Uncategorized

Tsatsuba Book 8 Littafin Yaki Na Abdulaziz Sani M/Gini

 

Ku Taba Nan Domin Karanta Littafin Tsatsuba Na Ɗaya Wannan Abdulaziz Sani M/Gini Ya Rubuta.

TSATSUBA

Littafi Na Bakwai (8)

Part A

Marubucin Littafin

Abdul azis Sani M/Gini

Posting by..

Abubakar Saleh AlQuyraemey

.

Lokacin da wannan sihirtacciyar halittar ta make sarki shardas ta luluka sararin samaniya ta bace, a dai dai wannan lokaci ne

boka labarusa ya karaso bakin kogin a guje ya isa inda sarki shardas ke kwance yana kumallon jinin.

.

Koda yaga halin da sarki shardas yake ciki sai ya dimauce hankalinsa yayi matukar dugunzuma nan da nan cikin hanzari ya bude jakarsa ta guzuri ya dauko wani garin magani ya hambadawa shardas a bakinsa ya hadiye sannan ya dauko wani farin mai ya shafe kirjinsa dashi faruwar hakan ke da wuya sai sarki shardas ya daina kumallon jinin da yake yi idanuwansa da suka wurkile suka zama jajaye sai suka dawo dai dai kuma ya dawo cikin hayyacinsa alhalin da yana . Numfashi sama sama.

.

A sannan ne boka labarusa ya dubeshi cikin girmamawa yace ya shugabana menene dalilin da yasa ka baro can kogon dutse inda muke kwance kazo nan kuma menene yayi maka wannan mugun naushi a kirji haka wanda in ba don kana da nisan kwana ba da tuni ka dade da shekawa barzahu ?

.

Koda jin wannan tambaya sai sarki shardas ya kawo gwauron numfashi ya ajiye cikin tsananin mamaki gami da takaici sannan ya dubi boka labarusa yace yakai dirkar birnina kayi sani cewa ba komai ne yasa na baroka ba a can kogon dutse sai saboda ina sha awar na shiga daji nayi farauta na samo mana naman da zamu yi kalaci dashi saboda na gaji da irin abincinmu na guzuri, nan dai sarki shardas ya baiwa boka labarin duk abinda ya faru gareshi har izuwa sa adda ya hadu da wannan shirgegiyar halitta da yadda aka sami sabani a tsakaninsu har yayi yunkurin hallakata a karshe kuma sai tayi masa duka daya wanda yai matukar galabaitar dashi, koda boka labarusa yaji wannan labari sai ya kurma uban ihu cikin tsananin takaici ya dubi sarki shardas a fusace yace, saboda me zaka zubar mana da wannan gagarumar dama da muka samu ??

.

To ka sani cewa wannan halitta ba komai bace face Aljani Arwasul masadul wanda muke nema ruwa a jallo shin ka manta ne na fada maka cewa duk mutumin da ya hadu dashi sai yayi masa jarrabawa tukunna sannan zai amince ya yarda dashi har ya taimakeshi ?

.

A cikin jarrabawarsa guda goma guda daya jal yayi maka yanzu kuma gashi ka fadi, haduwa da aljani arwasul masadul sai babbar sa a bare mu sami damar haye ragowar jarrabawar tasa guda tara yana yin Adalci guda daya idan mutum yaci jarrabawa biyar daga cikin goman yana iya taimakonsa kaga

kenan yanzu ka fadi jarrabawar farko,

.

Koda boka labarusa yazo nan a jawabinsa sai hankalin sarki shardas ya dugunzuma ainun ya rasa abinda yake masa dadi a duniya kuma ya kamu da tsananin takaici gami da bakin ciki mara misaltuwa saboda haka bai san sa adda ya kwarara uban ihu ba wanda amsa kuwwarsa ta cika dajin gaba daya har kwallar nadama ta cika masa idanu, koda ganin halin da sarki shardas ya shiga sai boka labarusa yaji ya kamu da tausayinsa don haka sai yazo daf dashi ya zauna ya tallafo kafadarsa izuwa kan kirjinsa yace ya shugabana kayi sani cewa mai dukkan rai baya cire tsammani da samun rabo don haka muna da sauran dama wacce indai muka yi amfani da ita zamu iya kaiwa gaci, tashi mu ci gaba da tafiya tunda dai himma bata ga rago kuma mai nema yana tare da samu, koda jin wannan batu sai sarki shardas yaji wani irin gagarumin karfi ya shigeshi don haka sai ya mike tsaye da sauri cikin matukar kuzari ya dafa kafadar boka labarusa ya dubeshi cikin murmushi yace kayi gaskiya yakai amintaccena kawai mu kara himma nan take suka juya suka koma izuwa wannan kogon dutse inda suka yada zango Wannan shine abinda ya faru ga su sarki shardas da bokansa boka labarusa a cikin tafiyarsu ta neman hular lamsara

”      ”       ”

LOKACIN da aka tafka wannan tsawa da walkiya bayan sake daurin auren shadila da hailur sai kowa dake cikin dakin walimar yaji zuciyarsa ta buga da karfi kuma tsoro ya baibayeshi amma sai aka basar aka cigaba da shagali har sai da aka kammala komai ango ya tafi da amaryarsa izuwa masaukinsa dake cikin gidan sarautar taron ya watse kowa ya kama gabansa lokacin da ango hailur ya kadaita da amaryarsa

shadila a cikin daki tana zaune akan gado ta sha lullubi kanta na sunkuye tana wasa da yan yatsun hannunta.

.

Koda hailur ya kamo hannunta da lafiyayyan hannunsa sai tayi doguwar ajiyar zuciya ta dago kai ta dubeshi cikin murmushi da tsananin farin ciki a lokacin da hawaye ya subuto mata, koda ganin wannan hawaye sai tsoro ya kama hailur ya dubeta a firgice yace yake masoyiyata ina dalilin zubar wannan tsadadden hawaye nakai mai tsada?

.

Shadila ta sake yin murmushi a gareshi a karo na biyu sannan tace yakai abin begena dare da rana ka sani cewa ba komai ne ya sakani wannan zubar hawayen ba face tsananin farin ciki na tunowa da daren farko na auranmu ni dakai ka tuna cewa daga wannan dare ban sake jin dumin jikinka ba a jikina, kuma ban sake ganinka ba sai a yau bayan shudewar wadansu shekaru dana jima da fidda rai da sake ganinka a wannan duniyar har abada na rantse da darajar iyayena daga yau ba zan sake yarda wani abu ya Rabamu ba face mutuwa domin a yanzu daka dawo gareni ka zama rabin ruhina idan babu kai ba zan iya cigaba da rayuwa ba a doron wannan kasa.

.

Koda shadila tazo nan a zancenta sai farin ciki ya sake lullube hailur ya rungumeta kuma ya kai hannu izuwa fitilar dakin ya kashe ta, wannan shine abinda ya faru ga sababbin ma aurata wato hailur da matarsa shadila bayan an sake daura aure a karo na biyu.

”      ”          ”

ACAN dakin yarima barmas kuwa sai da suka kusan raba dare suna hira shi da yarima hulkas akan masifar da suke ciki ta sharrin sarki shardas idan har ya gano halin da suke ciki, suna fara yin wannan hira sai yarima barmas yaga yarima hulkas yayi shiru yana tunani daga can kuma sai idanunsa suka ciko da kwalla ya fara zubar da hawaye.

.

Koda ganin haka sai shima yarima barmas hankalinsa ya dugunzuma ainun kuma ya kamu da tsananin tausayinsa don haka sai ya shiga rarrashinsa yana mai rokonsa da ya cire komai daga ransa cikin sanyin jiki yarima hulkas ya mike zaune daga kwancen da yake ya dubi yarima barmas cikin nutsuwa yace yakai abokina ka yi sani cewa ba komai bane ya

jefani cikin mugun bakinciki da takaici ba face rashin sanin cewa sarki shardas bashi bane mahaifina na jini Na dauki duk wani SO DA KAUNA ta duniya na bashi a zatona mahaifina ne shi, lallai bani da burin da yafi naga na kasheshi da hannuna domin na huce takaicin iyayena haka dai yarima barmas ya cigaba da rarrashin yarima hulkas amma sai ya zamana cewa shi yarima barmas din ne yayi barci ya bar yarima hulkas da kuma Yarima, a zaune zuciyarsa cike da tarin bakin ciki gami da sake sake har gefen asuba idanun yarima hulkas a bushe suke.

.

Koda yaga barcin ya kauracewa idanunsa sai ya mike ya fito daaga cikin turakar yarima barmas din ya kama kai kawo a cikin harabar turakar, yana cikin wannan hali ne kwatsam yaji wata irin iska mai matukar karfi daga sama ta lullubeshi kafin yarima hulkas yayi wani yunkuri ko ya daga kansa sama yaga abinda ya haifar da iskar sai kawai yaji an sunkuceshi anyi sama dashi nan take yaji kamar an zare masa dukkan lakar jikinsa gaba daya kuma sai idanunsa suka kama lumshewa a take barci mai nauyi ya daukeshi.

.

