Hausa novels

Ruwan Zuma Page 4 Hausa Novel

(04)  “Yarinyar nan ba haka ta barka ba Aliyu, a daa kana son zama kusa dani, amma yanzu na gane take-takenka, neman hanyar da zaka nisantar da kanka kake yi daga gareni. Haba Aliyu, ni ce fa mahaifiyarka.” Fad’in Umma tana sharce hawaye domin ta tsani taji abunda zai nisantata da Aliyunta. “Umma, kamfanin da kansu suka nema mini gurin zama suka ce in d’auko iyalina mu zauna zuwa gaba kafin nayi nawa na kaina. Kinga kuma idan na tafi ni d’aya zaman ba zai mini sauk’i ba, kullum kenan sai na sayi abinci kuma ke kinsan hakan 6arnan kud’i ne. Zan dinga zuwa duk bayan sati uku kafin komai ya daidaita, kuma bazan fasa muku aika ba.” Da kyar ya Lalla6ata da kuma alk’awarin kowanne sati biyu zai zo ya dubata sannan ta yarda.  A ranar Aliyu da k’annensa suka kwashe kayan d’akin Laila aka saka a mota ta kama hanya. Katifa kad’ai suka bari sai kuma wasu k’ananan abubuwa da zasu iya sayan sabbi a can. Da la’asar ta je gidansu ta yiwa iyayenta sallama sannan ta wuce gidan yayarta Ajidde bayan magriba tare da rakiyar Mas’ud, wanda yake manne da ita idanunshi na tara hawaye . “Kai Mas’ud abun naka ya fara yawa, da girmanka kake rik’e mata mayafi kana kuka? Shikenan sai kar tabi mijinta ta zauna da kai?” Cewar Ajidde wacce ta k’ulu har wuya da halin Mas’ud. “Kalti kenan.” Laila ta fad’a itama tana tara hawayen a idonta, in ba dole ba ai baza ta so tayi nisa da Mas’ud ba. Bayan Isha Aliyu ya zo d’aukan Laila, a nan ne shima ya tabbatar tsakanin ‘yan uwa biyun shak’uwa ce mai k’arfi, domin daga Laila har Mas’ud d’in kuka suke yi kace-kace. Ko iyayenta bata musu wannan kukan ba sai da ta zo rabuwa da k’aninta. “Ya Salam, Laila ke da zaki rarrasheshi kema kukan kike yi? Kiyi hak’uri ki hau mu tafi, Mas’ud hingo gashi ka hau mashin ka koma gida.” Aliyu ya mik’a masa Naira d’aya da fitti amma Mas’ud da yake kuka yana rik’e da hannun Laila ko kallonshi bai yi ba.  Sai da mijin Ajidde ya dawo sannan ya rik’e Mas’ud d’in shima Aliyu ya ja Laila aka rabasu suka tafi. Washe gari jikin Laila ba kuzari suka tafi tasha bayan sun yi sallama da ‘yan gidan nasu, kafin motarsu ta tashi ta hango Mas’ud tsaye yana waige-waige yana sanye da rigar makaranta da alama guduwa yayi. Ai kuwa ta kwala masa kira ya zo gurinsu da saurinsa yana washe musu hakwara. “Har ka hak’ura da kukan?” Aliyu ya tsokaneshi yana dariya. “Me ya hanaka zama a makaranta?” Shine tambayar da Laila ta fara mishi tana 6ata fuska. “Kalti da anyi hutu zan zo gidanku in yi hutun a can, jiya Baba yace zai barni in zo.” Ya sanar mata ba tare da ya amsa tambayarta ba, ga kuma farin ciki kwance a fuskarsa.  Fuskar Laila ta washe ta dubeshi cikin son k’anin nata ta ce, “Dama nima na tambayeshi, kace masa nagode da ya amince. Ka dinga karatu Mas’ud, ka kuma kula da Ummii dasu Safa da Marwa.” “Zan yi Kalti. Allah ya tsare muku hanya.” Da haka motarsu ta tashi suka gangara zuwa mafitar tashan Mas’ud na d’aga musu hannnu.   Gidan da suka samu gidan haya ne mai sashe biyu, kowanne d’aki biyu da band’aki d’aya sai k’aramin madafi. Makwabtansu Idris da Asiya ma’aurata ne tare da ‘yayansu biyu. Zaman gidan ba k’aramin dad’i ya yiwa su Laila ba, domin sai a lokacin suka sake suna nunawa junansu soyayya. Aliyu da yake jinshi kamar sabon Ango da kyar yake fita aiki ba don ya so ba.   