Haihuwa Da Hanji Page 33 Hausa Novel
“Rayyan a yau Allah ya nufa ka sake samun wani nauyi a kanka bayan nawa da na ƙannenka, na san ba wai ka ganta bane ka ji kana so har aka yi muku aure Allah SWT ka ba zaɓi shi kuma ya zaɓa maka abinda ya fi dacewa da kai da kuma rayuwarka, idan har ka ci amanar ta ko ka ha’inceta ba ita ka yi wa ba Allahn da ya baka shi ka yi wa, kar ka kalleta domin ni, kar ka so ta domin ni, kar ka yi mata wani abu na alfarma domin ni duk abin da zaka yi mata ka yi saboda Allah, idan ka so ta ka so ta saboda Allah don Allah ba don ni ba ka ba marar ɗa kunya. Ka zame mata gatan da ta rasa, ka zama uwa, uba kuma jigo a rayuwarta, ka zama majingina a gareta ka tallafi rayuwarta daga cikin duhuwa zuwa haske madawwami”A hankali ya ɗan ɗora kanshi a gefen kafaɗarta sai ta ji hucin zafin jikinshi na sauƙa Mata, hannunta ya kama “Mammi in shaa Allahu zan yi amfani da duk abin da kika ce”Daga haka bai sake magana ba, ta san a takure yake ta kuma san akwai abinda ke cinshi a rai a yanzu haka wanda bata tantama shi ya haddasa mishi zazzabi kuma muddin ya cigaba a haka ba zai yi bacci ba amma sam ba zata tambaya ba, ba za ta matsa mishi ba.”Ka tashi ka sha magani Saraki”Ta faɗa, da kyar ya buɗe lumsassun idanunshi da suka rine ainun ya miƙe zaune, karbar pills ɗin yayi ya sha wanda ta haɗa da panadol a hankali ya kalli time karfe tara ne da wani abin, Miƙewa yayi yana mayar da hannayenshi cikin aljihun hoodien jikinshi cike da dauriya yace “Sai da safe””Allah ya baka lafiya”Ya amsa da Amin kan ta mishi sai da safe ya fice da kallo ta bishi ta san sai a hankali zai saba da wannan sabuwar rayuwar kuma, ta san sai Afeefah tayi haƙuri ta kara juriya kafin ta samu yadda take so da shi matsalar kawai ya kasance ta shiga ranshi murmushi ta ɗan saki kan ta sha nata maganin itama ta shiga don kwanciya saboda kowa ya tafi baƙi kam duk babu kowa.Wani iri yake ji a haka ya kutsa kanshi cikin parlorn bakinshi ɗauke da sallamar da iya shi kaɗai ya san yayi kayanshi, taku biyar yayi ya samu kujera ya zauna yana dafe kanshi da kaman zai rabe gida biyu, numfashi ne yake mishi wahalar fita kuma ya san yanayinshi ne da tunanin da ya saka a ranshi, wani irin zafi yake ji kaman ana ɗora mishi wuta a kan zuciyarshi ina ma da zai iya da kuka zai yi da ihu zai yi ta yi sai ya samu salamar abin da yake ji a ranshi, zamewa yayi ƙasa kan carpet ya ɗora kanshi a kujeran yana rike zuciyarshi ya jima sossai cikin wannan yanayi sai da ya ɗan samu relief ya miƙe ya nufi ɗakinshi kai tsaye, ruwa ya sha har gora uku kan ya shiga zame kayan jikinshi daga wurin yana nufan bayi, ruwan sanyi ya sakarwa kanshi yana yamutsa gashin kan nashi a lokaci ɗaya yana dan buga glass ɗin wurin wankan da hannunshi.Sai da yaji zai iya faɗuwa idan bai bar wurin ba ya fito ɗaure da towel ya hau gadon ya kwanta ko ruwan jikinshi bai tsaya tsantsanewa ba ya ja bargon ya rufe har kanshi ba wai don zai yi baccin ba don ko ya rufe ido abin da ya tsana yake kallo.Ita kam Afeefah dama ta san ba zuwa zai yi ba, bayan kowa ya tafi ta miƙe tana kallon ɗakin har lokacin zuciyarta ke maimaita mata wai ita ce fa matar aure, yanzu ita ta tashi daga buduruwa matar auren ma wai matar Rayyan, Allah buwayi gagara misali Allah mai yadda ya so a lokacin da ya so, a hankali take bin ɗakin da kallo ya ji kaya iya kaya yayi kyau fiye da misali gashi wadatacce don za ta iya komai free ciki yana da girma, akwatunan da aka jera mata ta bi da kallo guda goma sha biyu