Hausa novels

Abban Sojoji Takun Ƙarshe Book 3 Chapter 101 Complete Novel

*Father of soldiers*

*🔥TAKUN ƘARSHE🔥*

Am sorry🙏

 

Babu abunda zan yi maki,a haka ma daɗi nake ji,kina kallona ina kallonki,”murguɗa mashi baki tayi tare da kawar da idanuwanta gefe guda,

Wuraren ƙarfe 8 na safe,nurse ɗin dake kula da abu ta ƙaraso,taimaka mata tayi wurin yin wanka a toilet ta gyara mata jikinta,da gashin kanta ko’ina ta wanke mata shi,lokaci guda Abu ta fito fess da ita,ƴar doguwar rigar material ta sanya mata,ita kanta abun sai murna takeyi da aka gyara mata gashin kanta da jikinta,taji daɗin jikinta sosai,Sehrish ce ta shirya masu breakfast gaba dayansu suka hallara a falo suka zauna suna ci,banda abu dake zaune a bedroom ɗinta tare da nurse ɗin,saboda ita kaɗai zata iya da ita,dama sune masu kula dasu a gidan mahaukatan,Sun san duk wasu dabaru da zasu bi wurin tafiyar dasu batare da sunsha wahala ba,a baki ta dinga bata abincin kalacinta tana ci,saboda bata iya ci da hannunta ba,Zubarwa takeyi a ƙasa,kamar ƙaramar yarinya haka take yin wasa da abincin,Bayan nurse ɗin ta kammala kimtsata,Dr yazo ya duba ta,bayan tafiyarshi ne ta samu bacci.

Also Download Banana Island Book 1 Hot Romantic Hausa Novel Complete Document

*SGR*

Da gudun gaske motarsu ta shararo izuwa cikin gidan yadda kasan zasu tashi sama,gudu bana wasa ba,Sam ya kasa samun natsuwa acikin zuciyarshi,jikinshi sai tsuma yake yi a ƙagare yake dasu ƙarasa cikin gidan,Armstrong nazaune agefenshi sai faman tausarshi yake yi ganin yadda ya tashi hankalinshi,slowly sojan daya ɗaukkosu from Airport ya rage gudun motar lokacin da ya ƙaraso wurin da zai yi parking ɗinta,saboda tsabar sauri,tun kafin a buɗe mashi ƙopa yasa ƙafarshi azafafe ya harba ƙopar,gudu gudu sauri dauri ya nufi cikin main palour ɗinsu,wayaam babu kowa tsit kake ji,A hanzarce ya haura upstairs direct ya wuce bedroom ɗin junaid,a buɗe ya samu ƙopar ɗakin hannu yasa ya tura tare da shigewa ciki,gabanshi ne ya faɗi rasss ganin babu junaid,saboda yasan cewa junaid bai zuwa ko’ina tunda sanyin safiya,adai irin wannan lokacin zaka same shi kwance saman gadonshi rungume da pillow,
Muryarshi tamkar zata fasa maƙoshinshi haka ya shiga ƙwala mashi kira”JUNAID!JUNAID!!JUNAID!!!”a gaggauce ya nufi toilet ɗinshi yasa hannu ya tura,nan ma yaga wayaam babu kowa,jiki asanyaye ya fito daga ɗakin junaid ya wuce bedroom ɗin Marshal Omar,tura ƙopar yayi ya shiga daga ciki,babu kowa a falonsa,bedroom ɗinshi ya nufa nan ma babu kowa,tashin hankali!
Wani irin wahallallan yawu ya haɗiya,fitowa yayi daga part ɗin Omar ya nufo downstairs,gudu gudu sauri sauri haka yake taka staircases ɗin,yana a second to the last step,yaji shigowar message a wayarshi,dakatawa yayi tare da sanya hannu cikin trouser pocket ɗinsa,duba screen ɗin wayar yayi,bayan ya sanya finger ɗinsa ya buɗe saƙon,a tsanake ya soma karantawa
_Gm Sir,ina fata ban takura maka ba,Marshal yana kwance a gadon asibitin mu yanzu haka_
Message from doctor Emran,Hankalinshi yayi mugun tashi,a ruɗe ya furta”Omar?kwance a gadon asibiti?

Karanta>>> Zurfin Ciki Book 1-4 Complete Novel Document

Da sauri ya nufi hanyar fita daga falon,fitarshi keda wuya,Hosana ta fito daga bedroom ɗinsu,tasha kuka kamar ranta zai fita,saboda an barta ita kaɗai,babu Jahad babu Sehrish babu Junaid,bugu da ƙari kuma babu Ya Omar,tun ɗazu take ta zaryar zuwa ɗakin shi,don taga ko ya dawo amma babu shi,palour ta dawo ta zauna saman sofa,hawaye wasu na bin wasu,fuskar ta jiƙe sharkaf,

“Hosana”!jin muryar Azmee yasa ta miƙe tare da juyowa tana kallonta,sanye take cikin doguwar jallabiya,tayi rolling mayafi akanta,
Tunkararta hosana tayi cikin shessheƙar kuka tace”A…aunty azmee har yanzu basu dawo ba,ni kaɗai aka bari,gidan duk babu daɗi,”
Janyota Azmee tayi tare da rungumeta ajikinta,tana ɗan lallashinta,
“Don’t worry ur self,wipe ur tears,in sha Allah nasan nan bada jimawa ba,Ya Omar ɗinki zai dawo cikin gidan nan,Just calm down ur mind,”ta ƙarasa maganar tare da ɗago hosana daga jikinta,
“Aunty azmee,shiru fa since yesterday night,kuma har kiran layinshi nayi wayarshi a kashe,Ni shikenan kowa ya tafi ya barni,dama ba so na akeyi ba,”tana magana hawaye na sharara akan fuskarta,ɗan murmushi Azmee tayi tare da kai hannunta saman fuskar hosana,taja kumatunta tare da cewa”Haba Babyn Omar,shalelen Abusufyan,kinfi kowa sanin yadda ya Omar ɗinki ke tsananin sonki,Ina da tabbacin cewa duk inda yake a yanzu,tunaninki yake yi,ya hosanata ta ke?me take yi a yanzu?tana kewata kuwa?
Murmushi hosana ta saki har hankalinta ya ɗan kwanta jin abunda Azmee tace,
“Aunty azmee kin tabbata cewa ya Omar yana tunani na yanzu haka”?
ɗaga mata kai azmee tayi alamar eh,kafin tace”Kina aransa mana,yanzu abunda za’ayi,me zai hana mu shiga kitchen atare mu haɗa mashi lafiyayyen breakfast,da zarar ya dawo gida kinga sai ki kai mashi,Zaiji daɗi sosai,”
Cike da zumuɗi hosana tace”Mu tafi kitchen ɗin,Hada chocolate zamu haɗa mashi,nasan zaiji daɗinshi sosai”
Ruƙo hannunta Azmee tayi atare suka wuce cikin kitchen,Suna aiki suna fira,gwanin ban sha’awa,