Lokacin da yarima hulkas ya farka daga barcin da ya daukeshi mai nauyi sai ya tsinci kansa a wani wuri na ban al ajabi wanda ya kasa tantancewa ko a sama yake ko kasa take ya tambayi kansa a cikin zuciyarsa yace wai shin anya kuwa a cikin duniya nake ba komai ne yasa yarima hulkas ya yiwa kansa wannan tambaya ba face ya tsinci kansa ne a cikin wani wuri mai dauke da kayan kawa na gaban kwatance kuma da ya dubi kasansa sai ya ga babu kasa babu shimfida tamkar akan gajimare yake tsaye kuma dayaga kafarsa ya yi tafiya sai yaji kamar akan daben lu’u lu’u yake tafiya shi dai wannan wuri ya kasance babbar fada wadda ta kayatu ainun ga kujeru na zinare ba adadi a kowacce kusurwar na fadar a bangaren gabas a tsakiyar fadar an girke wata kawatacciyar KARAGAR MULKI ta zinare da aka kawatata sai dai babu kowa akan karagar mulkin wani abun da ya kara daure masa kai kuma yayi matukar bashimamaki shine yadda yaga babu wata alamar kofa wacce za a iya fita ko shigowa cikin wannan fada daya tsinci kansa a cikinta kai tsaye yarima hulkas ya tunkari inda babbar karagar mulkin nan take a tsakiyar fadar yana zuwa daf da karagar mulkin sai ya risina ya sauke guiyoyinsa kasa ya kwashi gaisuwa a gareta tamkar dama ya ga wani akanta yana mai sunkui da kansa kasa cikin yanayi na girmamawa kwatsam sai yaji an bushe da dariya daga kan karagar mulkin.

.

A firgice yarima ya dago kansa yayinda Al amin na matsa baya

yayi arba da abinda yake yin wannan dariya ba wani bane  ya gani face Aljani Arwasul amsabur a cikin siffarsa ta ainihi Aljani Arwasul masabul ya kasance gabjeje kuma katon gaske mai matukar kwarjini da ban tsoro yana da kaho guda biyu akan tsakiyar kansa kunnuwansa biyu ne dogaye ne tamkar na zomo, amma idanunsa da hancinsa tamkar na bil adama suke

fuka fukansa manya ne don zai iya lullube gaba dayan jikinsa dasu hannayansa guda hudu ne haka ma kafafunsa, daga cibiyarsa zuwa kirjinsa siffar zaki ce dashi daga cibiyar kuma zuwa kafafunsa siffar dokine dashi, kaga kenan ya hada karfi biyu na zaki dana doki, tunda yarima hulkas yazo duniya bai taba ganin halittar data firgitashi ba ainun kamar Aljani Arwasul masadur Duk da cewa siyama ta taba bashi labarin aljanin amma bai kawo a ransa cewa shine wannan ba tunda bata siffanta masa kamanninsa ba cikin kaduwa yarima hulkas ya dubi Aljanin yace yakai wannan halitta wanene kai kuma akan wanne dalili ka daukoni daga can duniyarmu ta mutane ka kawoni wannan duniyar ta daban?

.

Lallai daka san gagarumin aikin dake gabana da baka rabani da iyayena ka kawoni wannan duniya ba koda yarima hulkas yazo nan a zancensa sai aljani.Arwasul masadul ya murtuke fuskarsa tamkar an aiko masa da sakon mutuwa kuma ya dakawa yarima hulkas Tsawa al amarin da ya kara firgita shi kenan ainun har ma yaji hantar cikinsa ta fara kadawa cikin alamun fishi Aljani Arwasul madadul ya dubi yarima hulkas yace wane irin yaro ne kai haka mara da a da har zaka rinka yiwa manya tambaya ?

.

Kamata yayi ka zuba ido ka ga yadda zamuyi da kai tukunna ka sani cewa mun daukoka ne domin mu taimaka maka bayan munyi maka jarrabawa ta tsawon kwana uku, koda jin wannan batu sai yarima hulkas ya zube kasa bisa guiwoyinsa cikin alamun tsoro da girmamawa yace kayimin afuwa ya shugabana idan ka rukeni anan har tsawon kwana uku ba karamar asara zanyi ba yanzu dai kaga gobene da safe yar uwata jaruma siyama za tayi wasanta na karshe da SADAUKI DARKUS a GASAR JARUMTAKA lallai ina son naga yadda wannan gumurzu nasu zai kasance Baya ga haka zamuyi wata gagarumar tafiya mai matukar darari nida…..

.

Caraf sai Aljanin ya tari numfashinsa yace na sani cewa kai da mahaifinka sadauki hailur da mahaifiyarka shadila tare dasu sarki hulbasu kuna son ku tafi neman HULAR LAMSARA to ka sani cewa jarrabawar da zanyi maka a cikin wadannan kwanaki uku indai har ka samu nasarar cinye su ina tabbatar maka zaka sami nasara abisa abinda zaku tafi nema ina son ka kwantar da hankalinka ka sani cewa kwana uku anan dai dai yake da jini daya na duniyarku kuma ka sani cewa nan kana inda kake kana cikin wata duniya ne daban dake cikin duniyoyin sama amma kuma zan saukar dakai izuwa taku duniyar domin ka fara fuskantar jarrabobinka, kafin yarima hulkas ya budi baki yace wani abu sai kawai yaji jiri ya kwasheshi kuma idanunsa sun lumshe, kawai sai ji yayi ji da ganinsa sun dauke dif ! 

.

Nan da nan hankalinsa ya gushe ya kasa gane halin da yake ciki Bayan cikar yan dakiku kadan kuma sai yaji komai ya dawo masa dai dai yana bude idanunsa ya tsinci kansa kwance a kasa bisa ciyawa a cikin wani kungurmin daji bayan ya dubi kowacce kusurwa na cikin wannan daji baiga Aljani Arwasul masadul ba kuma ya duba ko ina a jikinsa yaga ko wuka babu bare ya san cewa yana da wani makami wanda zai iya kare kansa dashi sai kawai ya mike tsaye yai shiru yana nazari da tunani, abin da ya fara fado masa a rai shine wai shin wacce irin jarawaba wannan aljani yake son yi masa har da zai kawoshi cikin wannan dokar daji ya ajiyeshi Anya kuwa wannan Aljani ba shi bane Aljani Arwasul masadul wanda yar uwata siyama ta bani labari?

.

Tabbas idan kuwa shine to lallai na yarda cewa taimakona zaiyi ba cutar dani zaiyi ba, koda gama aiyana hakan sai hulkas ya nufi gabas ya kunna kai izuwa cikin dajin kai tsaye ba tare da fargabar komai ba dajine mai dauke da manyan duwatsu dogayen bishiyoyi gami da koramu, tun da hulkas ya fara tafiya cikin wannan daji bai hadu da wani abu ba face kanana dabbobin daji irinsu birrai sai kuma kananun tsuntsaye amma ko dabbar datakai girman barewa bai gani ba haka dai yarima hulkas ya cigaba da tafiya a cikin dajin yana waige waige har tsawon sa a guda kwatsam sai yayi kicibis da wata gada a kwance male male cikin jini tana ta faman nishi tamkar ranta zai fita saboda yawan raunikan dake jikinta sannan kuma kafarta guda a karye take har ta fara kumbura kallo daya yarima hulkas ya yiwa gadar ya kau dakai har ya giftata zai yi tafiyarsa sai yaji tausayinta ya kamashi saboda ya tabbatar da cewa indai wannan jini na jikinta bai daina zuba ba mutuwa zatayi cikin gaggawa yarima hulkas ya dawo da baya ya tsugunna a gaban gadar yasa hannu ya yagi rigar jikinsa ya daure dukkan raunikan dake jikinta ya zamana cewa jinin ya daina zuba sannan sai ya mike tsaye da sauri ya ruga izuwa wata bishiya ya karo kirare yazo ya gyara karayar dake kafar gadar ya daureta.

.

A dai dai wannan lokaci ne hadari ya gangamo aka fara tsala tsawa da walkiya, koda yarima hulkas ya lura da irin yanayin garin ya gane cewa ruwa ne mai yawa zai sauko kawai sai ya sunkuya ya dauki wannan gada ya sabata a wuyansa ya ruga izuwa cikin dajin yana neman inda zasu fake, har sai da ruwan saman ya fara zuba sannan ya hango wani kogon dutse dan karami mara tsawo da fadi wanda baifi mutum uku ba kacal su iya shiga ciki kawai sai ya kunna kai ciki ya ajiye gadar a gefe daya shima ya zauna dirshan a kasa zaman sa keda wuya sai aka tsuge da ruwan sama mai karfin gaske tamkar da bakin kwarya tun safe aka fara wannan ruwa amma har goshin magariba ba a tsagaita ba nan fa yunwa da sanyi suka addabi hulkas da wannan gada babu shiri yarima hulkas ya mike tsaye ya karyo wadansu busassun itatuwa na wata yar karamar itaciyar sannan ya dauko duwatsu biyu a cikin kogon yayi kyastu dasu dakyar ya kunna wutar, nan da nan kogon yayi dumi amma sai yarima hulkas ya rinka yawan kallon wannan gadar yana kallon wannan dutar da ya kunna zuciyarsa na cewa dashi.

.

Ga nama kuma ga wutar gasa nama me zai hana ka yanka wannan gada ka fedeta ka gashe domin kayi maganin wannan yunwa da ta addabeka wata zuciyar kuma sai tace dashi A a ai tunda har ka ceci rayuwarta da farko bai kamata ka kasheta ba yanzu kawai kayi hakuri ai yunwa bata kisa face kwana ya kare

haka dai yarima hulkas ya mike tsaye da nufin ya fice daga cikin wannan kogon dutsen domin ya nemo musu abinda zasu ci shida wannan gadar, Kwatsam ba zato ba tsammani sai yaga wannan gada ta rikide ta zama Aljani Arwasul Masadul yana mai kyalkyala dariya….

