.*ASM Bk2045*
_Destiny may be delayed but cannot be changed…._
*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*
……..lokacin da suka iso kopar gidan k’arfe d’aya da rabi na dare Unguwar tayi tsit ba kowa sai hasken fitilu da yake akwae wuta, yana parker Motar ta kai hannu don ta bud’e ta fita amman sai taji kopar a rufe cikin muryar fushi tace ya bud’e mata ta fita bai ce komae ba wayar shi na a hannun shi yana kokarin kiran Amadu dama tun suna Asibitin bayan an shiga da Fatuu yay tunanin kiran shi cikin sa’a ya d’aga kiran anan ya sanar dashi cewa ayi hak’uri sun yi dare ne da yake ba’a fara program d’in da wuri ba amman gasu nan dawowa in ba damuwa kada yay bacci sai ya bud’e mata k’opa, yanzu ma da ya kira shin bayan yay picking yace mashi gasu nan k’opar gida ya amsa da to ya katse kiran ya aje wayar a gefe sannan ya d’auki wayarta dake aje kan seat ashe anan ciki ta barta tun bayan da ya kirata a wurin dinner yace ta fito, bud’e k’opopin Motar yay Fatuu na jin ya bud’e ta kai hannu ta bud’e shima bud’e ta side d’in shi yay ya fito ya zagayo inda take lokacin har ta zuro k’afafun ta hannu ya kai don ya taimaka mata tak’i 6ari ya ta6ata dole ya k’yaleta yana ta kallon ta cike da tausayawa har ta fito hannunta ruk’e da takalmanta ya duk’a cikin Motar ya d’aukko purse d’inta da ledan magungunan har ta fara tafiya ya bita ya tsaya a gefenta ta kauda fuskar ta tana niyyar cigaba da tafiya cikin wata irin murya ya kira sunanta shiru bata amsa shi ba sai dai ta tsaya bai damu ba yaci gaba da fad’in “am so sorry pls kiyi hak’uri nasan ban kyauta maki ba amman kamar yadda nace zan gyara laifi na in sha Allah zamu yi Magana kinji?” Shiru dae bata tanka ba ya mik’a mata ledan da purse yace “ga drugs en ki ki d’aure ki sha….and sun…ce ki rink’a sit bath with lukewarm water da d’an salt nasan baki rasa sanin hakan but kaman yadda nace kar ki fad’a ma kowa abunda ya faru pls” a wawware yake Maganar duk muryar shi ta canza ga wani nishi da yake yi in yana Maganar shiru dai tayi kanta na gefe jin k’arar ta6a k’opar gidan su alamar za’a bud’e yasa ta kai hannu ba tare data kalle shi ba ta amshi purse da magungunan daidai lokacin Amadu ya bud’e k’opar tunanin yadda zata cigaba da tafiya ta shiga yi tayi tsaye Haisam ya fahimci hakan sai ya kira Amadun ya nufo shi ya juya ya koma Mota Amadun na biye dashi a jikin Motar ya jingina Amadu ya iso ya tsaya gaban shi da murmushi ya gaishe da shi ya amsa yana kokarin daidaita voice d’in shi yace “am sorry na hanaka yin bacci ko?” Murmushi Amadu yay yace “ai lokacin da ka kira ni d’azun ban ma kaiga kwanciya ba ina chatting ne” jinjina kai Haisam yay ya d’an saci kallon Fatuu dake k’ok’arin shigewa cikin gidan yace ma Amadu “kana zance kenan?” Yar dariya mai sauti Amadu yay don bai tsammaci jin irin Maganar daga wurin Haisam ba yace mashi a’a, d’an yamutsa fuskar shi yay a kokarin shi na ya d’an yi murmushi kafin yace “Ok in ka shiga pls ka basu hak’uri” Amadu yace “toh naga ma tayi bacci yanzu d’azun ne da ta ga k’arfe 12 tayi naga kamar ta d’an