*SGR HOSPITAL*

Slowly Motarsu ta shiga cikin katafaren asibitin,bayan Armstrong yayi parking ɗin Motar,buɗewa Sgr yayi a hanzarce ya wuce cikin asibitin da saurin gaske,Armstrong na biye dashi,Tashin hankali,Soldiers ɗin da suka kawo Marshal Omar,Suna yin arba da fuskar Sgr nan fa kowa yasha jinin jikinshi,Hankalinshi a matuƙar tashe yake kallonsu one by one,Sara mashi suka shiga yi,batare da ya tanka masu ba,jiki a sanyaye yake tafiya kamar wanda aka zarewa Lakar jikinshi,tuni ya soma karaya,Zuciyarshi sai tsinkewa take yi,

Karanta>>> Wace Ce Ita (Who is she) Complete Novel

Lokacin da ya ƙaraso wurin da Major ke tsaye,Suna haɗa ido major ya saddar da kanshi ƙasa,yayin da zuciyarshi ke bugawa,Don yasan cewa dole ya tuhume shi game da kashe mashi waya da yayi,
“Major”da wata irin raunanniyar Murya Sgr ya ambaci sunanshi,
Batare da ya ɗago sun haɗa ido ba yace”Na’am yalla6ai,”
“Where’s Omar”?
Da hannu major ya nuna mashi medical room ɗin da aka kwantar dashi,batare da ya kuma tambayarshi wani abu ba,Ya wuce cikin ɗakin  har izuwa gaban gadon da Marshal ke kwance,babu alamun sauƙi a jikinshi,
biyo bayanshi Major yayi tare da Armstrong suka tsaya agefe,
Juyowa yayi tare da wurga eyeballs ɗinshi kan fuskar Major,tun kafin yayi magana a ruɗe Major ya dakatar dashi”Am sorry sir,don Allah don sonka da manzon Allah (SAW)kada ka tambayeni komai,saboda bazan iya amsa maka ba,”
gyaɗa kai kawai yayi tare da juyawa daƙyar ya iya ɗaga kafarshi har izuwa gefen gadon ya zauna,yana kallon Omar,ya jima yana mamakin menene silar kwantar dashi gadon asibiti?A iya sanin shi ba ƙaramin abune zaisa a kwantar da Omar gadon asibiti ba,
Turo ƙopa Dr Emran yayi ganin su Armstrong sunyi cirko cirko yasa shima yaja gefe ɗaya ya tsaya,To fa kowa tunani ya shiga yi taya zasu fahimtar da Sgr batare da ya haukace masu ba,
“Major!”ya ambaci sunanshi,
Hankali atashe major yace”Na’am Yalla6ai,”
“Meya faru da ɗan uwana ne?”ƴan kame kame major ya shiga yi duk yabi ya susuce ya rasa ta ina zai fara kora mashi bayani,
“Emran!meya faru da Omar ne”?ya sake tambayar Dr emran,Shiru Emran yayi shima ya rasa ta ina zai fara,Jin sunyi mashi shiru yasa zuciyarshi ta hasala,jikinshi na kerma ya miƙe tare da kallonsu,ranshi a matuƙar 6ace yake magana!
“Bazaku amsa mun ba!Kun wani zuba min ido kuna kallona,kun mayar dani tamkar wani shashasha,”hankalinsu ya tashi matuƙa,kowa sai motsa la66ansa yake yi,suna so suyi magana amma fargaba ta hanasu,
Hannu yasa ya daki ƙirjinshi da ƙarfi,lokaci guda idanuwanshi suka juye tamkar ba mutun ba,rarumar plastic chair ɗin dake agaban gadon Marshal yayi azafafe yayi wurgi da ita,nan take kujerar ta yi gefe guda ta daki ƙasan tiles,
A razane suke kallonshi,wata irin zufa ce ta soma gangarowa ta gefen fuskarshi,ɗaya bayan ɗaya yake binsu da kallo,jikinsu sai kerma yake yi,Dr Emran ma ƙoƙarin guduwa yake yi,Armstrong kuwa sai lalla6ashi yake yi akan su sanar dashi abunda ke faruwa tun kafin ya birkice masu,
“Rafayet”!muryar Marshal Omar ce ta dawo dashi cikin hayyacinshi,jiki na rawa ya juya yana kallonshi,a hankali Omar ke buɗe idanuwanshi waɗanda sukayi jawur dasu,zufa ta ko’ina ajikinshi duk da sanyin A.c ɗin dake akwai,da sauri Sgr ya koma gefen gadon ya zauna tare da ruƙo hannunshi,
“Omar pls tell me,what’s happening wit u?meyasa na ganka a asibiti?Are u not feeling well”?daƙyar Marshal ya samu ya yunƙura tare da mikewa ya zauna,numfashinshi da huci yake fita,bawan Allah yaji jiki sosai,wasu zafafan hawaye ne suka wanke mashi fuskarshi,
Muryarshi na rawa yace”Bro,Yaushe ka dawo Abuja?
Muryar Sgr tamkar zai yi kuka yace”Omar duk ba wannan ba,Where’s Junaid?nadamu akan son ganinshi,Daddy ma yana ta kira na saboda rashin samun Junaid a waya…”ya ƙarasa maganar yana faman haɗiyar yawu,
Marshal na ƙoƙarin buɗe baki yayi mashi magana,Karaf idanuwanshi suka sauka akan Major dake girgiza mashi kai alamar karya kuskura ya faɗa mashi,kasa magana Omar yayi,sai ma zuba mashi ido da yayi yana kallonshi,
“Wai menene haka?kowa na tambaya sai yayi mun shiru babu magana?meke faruwa ne!in wani abu ne ya faru ba zaku sanar mun ba ne?Ni fa Musulmi ne!nayi imani da ƙaddara mai kyau ko mara kyau,ku faɗa mun mana……”ya ƙarasa maganar fuskarshi ɗauke da matsananciyar damuwa,
Daƙyar Omar ya iya buɗe baki yace”Babu abunda ya faru,Junaid yana lafiya….”tunkan ya ƙarasa maganar Sgr yace”That’s impossible!Taya zaka ce mun junaid yana lafiya kuma in yarda?To idan yana nan a nuna mun shi inaso in ganshi!Meyasa layinshi a kashe?meyasa nake ganin hawaye akan fuskarka?
Daurewa kawai Omar keyi,saboda kukan dake cinshi,So yake ya fashe da kuka ko ya samu ya rage raɗaɗin dake acikin zuciyarshi,
Tausasa murya Sgr yayi”pls Omar,ka sanar dani!ina ƙanina yake?wani abu ya faru dashi ne?saboda shi jiya ko bacci ban samu ba,

