Ruwan Zuma Page 34 Hausa Novel
(34) A kwana a tashi asarar mai rai, yau wata hud’u kenan da auren Haydar da Laila. Soyayya suke gwadawa juna tsaftatacciya wacce tasa suka shak’u da juna bana wasa ba. Laila sosai take kula da mijinta tana kuma iya bakin k’ok’arinta ganin ta sauk’e duk wani hak’k’insa dake kanta. Tun tana mamaki da kuma kunyar ta auri wanda tafi a shekaru har ta daina ta fara ganinshi a matsayin babban mutum kuma mai daraja a gurinta. Kamar yanda Haydar yaci burin auren babbar mata kuma Allah ya bashi, sai ya kasance shima ya zama version na mijin da Laila take so, wanda hankali, dattaku da kuma sanin yakamata na cikin qualities d’insa. Har a wannan lokacin babu labarin Abul ko kuma inda ya shiga, duk da cewa kuwa Mas’ud da Haydar sun saka a nemeshi ba tare da sanin Laila ba. Duk wanda yasan Laila yasan tana cikin zullumi da kuma bak’in cikin guduwan d’anta Abul, sai dai bata bari hakan ya k’ara ta6a rayuwar aurenta ba kamar yanda Abul d’in yaci buri. Ta yarda da addu’an da take yi bazai ta6a fad’uwa k’asa banza ba, komai daren dad’ewa Abul zai bayyana matuk’ar yana raye. Fatanta da kuma burinta shine Allah ya shiryashi kafin lokaci ya k’ure masa, saboda ita mutuwa bata sallama balle ta bawa mutum damar tuba ko sallama ga ‘yan uwansa. Ana tsaka da hakan ne aka cire lockdown wanda ya bawa Laila damar komawa shagonta da tayi kewa. Haydar kuma har lokacin yana aikinsa a company Lu’a Ventures, wanda zai iya cewa yawancin aikin company a kansa yake. A yanzu da albashinsa ya k’ara yawa sai ya kasance ya hana Laila sayan kayan abinci na gidan ya zamana kowanne wata zai tura mata kud’i tayi musu shopping tare da Amminshi. Sannan yace duk wani abu da take buk’ata ta fad’a mishi ba sai tayi amfani da kud’inta ba. Laila data saba kashe kud’inta ba tare data tambayi kowa ba sai hakan ya zame mata takura bana wasa ba, domin tana jin nauyin ta tambayeshi kud’i sai take ganin hakan bai mata tsari ba. “Haydar na saba biyawa kaina buk’atar rayuwa ba tare dana tambayi wani kud’i ba for almost 20years, zai bani wahala yanzu rana tsaka in fara nema daga gareka. Tunda ka kar6i sayan provisions ka barni inyi sauran tunda nima Allah ya hore mini kuma kamar taimaka maka zan dinga yi. Da fatan ka fahimceni?�? Girgiza kanshi yayi ba tare daya kalleta ba yace, “Laila, a yanzu inada rufin asirin da zan iya d’aukan duk nauyinki na dole, tunda nace ga yanda nake so sai ki bini a hakan saboda hak’k’inki dake kaina nake son sauk’ewa.�? “Idan kuma nace na hutashsheka fa?�? “Baza ki mini wannan wayon ba.�? Ya fad’i hakan yana zuge zip d’in rigarta. “Yaya dai Mallam?�? Ta tambayeshi tana rik’e rigarta. “Abunda kika gani.�? “Ka tsaya muyi magana.�? “A zaune ma nake.�? Ya bata amsa bayan ya samu nasarar rabata da kayan jikinta. “Haydar yaushe zaka bari inje asibitin muyi Planning d’in.�? Dakatawa yayi da abunda yake yi yayi shiru bai ce komai ba. Jin yayi shiru yasa Laila ta k’ura mishi ido tana jiran amsarta domin tana son sanin ainihin me yake ransa game da Birth control d’in da take son yi. “Haydar kayi magana.