.

Wash! a nan zan daka ta saboda ganin wannan Abin mamaki yasa na kas ci gaba Kafinnan karku manta da sunan Abubakar Saleh AlQuyramey cewa Mu kwana lafiya sai mun sake haɗuwa. 

Karanta Littafi>>> Tsatsuba Littafi Na Uku (3)

.

TSATSUBA

Littafi Na Bakwai (8)

Part B

Marubucin Littafin

Abdul azis Sani M/Gini

Posting by..

Abubakar Saleh AlQuyraemey

.

Kwatsam ba zato ba tsammani sai yaga wannan gada ta rikide ta zama Aljani Arwasul masadul yana mai Kyalkyala dariya, al amarin da yai matukar razana yarima hulkas kenan yaja da baya a firgice yana mai tokare jikinsa a jikin dutsen kogon yana mai takure jikinsa gami da zazzare idanu.

.

Koda ganin haka sai Aljani Arwasul Masadul yayi shiru ga barin dariyar yace Yaro kaci jarrabawar farko saura jarrabawa ta biyu kacal ! Sannan na cika Alkawarina na taimakonka a maimakon na cikasa sauran jarrabobi bakwai a gareka, ba don komai ba sai saboda wannan jarabawa ta farko dana yi maka tafi dukkanin sauran muhimmanci gama fadin hakan keda wuya sai aljanin ya bace bat tamkar bai taba wanzuwa a wajan ba al amarin da yai matukar fusata yarima hulkas kenan bai san sa adda ya takarkace ya kurma ihu ba ya kama naushin kogon dutsen da hannunsa har sai da yaji kamar yatsunsa zasu kakkarye sannan ya daina, ba komai ne ya fusata yarima hulkas ba face ganin irin rainin hankalin da wannan aljani yayi masa wato yazo masa a siffar wannan gada.

.

Tabbas inda ya san cewa shine daba zai taba taimakonshi ba kai ko kallonsa ma ba zaiyi ba balle har takai ga ya taimaka masa, haka dai yarima hulkas ya fito daga cikin wannan kogon dutse a jigace yana.layi kamar zai fadi kasa saboda yunwa.

.

Koda yayi yar gajeriyar tafiya sai yayi kicibis da wani lambu a gabansa cike da yayan itatuwa nunannu, kamarsu tuffa, inibi, ayaba, fasa dabur, baure , ruman da sauransu Ba tare da jin tsoro ba ko shakkar komai sai yarima hulkas ya kunna kai cikin wannan lambun abin ka damai jin yunwa da zuwansa sai

kawai ya kama cin yayan  itatuwan dake cikin lambun ba sassauci sai kace dabba wani ma idan ya gwawiya sau biya sai ya jefar ya tsinko wani ya kama ci saboda ganin abin a banza haka yarima hulkas yayi ta ci ya yan itatuwan nan har sai da yaci ya koshi kuma yayi barna mai yawa a cikin lambun wato ya zubar da wadansu yayan itatuwan a kasa ya tattakasu

bai sani ba faruwar hakan keda wuya kuma sai ya hango wata yar karamar korama a gefen lambun, kai tsaye yaje ya durkusa a gaban koramar wacce ke dauke da ruwa mai kyau garai garai ya sha ya koshi har da yin gyatsa kawai sai yaji motsi a bayansa a lokacin da yake dago kansa daga cikin koramat, kafin ya juyo yaga abin dake bayan nasa sai yaji an gabza masa wani mummunan naushi a wuya saboda karfin naushin sai da yayi sama sannan ya fado cikin wannan koramar ya jike sharkaff cikin tsanani fishi yarima hulkas ya waigo da sauri da

nufin ya ga wanda yayi masa wannan naushi ya mayar da martanin dukan da akayi masa amman sai ya kasa sakamakon ganin wanda ke tsaye a gabansa, ba wani bane a tsaye a gabansa face wata kyakkyawar yarinya ta gaban kwatance wacce shekarunta a duniya basu da yawa wato ko yarima hulkas din zai girmeta to da yan shekaru ne kadan ya girmeta ma tun da yarima hulkas yazo duniya bai taba ganin ya mace mai kyan wannan yarinya ba, a karon farko yana hada

idanu da ita yaji ya kamu da tsananin kaunarta fiye da komai dake wannan duniya kuma ya aiyana a cikin ransa cewa lallai idan wannan yarinya ta zama cikakkiyar budurwa sai ta zama sarauniyar kyawawa ta duniya gaba daya domin ba za a taba samun wata mace wadda ta kai ta kyau ba.

.

Yarinyar na sanye da kaya ne na fatar damisa riga da wando a kuibinta na dama daure a jikin cinyarta wata zabgegiyar siririyar takobi ce a bayanta kuwa kwanson kibiyoyi ne a sakale, hannunta baka ne da ta daga kibiya a jikinsa ta tabe zaren bakan tana mai saita kirjin yarima hulkas da shi , da yi masa alamar yana motsawa zata sakar masa harbi, gashin kanta dogo ne kuma baki sidik wanda ya zuba har kasan mazaunanta sai sheki da walwali yake, idanunta manya ne kuma farare kal kal tamkar ruwan madar hancinta kuwa dogone siriri a saman dan karamin baki tamkar da wuka aka yankashi yarinyar ta dubi yarima hulkas fuskarta a murtuke kuma ta daka masa tsawa tace wanene ya baka izinin ka shigo har cikin lambuna kayi mini irin wannan mummunar barna haka ko kuwa tsautsayin mutuwa ne ya kawoka.

.

Koda jin wadannan tambayoyi guda biyu daga bakin wannan kyakkyawar yarinya sai yarima hulkas ya tuntsure da dariya sannan yace yakai wannan Aljani ka daina tunanin cewa zaka iya yaudarata a karo na biyu in banda ma toshewar basira irin taku ta aljanu ta yaya za ayi na yarda cewa mutum zai iya rayuwa shi kadai jal a cikin wannan mugun daji bare ma kuma yarinya karama kamar wannan wadda ke tsaye a gabana? Ai wannan aiki sai daiku Aljanu.

.

Koda jin wannan batu sai yarinyar ta fusata a karo na biyu ta tari numfashin yarima hulkas tana mai sake daka masa tsawa tace kai shashasha kalleni da kyau ka gani ni mutum ce kamar

ka ba Aljan ba anan cikin dajin uwata ta haifeni muka rayu mu

biyu kacal har tsawon shekaru shida sannan ta mutu ta barni a haka na cigaba da rayuwa ni kadai Har na kawo i yanzu duk wata dabba ko tsuntsu ko aljan dake cikin wannan daji a karkashin ikona yake amma kaine mutum na farko da na taba ganin yazo har nan inda nake shinka taba haduwa da Wani Aljani wai shi Arwasul Masadul ?

.

Koda jin wannan tambaya sai jikin yarima hulkas yayi sanyi kuma ya kamu da tsananin mamaki ya dubi yarinyar yace ke ya akayi kika sanshi wacece ke kuma menene dalilin zamanku a cikin wannan daji keda mahaifiyar taku har ta haifeki a cikin sa

koda jin wadannan tambayoyi sai yarinyar taja bakanta ta kara tabeshi tana mai kara saita kirjin yarima hulkas tace maza ka gaggauta amsa mini tambaya ta ta farko a gareka kafin kibiyata ta huda kirjinka saye ya baka izinin ka shigo har nan cikin lambuna kayi mini barna haka.

.

Koda jin wannan tambaya sai yarima hulkas ya tsugunna kasa bisa guiyoyinsa cikin alamun kaskantar dakai yace kiyi min afuwa yake wannan ma abociyar kyawu da kwarjini kiyi sani cewa yunwace ta galabaitar dani har ta sani nayi miki irin wannan barna gami kuma da rashin sanin cewa akwai mai wannan lambu, koda jin wannan batu sai yarinyar ta sauke kwarinta kasa sannan ta nufo kansa gadan gadan tana zuwa daf dashi sai ta sa kafarta ta doki kirjinsa saboda karfin dukan sai da ya kife kasa yana mai aman jini, kawai sai yarinyar ta durkusa a gabansa ta kamo habarsa da hannu daya ta dago kansa sama ta dubeshi tace wannan shine hukuncin barnar da kayi min yanzu babu bashi a tsakanina dakai, saboda haka yanzu sai ka bani labarinka ta yadda akayi ka sami nasarar zuwa wannan daji idan naji labarinka ya kasance zamu iya taimakon juna nida kai don na san bazaka rasa wani buri ba wanda ya gagareka kamar yadda nima nake da nawa burin.

.

Sa adda yarinyar tazo nan a jawabinta sai yarima hulkas ya mike cikin tsananin takaici ya tuno da cewa wannan shine karo na biyu da mace jaruma kuma yarinya ta nuna masa tafishi karfi da jarumta yar uwarsa jaruma siyama ce ta farko saikuma wannan bakuwar jaruma wacce basan komai a kanta ba yarima hulkas ya goge jini dake kan lebensa sannan kuma ya dan karkade kurar jikinsa ya dubi yarinyar cikin nutsuwa yace ta yaya zan iya baki yardata har na sanar dake koni waye ba tare dake kin fara gabatar min da kanki ba babu mamaki ke wakiliyar abokan gabata ce.

.

