Hausa novels

Mijin Marigayiya Page 2 Hausa Novel

Cike da murna Alhaji Muhammad wanda shine Babba a waliyyan ango yace ‘Ah ai mu a shirye muke, hakan ai ya fi sauki Alhaji, Alhamdulillah Alhamdulillah. Shi Mustapha ai a shirye yake, lefe ma da sauran kaya duk gobe sai mata su zo su kawo.’Nan da nan suka gyara zama, Baba Sani ya kirawo mahaifin Khadija ya sanar da shi wanda shima a take ya amince, sannan ya kirawo makota da wasu daga cikin dangi. Suma ‘yan uwan Mustapha suka sanar da shi ya taho shi da abokansa mutum biyu. Kafin minti talatin guest room din Alhaji ya cika da mutane ana ta murna.Ba tare da bata da bata lokaci ba aka daura auren Khadija da Mustapha.——— Tana kwance a parlor dinsu a kan doguwar kujera tana chatting a waya yayinda kanwarta Nabila take zaune tana kallon TV; kaninsu Ahmad ya shigo parlor din da gudu yana ihu ‘Ta zama matar aure, Ya Khadija ta zama matar aure…’Zumbur ta mike daga kujerar yayinda itama Nabila ta mike tana cewa ‘Kaifa kana da matsala, don Allah ji yanda ka firgita ni.’Khadija tace ‘Wai me kake cewa ne?’Yana dariya yace ‘Wallahi an daura miki aure da Mustapha yanzu a gidan Alhaji.’Ta bude baki tana kallonsa cike da tsananin mamaki. Nusaiba ta daki kafadarsa tace ‘Kai Ahmad kaji tsoron Allah.’Yace ‘Wallahi da gaske nake, kirawo Baffa a waya ki tambayeshi.’ A take Mommy ta fito daga daki rike da waya jiki a sanyaye, Ahmad ya kalleta yace ‘Mommy ai an daura auren Yaya Khadija ko?’Ta daga kai tana cewa ‘Eh, yanzu Baffanku yake gaya min an daura auren.’ ta juya ta dubi Khadija tace ‘Khadija kin zama matar aure.’Ta fada kan kujera kamar wadda aka tura, to murna zata yi ko me? Bata taba zata za a daura aure yau ba, ta zata za ayi yanda aka saba; a kawo kudin aure a zo a sa rana sannan a shirya biki a nutse. Shikenan yanzu ta zama matar Mustapha? Ikon Allah.Ta kai hannu ta shafa kwarmin idonta inda taji danshi; kwallace ta fado. To kukan me takeyi? Murna takeyi ko kuwa tsabar mamaki ne? Nabila ta zauna ta doro hannunta a kafadarta tana kallon Mommy tana cewa ‘To Mommy sai mu fara shirin bikin kenan ko kaita kawai za ayi haka?’Ta banka mata harara tana cewa ‘Sai kace wata kaza?’Mommy tace ‘Uhm, sai dai mu jira Baffanku ya dawo muji.’Ta koma daki ta barsu a nan.____ To Yaya? Me kuke tunanin zai faru? Ga amarya ga ango, kuma ga lockdown a hanya.Gaba daya tunanin Khadija ya tsaya, wannan daura auren da aka ce an yi mata yana nufin nan da ‘yan kwanakin zata tare a gidan Mustapha. Fatanta daya Daddy ya bari ayi biki don gaskiya tana son biki.Karar wayarta ne ya katse mata tunani, tana kallon wayar tayi murmushi “My love” shine sunan da tayi saving lambar Mustapha da shi.’Hello.’ ta amsa murya kasa-kasa.Muryarsa zakwai cike da farin ciki yace ‘Ya na ji ki haka? Ko ba kya farin ciki ne? Alhaji ya hutar da mu, kinga next weekend kawai sai a kawo min amarya ta.’Tayi dariya ‘I was just not expecting it to happen today, but Alhamdulillah. Ai babu abinda ya fi zama da masoyi dadi.’’Hakane. So me kike bukata na bikin, ki sami Yaya Mama kuyi lissafi zuwa an jima sai ki gaya min na turo miki ta account dinki. In sha Allah ranar Tuesday za a kawo lefe.’’Ok, hakan yayi.’’Common, ni ina so na ji muryarki tayi zaki zakwai kamar tawan nan.’Tayi dariya ‘Ka kirawoni in an jima kafin nan na sha zuma zaka ji zakin da muryar zata yi.’Suka yi sallama ta ajiye wayar ta koma ta kwanta a kan gadon cikin sanyin jiki.Dab da azahar Yaya Mama ta karaso tare da yaranta Anisa da Jawad. Itace Babba a ‘yayan gidan su Khadija. Bayan ta gama tsokanar Khadija ta shige daki inda ta tarar da Mommy tare da kanwarta Anti Naja’atu suna ta tattauna bikin; don Baffa ya sanar da su a shirya a yi biki ranar asabar da Lahadi idan an gama sai a kai amarya.Bayan ta gaishesu ta zauna suka cigaba da tattaunawa a kan bikin.Jimawa kadan Yaya Mama tace ‘Ni wallahi Mommy tausayi ma Khadija take bani, Allah ya sa dai da gaske yake sonta kuma ya cigaba da kula da ita. Ga yara har hudu yana shirin hada mata da su, ai sai a hankali.’Anti Naja tace ‘Kada ki damu ai mace komai kankantarta raino baya gagararta.’Mommy tace ‘Yaran ma fa yana kawosu nan wajenta, kamar suna da tarbiyya da saukin hali ma.’’To kin ji ma. Kada kiyi mata magana ma ki sa ta zata wani tashin hankali ne don na ganta tun da aka ce an daura auren nan jikinta yayi sanyi.’Haka suka gama tattaunawarsu suka tashi.………..Ranar Lahadi bayan Magriba aka shirya Khadija a ka kaita gidan MustaphaBai zo da abokansa ba sai mutum daya wato Badaru, ba tare da bata lokaci ba suka sallami kawayen amarya Badaru ya kwashesu. Bayan ya rufe gidan ya dawo ya sameta tana ta faman share hawaye. Ya zauna ya lallasheta har tayi shiru sannan sukayi Sallah ya bude musu abincin da ya zo da shi suka ci. Da kansa ya kwashe kayan da suka gama cin abincin sannan ya dawo ya sameta a zaune a inda ya barta. ‘Yauwa, tunda mun koshi taso na nuna miki gidan naki kafin mu kwanta.’ ya fada yana murmushi. Ta mike a kunyace, har sun kama hanyar fita daga dakin ya juyo ya dubeta yana murmushi yace ‘Bari mu fara daga nan, nan ne dakinki.’ Tayi murmushi murya kasa-kasa tace ‘Ok.’Ya wuce ta bishi a baya ya nuna mata ragowar gidan; bayan dakinta sai dakinsa sai kuma dakin yara inda nan ne kuma dakin baki. Sai kuma parlor guda daya da dining area a dai-dai kofar kitchen. Bayan sun gama zagayawa ya kashe fitulun sannan suka wuce dakinsa inda zasu kwana.………. Ranar da Khadija ta cika kwana uku da tarewa a ranar bakin danginsa da suke ta zuwa ganin amarya sun lafa, don tunda gari ya waye babu wanda ya zo har azahar tayi. Suna zaune a parlor suna hirarrakinsu aka fara kiran Sallah, ya mike yana cewa ‘Bari naje masallaci na dawo.’‘Ok, by then nima nayi sallar nayi serving lunch.’ ta amsa itama tana mikewa.Tayi masa a dawo lafiya ya fice ita kuma ta shige kitchen.Kafin ya dawo ta yi Sallah ta gyara kwalliyarta sanna ta jera abincin a kan dininga table. Yana dawowa tayi masa sannu da zuwa sannan ya zauna a dining table ta zuba abinci suka fara ci. Fried rice ne tare da sauce din hanta da salad, daga gefe kuma ga hadadden zobo. Shiru sukayi kowa yana ta kai loma, sai da Mustapha ya kusa cinye abincin nasa sannan ya ajiye cokalinsa ya dauki zobon da ta zuba masa a kofin tangaran ya kora. Yana ajiye kofin ya dauki cokalinsa yana gyara abincin ya dubeta yana cewa ‘Umm! Kin iya girki fa.’Tayi dariya tace ‘Ai da na zaci santin kurma kake da ka kasa magana.’ ‘Au ashe ma sa min ido kika yi.’ ya fada yana sake cika baki da abincin.

Back to top button