Harijin Sarki Page 31 Romantic Hausa Novel
A cikin daren da babu hasken farin wata, sararin samaniya ya rufe kamar ana zubar da jini daga sama. Kogunan da ke kewaye da masarautar Zirkan sun fara yin wani irin motsi kamar ana turzura su daga ƙasa.Sultan Rashid yana tsaye a saman Hasumiyar Zinare wadda take mafi tsayi a fadar. Gashinsa na rawa cikin iska, idonsa na kallon dogon sararin da yake ci gaba da yin duhu fiye da yadda ake gani da ido A cikin zuciyarsa yana jin wani abu da bai taɓa ji ba numfashin wanda aka ɓoye.“Na san kana raye, Ameer…”Ya furta da murya mai sanyi amma cike da iko.“Ka ɓoye shekaru ashirin da bakwai, saidai jininmu ɗaya ne. Idan ka dawo, to, wannan sarauta ɗaya ce da mutum ɗaya ne zai rayu a cikinta” Wata iska mai sanyi ta hura ta ratsa masa cikin jiki, kamar wani ya yi dariya daga cikin iska.“To ni nake raye, Rashid…”Wata murya daga nesa ta amsa.“Na dawo ne ba don sarauta ba sai don zuciya da ka lalata kafin haihuwarta”Cikin ɗan lokaci, hasken wuta ya fara yawan walƙiya daga ƙofar Haikalin Al-Balad, wuri da aka rufe shekaru da dama saboda tsafin da ke cikinsa.Tsafe-tsafe suka fara tashi daga ƙasa, ruhohi masu kama da ƙura suna yawo cikin iska suna yin wani irin kukan ban tsoro.A ɓangaren Dr. Samha tana cikin asibitin fadar, tana riƙe da wani tsohon littafi wanda Granny ta bata — littafin da ke ɗauke da sirrin hatimin jini da kuma yadda ake karya la’anar da ta haɗa jinin sarauta biyu.Tana karantawa cikin rawar murya, tsoro na shigar mata saboda kalmomin suna kama da suna magana da ita kai tsaye“Wanda aka haifa daga tsafin jini ba zai samu salama ba sai ya haɗu da wanda Allah ya zaɓa masa wadda zata iya ɗaukar zafin jikinsa kuma ta iya ƙona duhun da ke cikinsa da haskenta”Ta runtse idonta da ƙarfi zuciyarta ta buga tace“Ni ce…?” Ta tambayi kanta cikin tsoro.“Ko kuwa ni ce makamin da Allah ya halitta don Rashid, ko kuwa akwai wata bayan ni?”Wani zafi ya ratsa jikinta, jikinta na rawa, zuciyarta na bugawa da sauri kamar ana kiran sunanta daga wani wuri da ba’a gani.A lokaci guda kuma, a waje, iska ta narke, ƙasa ta motsa, kuma wani haske mai kama da toka ya bayyana daga tsakiyar ƙasa Sultan Ameer ya bayyana cikin sutturar duhu, idanuwansa ja kamar wuta.“Lokaci yayi, ɗan uwana…” “Lokacin da haske zai sadu da duhu, kuma duniya ta zaɓi wanda zata bi”Cikin ƙarfin zuciya Rashid ya janye takobinsa takobin Nurul Malik, wadda aka ce ba zata iya sare mutum ba sai wanda yake ɗauke da jinin sarkiSuka tsaya suna kallon juna zuri’a guda ɗaya jini ɗaya ƙaddara ɗaya, amma zuciyoyi biyu da Allah Ya raba da sirrin duniya.Sun jima suna kallon juna kafin Rashid yace “Saboda ɓoyyayar halittar da duk duniya Ni kaɗai nasan da wanzuwar ta cikin cikin matata Samha ka dawo duniyarmu yakai ɗan uwana Ameer, kayi sani zuciyata ta fara barin imanin tsafi tana komawa ga Allah ɗaya wanda aka haife mu akan addininsa amma sai aka cuɗanyamu da gargajiya da tsafi, na rantse da Allah wanda yake kare Samha a lokacin da ɓoyayyun ruhohi suke bibiyar sawunta, bazaka samu nasara akan Mata da jaririn haske dake cikinta ba domin ya an kasantar dashine tsakanin fitar wata da shigarsa, tabbas wannan ruhin abin kaɗaicewa da imani ne”Murmusawa Ameer yayi ya ɗago jajayen idanunsa yace “ba don shi kaɗai ba harda kai zan sha jininka don kafuwar ikona, an horar da zuciyata kada naso kada a soni saidai daga fitowata saman duniya na farajin ƙamshin abinda nake buƙata, a binciken da nayi kai ka rigani mallakar wannan ruhin da nake buƙata don haka zanyi duk me yiwuwa na karɓi abuna dake hannunka” ya faɗa yana ƙyaƙyacewa da dariyar mugunta ya riga yasan ɗan uwansa bashi da ƙarfin tsafin jayayya da ikonsa, yana gama dariyar ya ɓace yabar Rashid tsaye cikin wani yanayi daya kasa ganewa, cikin duhun dare……….