Koda jin wannan batu sai wannan yarinya ta bushe da dariya sannan tace wanda ya ajiyeni anan bashi da abokin gaba ko daya a cikin fadin wannan duniya tunda baka da yarda shikenan ni yanzu zan fara gabatar da labarina amma ba anan ba ka biyoni muje gidana tana gama fadin hakan sai ta juya tabi wani surkuki mai yar duhuwa shi kuwa hulkas sai ya kama binta da sauri yana mai mamakin yadda za a iya samun gida a cikin wannan kasurgumin daji, yar gajeriyar tafiya sukayi suka iso wani wuri daban mai ban al ajabi, wadansu irin duwatsu ne wadanda kallo daya mutum zai yi musu ya san cewa sassakesu aka yi  akayi gida a jikinsu mai dauke da katuwar fada ba wai haka suke ba tun fil azal abinda ya kara daurewa yarima hulkas kai shine shin wane gwanin iya gini ne yayi wannan gida haka, Tabbas wannan aiki yafi gaban aikin bil adama sai dai aljanu aljanun ma sai dai idan sune sarakan gini

na duniya shi dai wannan dutse asali kato ne tamkar tsauni amma sai gashi an fafeshi an yanyankashi kuma an fikeshi kai kace kasa ce aka kwaba akayi tubali sannan aka gina, ta kan wata matattakala yarinyar tabi da yarima hulkas suna fara tafiya akan matattakalar wacce ta nufi cikin wata katuwar kasaitacciyar fada mai wadansu manyan dakaru na aljanu ma abota kwarjinin gaske dauke da muggan makamai su da yawa babu adadi suka bayyana suna masu tokare kofar shiga fadar suka raste suka baiwa yarinyar nan hanya ta shige suna masu dukar da kawunansu kasa don gaisheta amma yarima hulkas na isowa daf dasu sai suka tare masa hanya suka zare takubbansu cikin razana da firgici hulkas yaja da baya su kuwa aljanun sai suka yi caa izuwa kansa da nufin su gididdibashi, cikin hanzari suka ja da baya suka koma inda suke tsaitsaye yarinyar nan ta dawo da baya ta dubi dakarun gaba dayansu tace wannan bakona ne na musamman, koda jin haka sai gaba dayan dakarun Aljanun suka risina suka gaishe da hulkas kuma suka dare suka bashi hanya, suna shiga cikin fadar sai yarima hulkas ya rude kuma ya dimauce domin bai taba ganin fadar da ta kawatu kamar wannan fada ba, sai dai babban abin bakin cikin shine fadar kango ce babu bafade ko guda daya a cikinta bare ma a sami talakawan da za a mulka kai tsaye wannan yarinyar ta nufi kasaitacciyar karagar mulkin dake cikin fadar wacce akayita da zallan Dutsen lu’u lu’u aka kawata shi da adon sarauta Da isarta kan karagar mulkin nan sai ta zauna tana mai harde kafa daya bisa dayar sannan tayiwa yarima hulkas nuni da ya zauna akan wata kujera dake daf da karagar tata ba tare da gardamar komai ba yarima hulkas ya zauna yana mai fuskantarta zamansa keda wuya sai yarinyar ta tafa hannunta sai ga tambulan na zinare tare da Kofuna sun bayyana a gaban su akan iska babu mai rike dasu kawai sai tambulan din ya karkata kansa ya zuba ruwan inibi a cikin kofunan nan biyu kofi na farko ya tafi ga yarima hulkas ya tsay dai dai hannunsa yarima hilkas ya dubi yarinyar cikin alamun tsoro ita kuwa sai tayi masa murmushi tace karbi mana kasha

idan so nake na zutar dakai ai tun kafin muzo nan zan cutar dakai din.

.

Koda jin haka sai yarima hulkas ya saki jikinsa ya karbi kofin ya kurbi ruwan inibin, a dai dai wannan lokaci ne itama yarinyar ta kurbi nata ruwan inibin shima kuma sai ya kurbi nashi ruwan inibin sannan tayi gyarar murya gami da gyara zama kuma ta

dubi yarima hulkas cikin nutsuwa ta ce yakai wannan bako yanzu saika saurareni da kyau domin kaji labarina

            … ….   …..   …

DA FARKO DAI sunana RULAIYA IBINI AMSAR IBINI WARHAS,

Kuma mahaifina ya kasance babban attajiri a birnin kisra, amma tun mahaifiyata na dauke da cikina wata uku aka kasheshi sannan kuma wanda ya kasheshi din yayi yunkurin kashe mahaifiyata sau goma sha daya amma bai samu nasara ba ita kanta mahaifiyar tawa tayi matukar mamakin yadda akayi take tsira da rayuwarta a duk sa adda aka kawo mata hari caraf sai yarima hulkas ya tari numfashin Rulaiya yace wane ne wanda ya kashe mahaifin naki kuma saboda me ya ke son kashe mahaifiyar taki.

.

Koda jin wannan tambaya sai rulaiya tayi tsaki tace hanzarin me kake yi haka ka bini a sannu mana zakaji komai a cikin wannan labari da nake baka kamar yadda na gaya maka baya a gaba dayan birnin kisra babu attajiri da kai mahaifina tarin dukiya da karfin arziki na fatauci, cinikin bayi da na makaman yaki duk wani isashshen sarki dake nahiyarmu mahaifina yana

da kyakkyawar alaka dashi saboda yana yi musu matukar biyayya kuma a duk karshen wata yana aika masa da kyautar bayi da dukiya don haka babu kasar da mahaifina baya zuwa don gabatar da fataucinsa ban da sarakai ma hatta mashahuran bokaye wadanda suka yi shuhura a duniya suna da kyakkyawar mu amala da mahaifina kuma suna taimakonsa da sirrinakan tsafi shi kuma yana yi musu alheri mai yawa, akwai wadansu amintattun rantsatstsun dakaru guda dubu daya wadanda ke baiwa mahaifina kariya ta musamman a duk sa adda zai yi tafiye tafiyensa na fatauci da kai ziyara izuwa ga sarakai ko matsafa na duniya, su dai wadannan dakaru kaifi da tsini baya tasiri a jikinsu kuma fiye da shekaru goma baya suke yiwa mahaifina aiki ba a taba shiga masifar da suka kasa kareshi ba ko dukiyar sa.

.

A duniya babu abinda mahaifina yake so sama da mahaifiyata

mahaifiyata ta kasance yaga shugaban yan kasuwar birnin hindu kuma masana da masu bincike sun tabbatar da cewa a zamanin da take budurwa babu wata ya mace mai kyanta kafin mahaifina ya sami nasarar auranta sai da yayi fama da abokan hamayya har ma ya kusan rasa rayuwarsa in ba don ma yana da kyakkyawan tsari ba na bokaye da tuni ya hallaka, A duk sa adda mahaifina ya ziyarci isassun bokayansa suna yi masa gargadi akan cewa ya cigaba da boye amaryarsa kuma kada ya kuskura ya rinka shiga manyan birane tare da ita, bisa wannan dalili ne ya zamana cewa duk sadda mahaifina zaiyi tafiya tare da mahaifiyata koyaushe fuskart da jikinta a lullube suke sosai ta yadda mutum ba zai iya ganin siffarta da kamanninta ba kuma in dai wani babban birni za a shiga to saidai a yada zango a bayan gari in yaso shi da tsirarun dakarunsa tare da hajarsu su shiga cikin garin ya bar mahaifiyata a hannun sauran dakarun nasa, A cikin irin wannan yanayi ne watarana mahaifina ya tunkari birnin wani gawurtaccen sarki wanda ake kira da suna SARKI SHARDAS shi dai wannan sarki anyi ittifakin cewa a duniya kaf babu wani jarumi wanda ya fishi karfin damtse iya yaki da kuma karfin sihirin tsafi, shi kansa mahaifina ba a son ransa zaije garin wannan sarki ba sai don kawai saboda ya amsa gayyatarsa ne domin gaba dayan mashahuran attajiran duniya sarki shardas ya gayyata domin ayi gasar siyen wani gida na musamman wanda aka ginashi a tsakiyar wani kogi a wannan lokaci shi dai wannan gida an ginashi ne da zallan hadin duwatsu uku, wato lu’u lu’u zinare jauhar da zubarjadu shi dai gidan ya sami shekaru goma sha biyu da ginawa amma ba a taba shigarsa ba, a tsawon wadannan shekaru sarki shardas yana tallaka gidan ne ga manyan sarakunan duniya da manyan fatake yana cika baki akan cewa tun daga farkon wanzuwar duniya kawo iyanzu lokacin ba a taba gina gidan da yayi wannan gida nasa kyau, kawatuwa da kuma tsari ba don haka a ranar da za a budeshi an yiwa kowa izinin yaje ya shiga ciki domin ya baiwa idanunsa abinci, kuma wanda duk ya sayi gidan da farashi mafi tsoka shine zai mallakeshi, kuma shi kansa sarki shardas din ya shiga gasar siyen wannan.gida nasa kafin sarko ko Attajiri ya shiga wannan gasa sai ya ajiye dinare miliyan daya tukunna a cewarsa wai hakan shine shaidar cewa ya isa ya shiga wannan gasa, an ce a haka ma sarki shardas ya tara miliyoyin dinaren da bai taba zaton zai Samu ba, A tunanin sarki shardas zai yi amfani da wannan gasa ne ya talauta gaba dayan sarakunan nahiyar da attajirai domin ya kasance duk karfin arzikinsu ya dawo hannunsa, shi kuwa wannan gida da aka gina akan tsakiyar kogi sai da aka shafe shekaru goma sha shida ana gininsa ba wai mutane ba hatta aljanu tsegumin gidan suke suna ta yadashi a duniya, lokacin da aikin ginin yayi nisa sai da sarki shardas ya sare, domin gani yayi tattalin arzikinsa na neman karyea, bisa dole ya kara ninka harajin da mutane ke biya a kasarsa kuma ya tsananta farautar bayi da kai harin sumame ana kwace dukiyoyin jama a wata nahiyar ana maishe su bayi.