wai akwatunan aurenta ne, ita dake da kayan da basu wuci biyar ba ita dake fama da allura da zare a kullum tana facin kaya ita dai Afeefah Annoba kuma Mayya, sai hawaye suka fara sintiri a idanunta tana jin karin imani tana jin wani irin yarda da ubangijinta. A haka ta shiga bayin shima ta ƙare mishi kallo komai na ‘yan gayu, bata yi wanka ba don sai da tayi wanka ta saka kaya aka kawo ta karamin akwatin da Abeeha tace mata kayan bacci ne ciki ta buɗe ta duba silk riga da wando cream Color yana da adon Black lace daga kirji da kuma ƙasan kafafun wandon ta saka, kamshinta da kamshin ɗakin har ya so yayi mata yawa ga sanyin Acn dake busawa kashe wutan tayi ta hau gado ta kwanta tana sake jin salama a ranta sam bata wani sa damuwar rashin ganin Sarakin ba don ta riga ta sakawa kanta haƙuri da juriya har Allah ya kawo karshen komai Dukda bata san yaushe ba bata san ko karshen zai zo ba amma she have her trust in Allah zai mata komai ba sai ta damu kanta ba Adu’a ne babba kuma zata cigaba.Washegari da safe bayan tayi sallah ta ɗan koma bacci, ƙarfe tara ta farka ta sauƙa daga gadon da kaman kar ta tashi tsabar daadinshi da take ji ta wuce bayi ta yi wanka ta fito ta fara neman kaya cikin sababbin dinkunan da telan Jannah ya chanchada mata, wani atampha doguwar riga A shape ta fitar ta shirya ciki tayi kyau sossai ta feshe jikinta da turarukanta sababbin waenda kamshin suka yi mata ta kafa ɗauri, bata sa kwalli ba sai ta saka lipstick kawai accesories da tayi anfani na silver sai suka ƙara haskata tayi kyau ainun gidan ba baƙonta bane amma sai ta fara tunanin ta saka gyale ne ko kar ta saka? Tsoro take kar ta fita su haɗu don yanzu ba kaman da bane da ba lallai ma su hadu ba in ba wurin Mammi ba, a hankali dai ta sa hannu ta buɗe kofan ɗakin ta sanyo kai cikin parlorn, ko taku biyu bata yi ba idanunta suka sauƙa kanshi a farko ta tsorata sai kuma ta fahimci kaman bashi da lafiya ne don ga matar da take matsayin likitarshi zaune a kujeran dake fuskantar shi, yayi relaxing sanye da wasu blue pjamas riga da wando complete, kafafunshi babu takalmi suna lume cikin tattausan carpet ɗin dake shimfide parlorn, fuskarshi yayi ja sossai haka gashin kanshi a hautsine.Wani iri taji a ranta sai taji tausayin shi na bin jikinta kaman ruwa, ta riga ta san dalilin da ka iya kawo mishi ciwon a hankali ta shigo cikin parlorn Likitar na kallonta ta saki murmushi itama ta mayar mata a hankali ta ɗan duƙa ta gaisheta ta amsa da kulawa tana tambayarta Ya Rayyan da jiki? Ita dai ta amsa da da sauƙi amma bata ma san bashi da lafiyan ba sai yanzu.A hankali ta kalleshi idanunshi na a lumshe har lokacin, matar ta miƙe “Allah ya baka lafiya zan zo gobe da safe, please make sure ka ci abinci ka sha waennan pills ɗin”Ta karashe tana ajiye mishi wasu pink pills a roba.Sai a lokacin ya ɗan buɗe ido”Thank you”Tayi murmushi ta yiwa Afeefah sallama ta fice.Sai aka bar su su biyu a parlorn, yatsina fuska yake don kamshinta har kanshi yake ji ba tun yanzu ya fara ji ba tun ranar da suka same shi a dining da Abeeha ya iya bambance nata kamshin da na Abeeha, yanzu ma gashi ta zo ta tsaya mishi sai hawa kanshi yake tsaki ya ɗan ja ya buɗe ido sai karap suka hada idanu don kallonshi dama take tana tunanin ta inda zata fara gaishe shi ganin ya kalleta sai tayi saurin cewa “Ina..kwana!”Ya yunkura ya miƙe zaune da kyau, bata yi zaton zai amsa ba sai jin deep and calm voice ɗin shi da bai yi matcing da situation da yake ciki ba ya ce “Good Morning!”Daga