Uncategorized

Zuciya Da Kwanji Chapter 8 Complete Hausa Novel

 

ZUCIYA DA KWANJI 

BOOK 1___8

Na Maimuna Idris Sani Beli

 Don Allah kawu gobe a kawo min motata. Nan take dama ta samu ga Abdullahi, ya yunkura cikin ladabi ya ce, “Don Allah kar a kawo mata kawu, ni bana son yawo, ita kuma na fahimci ba ta son zaman gida…. Ni da so samu ne ma ta yi irin wata shiddan nan ba ta fita ba” Fatima na zabga masa harara kawu na karfafa masa gwiwa.

   “To don me za a kasa samun abin da kake da iko? Me zata fita ta tsinta? Idan don ta mu ne na dauki nauyin zan dinga dauko momi duk karshen wata muna zuwa ganinta, ‘yan uwanta maza ma zasu  dinga zuwa”.

   Momi ma ta ce, “Haka ne, ni ma ban goyi bayan ka barta ta dinga fita barkatai ba! Idan ta kama ka hakura da wata sabgar taka ka kaita ku dawo tare, sannan ka sanya ido sosai a kan masu zuwa gidanka, duk matar da tarbiyyarta ba ta yi maka ba kar ka ji shakkar komai ka hanata zuwar maka gida”. Turkashi!

  “An kwance min zani a kasuwa”. Fatima ta fada tana kallon Abdullahi, wanda kamar ya kife saboda gajiya.

Babu yadda ta iya dole ta hadiye maitarta ita ma ta bullo ta wata kofar ta rokon a kawo mata. Tace to Momy dan Allah ki ara mani taki zuwa gobe.

 Nan ma Abdullahi ya sako baki. “Kar ki bata wayarki momi, jiya fa aka yi abin, kuma yau din nan zan kawo mata wasu. Nan ma ta kuma shanyewa ta ce, “Momi zo mu je can”. 

  Prof ya dubi agogo ya ce, “A’a ta zo mu tafi, ya ya abokan zaman naki, kuna zaune lafiya ko?” Nan ma karaf Abdullahi ya ce, “Lafiya kalau kawu, Fatima kaisu su gaisa”. Wani katon abu ya daki zuciyar Fatima, sai ta yi sararo tana duban Abdullahi, amma tana lura da yadda iyayenta suka sa mata ido, sai kawai ta tashi ta fita ba tare da ta san abin yi ba, a takaice ma ko kofar dakin kowaccensu ba ta sani ba. Kawai sai ta tsaya jikin karfen tanki tana kananan hawaye, dama gata da arhar kuka. Shi yasan ya yi kulli, don haka babu jimawa sai ga shi ba tare da ya girmama laifin da ya yi mata ba, ya hau share mata hawaye ya ce,

  “Yi hakuri zo mu kirasu tare.”.

   Bai jira amsarta ba, ya ja hannunta suka nufi daki Sadiya.

   Da sauri Sadiya ta bar jikin taga ita ma da tata kwallar don tuni ta ke lekensu tun daga rarrashin dazu da ya yi mata tana ganinsu, komai ya yi mata daci, don ta hango tsabar kauna da sadaukarwa a idanunwan Abdullahi a Fatima, fiye da zaton ko shaukin da ke rikita shi, ba ta taba samun shi a salube kamar yadda ta ganshi da fatima a yau ba, wanda komai na sa na nuna kauna a gare ta, idanunwansa, harshensa da sautinsa, duk suna samun umarni ne daga kwakwalkwasa bayan zuciya ta sanar da ita sun hadiye tarin kaunar Fatima . Tana jinsa yana buga mata kofa amman ta kasa ko motsi, sai da ta yi yaki da zuciyarta sannan ta zo ta bude kofar, amman sai  hakurinta ya gaza don suna shigowa ta hau hayagaga.   