Laila mai d’auke da cikin wata uku sosai take samun kulawa daga gurin mijinta, sannan duk sati zai d’auketa ya kaita gurin wayar tarho ta kira shagon Babanta su gaisa, a nan ne take jin labarin mutanen gidansu. Sati biyu da dawowansu Kaduna Mas’ud ya zo musu hutu har na tsawon sati uku kamar yanda Baba ya musu alk’awari, yana gama hutunsa ya koma Kano don cigaba da karatunsa.  Zaman Laila da Asiya matar Idris zama ne na fahimtar juna da kuma k’awance, sosai suke shiri hatta mazajensu sun sani. Wai sai an zauna ake aminta da sirrin juna ko? To hakan ya kasance tsakanin wad’annan makwabta biyu.    Duk wani sirri na Asiya, Laila ta sani, haka itama Asiya ta san na Laila hatta zamanta da surukarta da ta yi. Sai dai Laila na mamakin yanda Asiya da Idris suke yawan fad’a wanda ita da Aliyu basu cika yin hakan ba. Akwai watarana da Idris ya samu Aliyu yake fad’a masa matsalolin Asiya har yana cewa zai k’ara mata kishiya, Aliyu ya bashi hak’uri ya kuma sasantasu tun da ya saba yin hakan.  Da dare yake fad’awa Laila yanda suka yi da Idris har maganan aure da yace zai k’ara. Laila sam bata ji dad’in hakan ba, don haka washegari ta samu Asiya da zancen akan ko zata gyara zamanta da Idris. Ita kuma Asiya wacce tsabar gigicewa sai da ta tsinkawa d’iyarta mari wacce ta zo tana tambayarta wani abu. “Zai zo ya sameni, bani yace zai yiwa kishiya ba? Wallahi sai na nuna masa ba’a sabo dani.” Fad’in Asiya tana kumfar baki. Cikin Laila ya kad’a sosai don Aliyu ya sha mata gargad’in rik’e cikinta, musamman akan Asiya, amma sai take ganin hakan a matsayin takura har akan hakan suka yi fad’a sosai, daga baya ya zo ya bata hak’uri ya kuma daina mata maganan.  To yanzu idan Asiya ta samu Idris ta fad’a mishi, shima ya zo ya samu Aliyu ita kuma me zai faru da ita?  Aliyu yana da hak’uri sosai ita kanta tayi masa wannan shaidar, yana gudun 6acin ranta sannan ko laifi ta masa idan bata bashi hak’uri ba shi zai iya zuwa ya bata hak’urin don kawai ayi zaman lafiya. Amma wannan karon ta san ta wuce geji, ta masa laifi babba ta hanyar maida zancensa a inda zai tayar da husuma. Hak’uri ta shiga bawa Asiya wacce da kyar ta hak’ura, sannan hankalin Laila ya kwanta. Sai dai abun mamaki ranar da dare Aliyu na mata matsar k’afa dalilin cikinta da ya shiga watan haihuwa ta ji yana cewa, “Ke kuma sai kika samu mata kika fad’a mata cewa nace mijinta zai k’ara aure ko?” A take a lokacin cikinta ya murd’a ta ji tana son shiga makewayi sai dai bata nuna masa ba. Cikin kunya da tsoro ta sunkuyar da kanta k’asa hawaye na taruwa a idonta. Daga baya ma sai ta fashe da kuka dalilin Aliyu tsayawa yayi yana kallonta yana jiran amsarta. “Ni dai kika yiwa laifi amma ke kike kuka. Na sha fad’a miki ba komai ne zaki fad’awa mutum ba don kawai kina zaune dashi. Wannan karon farko kenan da kika min haka, don haka zan bari ya wuce amma gaba kar ki sake mini irin gangancin nan, Idan baza kiyi sulhu tsakanin mata da miji ba karki tunzura fad’an nasu. Kin ji kam?” Yace da ita yana mai sauk’e hannayenta daga