�? Ta kamo hannayensa wanda ya sauk’e a jikinta seconds uku da suka wuce. “Sai gaba.�? Ya bata amsar da kullum shi yake fad’a mata. “Yaushe kenan?�? Ta k’ara insisting. “Idan lokacin yayi zan fad’a miki.�? Ya fad’i hakan yana kwanciya a kan gadon ya bata baya. “Don Allah ka tashi yau kam muyi maganan nan. Kullum kenan amsarka ‘sai gaba�?, Ina k’ok’ari wajen ganin ban munafurceka ba naje nayi ba tare da saninka ba, amma kai ka kasa fahimtata kuma ka k’i mu zauna mu tattauna.�? “Bakya son haihuwa dani ne?�? Shine tambayar daya mata wanda bata yi tsammaninshi ba. “Ya za’a yi kayi tunanin haka Haydar? Don meyasa zan k’i son haihuwa da kai?�? “Ki bawa kanki amsa sai nima in san dalilin da kika takura dole-dole sai kin hana haihuwa dani.�? “Haydar abun bai kai haka ba.�? Ta fad’i hakan cikin sanyin muryar domin ta lura ranshi ya 6aci sosai. Tashi yayi ya zauna ya fuskanceta fuskarsa zallar 6acin rai yace, “Ina lura kullum na nemi biyan buk’atana dake sai kin kawo mini maganar Planning da kike son yi, saboda kina son in amince miki koda banyi niyyar hakan ba. Don meyasa kike son yin planning in ba k’in haihuwa kike dani ba Laila? Baki san bak’in cikin da nake ji ba Idan kika kawo mini wannan zancen, wallahi har na fara waswasi a zuciyata kan irin son da kika ce kina mini.�? “Me kuma ya kawo wannan maganan don Allah? Na sha fad’a maka dalilina cewa saboda na girma ne tsufa yazo mini Haydar. Na jima ban haihu ba wanda dole a yanzu idan zan haihu zan wahala sosai sannan ga jikin tsufa.�? “Wannan ba hujja bace Laila, mata da dama wanda suka fiki shekaru suna haihuwa kuma lafiya kalau. Wahala kuma da kike maganarta dama dolene ki sha tunda kowacce mace sai ta d’and’ana kafin ta kawo ‘yayanta duniya. Me kike nufi dani? In zauna banida ‘yaya har k’arshen rayuwata alhali matata zata iya haihuwa? Gaskiya baki so zaman lafiya dani ba muddin baki canja wannan k’udirin naki ba.�? Yana fad’in hakan ya sauk’a daga kan gadon ya maida kayanshi ya fita daga d’akin. Tana ji ya bud’e k’ofar falo ya fita daga gidan ma gaba d’aya. Zuciyarta bugu ta fara domin duk ranar data kawo mishi wannan maganan sai duka ransu ya 6aci. Meyasa ya kasa fahimtarta? A yanayin shekarunta da kuma dad’ewanta bata haihu ba zata sha wahala sosai Idan ta d’auki ciki. Tun ranar da suka fara had’uwa ta nemi ya dinga inzali a waje saboda amma ya mata dad’in bakin wai ba zata d’auka ba tunda ta jima bata san d’a namiji ba. Saboda gudun cecekuce a yayin da yake zumud’i da farin ciki sai tayi shiru bata mishi musu ba amma tayi addu’a sosai kan Allah yasa bata d’auki cikin ba. A wannan watan akan kwai take tafiya domin Haydar yak’i amincewa da k’udurinta sannan ga bak’ar jaraba daya tasata a gaba dashi, wanda har fata take a d’age lockdown kowa ya kama harkar gabansa. Wata na kaiwa k’arshe al’adarta ta dawo wanda tsabar murna har sujadar godiya tayi