Karanta>>> Tabarmar Kashi Chapter 1 By Safiyya Huguma

Da sauri Omar ya sanya tafin hannunshi tare da share hawayenshi,
“Rafayet!I won’t hide it for u,Junaid was kidnapped….”daƙyar ya ƙarasa maganar ganin irin kallon da Sgr ke jefa mashi,kallon tuhuma,
“Omar,ni kake faɗama cewa Anyi kidnapping ɗin junaid”?shiru Omar yayi batare da yace mashi komai ba,
“Omar,If it is true,Junaid was kidnapped,as a Senior Soldier with the rank of Marshal,you will be brave enough to rescue him,bawai na ganka kwance a gadon asibiti ba kana zubar da hawaye,”tausasa muryarshi yayi”don Allah Omar ka faɗa mun gaskiyar abunda ya faru,kada kasa zuciyata ta buga,Ina junaid ɗina yake?meya faru dashi?yanayin yadda yayi maganar ne yasa jikinsu kara yin sanyi lakwas,
Daƙyar Major ya daure ya cije,ya yi karfin halin bude baki yace”Sir,Junaid ya riga mu gidan gaskiya!junaid ya koma ga mahalicci…..”bai ƙarasa maganar ba sakamakon Zaburar da yaga Sgr yayi gadan gadan ya tunkareshi,yana faɗin”,repeat what u just said Major!”yana magana yana naɗe hannun rigarshi alamar zaiyi dambe,da sauri Omar ya ambaci sunanshi Rafayet,wanda hakan ya dakatar dashi tare da juyawa yana kallon Omar,
Cikin shesshekar kuka Marshal yace”Junaid has gone forever,wanda yafi mu sonshi ya kar6i abunshi,jiya da daddare around 8,Suna kan hanyar dawowarsu acikin mota shi da jahad,ta fita ta siya masu ice cream tabar junaid acikin Motar,kafin ta dawo,babbar mota tabi ta kan motarshi,Rafayet bamu samu komai daga sassan jikin junaid ba,Ya ƙone ƙurmus acikin motar……..”kasa ƙarasa maganar yayi,ya fashe da wani irin matsanancin kuka mai cin rai tare da buga hannuwanshi saman gadon,
Tashin hankali!!!Kasa motsawa Sgr yayi daga tsayen da yake,kamar an dasa mashi aya,Tsit ka ke ji,kowa yasha jinin jikinshi Sgr kawai suke kallo,
Almost 15 mins,Kafin ya motsa pink lips ɗinsa a hankali ya furta”Omar!Do you wanna say that Junaid is dead?
Jinjina mashi kai marshal yayi alamar eh,abun mamaki sai suka ga yana murmushi gami da girgiza kanshi yace”I can’t believe that junaid is gone,this is a fabricated lie, Omar you’re just kidding me and I don’t want it….”
Tsananin tausayinshi ne ya kama Omar,dama yasan cewa zaiyi wuya ya yarda cewa Junaid ya mutu,
“Sir,we are really sorry…..’Dr Emran ne ya ambaci hakan,a sukwane Sgr ya juya tare da kallonshi aruɗe yace”Sorry for what”?
Shiru yayi baice komai ba,ɗaya bayan ɗaya yake kallonsu,a wani irin yanayi mara misaltuwa,fuskarshi duk ta hargitse,jikinshi yayi laushi,guiwarshi ta sage,ƙafafuwanshi sun gaza ɗaukarshi,ga6o6in jikinshi duk sun saki,Zuciyarshi ta raunata sosai,
Wani farin ruwa ne ya kwanta luf acikin fararen idanuwanshi,jinjina kanshi kawai yake yi batare da ya furta komai ba,temperature ɗin jikinshi yayi zafi sosai,yadda ko mutun ya matso kusa dashi,sai yaji hucin jikin nashi,wata irin zufa ce ta soma tsastsofa mashi,a jikinshi lokaci guda ya jiƙe sharkaf,gaba ɗaya sun zuba mashi ido suna kallonshi,gwanin ban tausayi,
“Wai Junaid ne ya mutu?tatsuniya ce ko mafarki”?muryarshi na kerma yayi maganar,
“Enough is enough! What do you want me to say to our father? How can I inform him about Junaid’s death?saboda shi  ko bacci baiyi ba jiya,Nima haka,meyasa mutuwa zata yi mun yankan ƙauna ne?
Sulalewa yayi saman guiwowinshi wani irin biji biji ya fara gani a idanuwanshi,a hankali ya shiga furta”Innallilahi wa’inna ilaihirraji’un,Ya Allah kasa mafarki nake yi ba gaske ba,meyasa ni bata ɗauke ni ba ta ƙyale Junaid?Why!why!’da sauri Dr Emran tare dasu Major suka kewayeshi suna tottofa mashi addu’o’e asaman kanshi,wani irin jijjiga jikinshi ya soma yi,hakan ba ƙaramin ɗaga masu hankali yayi ba,a Ruɗe marshal ya saukko daga saman gadon ya nufosu jiki ba ƙwari ya zube agaban Sgr wanda tuni ya yanke jiki ya faɗi,kuka sosai Omar yake yi kamar ya haɗiyi zuciya,rungume Sgr yayi sosai ajikinshi,Ya tsorata da jin irin zafin da jikin Sgr ya ɗauka,tamkar hucin wuta ,
“His body temperature was very high,I think he got a heatstroke,yana buƙatar Emergency treatment,”Dr Emran ne yayi maganar,batare da 6ata lokaci ba a gaggauce suka ɗaukeshi izuwa saman medical bed ɗin da Omar ya sauka suka kwantar dashi,doctors ne suka taru akanshi,ga jinin shi ya hau sosai,

