Adam A Zango da Ado Gwanja sun shaƙi iskar ‘yanci bayan kaɗe wata mata da suka yi a Nijar
Masoyan Adam A Zango da Ado Gwanja sun cika da murna bayan dawowar su gida Nigeria daga ƙasar Niger bayan iftila’in da ya faɗa musu na hatsari da suka yi. Kamar yadda rahotanni suka bayyana jaruman sun samu hatsarin ne yayin da motar da suke ciki ta yi awon gaba da wata mata da yayan ta uku kuma nan take suka ce ga garinku nan.
Duk da kasancewar Adam A Zango ko Ado gwanja ba ɗaya a cikin su dake jan motar kuma an kama direban dake tukin amma an rike jaruman saboda masalaha ta tsaro kasancewar wasu daga matasan kasar sun fusata musamman saboda labarin da ake yaɗawa cewa bayan kade matar da yayan ta jaruman sun karasa gurin wasan da suka zo yi a ƙasar domin shi sun gudanar da wasan wanda wasu ke ganin hakan tamkar biris ne da halin ko inkula ga abin da suka yi.
Koda yake bayannan zango da gwanja sun fito sun yi video na ta’aziyya da jajantawa ahalin wayanda suka rasu da kuma jajantawa Al’ummar ƙasar hakan bai sa an daina maganganu marasa daɗi a shafukan sada zumunta kan ganin rashin kyantawar jaruman ba.
A jiya dai shafukan sada zumunta musamman Instagram suka cika da hotunan jaruman ana taya murna dawowa da jajanta musu akan abin da ya faru da su da fatan Allah Ya ƙara kiyaye gaba.
Read Also:
Wasu daga cikin Matasan Nijar na ƙoƙarin daukar doka a hannu kan Adam A Zango da Ado Gwanja