Uncategorized

Rabon Kwaɗo Book 1 Complete Hausa Novel Document

Tana zaune tayi tagumi hawaye nabin fuskarta babu kakkautawa,seda tanisa acikin tunaninta tafara magana cikin kuka 

       Kae rayuwa abar tsoroce yauni safiyya  nake ganin rayuwata haka gaskiya duk wanda beji maganar iyayensaba bazega daedaeba yanzu kafin nasamu abincin dazanci sau daya arana senayi aiki da karfina da gumina zansamu naci juya kanta tafara cikin bakin ciki tace imam kaci amanata bantaba tunanin zaka azabtar da rayuwata hakaba kodayaushe yanzu cikin nadamar aurenka nakeyi nabijirewa iyayena nabiyoka wlh se allah yasakamin zalintata dakayi.

     Shigowar sace yasata yin shiru takawar dakanta gefe taname zubar hawaye, bekoyi sallama yashigo abinshi halinda yaganta acikine yasashi tsayawa cikin bacin rae yace shin safiyya seyaushane zaki dena wannan kukan dakikeyi dame kikeso najee kukanki ko talaucin dayataru yaymin katutu atunanina addu ah itace maganin duk wata masifa ba kukaba.

     Safiyya bata tankashiba harya kare zancensa kuma bata kalleshiba gyara zaman ta tayi kan yar yaloluwar tabarmar su tanashare hawayenta sannan tadago tace imam yunwa nakeji kamar namutu kafita kasamomin abinda zan sawa cikina kada kamanta rabona da abinci tun jiya da rana gashi yanzu rana tanashirin faduwa kafaji tsoron allah kafita tunsafe kaci mekyau kasha mekyau nikabarni da yunwa tanashirin yimin lahani, anya kasan hakkina akanka kuwa.

      Ranshi abace yajawo kujerar karfen dake gefansa yazauna kusada ita yace to yar malamae sekiyimin wa azi kikuma gayamin hakkinki dabana saukewa banida kudi nafita bansamoba yakikeso nayine,tae murmushin takaeci tace nina tabbatar daga majalisar lado me tsire kake kuma wlh bazan iya kwana hakaba kasan abinda zaka kawomin naci.

    Murmushin mugunta yasaki yace to allah yakawo sena siyo miki amma yanzu asi bana magani, kumama senake ganin kamar bayunwa kike jiba tunda allah yayi miki azziki kin hana muci semuyita zama ahaka ay indae kuma basokike inyo sataba,cikin takaeci tace inkayi satarma aiba yau kafaraba mutane nawa kacuta a duniya bazasu kirguba kayaudaresu ka damfaresu wlh imam inbaka sauya haliba kaji tsoron haduwar ka da ubangiji.

Download>>> Ingarman Namiji Complete Document

  Tafasa zuciyarsa kawae take yaname mamakin irin kalaman da safiyya take gaya masa yau murmushin karfin hali kawae yayi, ita kuwa budar bakinta tace ay dole kayi murmushi saboda bakasan mekakeyiba bakasan zunuban dake kanka…….Marin datajine yasata yinshiru tadafe gurin tana kallonshi cikeda mamakin abinda yamata kuka kawae tasaki tamike tashiga daki ta kwanta kan katifarsu kuka take metsuma zuciya tana cewa ya allah kasan halinda nake ciki kayayemin wannan wahalar rayuwar dana tsinci kaena aciki allah kaga abinda mijina yakemin kabimin hakkina  yaune rana ta farko da aka fara marina nacuci kaena dana aureka da ‘yan uwana nabiyewa son zuciyata takaeni tabaroni.

