Hausa novels

Kanwar Maza Page 85 End Complete Novel By Ayshercool

Page 85

 

*WANDA KU KA KARANTA MINI LITTAFI BA TARE DA KUN BIYA NI HAKKINA BA, BA KUMA DAN BAKU DA SHI BA, IDAN KUN SHIRYA BIYANA HAKKINA GA ACCOUNT NUMBER NA 0009450228, AISHA ADAM JAIZ BANK*

 

 

 

Mahmud ya ce wa mai sunan baba, bai kamata su yi sanya ba, idan da dama kamata yayi kawai su tafi Gomben su bita can.

 

Mai sunan baba ya ce “Tayaya ni ban san a ina take a gomben ba”

 

“Tambayar mutanen gidan zamu yi, ba zamu yi sanya ba”

 

Ba tare da wani ɓata lokaci ba, mutanen gidan suka basu kwatancen in da Ade take, kasancewar sun san mai sunan baba.

 

***

Rumaisa kuwa gwaggo ce ta je zauna mata, saboda biƙi, mutane suna ta zuwa duba ruma tare da jajanta mata abun da ya faru.

Tana zaune a ɗakinta, suna video call da laila, sai kuka take yi mata, wai babyn ta ya mutu.

 

Laila sai rarrashin ta take yi, tana kwantar mata da hankali, tare da jaddada mata, idan komai ya dai-daita, lallai ta nemi maman Khadija, da maman ilham ta gyara, duk da yaron ya rasu, akwai buƙatar ta gyara jikinta sosai.

 

Rumaisa ta ce “To anty laila, in sha Allah ai ina da numbern su, ina Yasir”.

 

Laila ta ce “Yaya bacci yake yi bai tashi ba”

 

Ruma ta ce “Inyee su yaya manya, ina fatan dai ba ya miki rashin ji?”

 

“Ba wani rashin ji, rashin ji ai sai ke, wallahi na ji daɗin zuwan Yasir gidan nan rumaisa, very kind and brilliant guy, darling ya yi masa registration ma, very soon zasu fara lectures, baki ga daɗin da babansu ya ji ba zuwansa, su anam ma suna ta murna”

 

Ruma ta ce “Sai wani yabon sa ki ke yi”

 

“Dole in yabe shi mana, dole a sarawa mama, yaranta gaba ɗaya masu tarbiyya ne da nutsuwa, ke ce kawai mara ji”

 

Ruma ta ce “To nima papa yana yabona, yana sona a haka”

 

“Ai shi dama ba zai ga rashin jin da ki ke ba. Yauwwa mimi ya hatsaniyar gidan kuwa ta lafa?”

 

“Ina fa lafawa, suna can suna cigaba da tashin hankalin su, ni ina nan ina fama da kaina, da mutuwar ɗa na, mummy sun watse da Hajiya Lubabatu, ashe Jabir lalata suke shi da ruƙayya, abun duk babu daɗi mahmud dai ya rufe shi”

 

Laila ta ce “Lamarin gidan nan sai Innalillahi wa Innalillahi raji’un, Allah ya sa mu dace kawai mimi, bari na bari ki huta”

 

“To anty laila na gode sosai”

 

Tana gama wayar, Gwaggo ta shigo da kunun kanwa, ta ce ruma ta sha.

 

Ruma ta ce ita wallahi ta gaji da wannan kunun kanwar, gudawa yake sakata.

 

“To idan baki sha ba nonon ya zube ki huta ai, gyara ki nake son yi, na bayar da dawa ma a niƙota in sheƙa miki tuwo, ga yajin daddawar ki nan”

 

“Gaskiya gwaggo ba zan ci tuwon dawa ba, in haihu ki bani wani tuwon dawa taɓ. Kunu kuma ina da sauran sabayata, yaushe zan ta shan kunun kanwa cikina yana ciwo”.

 

“Kya ji da shi dai, ana yi miki abun arziki kina na tsiya”

 

Haka rumaisa suke faɗa da gwaggo, komai sai ruma tayi raki.