ga Allah. Haydar kuma daya samu labarin fuskarsa ba yabo ba fallasa, hasalima bai nuna mata komai ba sai kewarta da yace zaiyi a kwanakin da zata yi tana jinin. Tana gamawa ya cigaba daga inda ya tsaya wannan karon ta bashi shawarar yayi amfani da protection, karantar fuskarsa kad’ai da tayi yasa tayi saurin gyara zancenta da cewa taji wasu mazan haka suke yi idan sun hana matansu amfani da birth control. “Allah ya hanani amfani da Condom Laila, ni da matata sai na sanya labule tsakaninmu sai kace da karuwa zan kwanta?�? Wannan shine amsar daya bata wanda yasa taji haushi don meyasa zai kira sunan karuwa. Dalili kuwa a kwanakin baya ana yawan kiranta da wannan sunan, ta kuma tsani sunan da dukkan zuciyarta. Kwana biyu suka yi basa kula juna sannan daga baya suka sasanta, sai dai duk da hakan bata daina tambayarshi yaushe zai amince mata ba, shi kuma sai ya samu sabon salo na fad’a mata cewa wai ba yanzu ba. Yau dai gashi sun sake a karo na uku, wanda alama ya nuna ranshi ya 6aci sai dai itama ranta ya 6aci. Tana masa biyayya ba tare data dubi yawan shekarunta ba, tana k’ok’arin ganin bata karya dokarshi ko ta munafurceshi ba domin zata iya zuwa tayi ba tare daya sani koya gane ba. Sai dai ai Allah na ganinta, abunda akayi a rashin gaskiya kuma dole watarana sai Allah ya bankad’a sirrin, abunda zai biyo baya kuma ba dole a san adadin illan da zaiyi ba. Haydar yana fita ya tari achaba ya kaishi gidan Ammi wanda dama yau da yake asabar ne bai je ya gaisheta ba. A cikin d’akinta ya sameta da Meenat suna hira suna dariya, wanda hakan ya masa dad’i ba kad’an ba, domin bayan ya rabata da waccar mata mai ‘yayan sai ya zamana Meenat yini take a gidansu sai dare take komawa gidansu. Bayan Meenat ta gaisheshi ta fita daga gidan tana cewa Ammi, “Zan dawo anjima.�? Sai data fita sannan Haydar ya zauna a kan kujeran daya mata guda biyu wanda zasu iya shiga d’akin nata. Bayan ya gaisheta yake cewa, “Wai meyasa kullum idan nazo sai ta fita daga gidan kamar wacce zan gutsireta?�? “To kai daka k’ita don meyasa zata zauna tare da kai alhali tasan ba aurenta zaka yi ba?�? “Namiji mijin mace hud’u ne kuma ba’a san gaba ba.�? “Sai ta zauna jiran taga me gaban zai haifar tana sauraronka ko? Yaushe ma kayi auren da har zaka fara maganan k’ari. Haydar bana son jaye-jaye fa.�? Dariya yayi yana cewa, “Ammi ni na fad’a miki zan k’ara aure? Cewa nayi namiji mijin mace hud’u ne, kuma ba’asan me gaba zata haifar ba.�? “Hmm.�? Kawai tace tana kallonsa. Canja musu hiran yayi a nan take tambayarsa batun Abul d’an matarsa Laila. “Har yanzu shiru babu labarinsa Ammi. Amma yana kiran Maman nashi wai yaji ko ta kashe aurenta ya dawo.�? Ammi ta tafa hannu tana salallamai kamar yau ta fara jin hakan tace, “Yau ka gane mini k’addara don Allah. Tausayinta nake ji sosai wallahi. Kullum na kawo mata zancen sai naga fuskarta ta canja wanda uwa ce kad’ai zata gane halin da take ciki. Allah yasa taci wannan jarabawar, shi kuma Allah ya bayyanshi ya kuma shiryeshi.