  “Me ye ya faru zaka kwankwaso min daki kai da  wannan matar ku shigo min daki kana isa ta da ihu? Da sauri fatima ta kalle shi, amma da yake a kule ta ke, sai ta gaza barshi ya dauki mataki, ta yi tarangahumar tsoma baki. 

  “Toh! Au kare ne shi da yake miki ihu? Kin ga kuwa ko ni da nake da kason abinci…..” Da sauri Abdullahi yasa hannu ya rufe bakinta, sannan ya dora yatsansa akan labbansa ya amabata “hush!” Nan take ta karbi umarnin sa cike da shakkarsa har ya fahinci hakan, don haka ya dora don ta rage mata tsoron cikin zuciyarta. 

   “Kar ki kuma yarda wannan maganar ta hada ki da wani a cikin gidan nan, ki barsu kawai su shafta iyakar fahimtarsu su fassara…. Ba na son ki kara musawa kowa

kinji? Da abinci kawai kika tsira ranar girkinki duk da haka muna zaune lafiya babu wanda yasan cikinmu, kin gane?” Ta kada kai, kawai sannan ya juya ga Sadiya ya ce, 

  “Kina da lokacin da zan ci gaba da yi miki ihun ko na yi gaba. 

  A tunzure ta ce masa. “Ba ni da shi” Kai tsaye ya yafici fatima suka fice, sadiya kuma na yi musu Allah ya isan kebewar da suke a kwananta. Suna fita Fatima ta turje ta rungume hannu, ta ce, “Abdul, idan waccan ma kansa ba ka isa da ita ba kar ka fara kai ni wajenta ta wulakanta ni, don wannan masifar tasu tana daya daga cikin abin da yasa na kagu na bar gidan nan

  hindatu dama mace ce mai kara da boye bacin rai, don haka da ladabinta sosai ta gaishe da su kawu, yayin da Abdullahi ya bayar da uzurin Sadiya na wanka. Kawu ya hada Fatima da Hindatu ya dinga yi musu nasiha.

  “Don Allah ku rike amanar junanku, babu wata rayuwa me dorewa bare wayonka ya fissheka, an san dai zama ko da iyye ne ana sabawa, amma fahimtar juna ke hana kullaci. To ku janye kullaci a cikin zamanku, na tabbatar zaku ci ribar hakan a gaba ko bayan kasa ta rufe idanunwanku, ku kanku zaku kwanta cikin salama idan kuka bar iyalanku cikin mutunci da zumunci”.

  Hakika hindatu ta ji dadi maganganun Prof. wanda ta tabbatar abin da Fatima ta ke kawai albasa ce bata yi halin ruwa ba, kuma gatan da sadiya ta rasa ke nan, don kulliyar danginta tayata kishi suke, sau nawa uwarta ke zuwa gidan, amman ko hindatu ta gaishe ta sai ta shareta?

   Da hindatu ta ke sallama da su, sai Prof ya miƙa mata dubu biyar ya ce ta raba da yar’uwarta. Ta yi godiya sosai, da suka tashi tafiya sai ga ta da turaren wutanta, katuwar kwalba ta kawo wa momi, dama sana’arta ke nan.

   Fatima da Abdullahi suka yi musu rakiya har wajen mota kafin su shiga motar ne Abdullahi ya dinga nuna son su kebe da kawu, kawu na fahimtar hakan ya cewa momi, “Wai kuwa kin leka dakin nata? Kar ta ce mun yi mata “yan goranci, momi ta koma da baya, shi kuma suka Prof. ya keɓe shida Abdullahi. 

  Cikin tsananin ladabi Abdullahi ya ce, “Kawu don Allah kar a baiwa Fatima waya, babu abin da ya sami wayoyinta ni na kwashe su, ko cikin dabara ne a sanar da ‘yan uwanta kar su siyo mata waya, ko ta karbi tasu ta yi amafani da ita. A taimaka min da wannan kawu”.

   Prof ya yi kasake cikin bugun zuciya ya ce, “Wani abin ta yi ko?”