damu tana cewa ko lpy shine har ta kira wayarta sau biyu ba’a d’aga ba sai na nuna mata ba lalle in an fara da wuri ba don irin wannan ana yin African time sai akai har tsakar dare wasu ma kwana ake” d’an lumshe ido Haisam yay ya bud’e yace mashi ya shiga gida ya gode sosae yayi mashi saida safe ya juya idon Haisam akan shi har ya shiga gidan ya maido kopar ya rufe, hannu Haisam yasa ya dafe forehead d’inshi gaba d’aya ran shi a cunkushe yake rashin kwanciyar hankali ta hana yaji zafin zazza6in daya rufe shi ya d’an d’auki lokaci a haka shi kadae kaman Aljani acikin tsohon dare daga baya ya cire hannun daya dafe goshin ya rufe kopar da Fatuu ta fito kafin ya zagaya driver side ya bud’e ya shige bai yi tunanin zuwa gidan Hajiya ba duk da yasan ko ya koma Gra ba iya k’arasa aikin da ada shine zai maida shi can d’in ba, bayan ya tashi Motar ya juyata ya koma Gra, lokacin da Amadu ya shiga gidan har ta shige d’aki shima nashi ya shige tana shiga ta nufi gado ta aje ledar maganin da purse a gefe tay zaune tana ta sakin ajiyar zuciya a hankali can ta kai kwance ta kife fuskarta a jikin katifa kwalla suka fara gangaro mata abunda bata ta6a tunani zai faru da ita bane ya farun wai Ya Haisam ne yay raping d’inta wani ma in yaji wannan Maganar ai ba zai ta6a yarda ba wllh ita yanzu shikenan tasan ko aure tay mijinta bazai ta6a d’aukarta da daraja ba in ma ya zauna da ita kenan, runtse idonta tay tasa kuka mai ta6a zuciya ta fara raya miyasa Ya Haisam zai mata haka miyasa Ya za6i ya cutar da ita har hakane ko dai Khalid da kowa yasan halin shi ne bai cutar da ita kamar yadda Haisam yay ba shi da ma yake da aure wata zuciyar ce ta fara kokarin k’are shi tana ayyana mata sharrin shaid’an ne ba komae ba tunda shima ai tasan ba halin shi bane ko, wata zuciyar kuma tace koda ba halin shi bane dama ya so ya aikata mata hakan tunda ai ta rok’e shi amman yak’i saurarenta kuma dama yana yi mata wasu abubuwa da bai saba mata ba ko jiya a parlon shi ai saida ta gan shi yana kallon mata boobs hakan na nufin sha’awarta yake! tana yin wannan tunanin ta k’ara sautin kukanta abun da ciwo Mutumin da take tsananin k’auna amman shi sha’awarta yake ta yadda har ya kasa dannewa saida yay mata wannan aika aikar saida tay mai isar ta kanta na kife kafin ta rarrashi kanta ta yanke a ranta bazata bari kowa yasan abunda ya faru ba kuma ba ruwanta da Ya Haisam ta fita daga harkar shi daga yau wata zuciyar ta raya mata kar tace haka ta bari ya zo suyi Maganar da yace goben ta raya koma yazo ai bai wuce yace zai bata hak’uri ne ba wani abu ba, “in kuma yace zai aure ki fa??” ta sake raya mata shiru tay tana kikkafta ido k’arshe ta yanke tasan hakan ma ba mai yuwu bane mutumin da duka shekara d’aya da rabi kenan da auren shi koma ba haka ba taya Aunty Fanan zata amince ya aureta ta san hakan ba mai yuwuwa bane, “in shi yaga zai auren ki duk abunda zai faru ya faru fa?” Wata zuciyar ta k’ara raya mata wannan karon yunk’urawa tay ta tashi zaune fuskarta a tamke a fili tace “Bazan Aure shi ba wllh tunda ba don yana sona