 

Yanzu ma Adam ne ya je ya tarar da ita gwaggo na ta masifa, kamar ta ari baki, a kan rumaisa ta tashi ta je ayi mata wanka, tun yamma ake dafa ruwan, amma Rumaisa taƙi yadda ayi,  ta maƙale tana kuka, wai wallahi fatarta duk ta dahu saboda ruwan zafi.

 

Takawa ya shiga ɗakin suka gaisa da gwaggo, ya dubi ruma ya ce ‘Mimi meyasa ki ke da gardama ne?”

 

“Saboda ba ka ga uban tururin da ruwan zafin yake ba, da wanne zan ji, zafin haihuwa ko mutuwar ɗa na, ko na ruwan zafi?”

 

“Ai ni kin san bana jin zafin ruwa, zo mu je” yayi maganar yana miƙa mata hannu, ba kunya ta zagaye gwaggo ta bi takawa.

 

Gwaggo ta saki baki tana kallon ikon Allah, daga rumaisa har mijinta ba su da kunya ko kaɗan.

 

A banɗakinsa ya haɗa ruwa zafin dai-dai jikinta, ya taimaka mata, ta gyara jikinta ta yi wanka, sai dai rumaisa akwai langwai.

 

Suka fito ya bata abinci ta ci, sannan ya ɗauki magungunan ta ya bata ta sha.

 

Ya kalleshi ta ce “Na gode sosai papa, ya ku ke ciki a abujan ne, yaushe Abdallah zai dawo?”

 

Takawa ya kwashe komai da ya faru ya gaya mata.

 

Tayi ta rarrashin sa, tare da bashi tabbacin, Allah baya barin zalunci, amma kar ya ce zai cigaba da dagewa sai ya ga bayan wakili, saboda yana da goyon bayan manyan ƙasar.

 

Ya ce “Haka ne, in sha Allah na bar wa Allah”

 

Cikin dare rumaisa nono ya cika, ya takura mata da ciwo, saboda ba ta shayarwa, dan haka kwana tayi kuka, har da zazzaɓi.

 

Gaba ɗay tausayinta ya cika takawa, su mata komai na su abun tausayi ne, ta haihu ta rasa ɗan, amma akwai wani pain ɗin na daban.

 

Anty laila ya kira directly ya sanar mata, ta ce su yi haƙuri, da safe su kira maman ilham a waya, su sai maganin ta na gyaran nono, mace ko yaye tayi yana hana mata jin zafi, kuma baya bari nono ya lalace.

 

(0813 561 3021zaku iya neman maman ilham kai tsaye ta lambar wayarta. Haka zalika kar ku manta da haɗin maman Khadija na sabaya

0703 777 7442)

 

Da safe har wurin ƙarfe goma, sanna suka tashi ita da takawa, Gwaggo har ta gaji da jiran fitowar ruma ayi wanka, sai ganin ta tayi tsaf, ta sha wankanta sun fito ita da takawa. A kunyace gwaggo ta gaisa da takawa yayi musu sallama ya fita.

 

Yana tafiya Gwaggo ta din ga yi mata faɗa “Saboda rashin gado, kina jego ki ka bi miji ku ka kwana tare ko? Ki cigaba da biye masa wani cikin zai yi miki ya bar ki wahala, tun jikinki bai gama ƙwari ba, dama gashi kin ƙi bari ayi miki jegon kirki, ki je ki ƙarata”.

 

“Ni fa gwaggo ke ba kya lallaɓa ni kamar yadda yake yi mini, jiya har ranƙwashi na ki ka yi”

 

“An ƙi a lallaɓa ki, ku ƙara ina yin sati biyu zan gudu, ba zan iya baɗala ba” haka gwaggo ta cigaba da mita, ruma kuwa ko a jikinta.

 

Turaki tun da aka watse daga taron nan kuwa, kwanansa biyu ya rufe kansa a turakarsa, yana jinyar zuciyarsa daga raɗaɗi da ɗacin abun da iyalinsa suka aikata.