       Imam bekoyi tunanin zuwa inda takeba bare ya  rarrasheta sema tashi dayayi yabar gidan wanda betashi dawowaba seda dare yayi yashigo gidan yasiyo mata mura mesanyi, koda taganshi da furar nan mesanyi da irin kallonda yake mata yasata gane abinda yake nufi, murnushi yay mata yace safiyya bakida lpy kinga yadda kika fita ahayyacinki kuwa banida kudinda zankaeki asibiti amma gobe zannemi alfarma kamar kullum gurin alhj abubakar matarsa ta dubaki, bata tankasaba sema  tamau kuwa tadaure fuskarta ta anshi furar tasha sosae sedae daga karshe bandaki tashiga ta amayarta tass tawanke gurin tadauro alwala taje ta tada sallah ba ita ta idarba harseda tasomjin minsharin imam tukunna tafara karatun alkur ani seda tajuma sannan ta ajiye tayi addu o einta, sallayar datayi sallan kawae ta gyara tadauki pillow zata kwanta akan sallayan zama tayi tana addu an kwanciya bacci tana kallon mijin nata minshari yake hankalinshi kwance farine tass se dauda data dafar masa da fatarsa dogone sosae fuskarsa  siririya haka hancinsa sauke ajiyan zuciya tayi ta tofa addu anta shafa ta kwanta tana mecewa yadda nakejin tsanarka azuciyata bazan iya hada shimfida dakaeba muyita zama ahaka nibazan gajiba,   

          WASHE GARI

   safiyya bata iya tashin asuba bah saboda batajin dadin jikinnata harseda rana tafito tukunna tafarka sauri sauri kuwa tai alwala tayi sallah, tana nan zaune kan sallaya imam yashigo batako kalleshiba shima bedamu da gaisuwar tataba dukda shirun data masa bemae dadiba, dauke kansa yayi yace taso muje allah yasa Dr maryam din bata fitaba ta dubaki sauri kuma takeyi donhaka tashi muje kada kibata mata lokaci,  

Download>>> Matar Hariji Complete Document

  Sosae safiyya tashiga tashin hankali jin furucinsa datayi amma seta danne kuma sam batada mafita haka tamike da hijab din jikinta tazura silifas dinta suka tafi jikinta asanyaye , daga bakin gate yatsaya itakuma tashiga ciki tana shiga hawayen datake dannewa suka soma saukowa tasoma cewa ya allah katemakeni yazanyi idan yaya abubakar bayanan ko ganin masifaffar matarsa banasonyi bare tasan halinda nake ciki, tana tafiya kuwa tahangoshi tsaye da ma aikatan gidansa ajiyar zuciya tasaki tagoge hawayenta, tanufu gunsu tunkan takarasa yake mata fara ah koda ta gaishishi, ya amsa mata dacewa lpy kalau safiyya yajikinnaki imam yace bakyason zuwa asibiti inbaki da lpy kidena don allah kodan lafiyankima yake tadanyi masa tace insha allah zamudinga zuwa, yawwa to yanzu muje koh tanacan tana jiranki zata fita aikine, ma aikatan yabari yatafi tabishi abaya sunata taka step na bene zcyrt tana kara tsinkewa seda suka dangana da kofa ze murda handle muryarta tana rawa tace yayana! koda yajuyo hawayenda yagani fuskartane yadaga masa hankali yace safiyya meyayi zafi haka, kasa rike kukan ta tayi tace inacikin tashin hankali nakuma rasa inda zankae kukana asharemin nadaukeka tamkar yayana kamar yadda kace shiyasa zangaya maka matsalata katemaki rayuwata, cikin jimami yace to shikenan shigo ciki muyi magana, kofan yabude suka isa katon palor yazauna kan daya daga cikin kujerun palor din ita kuma tazauna akasa dasauri yace a ah safiyya zauna kan kujerar mana nan kamar gidan kune mikewa tayi tazauna adarare tasoma cewa dama baka fahimci abinda yake faruwa tsakanina da mijina bane, bama jituwa yanzu sau uku ina samun ciki imam yana zubarwa yace beshirya haihuwa yanzuba saboda talaucinda yake damunsa yakasa gane ‘ya’yan ma arzikine, yanzu haka ina daukeda juna biyu muddin yagano kuma wlh seya zubar dashi alfarmar danake nema yanzu tsam tamike, taje ta tsugunna agabanshi tace iname rokonka in Dr ta dubani kada tagayawa imam inadashi kawae tabani magani natafi gida, 

       Tausayintane yakama shi wanda haryakasa cemata komae sem kallonta dayake yana jimami dama tunda take maganar yake salati da sallallami,hannayensa yahade guri daya yace tabdijan,safiyya wannan ba maganar boyewa bace dole se imam yayi bayani cikin firgici  tadago dakanta tace kayi min rae yayana wlh inason cikina muddin yasani komeze faru seya zubar dashi gara kabari ko kwari cikinnawa yayi tukunna tunda ban isa naboye cikiba dama, tom shikenan koma gurinki kizauna safiyya kikuma kwantarda hankalinki dake duk haka yana faruwa bakiyi maganaba yanata cutar da rayuwarki, koda safiyya tazo mikewa tsaye se tsautsayi yasa ta take hijab dinta tabaya saura kadan tafada kansa shikuwa ganin zata fado masane yasa hannu yatareta.