Da sauri Abdullahi ya girgiza kai, amma bai ce komai ba. Kawu ya kara shiru sannan ya kada kai. “Nasan ba za a rasa dalili ba, sai dai ba zan matsa maka inji ba, hasalima zan yaba maka a matsayinka na namiji mai boye sirrin iyalinsa, kuma ina tabbatar maka zan ba ka goyon baya don ina zaton alkhairi tare da kai. Ban taba ganin mutumin da Fatima ta ke shakka bayan ni kamar kai ba, saboda haka zaka iya tarbiyyarta don ba ta lankwasuwa ga mutumin da ta rainawa wayo, zan karantawa ‘yan uwanta da suke zuwa gidan nan, kai ma ka sanya ido ga kawayenta ka bi shawarar momi, duk wadda tarbiyyarta ba ta yi maka ba, kawai ka runtse ido ka hanata zuwa gidanka, ina fatan ka fahimci ni?

   Cike da farin ciki Abdullahi ya dinga yiwa kawu godiya har momi ta fito suka ƙara yin sallama da su suka tafi.

  Fatima kuwa ta yi saurin shigewa cikin gida ba tare da ta jira shi sun jeru kamar yadda suka fito ba. Shi ma hakan sai ya yi masa dadi don yana fargabar kebewar su ta hau yi masa maganar tafiya. Yana shiga ya zira takalminsa ya fice, bai kara waiwayar gidan ba sai da sha biyun dare ta gota kowa ya yi bacci, kai daya idan ka dauke Fatima da duniyar ta yi mata kunci, tana jinsa ya shige dakinsa ya garkame kofa. Sai bayan sallar asuba ya nemi dakin hindatu domin ya wanke mata zuciya tunda ita ke da girki. Hindatu tayi hakuri ne kawai don ta gane lallai akwai tarin abubuwa da ke damun zuciyarsa a cikin lamarin Fatima, sannan ta tabbatar borenta ba zai amfane ta da komai ba, kamar yadda bai amfanin sadiya ba, wadda yake ganin KWALLIN goshinta a da, eh a da mana don a yanzu yanke wa abdullahi hukuncin inda zuciyarsa ta karkata abu ne mai wahala, sai dai idan an hutar da tunani ne ma za a ce akan fatima ta karkata, wadda a yanzu karkarin dai ace ba ya kwana a dakinta, ko kuma ita ba ta kwanan nasa dakin, amma duk wata ɗawainiya da shakka wadda ke tasowa karkashin soyayyarsa ita ta mallake su. Sai dai ta nuna masa ba ta damu ba.

   Suka yi harkokin arzikinsu tare har ya shirya fita, kafin ya sanya kayansa ya dubeta a nuste ya ce “Don Allah hindatu ki yi min afuwa na je na nema wa yarinyar can abinci”.

 Ta jima tana dubansa, ta jima tana kallonsa kafin daga bisani ta magantu,

  “Abu Turab don Allah wannan wanne irin zama ne? Shin kasaitarta ce tasa ba zata shiga kicin ta yi girki ba, ko kuma don ba ta iya ba ne saboda ta fito daga gidan hutu ko kuma tsabar soyayyarta ce ta sa ba ka so ta wahala?”