fuskarta wacce ta ca6e da hawaye. “Naga alama so kike ki zama uwar gulma amma zan taka miki birki.” Ya fad’a yana dariya yana mata cakulkuli. Tana dariya tana zullewa tana masa magiyar ya bari amma yak’i dainawa. “Don…Allah ka bari nayi… nayi… fitsari a zaune.” Ta fad’a tana dariyan dolen irin na wanda ake yiwa cakulculi. Da sauri ya dakata daga yin hakan, da gasken ruwa ne malale a inda take zaune amma wannan mai kauri kamar ba fitsari ba. Ciwon da taji a mararta yasa suka gane meke faruwa, a gurguje ya d’auki kayan haihuwar da suka jima da adanawa suka tafi asibiti da rakiyar wata babbar mata Mamayo da ke bayan gidansu. Washe gari da asuba ta santalo yaronta fari tass kyakkyawa kamar Babanshi. Sai da aka gyarasu sannan aka bari Aliyu ya samu ganinsu.  D’aukan yaron yayi yana kallonshi bakinshi a washe idanunshi na kyalli na tsantsar farin ciki, ita dai Laila kallonshi kawai take yi tana murmushi ganin yanda duk hankalinshi ya koma kan d’anshi. Sai da ya gaji don kansa sannan ya dubeta fuskarsa d’auke da tsantsar k’aunarta yace, “A watan February na had’u dake Laila, sannan shekara na zagayowa kika bani magajina a watan Feruary. Nagode Laila, kuma har gobe ina godewa Allah da yasa naje gurinki da niyyar gwadaki. Alhamdulillah.”  Washegari Ajidde ce ta zo ta zauna mata har suna, yaro yaci sunan mahaifin Aliyu wato Rufa’i, suna kiransa Abul Khair.   Umma ma ta zo suna, ko da ta saka idanunta a kan yaron ta d’auki son duniya ta d’ora a kanshi, domin kuwa shine jikanta na fari sannan ga k’arin sunan mijinta marigayi da aka saka masa. Bayan bikin suna da kwana biyu suka koma Kano wankan jego aka bar Aliyu shi kad’ai ciki kewar iyalinshi. Bayan ta yi arba’in ta dawo Kaduna suka bud’e sabon fegin soyayya. Haka rayuwa ta cigaba da kasance musu cikin jindadi da k’aunar juna. Shekara uku ciff da haihuwar Abul khair Laila ta k’ara haihuwar d’iyarta mace itama fara sol kamar yayanta. Tun daga asibitin Aliyu ke cewa yarinyar na kama da Mas’ud itama kuma ta yarda ta hakan don babu in da ta baro k’anin nata. Umma na jira ta ji anyi mata takwara sai ji tayi wai an yiwa mahaifiyar Laila, wato yarinya taci suna Falmata amma za’a dinga kiranta da Sabrin.   Fad’in tashin hankalin da ta shiga har ba’a magana, k’arshe tana kuka ta wayar hannu take fad’awa Aliyu cewa ta sallamawa Laila shi, da haka ta ajiyewa masu wayar abunsu ta koma gida, dama a gurin Jafaru mai wayar kud’i take magana da Aliyu.   Aliyu hankalinsa bai kwanta da halin da ya saka Umma ba don haka washegari ya dira a Kano. “Me zan ce da mutane da ‘yan uwa da na fad’awa cewa ni zaka yiwa takwara? Ka kunyatani Aliyu ka kunyatani a cikin ‘yan uwana da kuma idon mak’iya. Laila ta shanyeka ta rabani da kai Aliyu.” Umma ta fad’a tana kuka sosai wanda har cikin ranshi Aliyu yake jin d’aci. “Umma wai gani nayi haihuwar Abul khair sunan Abbana aka saka, shine nace tunda nayi nawa d’aya itama zan mata wannan adalcin. Kiyi hak’uri na yanke hukunci ba tare da na tuntu6eki ba, in Allah ya yarda yarana na gaba ke zaki za6i sunan da za’a saka musu, na miki wannan alk’awarin Umma.” Tana share hawaye tana cewa, “Shikenan tunda ka fini baki, ai ban isa in ce komai ba sai abunda Lamla ta fad’a.” “Matsayin Laila daban da naki Umma, har duniya ta nad’e bazan ta6a samun kamarki ba, karki manta ke kad’ai kika rage mini a duniya a mahaifana. Lailan ita kanta a k’ark’ashinki take tunda ni mijinta ma Aljannata na k’asan k’afarki ce, Ina sonki Ummata, kuma babu wanda nake so kamar ki.”  