      Fitowan Dr maryam kenan daga bedroom dinta tahangi safiyya gurin mijinta cikin razana tace abban muhammad mezan gani haka bakaramin tsorata safiyya tayiba cikin azama kuwa takoma gefe tatsaya tana kallonta harta karaso wani mugun kallo take antayawa safiyya, kallonshi tayi tace abban muhammad yarinyar dazan duba metakeyi agurinka ni maryan yau mezan gani agidannan saboda ita katsaidani banfita aikiba yanzu kuma nayi bakin gani dama tuntuni na dade ina zargin wani abu tsakaninka da yarinyar nan shisshigin datake maka ba a banzaba, 

      Cikin bacin rae alhj abubakar yace maryam mekike nufi kenan saboda tana gayamin matsalarta shine zargi zeshiga tsakanina dake shin kinmanta matar aurecene, cikin fushi tace  duk banga hakanba inda abin azziki kukeyi ai bazan hangeta ahannayenkaba saboda kunjini zatayi baya ita munufika, juyawa tayi kanta tana mata kallon tsana tace keda kikazo neman alfarma kinsamu kinshigomin gida shine zakici amanata har haka cikin gidana, cikin matsanancin fushi yanunata yace ya isheki haka maryam katseshi safiyya tayi tace kiyi hakuri Dr don allah wlh babu abinda yake tsakanina da mijinki, murmushin takaeci tayi tace ok hanya ta nuna mata tace to fitar min agida karna sake ganinki

     Da bacin rae yace yanzu kinfasa dubata kenan maryam, cikin fushi tace eh nafasa bazan duba mara kamun kae irin wananba wacca batasan darajar aureba, kuka safiyya tasaki saboda kalaman suntaba mata zuciya hanyar waje tayi aikuwa dasauri alhj yashiga hanyar tata yace kada kitafi safiyya kina bukatar temako sosae kika koma gida komae ze iya faruwa kibari nazo nakaeki asibitin dakaena daganan se nasan abinyi.

Download>>> Ana Dara Ga… Complete Document

      Sororo maryam take kallonsu cikeda al ajabi tace abban muhammad ga mijinta mezesa ka kaeta asibiti inbabu abunda kuke boyewa, bae ko kulataba yawuce yashige dakinshi itakuma safiyya tafita, cije baki kawae tayi tabita wajen dontasan halinshi kome yace zeyi seyayi, zaune kuwa taganta kan step ta kifa kanta tanata kuka baki tarike tace lallae yarinyar nan asheba tafiyar kikaeba kinajira mijina yakaeki asibiti ko shin waca larurace dake damijina yadamu nadubaki uban me kuke boyewa, safiyya tazaunane saboda kawae batada mafita ammah zcyrt kuna take mata, dagowa tayi takalleta tace bawani abu kedamunaba ni nasan matsalata mijinane yadamu kidubani ammah yanzuna bari natafi gida zance dashi kindubani.

  Cimimiyota maryam tayi tace to baki isaba senagano abinda kuke boyewa yau janta tayi har cikin room dinta ta kulle kofan,alhj yana fitowa yaga babu safiyya yakarasa har gurin gateman yatambayeshi safiyya yace aitana ciki bata fitoba murmishi kawae yayi yakoma palor yazauna yana jiransu, seda time yadanja tukunna daga kanda zeyi yaga maryam tashako shaffiya tana cewa lallae yarinyar cikin shege kikayi kenan tunda bakyason mijinki yasani yawon banza kike kenan to wlh koki gayamin cikin nawaye kona gayamasa kuma yasakeki, cikin firgici da kuka safiyya tace don allah kiyi hakuri wlh dan cikina bashege bane kawae banaso yasanine saboda rashin jituwar datake tsakaninmu kifahimceni, cikin tsawa maryam tace rufemin baki makaryaciya zaki gayamin gaskiyane kosena toni asirinki, karasowa alhj yayi cikin kakkausar murya yace wlh maryam kika kuskura kika sanarwa mijinnata sena dauki mummunan mataki akanki tunda bakida tunani da lissafi baruwanki da wannan maganar idan kuma kika shiga takice zatayi zafi, 

