Uncategorized

Jaruma Nafisat Abdullahi ta fice daga cikin shirin Labarina

 

Jaruma Nafisa Abullahi wadda akafi sani da Sumayya cikin shirin Labarina mai dogon zango ta bayyana ficewarta daga shirin saboda wasu dalilai, a wata takarda data rubuta zuwa ga mai bada umarnin shirin wato Aminu Saira tace baza ta iya ci gaba da fitowa a cikin shirin ba saboda bata da lokaci kuma abubuwa sun yi mata yawa.

Tace yanzu haka tana makaranta kuma tana da wani kamfani da take kula da shi, ga kuma kasuwanci wadannan da wasu dalilai yasa dole za a daina ganinta a cikin shirin Labarina.

KARANTA:

  Hukuncin Abincin Kirsimeti Ga Musulmi Fita ta farko

  Gwamnatin Tarayya zata dauki karin Matasa 400,000 aikin N-Power

 Dalilin da yasa mawaki Hamisu Breaker ya yi wa yan uwansa mawaka zarra.

 Rahama Sadau Da Shatu Garba Mata biyu da suka fi shan ce-ce-ku-ce a shafin sada zumunta

A karshe tabawa masoyanta haƙuri kuma tace itama ba a son ranta hakan yakasance ba. Sai dai akwai jita-jita dake yawo cewa Nafisa Abdullahi sun samu matsala ne da Aminu Saira shiyasa aka daina ganinta a cikin Labarina, amma acikin takardar data aika jaruma Nafisa Abdullahi tace babu wani sabani tsakaninta da Aminu Saira kawai dai bata da lokaci ne don haka tana ƙara bawa masoyanta haƙuri.

Back to top button