Harijin Sarki Page 32 Romantic Hausa Novel
Haka musayar kalamai da sihiri ta yawaita tsakanin jini ɗayan suna yaƙar junansu ta ƙarkashin ƙasa Sultan Rashid ya gano mugun shirin da ɗan uwansa Ameer yakeyi akansa da uwargidansa Samha da jaririn cikinta da kwanaki yasa yake girma har takai da ta daina fita ko ina kullum tana ɓangarenta sai Granny ce ta dawo Amzir domin kula da ita da abinda take tare dashi, kasancewar itama Najjisa ta kasa haƙura kullum cikin yi miyagun jefe jefe take wa Samha da abinda ke cikinta, saidai abinda ke bata mamaki yanda tsafinta yake juyawa gareta kullum.To Samha ta kasance cikin halwar addu’a kullum da ko yaushe tana neman tsarin Allah daga tsafi da kaidin Aljanun gadon wannan masarauta tana kuma barranta ɗan cikinta da duk wani abu daya shafi tsafi tare da faɗawa Allah ya basu kariya ita da mijinta da ɗansu daga wannan guguwa data mamaye gidan sarauta.A cikin dare mai cike da iska, Samha ta farka daga barci da bugun zuciya mai karfi. Idanunta suka buɗe cikin duhu amma ta fahimci wani zafi yana ƙona mararta.Tana riƙe da cikinta, tana jin kamar ana ja ne daga ciki da wani irin ƙarfin da ba a iya gani.Ta furta da murya mai rauni:“Subhanallahi… ya rabbil arshil Azeem……”A gefe guda, Sultan Rashid yana tsaye a tsakar fadar Hasumiyar Zinariya, yana tsaka da yaƙin ruhi da ɗan uwansa Ameer.Iska na busowa kamar ana ihu, kuma wutar tsafi na walƙiya tsakanin hannayensu biyu.“Ameer! Ka bar komai ya koma ga Allah!”“Allah?!” Ameer ya faɗa yana dariya mai cike da tsoro.“Tun lokacin da aka haife ni cikin duhu, Allah ɗinka bai taɓa waiwayeni ba! Na nemi haske, amma da aka ganni cikin ruɗani, sai aka kulle ni a duniya ta ƙasa! Yanzu ni zan hallaka duk wanda yake ɗauke da jinin ka da nake ƙi har da cikin da yake jikinta!”Cikin wannan magana, Ameer ya ɗaga hannunsa sama ƙura ta fara tashi daga ƙasa, iska ta rikiɗe zuwa kalar toka, kuma wata murya daga cikin duhu ta fara kiran sunan Samha.A cikin ɗakinta, Samha ta durƙusa bisa darduma, idanuwanta sun cika da hawaye, hannayenta suna rawa tana ɗaga su sama.“Ya Allah! Na sani babu wanda zai iya kare ni da wannan cikin face Kai. Idan duniya gaba ɗaya ta haɗu da tsafi, Kai ne Mai Tsarki, Mai kariya daga kowanne sharri. Ka tsare min cikin nan da sunanka Ya Qahhar, Ya Hayyu, Ya Qayyum!”Da ta faɗa hakan, haske ya fara bayyana a cikin ɗakin nata fari kamar hasken safiya, yana fita daga jikinta.Ameer da yake nesa, sai yaji wani abu ya tsaya masa a ƙirji, ya ja baya cikin tsoro.“Me ke faruwa?!”Ya furta, yayin da wutar hannunsa ta fara mutuwa.Rashid ya tsaya yana kallonsa, idanuwansa sun cika da hawaye ko kaɗan bai burin zama sanadin hallakar ɗan uwansa yace “Wannan ba ƙarfin tsafi ba ne, Ameer. Wannan ƙarfin addu’a ne… daga ita da jaririn da Allah Ya sanya a cikinta. Wannan shine ƙarfin da baka da shi.”Ameer ya furta cikin ɓacin rai:“Jariri?!”Cikin fushi, ya saki wata annoba ta tsafi, wadda ta nufi gidan Samha kai tsaye kamar wutar duhu mai ƙona haske.Amma kafin ta kai ga gidanta, wani sautin Addu’ar Annabi Yunus (AS) ya ratsa iska, daga bakinta:“La ilaha illa Anta, Subhanaka inni kuntu minaz-zalimin…”Sai ƙarar wani ƙarfe ya bugu da tsafin Ameer ya watse, duhun da ya aika ya rikide zuwa hayaƙi mai fari ya ɓace.Samha ta fadi a ƙasa tana kuka, tana riƙe da cikinta, amma zuciyarta cike da natsuwa ta san cewa Allah ne Ya kare ta, ba Rashid, da tsafi ba.Rashid da yake a fadar, sai yaji zuciyarsa ta yi sanyi, yana jin muryar addu’ar da ta kare duka fadar yace.