      Kuka tasaki maryam tasaki safiyya takuyi gefe catake abban muhammad bansanka da wannan halinba ‘yar karamar yarinya tarudeka haka, cikin mamaki yace maryam me kike nufi, cikin kuka tace ina nufin wannan cikin inba naka bane mezesa kace kar agayawa mijinta,tass tass taji saukar maruka afuskarta takuwa gigice safiyya bakaramin tsorata tayiba ganin tasaka ma auratan cikin tashin hankali, sosae take danasanin furta masa damuwarta, dayatsa alhj ya nuna maryam yace mahaukaciyar banza dalili shine mijinta bayason cikin zubarwa yakeyi ita kuma tana kaunar abinta kebame temaka mata bace bama, cikin ihu da hargowa maryam tace sam bazan yardaba incikin yagirma yazatayi dashi komakantarda mijin zatayi sedae yaganta tahaihu, 

    Safiyya jikinta asabule tace Dr dan cikina bashege bane gaskiya mijinki yafada miki kawae temakona zeyi bansan abin ze kasance hakaba ammah kiyi hakuri bari naje nasami mijinnawa nasanar masa insha allah ze fahimceni, bantaba yiwa mijinki wani kalloba inba na yayanaba, juyawa tayi gareshi tace kayi hakuri don allah ka gafarceni nahaddasa rigima atsakaninku kuyi hakuri zanta addu ah da lallaminshi harya fahimceni musasanta, bayyacca alhj ya iya yace  shikenan safiyya allah yatsareki yabaki lpy, tace ameen tasakae tafice yabita da kallon tausayi…

Tana fita ta tarar imam baya kofar gidan takuwaji dadin rashin ganinshi datayi, kae tsaye ta wuce gidan nasu  ta tura kofan tashiga tanata tunani sosae take cikin tashin hankali, koda tashiga cikin daki kwanciya tayi kan katifa tana dafe kanta saboda sara matan dayakeyi, cikin yanayin tausayi tace yanzu imam idan kasan inada ciki shima zubarmin zakayi ya allah gani gareka gashi Dr tayimin mummunan fahimta ina zan tsoma rayuwata ni safiyya yazanyi da raena, seda taci kukanta takoshi daganan bacci yadauketa.

    Dr maryam tana zaune a palor ko aikin takasa fita tunda suka gama rigimarsu da alhj yafice yabar gidan sosae ta tashi hankalinta saboda irin kishin dake damunta,tana nan zaune muhammad yafito cikin shirin uniform da mamaki yazauna gefenta yace auntie ya akae baki fita aikinba haryanzu kuma kince ma yau kinada ayyuka dayawa, kobakida lpy ne nagan yanayin ki yacanza, girgiza masa kanta tayi taname kakalo murmushi tace kawae nashiga damuwane yasa banajin fitanma, kallonta yayi dakyau yace wani damuwane yahanaki fita kuwa, kada kawani damufa tsakaninane da daddyn ka, tan tabe bakinsa yayi yace to ina ganin wannan ba abunda ze hanaki fita aiki bane inda sabo ai kunsaba ko zuwa anjima ne zaki iya gyara matsalan, murmushi tayi mesauti tace yes my boy kanada hankali sosae karami da tunanin manya kana abu sekace babba, smile yayi shima yace kae aunty kada kiyabeni dayawa,time takalla tace katashi kaduba kanwarka idan baba larae tagama shiryata kuwuce kaga kunkusa yin let, mikewa yayi yanufi room dinda kanwar tasa take tararwa yayi ana samata shoes dinta, da fara arsa yace sis nana angama shirin kenan setafiya, tana dagowa taganshi ta rugo dagudu yakuwa cafeta sama tana masa dry dama yasan abinda takeso kenan, magana take masa cikin gwarancinta baya fahimta abinda take cewa sosae yasashi juyawa yagaeshe da baba larae me aikinsu yadauketa suka fita yana rike da yar school bag dinta,sallama sukaewa Dr suka fita tabisu da kallon sha awa tana murmushi.