haka ya miƙe ya wuce ta ya shige ɗakinshi, ta sauke numfashin tsoro tana nufan kofa saboda knocking da ake, masu aiki ne rike da baskets na abinci kai tsaye suka jere mata su a dining suna gaisawa don sun saba da juna dama, plates, cups da spoons taje ta ɗauko ta zo ta ƙarasa haɗa dining ɗin amma bata sani ba ta kirashi ne ko ta kyale shi, ta san ba zai so shisshigi ba in ta dameshi ya iya karyata don ya sha ambata kalan ya zo ya faru ta shiga uku, abincinta ta zuba ta ci har ta gama karyawa bai fito ba don haka tayi sashen Mammi don ta duba ta.A zaune ta sameta ta gama karyawa tana shan magani tana ganinta fuskarta ya washe da fara’a “Ɗiyata ni da nace yau za ki huta sossai sai ga ki da sassafe? Sannu da zuwa”Yadda take mata sai ya saka kunya kamata kaman wacce ta fito daga wani unguwar, a ƙasa ta duƙa ta gaisheta tana mata ya jiki.”Alhamdulillah dawo nan gefena Afeefah, ina shi Sarakin?”Wani kunyar ne ya sake lullubeta ta kasa magana Mammi tayi dariya kawai ta janyo wayanta ta kirashi “Jiya ya tafi anan ban gamsu da yanayinshi ba, kun gaisa da safen nan?”Kai ta gyaɗa “Eh na fito na same su da likitan shi suna magana””kin ga ko, sai in rasa Meyasa yake ajiye damuwar da baya bayyanawa yanzu baya so in sani ne ya ƙi zuwa nan tun sassafe na kira ban same shi ba je ki ce ya zo”Gabanta ne ya faɗi rassss, ta ya zata fara kiranshi? A hankali ta miƙe ta fice zuciyarta na racing har ta shiga parlorn inda Allah ya taimaketa ma ta samu yana parlor a zaune kan dining yana karyawa wayanshi na a speaker alamu waya yake, a gefenshi ta ja ta tsaya sai ta ji Muryar dake tashi kaman ta san Muryar kuka me Muryar take har tana shidewa a hankali take cewa “Ya Rayyan bakin cikin Ya Saleem zai kashe mana Mommy, duk abubuwan da ya dinga yi a baya mai sauƙi ne yanzu ya kore mu ya saka surakanshi a gidan, bai damu da mun ci ko bamu ci ba, mun yi karatu ko ba mu yi ba muna lafiya ko babu tun muna zuba ido yanzu wata kenan da ko mun je gidan ba’a bari mu shiga, ga mommy kwance a asibiti saboda damuwa da hawan jini…!”Dukda maganan da take yi ɗin ya shige shi sossai, damuwa ya nuna a kan fuskarshi sai dai bai tanka ba har ta gama ta cigaba da kukan.”A wani asibiti take?”Ya jefa maganan a hankali “Tana 44 ne, anan muke da file”Kai ya gyaɗa kan ya katse wayan, Afeefah dake tsaye jikinta ne yayi wani irin sanyi a hankali zuciyarta ke motsawa da wani irin yanayin damuwa ba dai saleem da ta sani ake magana akai ba? Amma ai wannan Muryar ta Sadiqa ce, saleem ne har ya kori mahaifiyarshi a gidanshi? Ko jikinta duka kunnuwa ne ba zata yarda yana cikin hankalinshi yayi hakan ba, Wani irin tashin hankali ne ya zo mata har ta kasa boyewa ta manta waye a gabanta tace “Yaya Saleem ne cikin wannan hali? Shi ne ya kori mahaifiyarshi da kanshi? Su Samha ne ke cikin irin wannan damu…”Haɗa idanu da suka yi ya sa maganar ta katsewa idanunta har sun cika da kwalla suna shirin zubowa, gani irin kallon da ya mata ya sa ta saukar da idanun ƙasa, ajiye spoon ɗin hannunshi yayi ya zari wayan bai miƙe ba yana nuna ta da wayan ya ce “Kika kuskura kika sake hawaye ɗaya ya zubo miki a kan fuska za ki gane ba ki da wayo…!”Mukut haka ta haɗiye kukan zuciyarta na cigaba da racing cikin mixed feeling ga idanun da ya zuba mata yana jira ya ga zata yi kukan ne ko ba zata yi ba ga damuwar halin da ta ji wai saleem na ciki.”Mam..mi na ƙiran ka”Ta faɗa a ɗan tsorace. Kwafa yayi ya miƙe ya fice daga wurin da sauri ta dafa dining ɗin tana jan kujera ta zauna….