Wanda ya ɗora alhakin hakan a kansa, da kuma rashin jajirtacciyar uwa ga yaransa, kodayake auren biyayya ne na haɗi, duk cikinsu sharif ne kawai yayi tutsu, ya ce shi sai wadda yake so.

 

A kwana na uku, aka sanar da jikin galadima ya tsananta, dan haka ya shirya ya tafi jamus.

 

Mahaifiyar su Jamil kuwa ta sha kuka, duk wanda ta san zata kira, ta roƙi a saka baki a bayar da belin jamil, kowa yaƙi.

 

Samha ba ta taɓa zaton Jamil ne mutumin da wakili ya samu yake taimaka masa ba.

 

Ko da ta kira shi a waya, ya ci mata mutunci ya ce kar ta sake kiransa, shi yanzu ya samu biyan buƙatar sa ya san koba koma, yanzu Adam ya san su ba sa’anin yin ba ne ba!.

 

***

Su mahmud kuwa, basu wahala ba wurin kwatancen da aka basu, nan da nan suka isa gari da Ade take, kuma gidan ƙanin nata sam bashi da ɓaci.

 

Ras ta gane mai sunan baba, ta din ga murna da zuwansa, sai dai ta din ga kallon mahmud, kamar ta san shi a wani wurin.

 

Babu ɓata lokaci mai sunan baba ya wassafa mata abun da yake tafe da su, da kuma dalilin da ya sanya yake ta bibiyarsu tun a lagos, har biyo ta nan.

 

Ba tare da ya gaya mata waye mahmud ba, jiki a sanyaye ta ce “Adamu ne?”

 

Umar ya ce “Kin gane shi? Kin san Ammi?”

 

Tayi murmushi mai ciwo ta ce “Na san Bintu, bintu ƴar ɗakina ce sosai da sosai, lokacin da tayi aure tana goyon yaronta na biyu, muka bar garin, nayi kewarta sosai da sosai, sai dai wasu dalilai ya sanya ko da muka bar garin ko sunan garin bana ƙaunar ji”

 

Mahmud ya ce “Kin tuna jikar ki mairamu?”

 

Ade ta fashe da kuka, ta ce “Yarinyar da aka bar amanarta a wurin jauro, da dabbobin mu, muka yi gaba, ya iskemu ya ce: wai ƴan fashi ne suka kai musu farmaki, an kasheta ita da mijinta, dabbobinmu ma duk an tafi da su, kamar wanda ya rufe mana baki, babu wanda ya ƙaryata shi haka muka sha kuka. Bayan wasu shekaru yara suka fara fita neman ilimi, wasu suka zauna a riga, muna katsina a ka kai mana farmaki shekara uku baya, aka sake kashe mana ƴan uwa, muka sake yin hijira, shi kuma jauro ya ce a can zai cigaba da zama, sai daga baya labari ya iskemu, ashe jauro ɗan fashin daji ya zama, kuma shi ya kashe mijin mairamu ya gudo shi da matarsa, yayi asiri ya rufe mana baki. Wai sojoji sun kashe shi kwanan nan”.

 

Mahmud ya ce “Kar ki ce mini mutumin da rumaisa ta zana ta ce yana kama da Iman kawunta ne? Shi ne ya kashe mahaifin ta?”

 

Ade ta ce “Waye kuma ima?”

 

Sai a lokacin suka warware mata abubuwan da suka faru bayan barin su garin.

 

Jiki na rawa ta ce “Kuna nufin Bintu tana raye? Ita ta riƙe ƴar mairamu?”

 

Mahmud ya ce “Ƙwarai kuwa wannan mijinta ne ma?”

 

Ade ta rikice da kuka, tare da yi wa Allah godiya, da kuma sanya wa Ammi albarka.