  Kai tsaye ya amsa mata, “Duk cikin abin da kika fada babu dalilin Hindatu, ki yarda dai a ranki akwai dalilin sai dai kar ki kwadaitar da zuciyarki da son sani, domin sirrinmu ne ni da ita, fahimtar junan da ke tsakanina da ke ya sa na nemi ki goyi bayana. Bana son kananan maganganu da suke tasowa a tsakaninmu dalilin zuwan Fatima, kin sani hindatu ba a sanyawa namij karfi wajen mallakar soyayyarsa, amma ana iya mallaka ta hanyar kyautatawa da biyayya, shaidar da na yi miki ke nan, don Allah Hindatu kar ki canja, ki tayani neman abin da nake so sai ki ga Allah ya dora ki a kaina na yi miki adalci ko raina bai so ba. Ki daina bin yamma kina shan kida tunda ba ki san abin da ke fake ba, wai har ku dinga fitar da sirrina hindatu, ina amfanin kawayenki su zo ki fada musu zaman da nake da matata, wace ribar ki ka samu a hakan? Babu ma wanda ya fi bakanta min irin sanar da muftahu da kuka yi, raina ya yi mugun baci wallahi don dai kawai na shanye ne. Ke kanki kuma kin san wannan ba dabi’ar mace ta gari ba ce, ni ina saka ku kuna warwara, idan kuka korar min ita da wanne idon za ku dube ni? Ba zan munafunce ki ba Hindatu, Fatima tana da muhimmanci a rayuwata”.

  Hindatu ta ji ciwon maganarsa ta karshe, sai dai laifinta da ya fara gabatarwa ya danne shi, don haka fuskarta ta nuna nadama. A sanyaye ta ce “Ka yi hakuri da yarda Allah ba za a kuma ba”.

Suka yi shiru na wani lokaci,sannan ta kuma dagowa ta dube shi. “To ka je mana, sai ka yi gaggawa kar ka makara, ga shi yau monday”.

  Ya yi firgigit ya tashi yana cewa, “Haka ne, na gode da fahimtar da kika yi min”. Ya fice ta bishi da kallo tana maimaita wasu kalamansa a fili.

…….Ki tayini neman abin da nake so…. Idan kuka

korar min ita da wanne ido zaku dube ni………? Fatima na da mahimmanci a rayuwata’.

   

  Wadannan kalaman sun isa awon iyakar zurfin da abu turab ya yi a kaunar Fatima, don duk kaunarsa ga sadiya bai taba fitowa a gabanta ya fada mata ba….. To yanzu ina mafita? Tambayar da ta yiwa kanta ke nan. Wanda ba ta yi dogon nazari ba ta shawarci kanta rungumar hakuri da juriya.  Abdullahi ya jima a kofar Fatima yana addu’a kafin ya fara kwankwasawa. Ba a jima ba ta zo ta bude, gabansa ya kara faduwa da ya ganta kace-kace da hawaye. A dan tsorace ya kawar da kai kamar bai gani ba ya ce, “Kin tashi lafiya?” Ta yi gum da bakinta, sai ya canja fuska ya ce, “Lafiyaki kuwa?” 

  A tunzure ta ce masa “Ni ban sani ba.

  Ya sassauta murya ya ce, “Allah ya ba ki hakuri, ban hanya na wuce . Me kike so na girka miki?” Ta ki ba shi hanyar, sannan ta kara bata rai, (a ce “Ba na bukatar komai, kasan

matsalata,

saboda haka ita ya kamata ka magance min ba ka yi ta faman tura min abin ci ba. Ya dube ta da kyau ya ce, “Na zaci mun rufe wannan maganara, bana ce ki tsumaye ni zuwa gobe ba….? Ta tari numfashinsa da masifa. “Na ce maka ban amince ba…” Shi ma ya tareta da kaushin murya. “Idan kina da abin yi sai ki yi…. Abu daya zan cire miki a ciki shi ne, sanya kafa ki ce za ki fita daga gidan nan, yaji ko wata sabgar, kina daukan wannan matakin ni ma zan dauki nawa wanda na tabbatar ba zai miki dadi ba, wato zantar da kawu….

 Na ce ki ba ni gobe kin ishe ni da masifa haba!” Kamar turata ya yi ta kara ruwan masifar

 “Ka tafi inda ranka da taskar labarai ka fada Abdul….. Bisa wacce hujjar za ka ishe ni da naka iya yin….. Dama mun yi da kai zaka dinga kafe ni da wa”azi?.

