannan ta ajiye wayar hannunta still not looking at his direction fuskarta a daure ta mike ta ciro kayan da zata canza ta shiga bandaki, bayan 30 mins ta fito daga bathroom din taga baya dakin, sallolinta tayi sannan ta tashi ta cire hijab dinta tana linkewa ya shigo dakin, ta gama linkin hijab din ta juya zata koma daya side din gadon taga ya kashe wutan dakin ya fixgota, a fusace ta buge hannunsa zata kwace kanta tace “Meye haka??Ni ka kyaleni kar in maka ihu wallahi…”

Halysaah is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah, ur evidence 07087865788

Back to top button