Wannan kalaman yasa zuciyarsa Umma ta wanku fes har tayi fatan inama a gaban Laila ya fad’i hakan daa tafi yin farin ciki. Sabrin na da wata bakwai Kamfanin su Aliyu ya samu wani kwangilar aiki a Jos.  Dashi da maigidansa Alhaji Atiku ne suka je garin Jos domin duba aikin da za’a fara. Har Alhaji Atiku ya koma gida Kano Aliyu yana nan a Jos domin shi yake tsaye masa akan komai yake kuma aika masa da rohoton abubuwan da ke gudana.  Satinsa uku a Jos yayi niyyar komawa gida Kaduna amma wani aikin ya 6ullo dolenshi ya hak’ura zauna. Kwana biyu da haka yaje Kano ya kaiwa Alh. Atiku wasu takardu da zai duba, daga nan gidansu ya sauk’a da niyyar washegari zai wuce Kaduna. A daren ranar suka kwana da Umma suna hiran yaushe gamo domin rabonta dashi kusan wata biyu kenan. Shima sakewa yayi yana bata labarin aikin da suke yi har yana fad’a mata gidan da Alh. Atiku ya bashi yau d’innan wanda ke cikin Kano.  Umma ta yi murna kwarai da taji cewa gida ne mai girma kuma wai zata koma ciki, Idan kuma Laila ta zo Kano a nan zata dinga sauk’a.  Washegari yayi sallama da mutan Kano ya kama hanyar Kaduna cikin d’okin ganin iyalanshi wanda yayi wata d’aya bai gani ba. Laila ce ke kaiwa da kawowa tsakanin madafinta da kuma falonta in da tasa ake mata sabon fenti da Aliyu ya fad’a mata yau yana kan hanya, suna gamawa fenti ko bushewa bai yi ba ta jera kujerunta da kwabet d’inta sannan ta bud’e windo yanda iska zai yi saurin busar dashi.  A yanda Aliyu ya fad’a mata zai iya isowa bayan la’asar amma kuma shiru har magriba ta gabato babu shi babu labarinshi.  Tayi wanka tayi kwalliya na kece raini ita da ‘yayanta, ga abinci da ta girka masa har kala biyu a jere a sabbin tirerrukan da ta saya masa. Abul khair tuni yayi bacci a gefenta amma Sabrin na cinyarta tana shan nono tana wasa da gashin mamanta wanda aka yarfawa kitso ‘yan k’anana suna kwance a bayanta da kuma k’irjinta.  Kiran sallan magriba da aka fara yasa ta tashi Abul khair, zaunar da Sabrin ta yi kusa dashi yana mata wasa ita kuma ta shiga band’aki yin alwala, Laila bata so wanke fuskarta ba wacce ta yiwa kwalliya na gani na fad’a domin Aliyu. Bayan ta idar da sallah ne ta jiyo sallamarsa a waje, ai da sauri tayi cikin d’akinta da gudu don gyara fuskarta.  Bai shigo ba hakan yasa ta dakata da shafa hodar da take yi murna fal a fuskarta tana tsammanin so yake ta fito ta masa oyoyo. Da sauri ta gama shafa hodar sannan ta saka jan baki da kuma kwalli kana ta fito waje in da take jin muryar Abul yana wasa da Baban nashi.   Sai dai maimakon ta ga Aliyunta sai ta ga yayansa Nazifi ne yake rik’e da Abul yana shafa kanshi yayinda hawaye ke tsiyaya a idonsa. Gefensa kuma Babanta ne tsaye yana kallonta cike da tausayi.  