.

A haka dai aka samu aka kammala wannan kasaitaccen gida

na gaban kwatance, bayan an kammala ginin gidan ne sarki shardas yasa rana ta wannan gasa wacce a ranar za ‘a bude wannan gida wohoho tun kafin ranar tayi da tsawon sati hudu birnin nasa ya cika ya tumbatsa da baki daga ko’ina na duniya, yazamana cewa ko ruwan sha mutum ke siyarwa a garin yana samun kudade masu yawa a wannan lokaci kudin shiga birnin ma da aka samu ba’a taba samun kamarsu ba Al amarin mahaifina kuwa wato Attajiri Amsar…………

.

Wow Domin jin yadda zata kasance mu hadu a part na gaba

amma kafinnan nidinne dai.

.

Abubakar Saleh AlQuyraemey nake cewa mu kwana lafiya.

Karanta Littafin>>> Tsatsuba Littafi Na Biyu (2)

.

TSATSUBA

Littafi Na Bakwai (8)

Part C

Marubucin Littafin

Abdul azis Sani M/Gini

Posting by..

Abubakar Saleh AlQuyraemey

.

Al’anarin Mahaifina kuwa wato attajiri amsar, a cikin daji ya yada sansani da tazarar kwana uku a sannan ne ya debi dakaru dari biyu kacal ya bar ragowar dari takwas domin suyi gadin mahaifiyata.

.

Koda yazo zai yi sallama da mahaifiyata sai ta fashe da kuka tace yakai mijina ban taba rabuwa dakai ba tsawon yini guda amma yanzu gashi zaka tafi halartar wannan gasa har tsawon kwanaki bakwai lallai zan kasance a cikin kewarka da begenka, ka sani cewa na sami labari cewa wannan gida da sarki shardas ya gina a duk fadin duniya a yanzu babu kamarsa a kyau da kawatuwa lallai ina yi maka fata da addu ar ka mallakeshi, kuma lallai ina son naga wannan gida da idanuna koda kuwa ba zan sami damar shiga cikin sa ba sa adda mahaifyata tazo nan a jawabinta sai nan take idanun mahaifina suka ciko da kwallah ya dubeta cikin alamun tsananin takaici yace ki gafarceni ya masoyiyata kiyi sani cewa wannan ne karo na farko da kika tambayeni abinda ba zan iya baki shiba a cikin wannan duniya ki sani cewa idan na kuskura na shigar da ke cikin wannan birnin karshen zamana dake yazo bare ma har na kaiki kiga wannan kasaitaccen gida wanda za ayi gasa a kansa, wannan shine kashedin da bokayena suke yi mini idan kuma kina son mu rabu ne to shikenan sai na kaiki kiga wannan gida.

.

Koda jin wannan batu sai mahaifiyata ta rungume attajiri amsar ta fashe da matsanancin kuka tana mai kankameshi a kirjinta tace ai ko duniyar nan kaf za a bani in dai za a rabani dakai bana bukatarta, koda jin haka sai farin ciki ya lullube mahaifina sai da sukadan jima a kankame da juna sannan ya janye jikinsa daga cikin nata sukayi sallama ya hau kan dokinsa, kafin ya tafi sai da ya dada jan kunnen dakarun nasa su dari takwasa da zasu yi gadinta da kuma kuyangi uku da zasu yi mata hidima yace lallai su tabbatar da cewar wani abu bai kusanceta ba bare ya cutar da ita nan dai mahaifina attajiri amsar tare da dakaru dari biyu suka nufi cikin birnin sarki shardas , mahaifiyata da sauran jama arsa suka bisu da kallo har sai da suka ga sun kule.

”      ”         ”

BIRNIN ya ciki ya tumbatsa da al uma duk inda ka duba babu abinda zaka gani face kawunan bil adama rututu babu masakar tsinke, sai da ta kai cewa an rasa gidaje na haya inda ake saukar baki, dole jama a suka rinka kwana a kasuwa wasu ma a gefen gari suka rinka kafa tantuna sai dai siye da siyarwa ya shigo dasu cikin birnin gidan sarautar sarki shardas kuwa ya cika da manyan sarakuna manyan attajirai manyan bokaye da manyan yarumai kuma kowannansu an bashi masauki mai daraja kuma an girmamashi. A rayuwar sarki shardas yana son zama tare da wadannan mutane guda hudu wato sarakai, attajirai bokaye da jarumai, har izuwa safiyar ranar da za ayi wannan gasa hankalin sarki shardas bai gama kwanciya ba duk da cewa shi ya tara dukkanin sarakunan nahiyar da kuma amsu gayyata.

.

Al amarin daya sa wazirin sarki shardas ya fahimci cewar sarkin nasu yana cikin wata damuwa don, haka sai ya dubeshi cikin girmamawa yace wai shin menene yake damunka ?

.

Naga sai kallon kofar fada kake yi shin akwai wanda kake son ganin zuwansa ne, sarki shardas yayi ajiyar zuciya sannan yace ai banga sarkin attajiran ba attajiri Amsar ibn Warhas, anya kuwa zai amsa wannan gayyata tawa, koda jin wannan batu sai waziri ya dafe kirjinsa kuma ya zazzaro idanu yace, haba ya sarkin sarakuna , kaine fa zaki uban dawa kuma kaine dodon maza sa gudu maganin ki gudu yanzu kai a tunaninka akwai wani daya isa a wannan duniya da zai ki amsa gayyatarka, kome mutm yake takama dashi kafishi, kuma duk wanda yaja dakai sai yakai kasa

sarakuna nawa ne suka mutu a dalilin bakincikin da ka kunsa musu bokaye nawa ne suka jarraba karfin tsafinsu akanka suka mutu. Attajirai masu tarin dukiya nawa ne ka talautar dasu ai ina tabbatar maka da cewar ajali ne kadai zai hana attajiri amsar halartar wannan gayyata taka kuma ko don ma ya nuna matsayinsa akan sauran attajirai  ya amsa gayyatar ka amma abin tambayar shine wai shin menene dalilin da yasa ka damu da zuwan attajiri Amsar ibini warhas ?

.

Koda jin wannan tambaya sai sarki shardas yayi dan guntun murmushi sannan yace lallai ina son attajiri amsar yazo wannan gasa saboda sai yafi kowa siyan wannan gida nawa da daraja, to amma fa ina tsoron abu guda daya shin baka ganin cewa yana da kudin da zai iya siyen wannan gida nawa har ni kuma ya hanani mallakarsa ?

.

Waziri ya gyada kai yace haba ya shugabana yanzu ashe akwai attajirin da zai fika kudi a wannan nahiya tamu ai a ganina ko nawa attajiri amsar ya siyi wannan gida kai kuma sai ka kara kudinka ko ka ninka akan nasa sau talatin tunka ka san cewa babu asara a cikin aikata hakan ka tuna fa cewa daga cikin dokar wannan gasa shine duk kudin da mutum ya taya wannan gidan ba za a dawo masa dasu ba, kaga kenan komai yawan kudaden

da aka tara naka ne kai kadai, koda jin wannan batu sai farin ciki ya lullube sarki shardas ya kama yin murmushin murna yana mai cigaba da kallon bakin kofar fada sannan ya dubi wazirinsa yace gaba dayan manyan sarakuna da attajiran da na gayyata sun iso tare da iyalansu tun tsawon yan kwanaki kafin zuwan wannan rana ta yau me ya sa shi attajiri amsar baizo da wuri ba bare da iyalansa alhalin na dade ina son naga matarsa saboda naji ance agaba dayan birnin hindu babu mai kyanta, abinda yake bani mamaki shine duk karfin shirin nan nawa na tsafi na kasa ganin hoton siffar matar tasa a cikin madubin tsafina kuma a iya bincikena nakasa ganin ranar da zan ganta bisa wannan daliline yasa na ke dan shakkar al amarin attajiri amsar ibn warhas, domin lokacin dana fara zurfafa a cikin binciken sirrinsa sai na gano cewa yana samun kariya ne daga wani takadarin aljani wanda ni kaina ban sanshi ba kuma na kasa gano ko waye shi hatta bokana abin dogarona ya kasa gano min aljanin da yake baiwa attajiri amsar kariya, sarki shardas na zuwa dai dai nan a jawabinsa kwatsam sai ga attajiri amsar ibn warhas ya shigo cikin fadar dakaru dari biyu kacal nakewaye dashi.

.

