Uncategorized

Wace Ce Ita Chapter 45 Complete Novel

 

WACE CE ITA⁉️ (WHO IS SHE⁉️)

Unique Barakancy

                             FORTY FIVE📍

       Basuyi tafiyar 20mins ba suka karasa estate din su abby wanda yake dauke da mansions kala kala, ko wanne gida ka gani kasan yes kudi na magana, a haka har suka karasa na Abby wanda ya kasance biggest one a ciki……

Basu sha wahalar shiga ba kasancewarsu ma’aikatan Abby kuma suna sanye da kaya irin na securities din gidan, kamar yanda Abby ya umarcesu da su tawo da ita haka suka kirata ta landline suka fada mata Abby yace su tawo da ita da baby tee, mamaki ne ya kamata harta rikice ta rasa gane wani abby suke nufi, saida suka mata bayanin me gidan ne ya aikosu sannan ta gane, sake rudewa tayi tace yaushe ya dawo kasar, amsa suka bata da yau ya dawo, kashe wayar tayi ta hau shiri cikin gaggawa, ita fa gani take kamar be dawo ba kamar yanda sukace saidai tasan ba yanda zaayi su mata karya, bazama su fara ba dan bata taking nonsense, saidai abu daya ne ya fi daga mata hankali wai ta tawo da baby tee, second meya hanashi tawowa gida directly sai ya wani aiko a daukesu? Gwada kiran layinsa tayi taji a kashe, hankalinta ne taji ya tashi amma ta daure ta shirya ta fita ta samesu…… 

Tana fitowa suka taso da sauri suka duka suna gaisheta, babu wanda ta amsa har aka bude mata mota tashiga……

Ganinta ita kadai bayan su biyu akace a dauko yasa daya daga cikin securities din kallonta cikin girmama yace;

      “Hajiya yace a tawo harda baby tee”…..

Wani kallon banza ta masa ta harareshi cikin masifa tace;

     “Ina ruwanka! Ko angaya maka banji bane? To a bakin aikinka!”…….

Cikin tashin hankali ya durkusa har kasa ya hau bata hakuri kamar zeyi kuka

     “Dan Allah dan annabi kimin rai hajiya, wallahi aikinnan shine gata na, dashi nake ciyar da iyalina da iyayena, ki taimakeni hajiya”…….

Ko kallon gefen da yake bata karayi ba tace suja motar su tafi dan tsakani da Allah ta kagu taga abby ya amsa mata tarin tambayoyin dake ranta…..

Sunyi tafiya yafi na 10mins kamar a mafarki taga kamar samira take hangowa a titi tsirara ba kaya, da sauri ta cewa driver ya tsaya dan bata yarda da abinda idanta ke gane mata ba, bata fita daga cikin motar ba ta zuge glass din tayi kasa dashi, daidai nan samira ta juyo sukayi ido hudu da ammy, zaro ido ammy tayi cikin tashin hankali ta cewa driver yayi maza yaja su tafi, mom samira na ganin haka itama ta kwasa a guje tabisu a baya……..

In banda faduwa babu abinda gaban ammy ya keyi, sosai ta kadu da ganin yanayin da mom take ciki, duk da aminiyarta ce sosai amma wallahi bazata iya tsayawa ba a halin data ganta, gwara tayi ta kanta ta nuna bata santa ba……. 

     Kana kallon fatima zainab kasan a rikice take, gabadaya ta rasa me ke mata dadi kuma ta kasa gane meke going on a parlourn, ita dai tana makale da Umm duk inda tayi, data hau sama duba mami ma saida tabi ta, Umm batace komai ba ta riko hannunta suka tafi tare, haka sukaje suka dawo tare bayan mami ta rufe kofar, gashi deen sai banzan kallo yake mata, har bataso su hada ido dan dagaske ta tsorata da lamarinsa, ga hararar da yaketa aiko mata dashi daga inda yake, shi besan yanzu damuwarta daya halin da khaleel yake ciki ba, ga dai su daddy nan amma taga kamar suma jikinsu yayi sanyi kuma bata san dalili ba ko tambayar khaleel basu karayi ba, tana so ta tambaya amma idon deen ya hanata…

Kwafa deen yayi ya nufo inda suke zaune ita da Umm, shigewa jikin umm tayi sosai tana fadin;

     “Kice mishi kar yazo dan Allah, wallahi kashe ni yace zeyi”…….

       “Wani irin kasheki zeyi ana zaune kalau?”….

Umm ta fada tana kokarin dago ta, kin tashi tayi saima kara shigewa jikinta da tayi, daidai lokacin deen ya karaso inda suke… 

Tsaki yaja cikin hade rai yace;

    “Wani salon munafurci ne wannan da kike wani boye boye kamar ta Allah?”……

     “Babu ruwanka da ita, bana son neman rigima!”…….

Umm ta fada tana dakatar dashi…..

      “Umm dan baki san halin yarinyar nan bane shiyasa, can you believe har sunje an daura musu aure?”………

Deen ya fada kamar zeyi kuka…..

Zaro ido umm tayi tace;

      “Dagaske?”…

Cikin wata iriyar murya yace;

      “Wallahi dagaske! Wai su gasu yan iskan karshen zamani, I am just so disappointed in her, I never knew she’s this stupid!”….. 

Cikin sanyin murya Umm tace;

    “Ya isa, abu ya riga ya faru we can’t change that, Allah yasa hakan shine mafi alkhairi”….

Da sauri yace;

     “Bama shi bane alkhairin ba saboda nasa shi ya mata saki uku, kinga takardar a cikin aljihuna”…….