zai aure ni ba sai don ya goge laifin da ya aikata man ba zan ta6a amincewa ba yaje yaci gaba da zama da matar shi da yake so” idanunta ne suka sauka akan ledar magungunanta ta kai hannu ta d’aukko ta tana kallo ta raya yakamata ta 6oyeta can kuma tay tunanin dole fa sai tayi wankan tsarki kuma, shiru tay zuciyarta ta fara tariyo mata farkon yadda abun ya faru a hankali ta lumshe ido tana ta tuno lokacin kafin ta fita hayyacinta ji take inama ace da aure suka aikata hakan cike da so da k’aunar juna wasu kwalla ne masu zafi suka fara gangaro mata tunowa da haramun suka aikata da sauri tasa tafin hannunta cikin kuka take fad’in “Ya Allah ka yafe man na tuba bazan k’ara ba ba hali na bane sharrin shaid’an ne” can ta mik’e tana tafiya a hankali ta nufi wardrobe ta aje ledar magungunan bayan ta rufe tsaye tay tana tunanin yadda zata yi wankan in tace ta bari saida safe to saidai fa ta bari har gari ya waye bata yi sallar Asuba ba tunda ba yadda za’ai ta yi da Asuba sanin lokacin gwaggo ma ta tashi wata zuciyar ce ta ayyana mata kawae tayi yanzu tay tsaye tana jin tsoron kar ta je tana yi gwaggo kuma ta fito taga tana yin wanka cikin tsakar daren nan wata zuciyar ce ta raya mata in ma ta kamata sai tace sun dawo ne jikinta ba dad’i ta kasa yin bacci shine ta fito ta watsa ruwa still kaman hakan bai kwanta mata ba don gani take kaman duk da haka zata gane can dae tay shahada ta nufi wajen kitchen taje don tasan ana aje ruwan zafi a Electric kettle koda yaushe cikin sa’a kuwa akwai ruwan ta d’aukko butar gaba d’aya cikin fad’uwar gaba ta fito ta nufi Toilet har ta shige ba wanda ya fito, a ciki ta had’a ruwan tay wankan ta d’an zauna wasu duk da bata sa gishiri ba bata d’auki lokaci ba Saboda tsoron kada wani yazo ya ganta doguwar rigar ta maida ta d’aukko butar ta fito saida ta cikata da ruwa ta lalla6a ta maida ta kitchen d’in ta jona ta fito don tasan in ya tafasa zata mutu, har saida ta saki ajiyar zuciya ganin ta shige d’akinta ba tare da wani ya ganta ba wardrobe ta nufa ta fiddo doguwar rigar bacci ta cire ta jikinta tasa ta duk’unk’une wadda ta cire ta cusa ta a cikin Wardrobe d’in daga haka ta nufi switch ta kashe hasken d’akin kafin ta nufi gado ta haye taja bargo ta lullu6e ba laifi sosae rad’ad’in da take ji ya rago sai dae k’afafunta ne bata iya rufe su ba kamar in tana tafiya, lamo tay idanunta a waje tana kallon sama ta shiga ayyana yanzu da ace aure tay hakan ta faru tasan da yanzu mijinta na nan yana tarairayar ta amman yanzu gata tamkar mara galihu iya cuta dae ya Haisam ya cuceta wllh, a hankali take goge kwallan dake zubo mata ba laifi zazza6in ya sauka saidae jikinne duk ba dad’i take jin shi………