Download>>> Kwarata Complete Document

      Imam be waewayi gidan bah seda rana ta take tukunnah yasameta akwance hannunsa daukeda leda tanajinshi kuwa tamike zaune ta gyara zamanta tace imam kaenake jira kashigo dama inasone zamuyi magana tafahimta nidakae, ledar cefanan daya siyo ya ajiye gefe sanan yazauna yace to safiyya ina saurarenki, shiru tayi don tarasa ta ina zata fara masa magana sannan tace alfarma nake nema agurinka… sekuma tayi shiru shikuwa soyake kawae yaji abinda dazata gaya masa cikin kosawa yace kenake jira, idanu tazuba masa se hawaye suka soma saukowa a idonta tace dama ina dauke da juna biyune shine nake rokar arziki agurinka don darajar annabi da alkur ani ka kyalemin abuna kada kazubar min da ciki, badawaeniyar dazan dorama harna haihu nayi alkawarin nizan dinga yiwa kaena komae abinda nahaifa ma nizan dinga kulawa dashi bakaeba katemakamin inka rabani da cikin nan bazan iya rayuwaba don tamkar ka kashe nine kukan dayaci karfintane yasata yinshiru.

     Kallonta yake harta kare zancenta sannan yamike yazo yazauna kusada ita suna kallon juna, seda yasuke ajiyan zuciya yace safiyya zaki iya haihuwa mana ammafa idan kinso, kallon rashin fahimta tafara masa daga mata kae yayi yace eh mana sharadi dayane sekin daukomin sarkar ki ta gold nasiyar kudin nakara ajarina domin kulada lafiyarki data yaronki sam wannan yar sana ar wainar dakikeyi bazesa ki iya dawae niyarki data yaron cikinkiba, 

    Kallon takaeci safiyya take masa harya kae aya cikin bakin ciki tace tokuwa abinda kakeso baze yiwuba narasa meyasa ka kafamin kahon zuka akan gold dina, saunawa zance maka bana ganinshi amatsayin kudi darajarshi tawuce takudee agurina ita kadaece abar danake gani naji dadi araena aduk lokacinda natuno gidanmu itace siyayya takarshe da mahaifina yayimin nida yar uwata kafinna aureka inajin ma itace siyayya takarshe dazan gani da mahaifina yaymin, gaba daya kadarorina ka kwashe kasiyar banida komae yanzu dazance gashi agidanmu akaemin ka kwashe komae sannan wannan mah ka dafa mata to wallahi baze yiwuba cikine allah ne merayawa kuma me kashewa shine ze tsaremin abuna harna haifeshi.

    Hannu imam yadaga mata cikin bacin rae yace ya isa haka komae ay yazo karshe yanzu tunda bazaki temakeniba abinnaki harya kae ga haka dole nashiga duniya neman kudee seki zauna kiyita jirana har nasamu abinda nakeso nadawo dukbakece kika jaminba sam bana zama guri daya amma tunda na aureki bana zuwa ko ina to yau allah yakawo karshen abun kiyi abinda kikeso nima nayi nawa, 

    Jiyay kawae tashaki kwalar rigarsa kallonta yayi da mamaki idanunta sun kumbura saboda kuka magana tafara cikin kakkausar murya dagani bata hayyacinta baka isaba imam karya kake katafi kabarni allah ya isa tsakanina dakae bazan yafe makaba kacuci rayuwata bantaba ganin mugu irinkaba arayuwata  nabar kowa nawa nabiyoka shine kake azabtar dani saboda kaga ina sonka mugu azzalu….. Wa iya zubillah maruka tajee masu kyau wanda yasata fadawa kan katifar takuwa fara ihu tana kuka wanda hatta makota zasu iya jiyota, tsugunnowa yayi yace safiyya bantaba cutarkiba sedae in kekika cuci kanki yakamata kiringa tuna bani nace inasonki zan aurekiba ke kika likemin ahalayena bawanda baki saniba kikace kinji kingani bani nayi miki dole ki aureniba ina tafiye tafiyena dole dana aureki mahaifiyata tahanani tafiya ko ina harkar kasuwancina tayi kasa sannan kice bazaki temakeniba kuma ki hanani tafiya ay abinda baze yiwubane nakare agabanki kullum iya abinda zan miki inkinga zaki iya bina duk inda zani kihada kayanki mutafi, atoh.