Daga waje suka koma,Saman waiting seats suka zauna suna jiran tsammani,ɗage kanshi yayi jikin seat din yasa Hanky ya rufe fuskarshi,Allah kaɗai yasan irin raɗaɗin da yake ji acikin Zuciyarshi,bakowa yafi ji ma tausayi ba,Fa ce Abbansu,don muddin yaji irin Mummunar mutuwar da Junaid yayi tofa Zuciyarshi zata buga ne,A rasa duka biyun,Sojojin dake a kewaye dasu,sai tausarshi sukeyi ganin yadda kamanninshi suka sauya saboda damuwa,
“Haƙuri zamuyi yalla6ai,nasan abun da ciwo,raɗaɗinshi yafi ƙunar wuta,Amma ya zamuyi?mutuwa ce tana akan kowa,Junaid addu’armu yake bukata a yanzu,Allah ya jiƙanshi,ya gafarta mashi zunubbanshi,Yasa can yafi mashi nan,Su kuma waɗanda suka shirya mutuwarshi,Allah ya tonu asirinsu,don bazamu ƙyalesu ba,sai sun ɗanɗani kuɗarsu,”sosai Major ya shiga tausarshi yana ƙara ƙarfafa mashi guiwa,
a hankali Omar ya zame hanky ɗin dake akan fuskarshi,ta kumbura sosai la66ansa sunyi suntum,idanuwanshi sunyi jawur dasu luhu luhu,daƙyar ya iya buɗe baki yace”Nagode sosai Major,naji daɗi sosai,kalamanka sun dan sanyaya mun zuciyata,Amma inaso ka sani rashin Junaid atare damu babban gi6i ne,wanda babu wanda zai iya cike sa,he’s our weakness!maƙiyanmu sunci galaba akanmu!Sun kashe mana duk wani ƙwarin guiwa da muke dashi!laifin me junaid ya aikata da ya cancanci wannan ɗanyen hukuncin?

Karanta>>> Furar Danko Chapter 1 By Billyn Abdul

Yaron da baison komai ba,Soyayyar ƴan uwansa kawai ya sani,burinshi koda yaushe ya sanya kowa farin ciki,amma yau an samu wasu marasa imani,Marasa tausayi,sun yi silar mutuwarshi!wlh ɗaya daga cikinsu bazai shaba,Sai sunyi danasanin haihuwarsu da uwarsu tayi acikin duniyar nan,”yana magana hawaye na wanke mashi fuskarshi,
Major na ƙoƙarin buɗe baki yayi magana,Suka jiyo hayaniya daga can cikin asibitin,Sautin kuka suka jiyo mai sautin gaske,Gaban Omar ne ya faɗi rasss jin Muryar jahad wadda tun a jiyan su major suka sa aka maido ta nan,A hanzarce suka miƙe tsaye suna kallon wurin da sautin ke fitowa,da gudun gaske take tunkarosu nurses sun biyota da gudu,sae ihu takeyi tana faɗin”wuta!wuta!Junaid yana acikin wuta,ataimaka a fito mun da ɗan uwana,kada ta ƙona shi,”wannan shine sambatun da takeyi,tashin hankali!
Duk da jikinshi ba ƙwari haka ya nufeta,tare da ruƙota jikinshi,idanuwanta sun juye kwata kwata bata iya gane wanene agabanta,ita dai kawai sunan junaid take ambato acikin bakinta,hankalin Omar ba ƙaramin tashi yayi ba,tsoranshi kar ace ta samu ta6in hankali,don da alama abunda ke shirin faruwa kenan,
“Jahad!ki natsu ki kalleni,Ya Omar ne fa”
Kuka takeyi sosai,jijiyoyin wuyanta duk sun firfito waje,don bala’e Allurar kashe jiki akayi mata,Amma babu abunda allurar tayi mata,tamkar an ƙara mata ƙarfin jikinta,baiwar Allah taga tashin hankalin da bata ta6a gani ba,kuma akan Masoyinta da take tsananin so,
Jijjigata ya shiga yi yana ambaton sunanta”Jahad!Ina zaki je?
Firgita tayi agigice ta dinga faɗin”Gashi can!yana kuka wuta!wuta!ke ci ajikinshi!Yana kuka,Ya Omar a fiddo shi kada ya mutu ya barni,”da ƙarfi take yin maganar tamkar maƙoshinta zai 6allo,ƙoƙarin ƙwacewa take yi daga hannunshi don taje wurin abunda idanuwanta ke hango mata,Ko ina ta kalla,sai taga motar junaid tana ci da wuta,shine abunda idanuwanta ke nuna mata,
Hawaye ne suka kuma wanke mashi fuskarshi,tsananin tausayin jahad ne ya kamashi,gaba ɗaya babu natsuwa atare da ita,ta haukace ta gigice ta firgice,kamar wadda tayi shekara ɗaya tana hauka,
Hannu yasa tare da sa6arta saman kafaɗarshi,saboda rashin ƙwarin jikinshi,har tangal tangal yayi kamar zai faɗi daƙyar ya samu ya tsayar da kanshi,wuce wa nurses ɗin sukayi gaba yabi bayansu,yana jin yadda jahad keta bugun bayanshi,ta dunƙule hannayenta sae ɗumarshi take yi don ya saketa,Allah sarki innocent girl kamar jahad,yau ta zauce har tana bugun Ya Omar ɗinsu,
Er nurses ɗin suka wuce har zuwa room ɗin da aka kwantar da ita,Shiga yayi da ita ciki,a lokacin har jikinta ya fara saki,alluran da aka ɗurka mata sun fara aiki,a hankali ya kwantar da ita saman gadon,kamar matacciya haka ta koma,ko yatsanta bata iya ɗagawa,la66anta sun bushe sosai,sun farfashe sakamakon ciccijesun da tayi,tsayawa yayi daga tsaye yana kallonta,idanuwanta suna a rufe,tunda yake a rayuwarshi bai ta6a fuskantar tashin hankali irin na jiya da kuma yau ba,bai ta6a cin karo da mummunar rana ba,irin ta yau,ta ko’ina babu sauƙi,zuciyarshi har wani tafarfasa takeyi saboda ƙunar da takeyi mashi,
Shigowa cikin ɗakin Major yayi tare da wani baturen Likita,jin sallamarsu yasa Omar juyawa yana kallonsu,da sauri ya tunkari Doctor ɗin yana tambayarshi dangane da jahad,
“She is having a panic attack as a result of the incident”acewar Dr Antony,
Dafe kai Omar yayi da hannu ɗaya ya ɗan runtse idanuwanshi tare da buɗesu,Muryarshi a kasalance yace”Yanzu Doctor babu yadda za’ae yarinyar ta dawo cikin hayyacinta!”
Dr Antony yace”It will be very difficult for us to overcome her now,but we will do our best to see her regain consciousness,”
“Pls Dr,try as much as u can”
Jinjina kai Dr antony yayi,tare da dafa kafaɗar Marshal don ya lura baya acikin hayyacinsa