Lokacin da ya isa bakin gate d’in yana yin horn sau biyu Security yazo ya bud’e mashi ya shige, inda ya parker ta d’azun da suka zo anan ya k’ara parker ta bayan ya kashe d’an jimm yay kaman ba zai fito ba can ya kai hannu ya bud’e ya d’auki wayar shi dake gefe ya fita ya nufi cikin gidan, yana shiga Bedroom d’in idanun shi suka sauka kan gadon ya nufe shi a bakin gadon ya zauna idanun shi akan blood stains d’in dake jikin Farin bedsheet d’in tunanin yadda zai yi da shi ya fara zuciyar shi ta raya mashi wankewa yakamata yayi ya mik’e ya kai hannu ya fara cire bedsheet d’in bayan ya cire yana ruk’e da shi ya nufi hanyar corridor ya shiga laundry room ya bud’e Washing machine ya saka ya fara wankewa bayan ya gama koda ya fiddo shi sai yaga stain d’in na nan amman dai ya d’an rage zuciyar shi ta bashi ba lalle ya fita ba don ya bushe a jiki tunanin ko ya sa hannu ya wanke yaga in zai fita yay saidae shi bai iya wankin hannu ba don iya underwear d’in shi dana Fanan yake wankewa suma kuma a washing machine can dae ya yanke gwada wankewa da hannu ya juya yana tunanin a inda zai wanke don ba bucket a toilet d’in sai dai ya tafi part d’in Mom d’in shi ya d’aukko kuma da akwae tazara, dubara ce ta fad’o mashi ta ya toshe hanyar fitar ruwa ta bathtub d’in ciki sai ya wanke anan, bayan ya toshe a ciki ya k’ara wanke shi sam bai sha wata wahala ba duk da ba yin wankin yake ba saidae shi ba rago bane don ma jikin yayi weak ga zazza6in dake damun shi don har yanzu akwae shi a jikinshi cikin sa’a sai gashi ya fita don ma ba bleach a toilet d’in duk da bai sha wahalan wankewa sosae ba tunda fari ne, bayan ya d’auraye shi tunanin inda zai shanya shi yay ya yanke saidae ya fita can ta k’opar bayan gidan nan keda fence ta hanyar zuwa swimming pool har zai tafi can idon shi ya sauka akan k’opar laundry d’in yaga lafiya lou zai iya d’aura shi anan yay hakan sannan ya dawo ya wanke itama jallabiyar shi da ta 6aci, saida yay wanka ya tsarkake jikin shi ya canzo wata jallabiyar sannan ya dawo cikin bedroom d’in ya nufi inda kujeru suke ya zauna ya d’aura ha6ar shi kan hannuwan shi da ya dunkule tunanin halin da Zarah take ciki ya shiga yi gaba d’aya tsananin tausayin ta ya gama mamaye mashi zuciya ba kamar in ya tuna yadda yay da Fanan a first night d’in su nan da can ma sai ya d’auketa ya kaita ta dingi yi mashi rigima, gashi daga yadda Al’amarin ya faru yasan Zarah ta fita jin jiki kawai don tana da k’arfin hali ne, slowly ya lumshe idonshi underneath his breath ya furta “Am very sorry Zaraah I knew i hurt u…” tunanin ya kirata yaji halin da take ciki yay ya bud’e idanun a hankali kafin ya yunk’ura ya mik’e ya nufi can gefen gado inda ya aje wayar shi Lokacin da ya shigo saida ya kalli time biyu da rabi har ta wuce shiru yay yana tunanin ko ya kiratan can dae ya bud’e wayar yay sending mata kira lokacin har bacci mai nauyi ya d’auketa hakan yasa har kiran ya yanke ba’a d’aga ba ya sake wani kiran shima ba’a d’aga ba tunanin ko tayi bacci ko kuma fushin da take ne yasa bata d’auka ba yay ya aje wayar akan mattress yai zugudum can ya mik’e ya nufi gaban mirror ya jawo drawer chest ya fiddo wani d’an madaidaicin first aid box bayan ya d’aura saman mirror ya bud’e Panadol ya d’aukko ya 6alli guda biyu ya maida bayan ya rufe box d’in ya maida shi inda ya d’aukko wurin kujeru ya nufa walking very slowly ya zauna ya d’auki robar ruwa a cikin kayan Abincin da suka ci ya bud’e ya