“Samha… Kin zama garkuwar masarauta, ba don jini ba, sai don imani.” Ameer ya tsaya da ido jajaye yana kallonsu daga nesa, yana fitar da huci yace“Idan addu’a ta kare ku yau, ba zata kare ku gobe ba…”Ya ɓace cikin duhu, iska ta koma sanyi amma sarauta ta san cewa rigimar haske da duhu bata ƙare ba, sai jaririn da ke cikinta ya shigo duniya.*SHUƊEWAR WATA UKU*Daren bai taɓa yin shiru haka ba a masarautar Zirkan.Ko iska ta tsaya, ko hasken fitila ya dushe, tamkar duniya ta tsaya jiran abu ɗaya, haihuwar wanda sama da ƙasa ke jira.A cikin ɗakin Uwar Gida, an kunna ƙananan turare masu ƙamshi. Samha ta kwanta, fuskar ta cike da zufa, amma idanunta na cike da haske hasken da yake fitowa daga zuciyarta.Granny tana gefenta tana karanta Suratul Maryam da murya mai taushi, yayin da Dr. Mahraz ke lura da lafiyarta da tsoro a idonsa.Rashid yana tsaye a bakin ƙofa, hannunsa na saƙale a ƙirjinsa, cikin damuwa fuskarsa na nuna tashin hankali.“Ya Allah Ka kareta. Ka kare su duka.” ya faɗa a lokacin da ya tabbatar bashi da wata gudunmawa da zai bawa Samha.A gefe mai nisa, cikin duniyar duhu, Ameer yana zaune gaban wani kwano mai jini.“Idan wannan jariri ya rayu,” ya ce cikin muryar mugunta, “to ikonmu zai ƙare har abada. Ba zan bari haske ya sake rayuwa cikin jininmu ba.”Sai ya ɗaga hannunsa sama, ya haɗa jini da ƙura, ya furta kalmomin tsafi:“Tashi duhu, ka shiga jikinta, ka kashe abin da duniya ke kira alheri!”Iska mai hucin zafi ta tashi daga ƙasa, ta nufi fadar Zirkan.Fitilu suka fara rawa, turaren wuta ya ƙone, ƙasa ta fara girgiza.Samha ta yi ƙara tana riƙe cikinta, tana jin zafin da ba ta taɓa ji ba azabar ciwon naƙuda me neman ɗaukar rayuwa bakinta dauke da addu’o’i da Iklasin cewa Allan ta yana tare da ita a daidai wannan lokaci ne wuyar tsallakewa, tace “Granny! Zafin nan yayi ƙarfi yana ƙonani!”Granny ta ɗaga murya cikin Neman taimakon Allah tace “A’uzu billahi minash shaitanir rajimRashid A’uzu bikalmatullahi tammat min sharri ma kalaƙ” wannan ƙurar tsafi ta hudo ta window ta shigo da gudu, tana kallon hasken da yake walƙiya daga jikin Samha, Granny tace “Samha! Ki daina kallon ƙurar tsafi Ki rufe idanunki! Ki karanta Ayatul Kursiyyu!”Da ta fara karantawa, muryarta ta canza — ta koma mai ƙarfi fiye da yadda mace mai juna biyu zata iya.“Allahu la ilaha illa Huwa, Al-Hayyul Qayyum…”Wani haske ya cika ɗakin gaba ɗaya, ya fantsama zuwa sama kamar walƙiya.Ameer, a duniyar duhu, ya faɗi ƙasa yana ihu, hannayensa suna ƙonewa.“Aaah! Wannan addu’ar… tana ƙona ni!”Daga nan kuma, aka ji kukan jariri mai ƙarfi, mai cike da nutsuwa, mai ɗauke da wani irin sauti na ruhi.Granny ta ajiye littafin Al-Qur’ani ta nufi gadon da Samha ke kwance da sauri tace“Alhamdulillah! Allahu Akbar! Jaririn ya fito lafiya!”Rashid ya durƙusa, hawaye na sauka daga idanunsa yakai hannu zai ɗauki jaririn Samha ta janye ɗanta, cikin Muryar galaɓaita tace “Idsn ka taɓashi zai rasa kariya Sultan” da sanyin jiki ya kalleta yace “Allah Ya kare shi daga duhun da ya tsani haihuwarsa”Samha ta riƙe jaririn a ƙirjinta, ta ce da murya mai sanyi “Ka gani Rashid? Duk tsafin duniya ba zai iya doke addu’a ba”…………