Also Download Nurul Kalb Hausa Novel Complete Document

“Calm down ur mind,she will be ok,zamu yi iyakar bakin ƙoƙarinmu wurin ganin mun shawo kanta,”
Daga haka Major ya ruƙo hannunshi suka fito daga waje,zama fa bai gansu ba,Zarya ya shiga yi tsakanin room ɗin da Jahad take ciki dakuma room ɗin Sgr,sam ya kasa samun natsuwarshi tuni ya mance da shima mara lafiya ne,ana cikin wannan tashin hankalin,Tsautsayi yasa Omar ya kar6i wayarshi daga hannun Major,Yana kunnata kwatsam!sai ga kiran Abbansu ya shigo cikin wayar kamar jira yake yi,!
Zubawa screen ɗin wayar ido yayi,tare da ɗagowa ya kalli Major,tun kafin ma yayi magana,major ya riga shi cewa”Abba ne ko”?ɗaga mashi kai yayi alamar eh,
“Seriously I can’t pick his calls,saboda bansan amsar da zan bashi ba,if he asks about junaid,”ba don yaso ba haka ya katse kiran Abbansu,Abunda bai ta6a yi ba arayuwarshi,
yana ƙoƙarin kashe wayar gaba ɗaya sai ga message ya shigo ta sama,hannunshi na kerma ya buɗe message ɗin,fearfully ya soma karantawa,
_Omar kun kyauta ku dukanku,kowa yaƙi ɗaga kiran wayata,dama inaso in sanar dakai cewa,Yau zamu dawo gida_
Saboda tsabar kiɗima,Omar baisan lokacin daya saki wayarshi ba,ta faɗi ƙasa sosai ta daki tiles ɗin,
“Innalillahi wa’inna ilaihirraji’Un!Allahumma ajirni fil masibati wa’aklifni khairan Minha”wannan shine abunda yake ambato acikin bakinshi,
“Major menene mafita?Ka taimaka min!abubuwa sunyi mun yawa,Ya zanyi da rayuwata!Babu Junaid,Jahad ta zauce!Ga Sgr ma a kwance gadon asibiti,Na shiga uku ni yau!wannan wace irin baƙar rana ce!?
Wani irin tausayinshi ne ya lullu6e major,janyoshi yayi ajikinshi ya rungumeshi sosai,dama a buƙace yake da ya samu kafaɗar da zai aza kanshi,Ya zubar da hawayenshi sosai,ko ya rage raɗaɗin dake acikin zuciyarshi,
Cikin shessheƙar kuka yace”Major menene mafita yanzu?Ya zanyi da Abbansu?
Hannu major yasa yana ɗan bubbuga bayanshi yace”Sir,in sha Allah komai zai tafi dai dai,bazamu rasa abunyi ba bi’iznillahi,”
Ruƙo hannun Omar yayi suka koma saman waiting seat ɗin suka zauna,kwantar da kanshi ya kumayi asaman kafadar major,sai faman sauke ajiyar zuciya yakeyi,bakomai yake faɗo mashi arai ba,fa ce Fuskar Baby Junaid ɗinsu,mai ɗauke da wannan kyakkyawan Murmushin,

*Boss Bature*

*Sehrish*

Around 1:30 na rana,
Zaune take asaman Sofa ta zabga Uban tagumi,tunda Daddynsu ya sanar da ita game da tafiyar Sgr Abuja,take jin kanta kamar ba cikakkiyar mutun ba,Bataso tafiyarshi ba,duk da ta yi mamakin tafiyar tashi,kewarshi duk tabi ta lullu6eta,ga kewar gida yau 3 days kenan suna a kano,Yanzu gidan ya rage daga ita sai Oummansu,tun kafin a fara kiran sallah,Maman sadeeq suka koma gidansu,Abusufyan ne ya ɗaukesu acikin motarshi,hannu takai tare da ɗaukar wayarta dake ajiye agefenta,Contact ta shiga tare da lalubo numbar jahad ta buga mata kira,
Guntun tsoki taja,jin layin nata a kashe,Layin Junaid ta kira Shima a kashe,hakan ba ƙaramin ɗaga mata hankali yayi ba,Layin Hosana ta kira,a lokacin sun kammala haɗama Omar breakfast ɗinshi,har ta koma ɗaki ta shiga toilet tayi wanka,tana zaune gaban mirror tana kwalliya jikinta sanye da gown,wayarta dake ajiye saman drawer ta soma ringing,duk a tunaninta ya Omar ɗinta ne,jiki na rawa ta miƙe hada tuntu6e wurin yin saurin ɗaukar wayar,koda taga kira daga Sehrish ne,jiki na rawa tayi picking call ɗin tare da kara wayar a kunnanta,
Tunkafin Sehrish tayi magana,hosana ta ruga ta cewa”Wai yaushe zaku dawo ne?gidan fa ba kowa ni kaɗaice,
“Hosana wai ina jahad ne?ina kuma junaid?basu dawo daga shan ice cream ɗin bane tun jiya da suka fita?na shiga damuwa saboda rashin samunsu a waya,”
Hosana tace”Nima bansan inda suka je ba,babu fa kowa gida,daga ni sai Aunty azmee,ya Omar bansan shima ina yaje ba,”