sha maganin kafin ya rufe ya ajeta, maida bayan shi jikin kujeran yay ta d’age kai hannun shi d’aya dafe da forehead d’inshi, ya d’an d’auki lokaci a haka can ya d’ago ya mik’e ya kwashe kayan ya fita dasu daga d’akin bada jimawa ba ya dawo ya nufi Corridor toilet yaje ya d’auro Alwala bayan ya dawo ya shimfid’a prayer mat ya kabbara sallar Nafila raka’a hud’u yay don k’arfin hali kawae yake bayan ya d’aga hannu ya d’an jima yana Addu’oi kafin ya mik’e ya nufi gado har wani duhu duhu yake gani ko tunanin shimfid’a wani bedsheet bai yi ba a haka ya hau kan mattress d’in yaja duvet ya lullu6e jikinshi har kan shi nan da nan kuwa temperature d’in jikin shi yay high sosae numfashin shi ya fara fita da zafi a haka bacci ya d’auke shi amman bana dad’i ba, gab da kiran sallar Asubar farko k’arar wayar shi ta tashe shi alamar ana kiran shi ya bud’e fuskar shi duk ta canza kala da alamun mamakin mai kiran na shi a time d’in, yunk’urawa yay ya tashi zaune ya kai hannu daga d’an gaban shi ya d’auki wayar yana kai idon shi kan screen d’in ganin sunan mai kiran har saida gaban shi ya d’an Fad’i ya shiga tunanin ko lafiya jiki a sanyaye yay picking kafin ya kara a kunne..,
Har aka gama Sallar Asuba Fatuu bata farka ba rashin jin motsinta yasa gwaggo bayan ta gama azkar ta mik’e ta nufi d’akinta don tasan ta dawo lokacin da ake kiran sallar farko da ta fito ta d’aga labulan d’akin ta ganta a kwance, lokacin da ta shiga tana a kudundune har sannan gwaggo ta tsaya a gaban gadon ta fara kiran sunanta shiru har sau kusan ukku hakan yasa ta d’an duk’a ta kai hannu tana d’an bubbuga jikinta can ta fara motsi a hankali ta cire bargon dake rufe da fuskarta ta d’an juyo da fuskar da yake taba gwaggo baya ba saitin da take ba ta ke kallo koda tay arba da fuskarta da sauri tasa hannu ta dafe goshin ta ta yarda har idanuwanta ta d’an rufe ganin ta farka yasa gwaggo ta zauna a bakin gadon tana kallonta tace “Wane irin bacci kike ne haka baki san Asuba tayi ba ga gari har ya fara washewa baki tashi kin yi salla ba” d’an yamutsa fuska tay murya k’asa k’asa tace mata bata san gari ya waye ba bari ta tashi, ganin ta dafe kai yasa gwaggon tambayarta lafiya ta dafe kai haka wani irin bugu kirjinta ke yi tay k’ok’arin daidaita Maganar ta tace “Wllh kan ne ke man wani irin ciwo” da d’an alamun mamaki gwaggon tace “ciwon kai kuma to ya akai?” abu Fatuu ta had’iye ta fara tunanin abunda zata ce mata can tace “Wurin ne hayaniya tayi yawa sosae sai faman kid’e kid’e ake harda yan police band fa ga masu irin kid’an su na gargajiya in suka buga har tsakiyar kan Mutum wllh” yar dariya gwaggo tay tace to tunda shagali suke ai dole suyi kafin ta kuma cewa “gashi kuma kun dad’e sosae don har sha biyu ta wuce fa idona biyu ina dakon ki amman shiru ga wayar ki na kira ba’a d’aga ba……..” Da sauri Fatuu ta tari numfashinta tace “a cikin Mota na barta kuma ba’a fa fara ba da wuri anata jiran wasu manyan mutane da yake bikin fa d’an sarkin inyamurai ne sai wurin sha d’aya in ma bata wuce ba aka fara da aka gama da Aunty Feenah ma