�? “Ameen Ammi.�? “Jiya bayan tafiyanka da yamma Maman Zunnu ta kawo mana ziyara.�? “Ammi bazaki rabu da wannan matar ba ko?�? Fad’in Haydar yana jin ba dad’i a ranshi. Ya zo gidanta ne don ya huce daga abunda ya faru tsakaninshi da Laila amma itama da alama zata tura mishi wani. A wancan lokacin ya samawa matar gidan haya ya kuma bata jari daidai aljihunsa kan ta fara sana’a ta dinga ciyar da ‘yayanta. Sai dai Ammi bata so hakan ba domin taso su zauna ne tare, bayan tafiyarta kullum maganar Ammi Maman Zunnu wanda tasan Haydar baya son ji. Haka kawai ya tsani matar har cikin zuciyarsa ba tare da shi kanshi yasan dalili ba. “Ya za’ayi In rabu da ita? Ai mutum rahama ne balle ita abun tausayawa. Ni ya kamata ma inje in dubosu tunda sau d’aya na ta6a zuwa gidan.�? Yana jin hakan ya mik’e tsaye domin gidan har ya gundureshi. “Zan koma gida akwai abunda zan yi.�? Da haka ya mata sallama ya fita daga gidan ya koma gidansa. Daga bakin k’ofa yake jin hayaniya wanda yasan bana kowa bane sai Umma Kakar su Abul, tun 6acewar Abul yau zuwanta na hud’u kenan gidansu tana musu d’iban albarka. Ya so kai k’ararta gurin hukuma amma Laila ta nuna bata yarda ba domin Umma was once her mother in-law, ko menene take mata bai kai ta kaita gurin hukuma ba, ai abun da kunya da kuma nauyi ace ta kai mahaifiyar Aliyu police station. Yana shiga ya samu Laila zaune a kan kujera ta sunkuyar da kanta k’asa tana sauraron zagi da cin mutuncin Umma, wanda a kullum tazo haka zata gama bambaminta Laila bata cewa ko kanzil. Sai shi Haydar d’inne yake magana idan yaga abun ya fara mishi yawa. Wayarsa ya ciro yayi dialing number Nazifi wanda ringing biyu ya d’auka yana cewa, “Umma tana gidanku ko?�? “Eh, ta zo.�? “Kuyi fa hak’uri zan zo na d’auketa. Basa ankara take fita ba tare data fad’a musu inda zata je ba.�? Minti goma da haka Nazifi ya shigo gidan bayan Haydar ya masa iso. “Munafukai, algungumai. Nasan jikana bazai 6ata haka kurum don kinyi aure ba, waya sani ko sayar dashi ko tsafi kika yi dashi don aikata mugun nufinki? Lamla tsakanina dake Allah ya isa ban yafe ba, wallahi nayi dana sanin aurenki da Aliyu yayi, Allah kar ya k’ara nuna mini bak’in rana irin ranar da Aliyu ya had’u dake. Kin cuceni kin salwantar da rayuwar jikana. Allah ya isa muguwar mata mai bak’ar aniya.�? “Umma ya isa haka don Allah. Kizo mu tafi.�? Fad’in Nazifi yana isa gurinta ya kamo hannunta. Ai da sauran k’arfinta ta fisge hannunta, fad’an kuma nan take ya dawo kanshi. “Ni yarinya ce da matsiyacin can zai kiraka kazo ka mayar dani gida? Me kuke d’aukeni? Wallahi Nazifi idan ka sake matsa mini sai na d’aga maka nono. Saboda rashin zuciya irin taka d’an k’aninka suka sayar amma ka kasa d’aukan mataki a kansu. Da Aliyu ne yake da rai sai inda k’arfinsa ya k’are akan iyalinka amma kai har na fara tunanin har da had’in bakinka a ciki.