  Ya amsa mata kai tsaye cikin daure fuska “Aure ne hujjar! Wanda na tabbata ko giya kika kurba kin san ba a kulla shi da wasa kamar yadda lissafinku ya wallafa ke da wancan mutumin…. Ki bi ni a hankali Fatima, kin ganni nan? Ba ni da dadi ni ma”. Bai jira cewarta ba ya ja kofar da karfi ya barta tsaye a gurin dakin na juya mata, so ta ke ta yarda abin da ke faruwa a mafarki ne, amma ta gane yaudarar kanta kawai ta ke….   

  Wannan kalmar ta yi dai dai a wanne nau’in cikin masifa?. To amma ba ta son tabbatar da ita da nata saurin yanke kaunar, bari ta yi tsumayinsa zuwa goben tunda ya zama kadangaren bakin tulu……

  Hindatu ta ganshi ya dawo akan kari, kuma a birkice. Da kirkinta ta tare shi, tana dannar kirjinsa ta ce, “Anya ba zaka bi manganar muftahuba ku kai matsalarku gun manya ba?”

  Ya yi murmushin karfin hali ya ce, “Babu inda zamu Hindatu, wannan yakina ne ni kaɗai, don ni kaɗai na zunguro sama da kara, yakamata na ji a jikina ni kadai ɗin, ke dai kawai ki tayani da addu’a”.

  “Kana son fatima da yawa”. Ta fada don zolaya da bugun ciki, amma bai tanka ba, sai murmushi kawai da ya yi mata.

  Ta kuma kallonsa da wutsiyar ido ta ce, “Wannan karon malam ya yi abin a zo a gani a zabin da yake maka”. A nan ta samu ya amsa. 

  “Dama can Malam ba ya zabin banza”. Ta ce, “haka ne, sai dai a samu akasi shi ya yi zabi kalmar nan ta babu ruwan so da wayo ta yi aikinta”. 

  Ya bude ido sosai ya dubeta ya ce, “Ke duk fa lauyarki ba za ki sa ni fadar abin da zan daure kaina da kaina ba”. Kawai sai ta tuntsure da dariya, shi ma ya tayata, sai ya ji zuciyursa tana sanyi, wato ya rage ‘yan adawa a cikin gida, Hindatu ta bi ko ba ta taimaka da KWANJINTA ba, zata taimaka ta fannin kin tuzura masa Fatima. Amma da ya tuno kashedi da jaye-jayen bala’in da Alhaji ya yi masa a waya bayan ya kira shi da bakuwar lamba. Ya kadu da kashedin da tsoratarwar Alhaji ya yi masa. Sai ya watsar da tsaoron bayan kaunar Fatima ta yunkura ta nuna nata fin karfin. “Hum, Allah ka zamo gatana”. Ya furta a fili, yayin da cikin sauri Hindatu ta dago ta sanya masa ido, shi ma sai ya yi tsuru yana kallonta, alamar hankalinsa ba ya tare da ita, ko kuma fargaba, Allah ya sa ban furta abin da zuciyarta ke karantawa ba.

  Washegarin ranar bai shigo gida da wuri ba, sai dab da magarinba. A gurguje ya yi wanka ya fice masallaci, bayan sallar isha sai ya kasa barin

masallacin, ya yi ta kaiwa Allah bukatunsa har da

hawaye, tsawon lokacin sannan ya hakura ya bar

masallacin, ya siyo musu kaya motsa baki, sannan ya nufi gida. A sanyaye yake komai, ya mika wa Sadiya da Hindatu nasu, sannan ya koma dakinsa ya shiryo kayan baccinsa set uku cikin jaka, da kayan sawa set biyar, kannan kaya uku, manya biyu, da duk wani abu da yasan zai bukata cikin kwanaki biyun da zai yi a dakin Fatima, ya hada da wasu makudan kuɗaɗe da cek. Ya rufo dakinsa yana ja jakar zuwa nata dakin, sai dai bai samu kofar a rufe ba, don haka ba ya bukatar kwakwasawa, sai kawai ya shiga ya yi addu’a, sannan ya murza key.