Karanta>>> Idan Ba Ke Complete Novel Document

Hankalin sehrish yayi matuƙar tashi,la66anta na kerma tace”Hosana!yaya Rafayet baizo nan gidan ba”?
“Eh,baizo ba,ni banga kowa ba,”
Nan take ranta ya bata cewa wani abu ya faru acikin gidan,kuma bada kowa ya faru ba,fa ce Su Junaid da suka fita shan ice cream,saboda rashin dawowarsu cikin gidan
“Rishi ko breakfast na gaza ci,ina cikin matsananciyar damuwa,”
Ajiyar zuciya Sehrish ta sauke tare da cewa”Hosana ki kwantar da hankalinki,Zasu dawo cikin gidan ne,Yanzu zan sanar dake wani abun farin ciki nasan zaki ji daɗi sosai,
Muryarta aɗan shagwa6e tace”toh faɗamun menene”
Sehrish ta miƙe tare da nufar ɗakin Oummarsu tana faɗin”Nasan Daddy bai sanar dake ba ko”?
Hosana tace”meke nan”?
Shiga cikin ɗakin tayi wayarta manne a kunnanta,
Video call ta mayar da kiran nasu,bayan ta samu wuri ta zauna gefen Oummansu dake ta bacci hankalinta a kwance,
“Hosana kalli ki gani,Wacece wannan,”tayi maganar tare da saita Screen ɗin wayar saitin fuskar Oummansu,
Ƙura ido hosana tayi tana kallon fuskar oummasu,almost 7 mins,a hankali wani kyakkyawan murmushi ya bayyana akan fuskarta,a ruɗe tace”rishi Oumman mu ce ko?
“Eh itace,naso na sanar dake tun jiya,baki dauki wayan ba kuma bansamu halin sake kiran ba,An samu Oummanmu,Amma bata acikin hayyacinta ta samu ta6in hankali,
Uban tsalle hosana ta daka,da gudun gaske ta fito daga ɗakinsu,kaitsaye ta nufi kitchen inda ta baro Azmee tana gyare gyare,Cikin rashin sani Hosana taci karo da haroon,ta bangaje shi sosai har wayar dake hannunta ta kubce mata,kaitsaye ta faɗi ƙasa ta daki Tiles Screen ɗin ya fashe,
Hannu hosana ta aza asaman kanta ta fashe da wani irin matsanancin kuka,tana faɗin”Wayyo Allah wayata!Ka kashe mun wayata,Wlh bazan yafe maka ba,Allah ya isa,”
Rai a6ace haroon ya ɗaga hannu zai mareta,adai dai lokacin Azmee ta fito daga kitchen ɗin,A ruɗe ta ƙaraso ta damƙi hannunshi,wani mugun kallo daya jefa mata sai da gabanta ya faɗi rass saboda launin idanuwanshi da sukayi jawur dasu,fuskar nan tashi tayi suntum da ita,da sauri azmee ta saki hannunshi,cikin sanyin murya tace”Allah ya huci zuciyarka,”
Harara ya wurga mata tare da jan dogon tsoki mai sautin gaske,matsawa yayi izuwa inda wayar hosana take a ƙasa,Ya sanya faffaɗan tafin kafarsa mai sanye da takalmi,Ya take wayar ya rugurguzata,hakan ba ƙaramin ƙona ma hosana rai yayi ba,Abun ka ga mai ta6in hankali,Kamar kura ta mamayeshi tare da gartsa mashi cizo asaman damtsen hannunshi,Dama ƴar singlet ce ajikinshi,ƙoƙarin janyeta ya dinga yi amma taƙi cire haƙoranta daga saman fatar hannun,har sai da ta fasa shi,jini ya shiga tsastsafowa a wurin,waro ido waje haroon yayi ganin ta fitar mashi da jini a fatar jikinshi,ƙwaƙƙwarar damƙa yakaima Gashin kanta,Hankalin Azmee ba ƙaramin tashi yayi ba,Ga tsoron shiga huruminshi take yi don tasan halinshi ba imani ya cika ba,Yasha ɗaga hannu zai mareta,
Wurgi yayi da hosana,gaba ɗaya ta tafi zata faɗi ƙasa,Azmee takai hannu zata ruƙota,
Tsawa ya daka mata tare da cewa”kika kuskura kika ta6a ta abakin aikin ki cikin gidan nan!uwar shisshigi kawai,ki tsaya a iya matsayinki,”jiki asanyaye azmee ta tsaya tuni idanuwanta suka cicciko tab da ƙwalla,tana ji tana gani haka hosana ta kife ƙasa,fuskarta ta bugu sosai har hancinta ya fashe,
Haura ƙafa yayi ya wuce Can medical room ɗinsu,saboda yayi dressing raunin da taji mashi,
“Hosana”Azmee ce ta ambaci sunanta,tare da zuƙunnawa agabanta,tasa hannu ta janyota ajikinta,Lallashinta ta shiga yi,abun ba ƙaramin ƙona mata rai yayi ba,Haroon ya 6ata mata rai,
Cikin shessheƙar kuka tace”Aunty azmee,Kalli yarda ya fasa mun wayata,mutumin can baida imani shi ba jininmu bane,”hannu Azmee tasa tana share mata hawayenta,
“Kiyi hakuri hosana,Allah shi zai saka maki,”

Also Download FARRAH Hausa Novel Complete Document By Maman Shuraim

Daƙyar azmee ta samu ta lallasheta,har ta rakata ɗakinsu ta kwantar da ita tana ta ajiyar zuciya,cikin lokaci ƙanƙani bacci ya ɗauketa,
Dawowa falon Azmee tayi wurin da wayar Hosana ta fashe,hannu tasa ta ɗauki wayar tana kallon screen ɗin,Ya dagargaje sosai baka iya ganin komai,

A 6angaren Sehrish kuwa,duk tabi ta ruɗe lokacin da taji sautin kukan hosana,kafin haroon ya taka wayar ta ƙarasa mutuwa gaba ɗaya,zumbur ta mike tana zarya acikin ɗakin,kamar tayi tsuntsuwa ta tafi Abuja haka take ji,ta ƙagara tasan meke faruwa acan ɗinne … .. ‘