Da shigowar attajiri amsar cikin fadar sai gaba dayam jama ar dake wajan suka mimmike tsaye suka rinka dukawa suna gaishe da attajiri amsar saboda kwarjininsa tamkar ya kasance wani babban sarki, tufafin dake jikinsa ma babu wani basarake a wajan daya sanya mai kyansa da tsadarsu, hatta shi kansa sarki

shardas din kuwa kai ko mutum bai san attajiri amsar ibn warhas ba yana ganinsa dole ne ya girmama shi saboda tsabar kamalarsa da kwarjininsa ko shi kansa sarki shardas wanda kowa ke tsoronsa da yi masa biyayyar dole ba shi da irin wannan kwarjini da kamala na attajiri amsar don hatta manyan fadawan

sarki shardas basu san sa adda suka rinka rugawa izuwa ga attajiri amsar suna kama hannunsa suna sumbata ba haka ma sauran sarakunan da ke cikin fadar domin kowa gani yake kamar idan har ya sami nasarar sumbatar hannun attajiri amsar ya sami tabarrakin da shima zai zamo gagarumin attajiri kamar attajiri amsar din, koda sarki shardas yaga yadda ake girmama attajiri amsar sai ya kamu da tsananin kishi gami da matukar baki ciki ya fara tunanin cewa babu abinda yafi attajiri amsar dashi face jarumtaka, tunda yana da mace mai kyan da bashi da kamarta kuma yana da dukiyar da wata kila tafi tasa yawa bayan attajiri amsar ya gama gaisawa da manyan mutane wadanda suka yi ta shan gabansa suna hanashi zuwa wajan sarki shardas sai ya kukuta da kyar ya isa inda sarki shardas ke zaune bisa karagar mulki yana zuwa daf dashi sai ya zube kasa wanwar ya kwashi gaisuwa tamkar zaiyi masa sujjada don girmamawa al amarin da yai matukar baiwa kowa mamaki kenan shi kuwa sarki shardas sai farin ciki ya lullubeshi yaji kansa yayi nauyi don haka sai ya mike tsaye daga kan karagar sa ya taka matattakalar ya sauko har kasa har gaban attajiri amsar ya kama kafadun sa ya tasheshi tsaye ya rungumeshi cikin tsananin farin ciki tamkar wanda yaga dan uwansa na jini sannan kuma sai ya kama hannun sa ya jashi zuwa kan karagar mulki suka zauna tare akan karagar, Al amarin da yai matukar baiwa kowa mamaki kenan domin ba a taba ganin sarki shardas ya girmama wani mutum ba kamar haka yadda ya yiwa attajiri amsar nan take sarki shardas ya bada umarni kuyangi suka shigo cikin fadar dauke da abinci da abin sha irir iri na musamman irin wanda ba a taba kawowa ba tun daga ranar da aka fara saukar baki, sai da aka gama ciye ciye da shaye shaye ya zamana cewa kowa ya sami nustuwa sannan sarki shardas ya mike tsaye a lokacin da fadar tayi tsir tamkar mutuwa ta gifta yayi gyaran murya yace yaku manyan baki kuyi sani cewa yanzu taro ya cika tunda sarkin Attajirai amsar ibn warhas ya iso saboda haka yanzu ba tare da bata lokaci ba zamu dunguma gaba daya mu tafi izuwa inda wannan gida yake wanda nayiwa lakabi da suna DARUL DAULAT !

.

Duk wanda ya san zai shiga wannan gasa to ya tafi da dukkan shirinsa amma yanzu za a fadi dokoki uku na shiga wannan gasa, doka ta farko itace dole ne kowanne sarko ko kowanne attajiri ko boka ko jarumin da ya amsa gayyata ya shiga wannan gasa kuma duk kudin da ya zuba a gasar ba za a dawo masa dasu ba walau yayi nasara ko bai yi ba doka ta biyu itace idan aka shiga cikin wannan gidan gasa babu wanda zai fito har sai an kammala kuma kowa ya kwantar da hankalinsa domin an tanaji masauki da isashshennabincin da kowa zaici har a kammala, doka ta uku wacce itace ta karshe itace duk wanda ya lashe wannan gasa dole ne ya baro kasarsa ya dawo wannan gida da zama tare da iyalansa har izuwa karshen rayuwarsa, koda sarki shardas yazo nan a zancensa sai hankalin gaba dayan masu gasar ya dugunzuma ainun musamman attajiri Amsar domin wannan doka ta karshe ba karamar tayar masa da hankali tayi ba

.

Nan take ba tare da bata lokaci ba aka fito daga cikin fada aka debo jakunkunan dinare aka loada akan dawakai da rakuma da alfadarai sarki shardas ne da kansa yamjagoranci gaba dayan yan gasar kowa dakarunsa. Na bashi tsaro da kariya aka nufi bakin kogi inda gidan Darul Daulat yake sauran jama ar gari kuwa sai da wannan zuga tayi gaba da tsawon rabin sa’a sannan aka sa dakaru suka yi musu rakiya tafiyar kusan rabin sa a akayi aka iso bakin katon kogin dake bayan gari tun daga nesa hasken gidan darul daulat ya fara dallare idanun mutane kuma tsananin girman gidan da kyawunsa ya dimauta kowa hatta su attajiri amsar kuwa duk da cewa gidan a can nesa yake a tsakiyar kogi amma kowa ya firgita da ganin irin gini da akayi masa a bakin tekun an ajiye manyan jiragen ruwa sama da guda dari wadanda za a shiga a ketare kogin a isa gidan na sarakai , attajirai da wadanda suka isa sannan kuma akwai kwale kwale kimanin guda dubu na talakawa da zuwan su sarki shardas bakin tekun sai kowa ya sauka daga kan dokinsa suka rinka shiga cikin jirgin ruwan jirgin sarakai daban haka mana na attajirai da sauran bokaye da jarumai ko kyakkyawan motsi sarki shardas baya barin attajiri amsar yayi ma ana baya yarda yayi nesa dashi don gudun kada wani tsautsayi ya rabasu lokacin da jiragen ruwan suka yi nisa a cikin kogin suka kusanci tsibirin da aka gina gidan darul daulat sai kowa ya sake cika da tsakanin mamaki ba komai ba sai domin ganin tsananin girman nasa ya kai rabin birnin gaba daya na sarki shardas abin da yafi daurewa mutane kai shine’ wai shin ta yaya aka iya gina wannan gagarumin gida ? 

.

Tabbas aikin ginin wannan gida yafi karfin ace mutane ne sukayi shi dai sai aljanu aljanun ma sai dai idan wadanda suka gina birnin farisa ne suka yi ginin wannan gida nan fa kowa ya zama cikakken dan kauye aka rinka wangame baki ana kallo wasu ma basu san sa adda suka fara dalalar da yawu ba sai da gaba dayan jiragen suka iso bakin gabar kogin daf da kofar gidan sannan kowa ya fito daga cikin jirgin aka bi sarki shardas a baya, ita kanta kofar wannan gida inda za a cireta a baiwa mutum ta isheshi gudanar da sauran rayuwarsa ta duniya domin jarine babba saboda anyi tane da zallan dutsen lu u lu u mai tsawo da kaurin gaske gami da fadi inda karti dubu zasu taru ba zasu iya daga kofar sama ba saboda nauyinta su kansu aljanun da suka kerata sai da aka zabo majiya karfi arba in sannan suka iya dagata sama suka kafata a jikin ginin, nan take sarki shardas ya zaro wata kuba ta zinare ya mitsitsiya kuma siririya ya zurata a cikin kofar mukulli, shigar kubar keda wuya sai aka ji sakata na zare kansu, wani zagayayyen mukulli mai kauri da tudu ya rinka zagaya kansa a tsakiyar kofar har sai da ya kewaya sau goma sha biyu sannan sakatun suka gama zarewa duka, take kofar ta bude wanwar da kanta, a dai dai wannan lokaci ne sarki shardas ya waigo cikin murmushi ya dubi gaba dayan yan gasar yace duk wanda ya lashe wannan gasa shizan damkawa kubar wannan gida, yana gama fadin haka sai ya zura hannunsa cikin kofar mukullin ya zare kubar ya zurata a cikin Aljihun wandonsa sannan ya kama hannun attajiri Amsar ibn warhas yaja shi suka kunna kai izuwa cikin wannan gida na darul daulat, take suma sauran, sarakai Attajirai da jaruman gasar suka rufa musu baya

Wohoho !! An dade ana bautawa kasa anyi mata ado da dukiya !

.

Duk wanda ya sanya kafarsa ya taka lu’u lu’un da aka shinfida a kasan gidan ya ga yadda ko ina ya kasance fes fes ! Babu ko kura ko guda daya bare yanah, sai ya cika da al’ajabi kai kace kullum akwai hadimai sama da miliyan goma masu share ko ina da gogewa alhalin babu wata halitta guda daya mai rai a ciki ba tare da wani bata lokaci ba sarki shardas ya wuce kai tsaye izuwa cikin wani babban falo na gidan wanda ya ninka fadarsa sau goma a girma da kawatuwa…

Nima kuma sai nabishi a bayaaaa.

Abubakar Saleh AlQuyraemey zan dakata Anan saikuma Allah ya kaimu Jibi zamu cigaba.

Karanta Littafin>>> Tsatsuba Littafi Na Huɗu (4) 

TSATSUBA

Littafi Na Bakwai (8)

Part D

Marubucin Littafin

Abdul azis Sani M/Gini

Posting by..

Abubakar Saleh AlQuyraemey

.