 

Ta ce “Wallahi yaro Bintu tana zuciyata, ka ga dai gani a cikin garin gombe, amma har yau ko tuna rigar da muka zauna bana yi, ko in hanyar garin take bana son ji, gaba ɗaya tsoron mutane nake ji, Jauro bai yi mini adalci ba, dan Allah ku tashi ku kaini na ga Bintu, naga abun da mairamu ta bari” nan ta din ga basu labarin kyawawan halaye irin na mairamu, na rashin magana da haƙuri, yadda ta rayu a gidan jauro, ana azabtar da ita, tun tana yarinya saboda kawaici suka baro ta, suka sauya riga, an yi mata aure sun taso tare suka ya da zango, ta haihu tukuna, amma jauro ya cuce su.

 

Ade ta din ga murna tana cewa amma ta ji daɗi da malam umar ya zamana mijin jikarta.

 

Nan da nan ta saka a kira Alhaji Aminu, tare da ce masa duk in da yake ya dawo, ko kuma yazo ya tarar ta tafi kano, an ga jikirta a birnin kano, tun da ba a kaita kano dan Allah ba, yanzu dalili ya samu dan haka babu mai hanata tafiya.

 

Nan da nan riga ta ɗauka, an samu ƴar mairamu a raye, ashe kan ta mutu ta haihu, aka din ga zuwa ganin mai sunan baba da mahmud. Sun sha karramawa kala-kala.

 

Washegari da wuri Alhaji Aminu ya sauka a garin, tare da jin batun tamkar almara, abun da ya faru shekaru kusan goma sha tara baya, yaya za ayi ace, wai an ga ƴar mairamu.

 

Sai dai ya tsinke da lamarin, bayan saukarsa mai sunan baba ya nuna masa hoton iman.

Alhaji Aminu ya ce “Malam Umaru, amma ka kasa gaya mini wannan abu, duk da ban wani san mairamu ba, amma wannan kamarta ɗaya da ade, kuma ba shakka jininmu ce, yanzu meye abun yi?”

Kanwar Maza Complete Novel Document Txt

Mai sunan baba ya ce “Idan ba damuwa, sai mu taho da iman ɗin da amm…

 

Ade ta ce “Wane mutum, da ƙafar nan tawa ko a ƙafa zan taka na je kano, na ga Bintu”

 

Alhaji Aminu ya ce “Da wace ƙafar? Ƙafa duk sai saura? Ki zauna a shirya tafiya, sai a tafi gaba ɗaya ”

 

Nan ya sake warware musu irin zaluncin da jauro yayi musu, ya din ga haɗa kai da ƴan bindiga ana cutar da su, wanda hakan ya sanya da yawansu suka tarwatse, da farko basu gano shi ba, sai daga baya amma an ce sojoji sun kashe shi.

 

Da daddare takawa ya ceea rumaisa, ta zo su tafi su kwanta, ta ce “Ba zani ba gwaggo ta ce idan na biye maka wani cikin zan samu, kuma wallahi haihuwa da wahala”

 

Dariya yayi ya ce “Ai shikenan”

 

Gwaggo ta kawo wa ruma abincin dare, ta ce “Yau ba zaki bishi ba?”

 

“Ai na gaya masa kin ce bamu da kunya, kuma idan na cigaba da biye masa wank cikin zan samu da suri”

 

Gwaggo ta ɗora hannu a ka ta ce “Rumaisa ba ki da hankali? Ki ka ce ni na faɗa, ashe halinki na wauta na nan, da wani idon zan kalle shi? Wallahi dole in tattara kayana in bar gidan nan”

 

Ruma ta ce “Ashe kuwa zaki maimaita masa abun da ki ka faɗa mini, dan sai ya bi ba’asi”

 

Ta samu ɗan kwali ta kwaɗawa ruma a baya ta ce “Shashasha uwar wauta, shikenan zai daina ganin mutuncina”.

 

**

Mahmud ya kira Ammi a waya, ya ce “Su shirya, su haɗu a wuri guda, suna tafe da manyan baƙi zuwa kano shi da mai sunan baba.

 

Ba yadda ammi ba ta yi ba, amma yaƙi gaya mata ko suwaye, ya ce amma muhimmancinsu ya kai ace har mai girma wambai ko turaki yana wajen.