Cikin mamaki umm tace;

     “Kana cikin hankalinka kuwa saif? Saboda me zakayi haka bayan tana san shi, gaskiya banji dadin abinda kayi ba…..”

Karab fatima zainab tace;

      “Nifa ba wani sakina da yayi kuma….”..

    “Yi mana shiru shashasha kawai! Ba ga takardar nan a hannuna ba, in kara jin bakinki a gurinnan na lahira sai ya fiki jindadi wallahi! Kin bari ya miki wayo wawuya kawai!”…..

Deen ya fada kamar ze daketa…..

Da yake ba taji sai ta tashi zaune tace;

     “Nifa ba wani wayo da yamin, da kaina na bishi because I love him!”…..

Ai ji yayi kamar an soka masa mashi, ya rasa meyasa ta iya fadan duk wani abu daze bata masa rai, ko batasan tana hurting dinsa bane?, hannunsa yasa ya bige mata baki ya dauko belt din daya gama zena mom dashi yayo kanta…..

Cikin tashin hankali umm tasa hannunta ta tare ganin dagaske nema yake ya daki yar mutane sannan cikin kakkausar murya tace;

     “Wai me yake damun brain dinka ne? A gabana zaka daketa? Saif me kake san zama ne haka?, yanzu dan maganarnan ya kai a duki mutum, my friend get out!”……

    “Amma umm ita bakiga…”….

Daka masa tsawa tayi tace;

     “I said get out!!!!”……

Juyawa yayi ya cilla belt din inda su daddy suke belt din ya sauka akan daddy, ko a jikinsa ya nufi hanyar fita, ya kusa kaiwa bakin kofa kenan wayarsa ta soma ringing, fito da ita yayi yaga sameer ne ke kiransa, dauka yayi da sauri da niyar fadamasa yaga yan iskan daketa wahalar dasu…..

      “Boss kaji mutanenka sunyi Australia?, yanzu khaleel ya kirani yake fadamin, na rasa me yake damun khaleel, sunata yawo kamar wasu kaji”……

Ya jiyo muryar sameer ta katse masa maganar da zeyi……

Ransa ne yaji ya kara baci dama ransa a bace yake tuntini, wato all this while sameer playing dinsa yake kenan? It means suna dubai tin farko dayace masa amma shine ya kirashi yana shirga masa karya, ya sashi yawo kamar mahaukaci…….

     “Rufemin baki dan ubanka habibu!!! Sameer ni zakayiwa karya? Wallahi wallahi duk ran da muka hadu dakai saina karya maka kafafuwa, zakasan kayi dani shege makaryaci kawai!!”……

Be jira abinda sameer zece ba ya kashe wayar, alhaji habibu ne ya mike da sauri ya nufi inda deen yake, cikin rashin mutunci yace;

    “Da wani sameer din kake waya?”…

Kamar jira deen yake kai tsaye yace;

     “Danka mana! And yes kaina zaga”…..

    “Ni kake gayawa haka? Lallai wuyarka ta isa yanka yaro, amma zanyi maganinka!”…..

     “Saidai ni inyi maganinka munafiki kawai!!!”…..

Dad da abby na jinsu amma sun kasa cewa komai dan abinda ya damesu yafi karfin chachar bakin da suke…..

    “Saif!!!”…..

Yaji muryar umm ta kira sunansa da karfi, yasan gani take kamar yana rashin kunya ne amma shi kadai yasan abinda yasani akan mutumin, zeyi magana kenan sukaji sallamar ammy…….

Abby da ya kasa magana tindazu duk dramar da akeyi ya mike da sauri yana jiran yaga shigowar baby tee, ya bawa umm yarta ko ya samu ta kulashi suyi magana dan he has alot to discuss with her, bayan ammy ya kalla yaga wayam, da sauri ya kalleta yace;

    “Yana ganki ke kadai ina baby tee din?”…..

Kamar batasan magana tace mishi;

    “Tana gida!”….

    “Bangane tana gida ba? Ya zaayi ki barta bayan nace ku tawo tare”…

Cikin halin ko in kula tace;

     “Bansan inda zasu kawo mu bane, shiyasa na fara zuwa ni kadai”….

Cikin bacin rai abby yace;

      “Amma tinda ni nace kuzo ai kinsa bazance kuzo inda zaa cutar daku ba, ki koma ki tawomin da ita yanzu!”……

Chewing gum din bakinta ta tauna ya bada sautin kasss tace;

     “Babu inda zata zo kasan banaso tana shiga cikin mutane”……

Ba shiri umm ta mike jin wani irin zance dake fitowa daga bakin ammy, daga sama ammy tajiyo muryar umm na fadin;

     “This must be a joke! Yar tawa ake magana akai haka kamar wata babyn roba? Mallama wuce muje ki bani ya’ta tinda bake kika haifomin ita ba”…….

A gigice ammy ta dago ta kalli umm, jan baya tayi da sauri tana murza ido dan ta tabbatar umm din take gani da gaske ko kuwa….

Chakumo wuyar abby tayi cikin masifa tace;

    “Ni zaka yaudara? Ashe dama kuna tare haryanzu? Shiyasa baka damu ba da ban zo ba? Allah ya isa ban yafe ba wallahi ka cuceni!!”…

Hankadata abby yayi ta fadi kasa, ta dago zatayi magana kenan idonta ya sauka akan fatima zainab, wani irin ihu ta saki ta kalli fatima zainab tace;

     “Wacece ke?!”….

Sai kuma ta zube kasa a sume…..

Domin Sauke Littafin Sai Ku Dannan inda aka saka Download Now!

Back to top button