akace in bi gidanta wai in kwana ni kuma na matsa sai na dawo tunda ba haka mukae da ke ba” jinjina kai gwaggo tay da d’an murmushi tace “Allah sarki ai da kin bitan ba wani abu dama dai aji shiru shine matsala amman indai ansan inda ake ai ba komae” juyar da kai Fatuu tay gefe jin k’walla na son zubo mata don wani irin tausayin gwaggon taji ta bala’en yarda da Haisam ta yadda ko kusa ranta bai bata wani abu mara kyau a game dashi, kokarin mik’ewa ta fara yi tana fad’in ta tashi tay sallar in tayi breakfast sai tasha magani akwae ruwan zafi a cikin flask a cikin kitchen da bread ita bari taje ta kwanta ta huta tunda yau bazata aiki ba daga haka ta fuce, wani irin kuka mai cin zuciya Fatuu ta saki zuciyarta ta raya mata yanzu fa ba kuka bane a gabanta ta fara tunanin yadda zatai jinyar kan ta ba tare da an gane ba don a iya tafiyarta ma kawae da gwaggo ta gani to tabbas zata iya zargin wani abu koma ta gane yin wannan tunanin yasa da sauri ta goge kwallan ta fara k’ok’arin sauka daga kan gadon a hankali ta fara tafiya k’afafu a wawware tana d’an yamutsa fuska don wurin yay tsami tana buk’atar ruwan zafi, saida ta d’an lek’a fuskarta ta labule ta kalli kopar d’akin gwaggo tsoro take kada ta fita itama ta fito su had’e ta d’an d’auki lokaci a haka can dai tay Addu’a ta yaye labulen ta fita gabanta na wani irin bugu tamkar ana mata luguden ta6are, kasa tafiya tay tayi tsaye a wurin can ranta ya bata ta lek’a taga mi gwaggo ke yi ta nufi d’akin a yadda take tafiya har ta k’arasa without making any sound a hankali hannu na rawa ta d’an d’aga labulan ta hangota saman gado ta lullube rabin jikinta har saida taji wani sanyi ta saki labulan ta juya, sosae ta d’aure tana cije baki ta rink’a tafiya yadda zata d’an yi sauri ta nufi kitchen ta d’aukko electric kettle ta nufi Toilet bayan ta fito, saida ta zauna ruwan zafi sannan ta d’auro Alwala, zaune tay bayan ta gama sallan da k’yar ta shiga tunanin yadda zatai don yadda take tafiya tsab asirinta zai tonu tana ta sak’e sak’e can dubara ta fad’o mata ta ta tafi Makaranta kawae kafin gwaggo ta tashi ko Kawu Amadu don shima ta san yanzu bacci yake tunda weekend ne sai d’an anjima zai tashi ya bud’e shago da wannan tunanin ta lalla6a da sauri ta tashi bayan ta d’auke abun sallan ta nufi Wardrobe ta fiddo wata doguwar riga ta zumbula ta ciro yar madaidaiciyar hijab ta saka lokacin idanunta suka sauka kan ledan magungunan ta d’aukko su bayan ta rufe ta d’aukko jakar goyonta da komae na karatun ta ke ciki ta bud’e ta saka magungunan ta sake bud’e wardrobe ta d’auki k’ananun kaya kala biyu da undies don acan tana da kaya bayan ta rufe wardrobe d’in ta d’auki wayarta dake ajiye gefen gado itama ta saka ta kauda duk wani abu da zata kauda daga haka ta nufi hanyar fita hannunta ruk’e da jakar saida ta lek’a ta tabbatar ba kowa sannan ta fita ba sai na fad’i yadda gabanta ke fad’uwa ba sai Addu’a take a cikin ranta cikin sa’a har ta kai zaure bata ji motsin wani ya fito ba ta bud’e gidan wanda sakata ce kawae Amadu ya sa da ya dawo daga sallar Asuba.