�? Wannan magana ta Umma ya sosa ran Nazifi domin tana yawan masa gorin da kuma nuna masa tafi son Aliyu a kanshi. Shekaru sun yi yawa wanda shima har ya fara tsufa amma har gobe yana jin zafin kwatantashi da take yi da k’aninshi. Laila tana jin hakan ta tashi ta shige d’akinta ba tare da Umma ta lura ba domin tasan Nazifi bazai ta6a bari ta bita cikin d’akinta ba. Haydar kuma da yake zaune yana danna wayarsa bai ko d’ago ya kallesu ba domin har ya saba da cin mutuncin Umma kuma duk abunda ta fad’a baya kai zuciyarsa balle ya 6ata masa rai, shi dai hayaniyar ce baya so sannan ya k’i jinin ta d’agawa matarsa hankali. “Allah ya huci zuciyarki Umma, amma ya kamata mu tafi gida ba wai tilasta miki zan yi ba.�? Fad’in Nazifi ciki rarrashi. Fashewa tayi da kuka alamar itama ta gaji da maganan tana son hutawa, da haka ya jata suka fita waje tana tsinewa Laila da Haydar albarka da kuma zuriyarsu gabad’aya. Minti biyu da fitarsu gidan yayi shiru, Haydar da yake danna waya bai san ma Ina yake shiga ba domin hankalinsa na kan Laila wacce ya sani yanzu haka tana can tana kuka. Zuciyarsa ce ta karye na tsantsan tausayinta domin dalilin aurensa da tayi duk wannan abun yake faruwa. Mik’ewa yayi ya shiga d’akin ya sameta kwance a kan gado tana share hawaye a fuskarta. Zama yayi a gefenta kana ya d’agota ta zauna tana rufe fuskarta wanda ya 6aci da hawaye. “I’m sorry domin nina jawo miki hakan. I’m so sorry.�? Bata ce komai ba sai dai kukanta daya yawaita wannan karon har numfashinta na sark’ewa. Hugging d’inta yayi tsam a jikinsa yana buga bayanta a hankali yana kwantar mata da hankali. “Karki bari maganganunta suyi tasiri a zuciyarki domin hakan take so ya kasance. Abul kuma da yardar Allah zai dawo gareki kuma ya shiryu. Don Allah ki daina kukan nan domin har cikin zuciyata nake jin zafin hakan.�? Ya d’ago fuskarta zai share mata hawaye ta kawar da kanta tana sharewa da hannunta. “I’m so sorry.�? Da haka yaci gaba da lallashinta har ta kimtsa kanta sannan ya bata maganin ciwon kai ta sha bayan ta fad’a mishi kanta na ciwo. Kwanciya tayi ta rufe idanunta shi kuma ya tsaya yana kallonta cike da tausayawa. Da yana da iko daya binciko duk inda Abul yake a duniya ya kwankwasa masa hankali a kwakwalwarsa ko don Laila ta daina damuwa. Yana yawan tunani da kuma jin zafin gudun Abul wanda idan ya tuna har d’aci yake ji a mak’oshinsa, hakan yasa yake k’ara tausayawa Laila domin yasan abunda take ji ya ninka nashi sau dubu saboda ita d’in uwa ce. Shi kanshi ya sani ba k’aramin k’okari take yi wajen ganin abunda ya faru da ita ya shafi aurensu ba, yasan tayi jarumtaka kuma ta cancanci duk wani farin ciki na duniya saboda hak’urinta. Yana zaune a gefenta har bacci ya d’auketa tana rik’e da kanta wanda tace yana sara mata kamar zai tsage. Addu’a ya mata kana ya tofa mata a kan nata ya tashi ya fita daga d’akin don d’aura musu abincin rana, zuciyarsa kuwa cunkushe take da tunani kala-kala da kuma neman mafita ta wata hanya daban. Kwana biyu da haka Laila ta dawo normal yanda take, wanda dama duk ranar da Umma tazo sai mode d’inta ya canja na wasu kwanaki. Haydar bai yi k’asa a guiwa ba ya nemi biyan buk’atarsa ta kuma bashi kanta ba tare data masa maganan Planning ko wani abu ba. Sai dai yana gama abunda zai yi ta tashi ta d’aura zaninta ta fita zuwa kitchen. Curiosity yasa ya bita a baya domin a daa takan d’an huta kafin ta tashi ta shiga wanka. A kitchen ya samu ta jik’a ruwan gishiri zata sha. “Laila me wannan d’in?