Kimiya da Fasaha

Matasa Ga Wani Sabon Tallafi Daga Kamfanin MTN

Assalamu alaikum warahmatullah, barkanmu da warhaka, a yau zamuyi bayanine dangane da kamfanin MTN Nigeria wanda ke ta hannun MTN foundation zasu bada tallafi na training dakuma kayan aiki koh kudi ga matasa a wasu daga cikin cikin jahohin Najeriya

Shirin na ICT and Business Skills Training phase 6 na hadin gwiwa ne a tsakanin kamfanoni kamarsu.

  • Microsoft
  • Meta (Facebook)
  • MTN foundation

Wannan training za ayi shine tsawon wata biyar kuma a online za ayi shi sannan kuma kamfanin MTN zasu rinka tura muku data har kugama wannan training din da aka shirya wanda mutane dubu uku ne zasuyishi, sannan acikin mutun dubu ukun za’a zabi mutun 300 da sukafi kokari araba musu kayan aiki na kimanin million casa’in.

Kunga kenan kowa zai samu kayan aiki na kimanin dubu dari uku, ammafa wanda sukafi kokari mutun dari uku sune kadai zasu samu wannan daman.

Sai kuma sharuddan cika wannan shirin wato abinda ake da bukata sune kamar haka

Matashi daga shekara 18-35
Yakasance yanada kasuwancin da yakeyi wanda yakasance yana aiki kar yayi kasa da shekaru biyu
Yakasance kasuwancinka yana daya daga cikin wannan jahohin

  • Yobe
  • Niger
  • Kebbi
  • Ebonyi
  • Edo
  • Ekiti

Yadda zaka cike wannan shirin na ICT and Business Skills Training phase 6 shine, da farko zaka bi wannan link din dake kasa, kashiga 👇👇

 

https://www.mtn.ng/mtnf-ict/

 

Kana tabawa zai kaika shafin MTN foundation saika tsaya ka karanta, inka gama karantawa zakaga inda aka rubuta click here to apply saika taba wajen.

Kana tabawa zai kaika inda zaka fara cike wannan form din, saika fara cikewa amma ka tabbatarda kasa bayanai masu inganci da kuma email address mai amfani sbd ta email dinne zasu turo maka sakon tabbacin ka samu ko akasin hakan.

Kana gama cikewa saika taba kan Next step zai kaika inda zakasa address dinka dana kasuwancinka.

Shima kana gamawa saika taba kan Next ma’ana zuwa matakin gaba kenan.

Mataki nagaba kuma bayanaine akan kasuwancin da kakeyi saika cike, shima kasa bayanai na gaskiya a wurin.

Sai mataki na kusa dana karshe shine zakasa abinda yasa kakeson yin wannan training din saika zaba abinda yasa sannan ka taba kai Next

Mataki na karshe kuwa shine matakin karatu wanda zaka zabi matakin karatunka misali SSCE koh Degree dadai sauransu.

Toh daganan saika taba kan Accept our terms and condition sai kai submit shikenan ka gama saika jira mataki na gaba wanda sune zasu tuntubeka ta email koh lambar wayar dakasa aciki.

Back to top button