     Safiyya murmushi tayi lokacin idonta yabushe tanemi kukan tarasa saboda tashin hankali cikin suyar rae tace imam butulu kenan dama ance kaji tsoron wanda kafiya kyautatawa  bantaba tsammanin wannn kalaman daga bakin kaba to amma banga laefinkaba tunda ninace naji nagani to amma kasani bazan taba kuma binka wani guriba inkaga nabar garinnan to garinmu na nufa zankoma wa iyayena kace musu lagos zamu tafi karshe ganu a kano koda iyayena suntashi nemana can zasu tafi banan bah to gara nakoma garesu ko allah zesa suyafemin bazan kuma gangancin binka wani guriba, kaekuwa bazan hanaka tafiyaba duk inda zaka amma kasani bazaka tafi da aurena akankaba dole kasakeni tunda dama nikadaece nake kaunar kah, cikeda mamaki imam yake kallonta sam ba alamun shakka ko tsoro atare da ita mikewa yayi yay waje batare dayace mata kalaba.

Download>>> Yaro Ne Complete Document

     Alhj abubakar yini yayi tunanin safiyya halinda take ciki sosae yake tausaya mata matuka yanata tunanin hanyardaze bullowa imam kan lamarin matar tasa safiyya, gabacin randa yakunsa gurin uwar gidannashi Dr,bedawo gidannashiba se dare haka shima imam seda dare yayi sosae yashigo atunaninshi tayi bacci besan idonta yariga yabushebah shikawae take jira, wannan daren kuwa bakaramar rigima sukayiba tsakaninsu yadage seya tafi ita kuma tace to sedae yasaketa imam ganin abinnata babbane yasashi kyaleta yakwanta abinshi, to kasancewar tana raena jikin nata zazzabi yarufeta batasan  time dinda bacci me nauyi yadauketaba harseda asuba gari yasoma haske allah yafarkar da ita taje tayi alwala tayi sallah sedae zcyrt cikeda tsoro rashin ganin imam datayi agidan abinda betaba yiba don baya zuwa sallan asuba, tana azaune tana azkar har gari yayi haske rana tasoma fitowa asannan ta kulada takaddar dake ajiye kan katifa, jikinta kuwa har bari yake tamike taje tadauki takaddar cukurkudaddan rubutunsane aciki kamar haka

    “Safiyya inason kisani cewa inasonki ina kaunar kasancewa dake, abinda yasa nake kyamar abindake cikinki mahaifinki banasonshi ko kadan kuwa banason hada jini dashi samba mutumin kirki bane ya wulakantani arayuwa dake kanki ya tozartamu segashi daga karshe kema kin bani kunya kince sena sakeki bisa bukatar hakan dakikayi nasakeki saki daya abindake cikinki koda yazo duniya toki sama masa uba tunda kindage sekin haifeshi tafiyace bazan fasaba inaso kiyimin fatan alkhairi kamar yadda nake miki nima allah yasake hada fiskokinmu anan gaba.”

    

WRITTEN BY:      NANA BMB

NOVEL NAME:.     RABON KWADO BOOK 1

UPLOADER:     AIHAUSANOVELS 

  DOCUMENT SIZE:         26KB

DOCUMENT TYPE:              TXT

MODIFIED DATE:      1- SEPTEMBER -2022

CATEGORY:               LOVE   STORY

PRICE:                            FREE

Proceed To Download Rabon Kwaɗo Book 1 Hausa Novel Document.

Domin Sauke Littafin Sai Ku Dannan inda aka saka Download Now!

Karanta Littafin>>> Maciji Ne Hausa Novel Complete 

Domin Karanta Littafin Sai ku Danna Inda Aka Saka Read More

DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.

Visit > https://www.aihausanovels.com.ng

Ka tura mana sako ta adireshinmu na email, domin tuntubarmu ko turo mana hausa novel ko kuma post.

Email > aihausabooks@gmail.com

******* FOLLOW US ******

Facebook: Ai Hausa Novels

Twitter: Ai Hausa Novels

Telegram Channel: https://t.me/Aihausanovels

Copyright 

If you are the right owner of this novel and you want us to remove it from our site please mail Us at aihausanovels@gmail.com

Back to top button