Ba tare da wani bata lokaci ba sarki shardas ya wuce kai tsaye izuwa cikin wani babban falo na gidan wanda ya ninka fadarsa sau goma a girma a ƙawatuwa hatta kujerun da shimfidar dake cikinsa babu wanda ya taba ganin makamantansu, duk yawan jama ar da suka halarci wannan gasa suna shiga cikin wannan falo sai suka zama yan kadan tamkar an sanya kwayar gero guda daya jal akan faranti, har izuwa wannan lokaci sarki shardas na rike da hannun attajiri amsar ibn warhas, shi kuma attajiri Amsar yana dogara wani dan karamin kwagiri na zinare dake hannunsa, kwagiri ne na zinare wanda aka kawatashi da adon sarauta, irin sane kwagirin da manyan sarakai ke dogarawa yayin da suke tafiya don kawata kwalliyarsu, kai tsaye sarki shardas yaja attajiri amsar suka je suka zauna akan wata luntsumemiyar doguwar kujera mai daraja, shi kuwa wazirin sarki shardas tare da sauran fadawansa sai suka rinka kai sauran manyan baki izuwa mazaunin da ya dace dasu.

.

Kafin kowa ya zauna sauran talakawa sun iso a cikin kwale kwale dakaru na shigowa dasu suma ana zaunar dasu a inda ya dace duk a cikin wannan babban falo sai da kowa ya gama zama sannan sarki shardas ya mike tsaye yayi jawabin farinciki na ganin wannan rana gami da godiya ga dukkanin manyan baki da suka amsa gayyata sannan yace  yaku jama ata ina mai sanar daku cewa inda zan jagoranceku mu zagaya cikin wannan gida domin muga ko ina da ina kuma muga duk irin daular da aka shirya a cikinsa da sai mun shafe a kalla tsawon kwaanaki bakwai bamu gama shiga kowanne daki da kowacce fada ba.

.

A cikin wannan gida na darul daulat akawai dakuna guda casa’in da tara sannan akwai fadoji guda arba in kowacce fada guda ta

ninka fadata sau talatin a girma, akwai kasuwa da asibiti a cikin wannan gida kuma akwai gidajen gona guda arba in da bakwai Sannan lambu na shakatawa kala tamanin da bakwai , duk wanda ya lashe wannan gasa ya mallaki wannan gida to a ranar da ya tare a cikinsa ne hadiman Aljanu dubu dari tara da casa in da tara zasu fara kular masa da gidan, sauran hadimai na aljanu kuwa ya nemo iya adadin da yake bukata. Yanzu take ba tare da bata wani lokaci ba zamu fara wannan gasa kuma ta kaina za a fara don haka ni na bude wannan ciniki da dinare miliyan uku

ga kudina lakadan yanzu zan dankasu a hannun alkalan Kasa !!?

.

Sarki shardas na gama fadin hakan sai ya tafa hannunsa nan take hadimai sukaje can wajen kofar gidan suka fara dauko buhunhunan dinare daga kan dawakai da rakuma na sarki shardas suna shigowa dasu suna zubesu a tsakiyar wannan babban falo har sai da suka ajiye jaka talatin wato kowacce jaka na daure da dinare dubu dari.

.

Koda ganin wannan al amari sai sarakai da attajirai suka kama yin murmushi saboda sun raina kudin da sarki shardas ya fara bude wannan gasa dasu duk kuwa da cewa kudade ne masu yawan gaske sun ishi talaka iya rayuwarsa koda sarki shardas yaga yadda sarakai da attajirai keyin murmushin murna don ganin suna da ninkin kudin da aka fara gasar dasu sau da yawa sai yayi dariyar mugunta a cikin ransa yace a zuciyarsa Uhm ! Ai sai miya ta kare sannan ake sanin maci tuwo muje zuwa wai mahaukaci yahau kura, tsawon yan dakiku sai falon yayi tsit ba a sami wanda ya sake taya gidan ba har sai da sarki shardas ya sake budar baki yace, wai shin babu yan kasuwa ne a wannan waje ? 

.

Koda jin wannan tambaya sai sarkin birnin misra yace ya ninka wannan kudin da sarki shardas ya siyi gidan sun koma dinare miliyn dubu shida take aka kawo kudin aka zube a gaban jama a

daga nan ne fa kowa ya sami bakin magana sai da sarakai da attajirai dari uku suka ninka kudin kuma aka kawo kudaden aka zube a tsakiyar fadar ya zamana cewa yan gasar mutum dubu uku da doriya gaba dayansu kowa ya zuba kudinsa saura mutum daya ne jal bai sa ba ba wani bane fwannan mutum guda da ya rage ba face ATTAJIRI AMSAR IBN WARHAS wanda har izuwa wannan lokaci ba a daina kawo rakuma da dawakan dake dauke da dukiyarsa izuwa bakin kofar wannan gida na darul daulat ba.

.

Kaji Manya Hm dama ance ta safe ta yara ce Ai amma kowa an gama kawo tasa dukiyar sai ta sarki shardas take ta bayan tasa, kafin a gama shigo da dukiyar wacce ta ninka duk ta sauran attajiran gasar dare ya raba a sannan ne fa gaba dayan sarakunan da attajiran suka tsorata ainun da al amarin Attajiri amsar suka fara tunanin cewa Aljanu ne ke sato dukiya daga bangarorin duniya suna kawo masa, haka kuma a sannan ne suka tsinke da al amarin sarki shardas ma domin har a sannan shima ba a gama shigowa da dukiyar daya tana da ba don wannan gasa

.

Koda sarki shardas ya fahimci cewa dare ya raba kuma kowa ya gaji ana jin yunwa da barci sai ya mike tsaye yace to a halin yanzu dai babu wanda yafi attajiri amsar farashi na wannan gasa, kuma tunda jama asun gaji kuma gashi dare ya raba to za a tsayar da wannan gasa domin akai kowa masaukinsa yaci abinci ya kwanta yayi barci sai gobe da safe a cigaba da wannan gasa     A zagaye na biyu.

.

Koda gama fadin hakan sai fadawan sarki shardas suka yiwa manyan baki jagora aka kai kowa masaukinsa duk wanda ya shiga falonsa sai dai ya iske abinci da abin sha a shirye yana jiransa na kasaita kuma kala kala wani kalar abincin ma mutum bai taba ganin irinsa ba da idanunsa.

.

Al amarin daya bai wa kowa mamaki kenan kuma ko ya kwayar abinci daya ta dira a kasa sai dai aga ta bace bat Don kada a sawa wajen datti kai da gani ka san cewa wannan aiki ne na mutanen boye, bayan sarakuna da attajirai sun ci sun sha sai kowa ya zauna tare da jama arsa aka shiga tsegumi ana tattaunawa akan gasar inda kowacce jama a ke baiwa shugabanta shawara akan cewa kada ya kara zuba kudinsa a cikin wannan kasa tunda Al amarin ya shallake tunanin mutum.

.

Duk sarkin da ya ce zai fara zuba kudi ko attajiri to lallai karayar arzikinsa tazo, nan take kowanne sarki ya gama yanke  hukunci a ransa cewa sai dai ya zama dan kallo a wannan gasa yabar wa manyan giwaye biyu dama kuma kudin da ya zuba a yanzu ya bar su a matsayin asara da kaddara, Kashi gari kuwa da sassafe aka

sake haduwa a wannan babban falo na cikin wannan gidan darul daulat sauran jama ar gari ma yan kallo duk a wajen kofar gidan suka kafa tantuna suka kwana don kada wannan gagarumar gasa ta wuce su bayan dakin gasar ya gama cika ga tarin jakunkunan dinare jibge a tsakiya sai gaba dayan sarakunan da

attajiran gasar suka sanar da alkalan gasar cewa su sun janye sun barwa sarki shardas da attajiri amsar sun sallama cewar ba zasu iya ba.

.

Koda jin wannan batu sai sarki shardas ya bushe da dariyar mugunta gami da farinciki saboda ganin cewa gaba dayan wadannan makudan kudaden da yan gasar suka zuba sun yi asararsu kuma shine zai mallake su a banza.

.

Sannan kuma har a can karkashin zuciyarsa yana ganin cewa lallai shine zai lashe wannan gasa saboda ya yarda da dukkan shirin da yai akan gasar da kuma tanadin da yayi na tsawon shekaru goma sha, ba tare da wata fargaba ba sai sarki shardas ya dubi Alkalan gasar cikin takama da jin izza yace na linka kudin da attajiri amsar ya siyi wannan gida a yau.

.

Koda jin wannan batu sai falon ya rude da shewar jama a aka shiga yiwa sarki shardas kirari ana kodashi, saboda ana ganin cewa  ya gama lashe wannan gasa domin attajiri. Amsar ba zai iya linka wannan kudin ba nan take aka fara shigo da kudin da sarki shardas ya siyi wannan gida adadin ninkin wadanda ke zube a wajen saboda yawan wadannan kudade sai da aka yini ana shigo dasu sannan aka kammala duk yawan dabbobin da suka dauko kudaden na sarki shardas sai da kaso daya da rabin dukiyar cikin uku ya kare. Shi kansa attajiri amsar yayi mamakin yadda akayi sarki shardas yayi wannan kundunbala shi kuwa sarki shardas sai ya kamu da tsananin farincika ya rinka washe baki saboda gani yake kamar attajiri amsar ba zai iya sake ninka wadannan kudade ba sai dai ya hakura da gasar tsawon dakiku alkalan gasa suna tambayar attajiri amsar shin zai iya ninka wadannan kudade ko kuwa ya sallama amma sai yai shiru ya kasa cewa komai saboda jinjina wautar sarki shardas yake yi a cikin ransa har alkalan gasar sun mike tsaye zasu fadi jawabin cewa gida ya zama na sarki shardas sai attajiri amsar ya tari numfashinsu yace na sake ninka wannan kudi wanda sarki shardas ya siyi wannan gida.