Tashin hankali!Su marshal na zaune zaman jiran tsammani,sae ga Sgr ya fito daga room ɗin da aka kwantar dashi,Ko riga babu ajikinshi ya yageta ya cireta,ƙirar ƙarfin nan tashi mai matuƙar tsoratarwa gata nan a bayyane,Tsokar jikinshi sai rawa takeyi,miƙewa sukayi gaba ɗayansu suna kallonshi,
“Rafayet”!Omar ne ya ambaci sunanshi tare da tunkarar shi,damtsen hannunshi ya ruƙo acikin nashi yana sake ambaton sunanshi
“Omar!I can’t believe that junaid has gone,till the day i found out those who planned his death!One by one sai na kashe su da hannuwana,daga nan ne zan yarda cewa Na rasa shi na har abada,wlh in har ban aikata abunda na faɗa ba,Sai na ajiye aiki na”daƙyar yake magana saboda zuciyarshi dake a harzuƙe,jininshi na akan akaifarshi,
ƙoƙarin kama hanya yake yi yabar wurin Omar ya rurruƙeshi saboda baisan inda zai dosa ba,Likitocin dake kula dashi duk sun kewaye shi sae faman tausarshi sukeyi suna lallashi,Amma ina idanuwanshi sun rufe rufff,baya ji baya gani,
“Rafayet ka kwantar da hankalinka mana!Duk yarda ka ke jin radadin mutuwar nan nima haka nake ji,nama fika jin raɗaɗi saboda Gani nake yi kamar ni ne silar mutuwarshi,Akan idona Junaid yabar gidan acikin motarshi na gaza dakatar dashi,Har Major sai da ya bani shawara amma banyi saurin ɗaukar mataki ba,Wlh kamar na haɗiyi zuciyata na mutu haka nake ji,”dakatawa ya ɗan yi da yin maganar yayin da suke kallon juna,shi da Sgr idanuwan kowannansu cike tab da Hawaye ba ƙaramin jiki suke ji ba,
Tausasa muryarshi yayi kafin yaci gaba da cewa”Rafayet!yakamata muyi tunani akan mahaifinmu!mu nemi mafita,domin kuwa ya sanar dani cewa suna akan hanyar dawowa gida yanzu haka,kaima kasan irin yadda yake jin junaid aransa,muddin yaji mutuwarshi tofa zamu rasa shi ne,a yadda shekarunshi suka ja ɗinnan bakomai zai iya jurewa ba,”
Jikin Sgr ba ƙaramin sanyi yayi ba,bawan Allah duk yabi ya susuce ya rasa kuzarin jikinshi,
“Omar,yanzu ina ita yarinyar take ne”?yayi tambayar yana kallonshi,
“Jahad ta zauce yanzu haka an kwantar da ita,ta samu bacci,”
Jinjina kanshi ya ɗan yi,Shiru sukayi na wani lokaci,kafin Major yace”Yakamata mu nemi mafita,lokaci yana ƙure mana!”

Doctor Emran ne ya basu shawarar su shiga ɗaya daga cikin resting rooms na asibitin,yadda zasu ji daɗin tsara yadda zasu tunkari Abbansu,

Katafaren ɗaki ne ya haɗu sosai,wuri kowannansu ya samu ya zauna,Omar Da Sgr suna zaune daga gefen gadon ɗakin,Major tare da Dr Emran da Armstrong suna zaune asaman doguwar sofa ɗin dake a ɗakin,Sanyin A.c ɗin dake a ɗakin ba karamin sanyaya masu zuciya yayi ba,almost 15 mins kowa yayi shiru babu mai magana acikinsu,Kowa da abunda ke zuwa mashi aranshi,
“Yalla6ai mi zai hana asamu babban malamin addini ya fahimtar dashi ta hanyar tausarshi da daɗaɗan kalamai,tare da janyo mashi ayoyin al kur’ani,”acewar Major
Dr Emran yace”that wouldn’t be a solution a yanzu dai,gaskiya a yadda naji irin son da yake yi mashi muddin yaji irin mummunar mutuwar da Junaid yayi tofa wannan ba zai yi tasiri ba,zamu rasa shi,Zuciyarshi zata buga ne….”
Armstrong yace”Koda za’a sanar dashi,Ni shawarata kada a faɗa mashi ainihin abunda ya faru,Ina nufin irin mutuwar da Junaid yayi,kawai asanar dashi cewa Ya rasu ne ta hanyar rashin lafiya na rana ɗaya…”tun kan yakai ƙarshen maganar Omar yace”idan ya nemi ganin gawarsa fa?Ya zamuyi kenan”?
Shiru Armstrong yayi can yace”sai ace anyi burying dinta tunda dama ku baku taking time kafin ku rufe deceased” wani kallo Omar yayi mashi yace”kana ganin in ance masa hakan zan yarda ne,alhalin yana araye,sam hakan ma ba mai yuwuwa bane” shiru Armstrong yayi don kuwa bai yi nazari ba kafin ya bada shawarar,
“To yalla6ai mezai hana kawai a 6oye mashi komai game da mutuwar Junaid ɗin!in yaso koda ya tambayeshi sai asanar dashi cewa,Sgr ya tura shi U.s ne,wurin yin training ɗin aikin soja,”Major ne yayi maganar,
Murmushin takaici Omar yayi tare da kallonshi yace”Ita kuma jahad ɗin fa?ko itama mun turata U.s ɗinne training?
Duƙar da kai ƙasa major yayi,Sgr dai bai tanka masu ba shi kaɗai yasan irin tafarfasar da zuciyarshi keyi mashi,
“Gaskiya akwai gagarumar matasala!yanzu idan muka ce an tura Junaid U.s zai kar6i training ɗin soja,Jahad kuma ya zamuyi da ita?Zata tona mana asiri ne,ta hanyar sambatun da takeyi in har bata dawo hayyacinta ba,koba wannan bama Shi Abban zai iya buƙatar yin waya da jubaid!Dole fa ya nemi layin waɗanda ke a u.s don yaji ya lafiyar ɗanshi,duk kuma in hakan bata samu ba zai ce zaije can ne don ya ganshi”Marshal Omar ne yayi wannan jawabin
Armstrong yace”Inaso naji abunda Sgr zaice,Saboda nasan baza a rasa mafita a wurinshi ba,”
Mayar da hankalinsu su kayi akan Sgr wada ya ɗan lumshe idanuwanshi,
Cikin sanyin murya Omar yace”muna sauraronka ya zamuyi yanzu?Daddy yakusa dawowa,kuma da alama bashi kaɗai zai dawo ba,dukkansu zasu dawo”,saboda tsabar tashin hankalin da suke ciki,Ko tunanin abinci ma basuyi,bawai don basu jin yunwa ba,
Slowly ya buɗe idanuwanshi sai lokacin ya soma magana atsanake