 

Ammi ta ce “Turaki baya nan, ya je Germany wurin galadima, jikinsa ya tsananta, sai dai wambai”

 

Mahmud ya ce “Baƙi ne masu muhimmanci, har mimi muna buƙatar ta a wurin” Ammi ta din ga mamakin wane irin baƙi ne kuwa haka?”.

 

Da ta sanar da wambai kuwa, ya ce babu laifi, a jira ƙarasowar ta su, aji wani irin baƙi ne, ya ce idan sun iso a kira shi.

 

Ammi ta sanya aka yi ta ɗorawa da saukewa, duk da bata san wane irin baƙi ba ne, amma akwai buƙatar ayi girki.

 

Duk nacin ruma da iman, a kan son sanin suwaye baƙin, ammi ta ce musu ita fa ba ta sani ba.

 

Duk suna falon mai sunan baba ya yi sallama, iman ta tashi da sauri ta ce “Hero suwaye baƙin?”

 

Ruma ta gwale baki ta ce “Su hero manya”

 

Takawa ya ce “Umar kun bar mu a duhu kai da ƙaninka, ku muke ta jira”

 

Yayi murmushi ya ce “Yanzu za su shigo” ya kalli iman ya ce “My yellow, yakamata ki bani tukuici kan ki ga baƙin nan fa” yayi maganar yana jan karan hancinta, a gabansu.

Kunya ce ta kamata ta ce “To me zan baka?”

 

“Saniya zaki sai mini” gaba ɗaya suka hau dariya, Ammi ta fito ta ce “Mai sunan baba kun sauka? Ina baƙin?”

 

Mahmud ne yayi sallama, sai Alhaji Aminu a bayansa ya riƙo ade, sai ƙannenta guda biyu.

 

Sakin carbin hannunta ade tayi, ta ce “Ade” da ƙarfi.

 

Jiki na rawa saboda tsufa Ade ta ɗago ta kalli Ammi ta ce “Bintuna”

 

Da sauri Ammi ta ƙarasa ta riƙo hannun Ade, hawaye ya wanke mata fuska ta ce “Dan Allah gaske ne ba mafarki nake ba, Ade ke ce a gabana? Ade ba irin neman da ban yi miki ba”

 

Suka rungume juna ita da ita.

 

Alhaji Aminu ya ƙurawa iman ido, ya ce “wannan ce ƴar ta mu?” Kamar sokuwa haka iman ke bin su da kallo.

 

Mahmud ya ce “Hajjaju ga ƴan uwanki, mijinki ya nemo”

 

Jiri ne ya fara ɗibar iman, saboda ba ta san mafarkin nan ya cigaja da yaudararta.

 

Umar ya riƙe ta ya ce “Iman, calm down mana menene”

 

“Dan Allah ka tashe ni daga baccin, kamar ba zai faru a gaske ba fa?”

 

“Ba mafarki bane ba fa” yayi maganar yana zama tare da ita, saboda har numfashinta ya fara sama.

 

Alhaji Aminu ya ƙaraso gaban iman, ya riƙe hannunta, ya ce “ƴa ta ba mafarki bane ba, mu ne ahalinki” bayan gama kukan ammi ta ce Aminu haka ka girma sosai? Iman ga Ade da nake baki labari, wannan su ne ahalin mairamu”

 

An sha koke-koke, Ɗan aike ammi ta tasa, aka kira wambai, sai dai yaji kunya da nauyin abubuwan da suka din ga yi wa Ammi da iman, a kan rashin sanin wacece, wanda hakan yana da alaƙa da zigar Mummy.

 

Nan Alhaji Aminu ya gaya musu cin amanar da jauro yayi musu, da ƙiyayyar garin da ya sanya musu, suka kasa komawa, balle su binciki abun da ya faru gaske ne ko ƙarya.

 

Takawa ya ce “Tabbas wannan mutumin shi ne rumaisa ta zana mini, ta ce da wa yake kama? Na ce mata iman, ta ce a yanayin da ta ganshi ne ya sanya ba zata taɓa cewa ta ga wani mai kama da iman ba, kasancewar sa mutumin banza, dan har tattaunawa da shi ta yi”

 

Iman ta rasa mai zata cewa mai sunan baba saboda murna, sai kuka take yi.