.

Koda jin haka sai gaba dayan jama ar da ke wajan suka kame kAm ! Inji Gwanja Hahhh… Kamar Gumaka kowa ya wangame baki tamkar matattun kadoji a wajen saboda tsananin mamakin kasassabar da attajiri amsar yayi, nan take kuwa aka fara shigowa da jakunkunan kudin har sai da aka gaji, lissafi ya kwace musu a lokacin da zakara ya fara carah sakamakon wanzuwar asubahi.

.

Duk da haka a kofar wannan gida na darul daulat dawakai da rakuman dake dauke da jakunkunan dukiyar Attajiri Amsar sai ketaro kogin ake yi dasu bisa dole alkalan gasar suka dakatar da gasar domin kowa yaje ya kwanta yayi barci nan fa jama a suka  watse kowa ya tafi yana fadin albarkacin bakinsa wasu suka rinka cewa duk yadda akayi wannan dukiya ta attajiri amsar dukiya ce ta iska kawai wato aljanu ne ke kawo kudin Wasu kuma suka rinka cewa to ai shima sarki shardas din ai tasa dukiyar ta iska ce tunda ba a gama kureshi ba nan fa jama a suka yi ta dokin ganin gari ya waye ayi zagayen karshe na wannan gagarumar gasa domin aga wanda zai yi nasara tsakanin sarki shardas da attajiri Amsar.

”         ”        ”

Cikin farin ciki da kwanciyar hankali attajiri ansar ya je masaukinsa ya kwanta yana mai ayyana wa a ransa cewa lallai idan gari ya waye aka dawo zagayen karshe na wannan gasa shine zai yi nasara, koda ya kwanta akan luntsumemen gadon dakin fuskarsa cike da murmushi sai tunanin mahaifiyata ya fado masa ya tuna cewa yau fa kusan kwanaki biyar ke nan fa rabon da suga fuskokin junansu nan take yaji wani irin bakin ciki yayi katutu a cikin ransa amma daya tuna cewa yana daf da lashe wannan gasa sai zuciyarsa tayi fari fat kuma idanunsa suka fara kekashewa ya Fada cikin sabon kogin tunani inda ya rinka ganin su a cikin wannan gida na darul daulat wato shi da mahaifiyata suna ta kewayawa suna shiga daki daki da ko ina na cikin gidan yana nuna mata irin gagarumar daular da aka shirya a cikin gidan a haka ne barci ya sace shi bai sani ba.

—              —               —

Al’amarin sarki shardas kuwa tun da aka baro dakin gasa ko zama kasawa yayi bare ya kwanta yayi barcin kawai sai ya kama zarya a cikin dakin yana ta ciza yatsa da lebe yana tsaki gami da mamaki da takaici Zuciyarsa kuwa sai ta kama tafarfasa kamar zata kone saboda tsananin bakin ciki ya fara tunanin cewa lallai a gobe idan gari ya waye watan jin kunyarsa zai tsaya muddin aka yi zagayen karshe na wannan gasa domin tun a daren jiyan ne dawakai da rakuman dake dauke da dukiyarsa suka daina ketaro kogin domin sun kare, amma na attajiri amsar cigaba suke da zuwa tamkar ba zasu kare ba tabbas idan ya ninka dukiyar da attajiri amsar ya sayi wannan gida abu ne ma wuyaci kudin nasa da suka rage sukai adadin hakan.

.

Koda sarki shardas yazo nan a zancensa sai ya zura hannu a cikin Aljihun Alkyabbar sa ya fiddo madubin tsafinsa ya shiga sabon bincike Yana cikin wannan bincike ne yaga bokansa ya baiyyana tsulumm a gabansa yana mai kyalkyala dariya, cikin fushi sarki shardas ya dubi bokan ya ce sabo da me tuntuni zaka

tafi ka bar ni a cikin wannan zullumi da fargaba ko kuwa so kake daraja ta ta zube a idon duniya kuma arzikina ya karye ?? 

.

Koda jin wannan tambayoyi sai bokan ya tsuke bakinsa yayi shiru ga barin yin dariyar sannan ya matso daf da sarki shardas yayi masa rada a kunne tun kafin gari ya waye gari yayi haske, falon gasa ya cika ya batse da jama akowa ya hallara a wajan babu wanda ake jira face mutum daya jal ba wani bane ba ake jira face sarki shardas da kanshi.

.

Al amarin da yabaiwa kowa mamaki kenan aka rasa dalilin da yasa ya makara. Ashe sarki shardas kwanciya yayi yana ta shara barci abinsa shi kadai ne ya rama bashin barcinsa na jiya da daddare sai kuma attajiri amsar wanda barcin ya daukeshi yana tsakiyar tunanin mahaifiyata, har sai da hasken rana ya fito sosai sannan aka ji bugun tambura gami da bushin algaita alamar cewa ga sarki Shardas nan zai shigo falin gasar, nan fa dakin gasar ya kaure da shewar  jama a gami da ihu da tafi jim kadan sai ga sarki shardas ya shigo cikin falon cikin ado na kwatance kuma fuskarsa cike da annuri dakarun dake bashi tsaro na take masa baya nan fa kowa ya mike tsaye don girmamashi har sai da ya je ya zauna a kusa da attajiri amsar sannan kowa dake falon ya zauna ba tare da bata lokaci ba mai gabatar da gasar ya fara jawabi yana mai cewa yaku jama akamr yadda kuka sani cewa ayau ne za ayi zagayen wannan gasa na karshe don haka yanzu zamu ji daga bakin sarkinmu mai daraja shin zai iya ninka kudin da attajiri amsar ya sayi wannan gida nasa, ance dai waka

a bakin mai ita tafi dadi don haka mai wuri yazo sai mai tabarma ya nade.

.

Koda gama fadin hakan sai mai gabatar da jawabin ya koma mazauninsa take sarki shardas ya mike tsaye ya dubi gaba dayan taron jamar dake cikin falon cikin murmushi maimakon yace wani abu sai ya juya ya kama hannayen attajiri amsar ya tasheshi tsaye ya dubeshi cikin murmushi a lokacin da falon gasar yayi tsit tamkar babu mai rai a cikinsa yace yakai abokina ina tayaka farinciki ka lashe wannan gagarumar gasa daga yau wannan gida na darul daulat ya zama naka kuma mallakinka.

.

Koda jin wannan batu sai falon gasar ya rude da shewa da ihun jama a shi kuwa attajiri amsar sai ya rungume sarki shardas cikin tsananin farinciki mara misaltuwa yana mai yi masa godiya

ba zato ba tsammani sai sarki shardas ya yi wuf ya fisge kwagirin dake hannun attajiri amsar sannan ya zato wata wukar tsafi daga cikin alkyabbarsa ya lumawa attajiri Amsar ita a ciki Nan take wukar tsafin ta lume a cikin attajiri amsar jini yai tsartuwa. Attajiri Amsar ya kwallah kara tare da sulalewa kasa yana kakarin mutuwa, Al amarin da ya razana kowa ke nan a dakin gasar aka yi tsit ana kyarmar jiki saboda tsabar tsoro shi kuwa sarki shardas sai ya dubi dakarunsa ya daka musu tsawa yace maza ku ruga izuwa can bayan gari tafiyar kwana uku zaku riski matar attajiri amsar tare da dakarun dake tsaronta lallai ku kashe gaba dayan dakarun ita kuma matar tasa kuzo min da ita

nan a raye.

.

Koda jin wannan batu sai dubunnan dakarun suka ruga waje da gudu suka shiga cikin jiragen ruwa suka ketare kogin. A wannan lokacin falon gasar yayi tsit tamkar babu mutum daya mai numfashi a cikinsa, ba ma attajirai, bokaye da jarumai dake wajen ba hatta sarakunan jikinsu karkarwa yake yi sabo da tsananin tsoron sarki shardas !!

.

Kai Nima Kaina Abubakar Saleh AlQuyraemey, Saboda tsananin

tsoro yasa nakasa ci gaba.

.

SHIN ATTAJIRI AMSAR YANA MUTUWA SAKAMAKON SUKAN DA SARKI SHARDAS YAYI MASA??

.

YAUSHE YARIMA HULKAS ZAI GAMA LASHE JARRABAWAR  ARWASUL MASADUR YAKE MASA HAR YA TAIMAKA MASA  YA MALLAKI HULAR LAMSARA ?

.

TSAKANIN SARKI SHARDAS DA YARIMA HULKAS WAYE

YAKE MALLAKAR HULAR LAMSARA??

.

SHIN YARIMA HULKAS YANA SAMUN NASARAR KASHE SARKI

SHARDAS DA HANNUNSA KAMAR YADDA YA DAUKI ALKAWARI

DUK DA CEWAA BAYA SHI YAKE DAUKA A MATSAYIN

MAHAIFINSA KUMA AKWAI SOYAYYA DA SHAKUWA A TSAKANINSU ??

.

Marubucin Yace Mu Hadu A Littafi Na Gaba Don Jin Cigaban Wannan Kasaitaccen Kayataccen Daddadan Labari.

.

Author Abdul Aziz sani Madakin Gini

Typer Al amin Ahmed Misau

Posting Alquyreamey

.

A karshe nake cewa Ku meye ra ayinku dan gane da yadda labarin littafin nan yazo karshe haka yaya haduwar zata kasance ne kam sai naji daga gareku, ayi hakuri da jinkirin da aka samu.

Back to top button