�? Ya tambayeta yana k’ar6an kofin daga hannunta. Bata nuna ta razana ba illa ficewa da tayi ta barshi a kitchen d’in yana rik’e da kofin nata. Bin bayanta yayi yana tambayarta tayi shiru bata ce dashi komai ba, shiga band’aki tayi yabi bayanta yana cigaba da demanding dalilinta na shan ruwan gishiri. Mutuwa take son yi ko dai maganin hana d’aukan ciki ne? “Magana nake miki kinyi banza dani, me zaki yi da ruwan gishiri?�? Laila ta kunna shower ta fara wanka bayan ta juya mishi baya. “Duk abunda zaki yi baza ki hana hukuncin Allah ba Laila. Sannan baza ki hanani haihuwa ba domin ina so sai dai in Allah ne yayi bazan haihu ba. Sannan idan kika k’ara amfani da maganin hana d’aukan ciki na barki da Allah.�? Yana gama fad’in hakan ya ajiye mata k’ofin nata a k’asa ya fita daga band’akin yana jin wani irin mugun zafi a zuciyarsa. Wardrobe d’insu ya bud’e ya ciro kayansa kaff da yake ciki ya kaisu d’akin Mas’ud na da, wanda babu komai a ciki sai katifa da wardrobe. Da haka ya dawo ya d’auki sauran tarkacensa Laila na kallonshi bata ce mishi uffan ba domin itama haushinsa take ji bana wasa ba. Dawowansa na biyu ya shiga band’aki ya d’auki abubuwansa dake ciki ya fito zai fita tace, “Ina zaka je?�? “Away from you tunda kin tsaneni.�? Kafin ta k’ara yin magana ya fita. Zama tayi a bakin gado tana jin duniyar ya fita a kanta dalilin halin da suka tsinci kansu da kuma aurensu a ciki. Dama akwai ranar da Haydar zai iya raba musu makwanci? Meyasa ya kasa fahimtarta? Saboda shi an daina tsokanarsa da kuma aibatashi akan aurenta da yayi? Har yanzu, kuma har gobe wasu mutane basu fasa yi mata bak’ar magana kan auren Haydar da tayi ba. Ya zata d’auki cikinshi tayi yawo dashi mutane na nunata da yatsa ana cewa yaro ne ya mata ciki? Da girmanta ta yaya zata iya haihuwa? Ga uwa uba ‘yarta Sabrin wacce itama yau ko gobe za’a iya cewa tana da ciki. Ina zata kai wannan abun kunyar ace tana tura cikin Haydar, Sabrin ma na tura ciki? Surukinta yazo gaisheta ya ganta da ciki yana yana ayyanawa a ranshi Haydar ne ya mata. Wannan abun kunya har yaushe? Yanzu ma da take aurenshi bata huta ba, idan kuma ta kuskura tayi ciki abun zai fi haka domin Umma ma kad’ai ta isa tasa taji ta tsani duniyar da duk abunda yake cikinta. Bata shirya d’aukan ‘yayansa ba, kuma bata tunanin zata iya haihuwa dashi. Yayi hak’uri ya zauna a haka ko kuma suyi adopting yaro ko yarinya daga Orphanage. Ko dai zai ce zai k’ara aure tunda ta k’i haihuwa dashi? Saurin girgiza kanta tayi dalilin d’acin da taji a mak’oshinta data hasko wata mace tare da Haydar d’inta ba ita ba. “Ba zai iya rayuwa da kowacce mace ba sai ni.