Lokacin da ta fito wajen kwalam ba mutane bata bi ta hanya ba ta lungun gidan Hajiya tabi tana yi tana dafa bangon gidaje in ta gaji sai ta d’an tsaya ta huta kafin taci gaba tana cikin hakan tazo daidai kangon da su goga suka so raping nata wanda yanzu gida ne masu shima har sun dawo yanayin fuskarta ne ya canza ta shiga tuno yadda abun ya faru a lokacin har Haisam yazo ya ceceta da kuma lokacin da ta je part d’in shi daga baya har yace mata dama ita yar iska ce, a hankali kwallan da suka taru suka fara gangaro mata a fili ta furta “Ya Haisam yanzu ai kasan in ni yar iska ce ko…..” Cigaba da lalla6awa tay tana yi tana cigaba da goge kwalla ta d’auki lokaci kafin ta kai bakin hanya don ba ranar aiki bace sam bata ga wani abun hawa a layin ba saida taje bakin hanya nan ma saida ta d’an yi jiran samun Napep don babu sai masu mashin ne keta tsayawa tana girgiza masu kai don tasan ba iya hawa zata yi ba daga baya ta samu Napep d’in ta fad’i mashi inda zata je suka tafi, lokacin da suka isa da kanta ta rok’i mai gadi kan ya bari a shiga da ita ciki bata lafiya ne da yake sun saba sosai yace to amman yay sauri ya fito suka shige bayan tayi mashi godiya, har bakin Hostel ya kaita bayan ta fito ta biya shi shima saida yay mata Allah ya sawak’e tay mashi godiya sannan ya juya Napep d’in ya tafi, harta shige bata ga kowa ba anata baccin weekend wad’anda suka rage a hostel d’in wanda ba yan gari ba don yan cikin gari da garuruwan kusa duk weekend suke tafiya wani lokacin, data zo hawa bene nan abun ya zama aiki tana yi tana dafa bango tana runtse ido had’i da cije baki a haka har ta haye ta nufi d’akin su a cikin bag d’inta ta fiddo makullin da yake hannunta don Fauzy ma ta tafi gidan Aunty Mareeya Weekend, bayan ta bud’e ta shige ta turo kopar ta nufi gado ta zauna ta aje jakar a gefenta har taji d’an sanyi yanzu sai tunanin abunda zata fad’a ma gwaggo in ta kira ta shiga yi, tana ta zaune jugum ga wata irin yunwa da take ji tun a gida can ta mik’e don ta samu abunda zata ci d’an gas d’insu ta kunna ta d’aura ruwa acikin yar babbar tukunya ta koma gefen gado ta zauna har ya tafasa sannan ta tashi ta d’ibi wanda zata had’a tea cikin d’an Flask ta saka Lipton kafin ta rufe sauran ruwan zafin ta juye a cikin bucket ta d’an sa gishiri sannan ta fita zuwa toilet, sosae taji dad’i bayan ta fito saida ta soya k’wai sannan ta had’a tea d’in ta had’a da biscuit ta ci data gama tasha magungunan ta haye gado ta kwanta ta lullu6e rabin jikinta tay ma bango k’uri zuciyarta ce ta raya mata Ya Haisam yace zasu yi Magana gashi har yanzu bai kira ba balle ma yaji ya take d’an ta6e baki tay ta raya ita tasan ba wata Magana data wuce ya bata hak’uri, a hankali ta fara lumshe ido a haka har bacci Yay awon gaba da ita. Lokacin da gwaggo ta fito sam bata yi tunanin tashin Fatun ba don tasan tace mata kanta na ciwo hakan yasa ta k’yaleta ta wuce kitchen koda ta shiga bata gane bata yi breakfast ba don Amadu ya shiga ya d’iba sai tay tunanin ko Fatun ce itama had’a nata tay ta koma d’aki, bayan ta gama ta fito da kayan ta maida kitchen kafin ta fara kokarin gyara gidan a haka har lokacin d’aura Abincin rana yay ta d’aura tana cikin yin girkin tace bari ta duba Fatuu baccin yayi yawa ko ciwon kan yayi tsanani ta nufi d’akin ta…………
Some Of Related Hausa Novels
Be With Us
-
- Follow our Facebook Page : Ai Hausa Novels
- Follow our Twitter Page : @ Ai Hausa Novels
- Follow our Youtube Channel: Ai Hausa Novels
DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.