Zuciyarta ce ta buga da k’arfi domin bata yi tsammanin su zata gani ba, murmushi ta k’ak’alo wanda ya bayyana hakwaranta ta nufo Baban nata tana musu iso. “Sannunku da zuwa Baba, bismillah ku iso falo.” Ta fad’a tana mai musu nuni da hanyar falon. Nazifi ne ya fara yin gaba kana suma suka bi bayansa, cikin d’aki Laila ta wuce ta d’auko mayafinta sannan ta 6oye gashinta sanin cewa Nazifi ba muharraminta bane, ko a daa da suka zauna a gida d’aya bata bari yana ganinta haka jiki babu lullu6i. Ta fara’arta ta d’auko musu ruwan sanyin da ta tanadawa Aliyu ta ajiye a gabansu tana murmushi yayinda bakinta bai bar fad’in mamaki da kuma jindad’i da tayi da ta gansu ba. Ganin duk cikinsu babu mai murmushi yasa ta sha jinin jikinta, “Baba me yake faruwa? Waye ba lafiya? Ummii ko Mas’ud?” Ta tambaya a numfashi d’aya tana kallon Nazifi mai d’igar da hawaye. “Laila kafin nace miki komai Ina so ki tuna kowanne mai rai mamaci ne….” Baba bai kai ga k’arasa magananshi ba Laila ta tashi tsaye ta rugo zuwa gurinshi ta durk’usa tana kamo hannayensa, tuni kuma hawaye suka fara ambaliya a fuskarta har bata ganin fuskar Baban da kyau. “Baba wa ya rasu? Wallahi nasan kowanne mai rai mamaci ne amma Baba ka sanar mini yanzu tun kafin zuciyata ta buga. Ina Ummii Ina Mas’ud? Baba waye ya rasu?” Ta k’arishe maganan tana jijjigashi tamkar ma bata cikin hayyacinta. Kwantar mata da hankali Baba ya fara amma Ina bata sauraro kawai cewa take yi ya sanar da ita wanda ya rasu. Sai yanzu ta gane irin canjin da taji a jikinta wunin ranar ba don d’okin ganin mijinta bane, ashe rashi ta yi wanda bata ma sani ba. “Baba ka fad’a mata kar ta gigice, ka duba halin da ta shiga.” “Baba waye ya rasu?” Ta k’ara tambayanshi cikin gunjin kuka. Abul da yake jikin Nazifi ya zo da gudu ya rungumeta yana ihu saboda baya son ya ga mamanshi tana kuka.  Sabrin da take gefe ma kukan ta saka tana d’aga hannunta sama alamar mamanta ta d’auketa. “Laila, kisa dangana da kuma hak’uri a zuciyarki. Allah ya yiwa Aliyu rasuwa a mafitan Kano tun kafin suyi nisa da barin cikin gari……”  Dummmmm ta daina jin komai da yake fita daga bakin Babanta, zama tayi dirshan a k’asan kusa da k’afafunshi tana kallon Nazifi ya d’auki Sabrin ya fita da ita shima kukan yake yi hani’an.   Abul da yake jikinta ma Babanta ya jawoshi yana rarrashinsa amma shima idanunsa sun yi jawur kamar garwashi yana mata magana. Me yake cewa? Wannan ne bata sani ba. Hawayen da suke fita daga idanunta suka kafe tana jin k’irjinta na zafi sosai tamkar ana hura mata wuta.  A razane ta mik’e cikin sauri ta yi hanyar d’akinta tana magana a hankali kamar mai rad’a, “Aliyu ba zai mutu ba Baba, yace mini yana hanya, zai dawo…” Kafin ta kai ga isa bakin k’ofa ta fad’i a k’asa sumammiya.Ba’a ma yi komai daga labarin rayuwar Laila ba. Ruwan Zuma littafin kud’i ne a Naira dari kacal N100. Zaku turo kud’inku ta bank 5139579011 FCMB Suwaiba Babagana, ko kuma katin waya Zain/Airtel ta wannan number 09023713064, Zaku yi amfani da wannan number dake sama domin nuna shaidarku na biyan kud’in Ruwan Zuma. Ga maza masu son shiga, kuma zaku turo kudinku sai ku yiwa wannan number magana 0903 662 1442 a sakaku a group na maza zallah.  Sannan Ina wad’anda basa son hayaniyar group? Zamu iya tura muku ta private a farashin N300 mace ko namiji. Sai na jiku.

Back to top button