�? Ta furta da fatar bakinta wanda ya isa kunnenta ya aikawa kwakwalwarta ita kuma ta hau kan zancen ta zauna daram da6es. “Ni kad’ai na isheshi rayuwa domin ina da tabbacin ba zai iya had’a soyayyata da kowacce mace ba.�? WATA RAYUWA… Abul ne tsaye a bakin wani chemist sanye da kod’addun kaya yana jiran mutanen da suka zo sayen magani su watse kafin ya shiga ya sayi abunda ya kawoshi. Idan ka ganshi a wannan lokacin bazaka ta6a cewa shi bane dalilin rama da kuma kod’ewar da yayi wacce ta saka ya zama baki kamar wanda ya k’one a gobara. Fuskarsa ta tanik’e kumatunsa sun burma ya zama tamkar k’ashi da rai yana yawo kwararo-kwararo neman abinci da kuma kud’in da zai sayi kayan maye. Abunda ya faru a rayuwarsa a baya shi kanshi baya son tunawa dalilin bak’ar wahala da azabar da yasha. Yana nan tsaye har mutane suka k’are sannan yaja k’afarshi da yake d’ingisawa ya shiga Chemist d’in. “A bani Codein.�? Shine abunda ya fara fad’a musu bayan ya shiga. Wani irin wawan kallo masu shagon suka watsa masa sannan d’aya daga cikinsu wanda daga ganinshi kaga Ustaz yace, “Akwai amma ba zamu baka ba saboda amfani dashi da zaka yi ka 6atar da hankalinka. Ka gyara rayuwarka ka tuba zuwa ga Allah domin wannan rayuwar daka jefa kanka a ciki baza ta haifar maka mai kyau ba.�? “Banza shashasha. Wa’azin uban me zaka mini da wani gemunka kamar bunsuru ka d’agashi sama kana mak’e murya? Idan ba zaku sayar mini ba akwai Chemist dubbanni da zasu sayar mini.�? D’ayan mutumin wanda k’ani ne ga wanda Abul ya zaga ya tashi a zuciye zai gaurawa Abul mari yayanshi Ustaz d’in ya dakatar dashi. “Idan kace zaka dinga saurin 6ata rai da irinsu to da kai dasu baku da banbanci, idan basu da hankali kai kayi amfani da naka hankalin kar ka biye musu.�? “Yen yen.�? Fad’in Abul yana barin shagon bayan ya tofar musu da yawu a bakin k’ofa. “Yaya kana gani ya zubar mana da yawu kan tiles?�? “Ka barshi, ka kuma mishi addu’a Allah ya shiryeshi domin yana cikin jarabawar rayuwa. Alhamdulillah bi ni’imatil lah.�? Jikin k’anin ne yayi sanyi tunowa da yayi da rayuwar yayan nasa kafin ya zama Ustaz d’in. Shima ya fuskanci jarabawa ta sace-sace kafin Allah ya shiryeshi, ya zamana kaff yaran gidansu babu mai hankali da kuma nitsuwarsa. “Hakane Yaya. Allah ya shiryeshi da kuma masu hali irin nashi.�? “Ameen thumma Ameen.�? Abul yana barin gurin ya koma ainihin unguwar da yake zama da k’afa tsabar rashin kud’i. Dalilin da yasa yaje wancan Chemist d’in shine wanda yake sayar musu a unguwar nasu yana binshi bashi har na dubu daya amma bai biyashi ba. Kuma yace matuk’ar bai biyashi duka kud’insa ba bazai sake sayar mishi da magani ba. Yanzu dolenshi zai je ya rok’i Imaa ya taimakeshi ya bashi saboda babu inda ya sani inda zai je a bashi magani babu prescription. Zaman Abuja kenan sai wanda ya shirya. A bakin shagon Imaa ya samu abokan shashancinsa suna shan taba ya wucesu ba tare daya musu magana ba. “Imaa bani Codein mana.