 

Bayan an nutsa, ammi ta saka aka kawo abinci, takawa ya ce “Shi da matarsa zai ci abinci, mai sunan baba ya ce shi ma haka. Mahmud ya ce “Ni za a yi wa gori? Sai in ci da ammina”

 

Haka suka wuni cikin raha da dariya, iman ta rasa in da zata tsoma dan farinciki.

 

Labari ya bazu, Mijin iman da Mahmud sun gano iyayen Iman.

 

Hankalin Mummy ya ƙi kwanciya, sai da ta zo ta ganewa idonta, Ade ga jikarta, amma ta yi ram da rumaisa, saboda yadda yarinyar ta yi mata.

 

Da yamma ammi ta ce ruma ta tafi gida, tun da jego take yi, takawa ya ce ta ƙyaleta, duk tare za su zauna, su taya iman murna.

 

Mai sunan baba ma barin iman yayi a gidan, ya tafi gida dan ya huta.

 

Iman da rumaisa gami da nusaiba, sun kewaye Ade, sai dariya take basu, suna yi mata tambayoyi, har bacci ya kwashe su.

 

Takawa dama yana ɗakinsa na sashin Ammi, fitowa yayi, kusan sha ɗayan dare yana nunawa ammi wayarsa, ya ce “Ammi ina mimi, a taso mini ita”

 

A daren aka wallafa labarin kama Khalifa wakili a Mexico da cocaine.

 

Ammi ta ce “Bacci take yanzu, ka bari da safe”

 

Ya ce “Ammi ba zan iya jira ba, a taso mini ita dan Allah”

 

Haka Ammi ta je ta taso masa ruma, ya ja ta ɗakinsa ya nuna mata.

 

“Ban gaya maka ba papa, duk wani azzalumi da ya fi ƙarfinka, bai fi ƙarfin Allah ba, ka zuba ido zaka ga yadda Allah zai ɗaiɗaita azzalumai, yanzu ma ga ta in da ɗan nasa zai yi takara, kuma wannan abun da aka kama ɗan sa da shi, ya isa ya saka baban nasa ma su faɗi zaɓe”.

 

Alwala takawa yayi, ya din ga salla yana godewa Allah, ko wannan tashin hankali ya isa hana wakili sukuni, ɗan sa yayi laifi da ƙasar da bashi da halin yin cuwa-cuwa.

 

Ruma kasancewar jiya ba ta yi bacci da wuri ba, ya sanya take ta bacci da safe.

 

Ammi ta saka aka ɗorawa ruma ruwan zafi.

 

Ade ta ce lallai a kai su su gaida iyayen mai sunan baba ma, Ade ta yi wa Ammi addu’a da iyalan ta da fatan alkhairi, bisa jajircewa kan riƙe amana.

 

Takawa ne ya je yana tashin ruma, ta buɗe ido ta tashi zaune, ya ce “Ammi ta ce ki tashi haka, ki yi wanka sabuwar kakar ki ma tana nemanki”.

 

Wani irin zilllo ruma ta yi tana haki, ta yakushi takawa a wuya ta fita da gudu daga ɗakin, bayan ta ya bi yana kiran sunanta, ta baya ta ɓulla in da ake girki idan da baƙi a gidan, ta kefa wani abu a cikin murhu.

 

Kan ya ƙarasa wurin kuma ta faɗi, cikin tashin hankali ya ɗauke ta, ya kaita ɗaki, sai dai a sume take.

 

Ammi ya je ya gayawa abun da yake faruwa, hankali tashe suka nufi ɗakin da take.

 

Kasancewar iman nursing take yi, ta dudduba ruma, amma babu wani abu da yake nuna akwai matsala a vitals ɗin ta.