Download>>> Bintu Diyar Bayi Ce Book 1 Complete Document

“Duk shawarwarin da kuka bayar ba masu 6ullewa bane,a karshe dai dole mahaifinmu yasan cewa ɗanshi ya mutu,Ba don naso ba,Amma ba yadda zanyi ne,ya zama dole muyi wa mahaifinmu ƙarya a karo na farko don mu ceto rayuwarshi….”dakatawa ya ɗanyi da yin maganar,yana sauke ajiyar zuciya kafin ya ɗaura da cewa”Shawarata shi ne,Za’a sanar dashi cewa,Anyi kidnapping ɗinsu su duka biyun!saboda babu junaid jahad kuma ta zauce,muddin muka mayar da ita gida asirinmu zai tonu ne,kuma mahaifin yarinyar yanzu yana cikin farin cikin ganin mahaifiyarsu,idan har ya dawo ya samu ƴarshi a cikin wannan yanayin yaya kuke tunanin zaiji aranshi?ga kuma babban rashin da mukayi na Junaid!that’s the reason why ya zama dole a killace Jahad acikin asibitin nan na tsawon wasu kwanaki har asamu ta dawo cikin hayyacinta,hikimar yin hakan shi ne na farko idan daddy yaji cewa anyi kidnapping ɗinsu,tabbas hankalinshi zai tashi sosai,Amma zai sa ran bayyanar junaid a koda yaushe,kuma zamu sanar dashi cewa Junaid zai dawo Zamuyi ƙoƙari wurin ganin mun ku6utar dashi hakan zaisa Ya ɗan ji sauƙi aranshi duk da zai shiga matsananciyar damuwa,mu kuma zamuyi ƙoƙari wurin ganin mun shawo kanshi,Abu na biyu shi ne bayan wasu ƴan kwanaki idan Allah yasa Jahad ta dawo cikin hayyacinta,Zamu lallasheta ne nasan zata fahimce mu,Zamu fara sakinta ta koma gida a matsayin su kidnappers ɗin suka saketa,Wannan zai ƙara kwantarwa Abbanmu hankali saboda zaisa Ma ranshi cewa shima junaid zasu sako shi,Ta wani 6angaren Abusufyan ma zaiji sauƙi aranshi in yaga dawowar Jahad,may be ma kafin ya dawo daga kano zata koma,so daganan a hankali a hankali zamu cigaba da ƙoƙarin fahimtar da Daddy,koda zaisan cewa junaid ya mutu sai daga baya lokacin komai ya wuce kamar next 1 to 2 month haka,Sae asamu babban malami ya zaunar dashi yayi mashi nasiha sannan ya sanar dashi ainihin abunda ya faru,radaɗin da zaiji aranshi bazai kai raɗaɗin da zaiji ba a yanzu idan aka sanar dashi…”yana kai ƙarshen maganar shi,ya rufe idanuwanshi yayin da zuciyarshi keta harbawa,
“Good Idea”!acewar Armstrong,
Major ya ɗaura da cewa”Yanzu yakamata a fara kawar da duk wani abu wanda zaisa Labarin hatsarin daya faru yaje masu,dama an kori ƴan jarida daga wurin,yanzu haka akwai sojojin dake kewaye da wurin an rufe shi,basu bari kowa ya ɗauki video ko hoton abunda ya faru ba,Zamusa su tsananta bincike akan mutanen dake a wurin dama kuma ba wasu mutane da yawa ne su kai witnessing incident din ba,ko masu wuce wa a mota babu sosae,dakuma mai siyar da ice cream ɗin nan,Hatta wayarshi za’a canza mashi saboda gudun kar ace ya dauki rahoto in ma ta kama asa ya canza wuri ne sai ayi hakan,Zamu toshe duk wata hanya da zaisa labarin mutuwar Junaid yaje kunnan mutanen gidan in sha Allah,”
Jinjina kai Omar yayi tare da cewa”hakan yayi,Yanzu yakamata a hanzarta zuwa yi mashi jana’iza,Yamu yamu zamu halarta wurin yi mashi sallah,mu binne tokarsa awurin,bayan an kammala sai a kawar da ƙarahunan Motar,A shafe duk wani abu da zai nuna cewa Anyi hatsarin mota a wurin,”cikin karyayyar murya ya yi maganar.

Sun jima suna tattaunawa akan yadda zasu tafiyar da komai,daga bisani wuraren karfe 2,Suka ɗunguma gaba dayansu zuwa wurin da incident ɗin ya afku,Sgr kamar yayi hauka lokacin daya yi arba da motar Junaid,Yaji mutuwar nan har cikin ranshi,daƙyar suka samu kowa ya dan daidaita natsuwarshi,Alwala su kayi gaba ɗayansu banda Armstrong da wasu da suka kasance ba musulmai ba,Anan sukayi mashi Sallah tare da burying ɗin tokarsa A gefen wata bishiya,bayan sun gama jana’izar,sojoji suka kawar da motarshi daga wurin,jikin kowa fa yayi mugun sanyi,Don suna kammala sallar jana’ixar Sgr ya zukunna gefen ƙabarin Junaid,tare da kwantar da kanshi asaman ƙabarin,Addu’o’e ya shiga jerowa abakinshi yana tottofa mashi,a ƙarshe yace”Allah ya jikanka Junaid,bazan ta6a yafewa kaina ba,idan har ban ɗauki fansa akan irin kisan wulakancin da akayi maka ba,Na ɗaurawa kaina alhakin mutuwarka,Saboda laifina ne Junaid da ban baka kariya ba,na tabka babban kuskuren da har duniya ta naɗe bazan ta6a mantawa dashi ba,”
Kasa ɗagowa yayi daga kan ƙabarinsa,

 

Back to top button