  Tun daga nan gaban Fatima da ke zaune tana

kallonsa ya fadi. Amma fuskarta ba ta nuna razana ba, kawai sai ta kawar da kai ta zubawa talabijin ido.

Shi ma bai dube ta ba,ya wuce kai tsaye dakin baccin da ya fahimci ta fi mu’amala da shi. Ya jima a tsakiyar dakin numfashisa na neman shiɗewa saboda kayatuwar dakin da ni’imar da ya hada, ga kamshi mai dadi da sanyi mai kwantar da zuciya, amma ga ma’abociyarsa cikin kunci da jazawa kai tashin hankali. Ya jima zaune a gefen gado ba tare da ya yanke shawarar ta inda ma zai fara abin da ya kwaso ba, a karshe ya

hakura ya dora jakarsa kan chest of drawer ya kashe wayoyinsa ya zira su a jakar sannan ya fito.

Nan ma bai dubeta ba ya wuce kicin sai ita ke binsa da satar kallo kawai. Ya zubo gasassun ‘yan shilan da ya shigo da shi a faranti, ya kawo fresh milk, lemo da ruwa, yana komai cikin gumin

fargabar tashin hankali duk kuwa da sanyin da ke ratsa dakin. Don haka ya zabi ya kuma yin wani wankan, wanda ba ya nufin komai a wajen Fatima sai jan lokaci. Ya koma dakinta ya canja wasu kayan, ya yi amfani da turarenta, sannan ya fito falon dauke da envelop. Ganinsa da wannan envelop din wani matsanancin farin ciki ya daki zuciyarta har sai da fuskarta ta nuna, sai nasa kishin ya motsa, sai dai babu yadda zai yi, dole

ya hadiye shi ya share. Ya ajiye envelop din kan kujera ya zauna gaban abincin anan ya dubeta kai tsaye. “Zo mu ci abinci”.

  Ta kawar da kai tana yamutsa fuska. “Ni fa tuni na fada maka, ba abinci ne a gabana ba”.

  Tana rufe baki ya amsa cikin dakewa. “Ashe ke nan zamu ɗaga tattaunawanmu zuwa wani lokaci, domin abin da na zo da shi yana bukatar nutsuwarki da koshinki… Ko zamu ɗaga zuwa gobe? Ni dai nasan akwai yunwa a tare da ke, har ma kin dan rame fa! Bana bukatar mutanen gidanku su ganki da rama”. Ya zuba mata ido kawai sai ta yunkura ta tashi zaune tana gyara riga ta yi fuska ta ce,

  “Sai ka zubo min nawa, don babu dalilin da zai sa ka ce sai na ci abinci da kai”.

  Ya ce, “Na sani, amma tunda babu dalilin da zai hana mu ci tare, ina laifi don mun ci? Ranar yau ta zame mana ranar tarihi mana Fadima? Zo mu ci don Allah ki yi hakuri da laifin da kike jin na yi miki, in Allah ya so zan takaita shi”.

  Sai ta kasa tankwabe magiyar tasa, musamman da yake yayi mata magana cikin taushin harshe. Amma tana ji a ranta shakkarsa ce kawai ke dawainiya da ita, kamar ba ta son bacin ransa. Ta tashi ta shiga bandaki ta wanko hannu da baki, sannan ta zo ta zauna gabansa ta tankwashe kafafunta suka fara ci. Kamar dama don ita ya tashi cin abincin, ita ya dinga yiwa hidimar zarewa kashi yana tura mata tsokar gabanta abin da ya kara faranta ransa ba ta tankwabe kokarinsa ba har sai da ta gamsu sannan ya zuba mata madara ya mika mata, ajiye kofin ta yi, ta dauki ayaba guda ta koma gefe tana cinyewa ta tashi zuwa kicin ta koma ta wanko baki da hannu, sannan ta dawo ta zauna tana tsumayinsa, wanda sai sannan ya mayar da hankalin yana cin nasa. Ya dinga yanga kamar ba