 

A hankali ta yi juyi, ta ta da kai da hannunta kamar mai bacci, Ammi ta ce “Alhamdilillah, iman ku ɗaukko mp a kunna karatun Alkur’ani, ko wani abun ne ya sameta” iman ta jinjina kai ta aiwatar da abun da Ammi ta ce.

 

Mutane na ta zuwa ganin dangin iman, su Ade sai godiya suke yi musu na riƙe musu ƴa.

 

Ade ta dame su da tambayar ina rumaisa, iman dai ta fito ta gaya mata halin da ake ciki.

 

Har kan rumaisa Ade ta je, ta dafa kan rumaisa ta ce “Wannan ai kamar shaiɗanu ko sihiri”

 

Tun sanin da Ammi ta yi wa Ade, mace ce mai ibada da yawan addu’a, duk da kasancewar ta ba wata mai ilimi mai zurfi ba.

 

Ta dafa kan rumaisa tana ta yi mata addu’a, a hankali ruma ta ce “papa”

 

“Na’am mimi”

 

“Wata mage ce za ta sha maka jini a wuyanka, ta kasa”

 

“Babu wata magge fa, tsorata ki ka yi, bacci ki ke yi”

 

“A’a ta yakushe ni a hannuna, idonta hayaƙi ma yake yi” ta nuna musu hannunta, in da aka karta mata farata.

 

Ade ta ce “yarinya na jego kun barta tana yawo ko ina, gashi ba ta son ɗan kwali, idonta ne ya buɗe take gane-gane ai”. Aka samu dai ruma ta farfaɗo, sai dai ba ta magana sosai.

 

A yammacin ranar su Ade har gida suka je, suka gaida mama, dan a washegari suke son komawa.

 

Mai sunan baba ya tabattar musu da yardar Allah, zai kawo musu iman, ta ga dangin ta.

 

Har gida suka sake bin mai girma wambai, suka sake yi masa godiya, turaki kuma a lokacin yana Germany.

 

Hajiya Lubabatu wani irin ciwon kai ta din ga fama da shi, mai tsananin gaske, da har ta kai ba ta gane mutane sosai, kuma ba ta son haske sai duhu, tayi ta surutai na fita hayyaci, haka aka kaita asibiti aka ajiye.

 

Ranar da su Ade suka koma, ranar mai sunan baba ya koma lagos shi ma, sai dai mahmud ya rasa sukuni, amma bai gayawa kowa abun da yake damunsa ba, iman ta yi wa mahmud godiya, daga shi har mijinta, bisa ga namijin ƙoƙarin da suka yi mata

 

Still a yammacin ranar, wani tashin hankalin ya sake afkuwa, Allah ya yi wa galadima rasuwa, wato mahaifin jabir, Senator wakili kuma ya hau jirgi domin zuwa Mexico, sun samu plane crash, da shi da wasu manya-manyan ƙusoshi a Nijeriya, wanda galibin su tare suke harƙallar smoke duk suka mutu.

 

Duk mutuwa mutuwa ce, takawa yana jimamin rashin ɗan uwan mahaifinsa, gefe guda kuma yana farincikin hukuncin lokaci ɗaya, da Ubangiji Allah ya haɗa azzalumai yayi musu.

 

Ahalin masarautar kuwa suka shiga taradaddi da damuwar gagarumin rashin da aka yi, turaki ne ya yi clearing komai, ya taho da gawar Kano.

Ga matarsa na can kwance a asibiti, ɗan sa kuma aka kawo shi cikin sarƙa, sai a lokacin mutane hankalin su ya koma kan cewa matar galadima ba su suka yi jinyarsa ba, baro shi suka yi a can, aka din ga Allah wadai da ita.

 

Kwanaki uku da rasuwar galadima, ba a ga Mummy ba, mutane suna ta tambayar Ammi, wai ba su ga Mummy ba.

 

Kwana na huɗu mahmud ya je ya samu ammi, ya roƙeta dan Allah ta kira takawa da rumaisa da iman, su haɗu a sashin Mummy.

 

Ammi ta ce masa ba damuwa, dan kuwa yanzu ba ta ƙaunar duk wani abu da zai sanya mahmud ɗin damuwa.