�? “Sai ka biyani kud’ina don ubanka.�? “Nace ka daina zagin ubana, ka zagi uwata amma banda wancan daya mutun.�? “Gerrout before a bash your head for this wall.�? Wannan karon cikin fushi yayi maganar domin ya tare mishi k’ofar tsukakken Chemist d’in wanda ta nan yake shan iska. “Please na, kaga yau nazo da kudina zan biyaka.�? Ya ciro d’ari biyu da hamsin wacce aka bashi bayan kwadagon da yayi a kasuwa. Kamar walkiya Imaa ya wafce kud’in ya soketa a cikin aljihunsa yana zare masa ido. Abul da sai a lokacin hankalinsa ya dawo jikinsa yayi saurin shiga shagon yana cewa Imaa ya bashi kud’inshi amma tuni Imaa ya hankad’oshi waje, sai gashi ya zube a k’asa a gaban abokan nashi. “Dan iskan yaro lalatacce ni zaka nunawa rashin kunya?�? Fad’in Imaa yana naushin cikinshi da k’arfin da Allah ya bashi. Wata siririyar k’ara Abul yayi mai tattare da wahala ya dunk’ule guri d’aya yana rik’e da cikinshi. Wanda suke zaune a bakin shagon suka tashi tsaye suna kallonshi sai dai sun san shiga fad’an Imaa death wish ne, domin zai iya had’asu duka yaci uwarsu ba tare daya gaji ba ko kuma suyi nasara a kanshi ba. K’ato ne, bak’i mummuna kuma mai tsayi. Baya shan kayan maye amma ya fisu hauka dalilin rashin imaninsa da kuma rashin tsoro. Wata naushin ya k’arawa Abul wacce tasa ya fara kakarin amai, Imaa na ganin hakan ya jawo kwalar rigarshi ‘kiiii�? ya kaishi bakin kwatan unguwar ya watsar dashi. Amai Abul ya fara yi wanda yake fitowa kore kamar ganyen bishiya kuma mai yauk’i. Yanda yake aman kamar ranshi zai fita ya bawa Banney tausayi, ya tako ya iso gurinshi ya tsaya a kanshi. Sai daya gama aman da taimakon Banney ya mik’e tsaye suna layi dukansu suka wuce d’akin da suke kwana wanda shago ne k’arami, k’ofar shagon da yake na katako ne k’asan ya bangare yanda mutum ko dabba zasu iya shiga koda kuwa an kulle. Banney ya watsar da Abul kan tsummokaran kayansu kana ya koma lungun da yake kwanciya ya toni rami ya d’auko chocolate snickers ya bawa Abul. “You are sick man. Typhoid ne yake damunka daga ganin aman da kayi. You should see a Doctor asap.�? Murmushin yak’e Abul yayi kana ya 6are chocolate d’in ya fara ci bai yi magana ba. A ranshi kuma cewa yake yi duk cutar da take jikinshi sai dai ta kasheshi saboda bashi da kud’in neman magani. Banney da shima k’addarar rayuwa ta jefashi a halin maye ya dubi Abul yace, “Ka koma gida, zaman nan bai dace da kai ba.�? A fusace Abul ya juyo yace, “Kai don uwarka meya hanaka komawa? Da yanzu ka zama d’aya daga cikin successful Doctors d’in da ake ji dasu a Nigeria.�? “Do not bring my past into this.�? Yayi warning d’in Abul yana masa mugun kallo. “Nima karka sake mini maganan komawa gida. I have no family left.�? Da haka suka yi shiru Kowa da abunda yake sak’awa a ranshi, a yayin da Banney ke tuna dalilinshi na barin gatanshi shi kuma Abul tuna wahalar da yasha yake yi har rana mai kamar ta yau kamar haka;…..
Mum Fateey👌