ya so har dai ya kai ga kammalawa ya kwashe kwanukan ya wanke nasa bakin, sannan ya cin mata, inda kai tsaye ya zarce ya dauki envelop din ya mika mata, bai jira ta ce wani abu ba ya wuce daki ya dauko kudin da ya zubo a jaka. Kafin ya fito ta farke envelop din ta zaro takardar da maimakon takardae saki uku sai ta tarar da taller da copy na cek din kudin na 700,000. Wanda cikin sakanni ta gane dangantakar cek din da Alhaji ya ba shi ne. Fiye da wasu sakanni masu dama zuciyarta ta tsaya da aiki cak! Ta ki gaba, ta ki baya, don haka ta kasa dorar da komai bare ta yi tunanin baya. Tana tsaye da takardu a hannu kamar mutum mutumi idonta akan kofar dakin da Abdullahi ya shiga, har Abdullahi ya fito, sannan zuciyar tata ta fara harbawa harta aikawa kwanyarta sakon neman dalili ita kuma ta yiwa harshenta umarnin furtawa. “Ina bukatar karin bayani Abdul”.

  Ya yi fuska ya ajiye kudin kusa da kujerar da ta ke zaune a hannunta, sannan ya dauki remote ya nemi guri ya zauna,ba tare da ya dubeta ba ya ce, “Kudin da Alhaji ya ba ni ne nake nufin dawo muku da shi don ina son na mallaki ‘yancina, na dawo maku da wannan kudin ne domin hakan zai ba ni damar ci gaba da yiwa Allah biyayyar da kuke son gotar da ni, ya kuma ba ni damar zama da abin da raina ke so ba tare da an yi min kallonm mai ci da karfin ba”.

  Ta mike cikin tangadin tashin hankali, sannan ta dake ta tsaya da kafafunta tana fuskantarsa, ta ce, “Gajarta min abin da kake nufi a kalmomi goma zuwa ashirin idan zai samu” Tana rufe baki ya amsa mata.” 

  “Na karɓi tayin auren kisan wutar da Alhaji ya yi min da zummar in kubuta da ku zaman haramcin da kuke yiwa kanku tanadi, tun kafin na sanyaki a idona. Na dauki hakan jahadi, sai dai aka dace ina dora idanuna a kanki na kamu da matsananciyar ƙaunarki, daga lokacin na fara nawa acting din wanda ya sha bam ban da naku….”

 Ta dakatar da shi cikin haki da neman sarkewar numfashi, cikin kakkausar murya ta ce, 

 “Ya ishe ka! Zan duddura maka zagi wallahi!

  Bai damu da masifarta ba, ya tari numfashinta “Ki zage ni mana Fatima, sai me? Kin san dai zagi

ba hanya ce ta samun solution ba, kuma bai cika zubar da kimar wanda ya yi, musamman idan wanda ya isa ya zagi wanda bai isa ba”.

Hankalinta kamar ba ya jikinta ta watsar da takardar ta nufe shi gadan gadan kamar tana zuwa hadiye shi zata yi. Marubuciyar ta ce “A nan zan dakata, sai a nemi littafi na biyu don dorawa. Taku MAIMUNATU IDRIS SANI BELI

VISIT www.aihausanovels.com.ng For More Novel.

AIHAUSANOVELS is website consists of hausa novels note, the reason of launching this site is to Entetaint, Motivate and Educate our readers.

We provided hausa novels of many type,  Such Adventure, love, romance, fiction, non-fiction, mystry, fantasy, action e.t.c from hausa Authors 

We provided a new and old novels both softcopy and hardcopy from our Author with thier permission.

 AIHAUSANOVELS shafin yanar gizo ne wanda yake ?auke da littattafan hausa, dalilin bude wannan shafin shine domin Kayatar masu karatu da kuma ilimantar da su.

Back to top button