 

Hankalinsu ba ƙaramin tashi yayi ba, da suka ga Mummy, gaba ɗaya jikinta a ƙone, sai ihu take tana kiran sunan rumaisa, ruma kawai ta fashe da kuka ta rirriƙe takawa saboda tsoron da Mummy ta bata.

 

Wambai ya kalli Mummy ya ce “Jamila, ya aka yi ki ka ƙone haka?”.

 

Cikin matsananciyar damuwa da tashin hankali, ta din ga faɗar miyagun abubuwan da ta aikata ita da Hajiya Lubabatu, babu wanda yafi ɗaga musu hankali, irin yadda ta kai Adam wurin boka a ka zuƙi jininsa, kuma duk shekara irin bala’in da yake shiga saboda asirin da tayi masa.

 

Kasancewar sa da runaisa ne, ya sauƙaƙa masa wasu abubuwan, kuma a wannan karon ma, aljanar ce ta zo shan jini da take duk shekara, ta kasa ta sanya ruma naƙudar dole ta kashe ɗan, still ta cigaba da bin adam ta sha jinin da ta saba, saboda ba zata iya cigaba da aikin da aka bata ba, sai da jininsa, shi ne take ta dambe da rumaisa, ta fito a suffar mage, rumaisa ta jefata a murhu. Shi ne ta shiga jikin Mummy, ta ce sai dai tayi jinyar a jikinta, idan mutuwa ce su mutu tare tun da tsayin shekaru ita take yi wa aiki.

Wannan matar da rumaisa take gani, da hayaƙin da idonsa ke yi, aljanar take gani. LA ILA HA ILLA ANTA SUBHANAKA INNI KUNTU MINA ZALIMIN, da rumaisa ta riƙa, tun da lokacin da ta san falalarta, take ganin fa’idarta a rayuwar ta.

 

Wambai ya ce “Anya ba surutan ciwo ne ya sanya take maganganun nan ba”.

 

Mahmud ya girgiza kai ya ce “Ba zafin ciwo bane, muna bibiyar duk wayar da Mummy take yi, kuma tun asali na san wasu abubuwan, ba abun da zan iya yi a kai ne”

 

Kuka ammi take kamar ta fita a hayyacinta ta ce “Jamila me nayi miki haka a rayuwa ne? Haba Jamila shikenan bawa ba zai ɗau ƙaddara ba, duk saboda marigayi ya fara aure na?”

 

Mahmud ya zube a gaban Ammi ya ce “Ammi, dan girman Allah ki yafewa Mummy, na sam ta cutar da mu, amma ta riƙe ni kamar ita ta haifeni, dan Allah ki yafe mata”

 

Ruma ta ce “Wallahi ba zata yafe ba, nima ban yafe ba, dukkanin mu bamu yafe mata ba, dare na din ga bi, ina kai ƙarar ku wurin Allah, sunayenku na din ga gaya wa Allah, kuma yayi mana maganinku, yau na cika alƙawarin da na ɗauka”.

 

Su Fauziyya sai kuka suke yi, wambai ya ce “Jamila baku yi wa kanku adalci ba, ki ka saka na din ga ganin baiken Binta, ina goyon bayanki, kanki ki ka yi wa. Binta ki ɗauki yaranki ki tafi da su, Allah ya haɗa miki kansu, mun yi magana da mai martaba da ƴan majalisar sarki ma, Adam ne zai gaji kujerar galadima.

Binta ki yafe mini abubuwan da suka din ga faruwa, ke kuma wannan yarinya rumaisa Allah ya ƙara haskaka rayuwarki, kin kawo sauye-sauye da tarin alkhairi a wannan gida”.

 

Ammi ta rungume Mahmud tana rarrashinsa, sosai yake kuka yana Ammi ta yafe musu baki ɗaya.

 

Su Fauziyya sai kuka suke yi, ruƙayya na gefe ba ta iya magana, dan tun da Mummy ta fara rashin lafiya abun ya shafeta, take abu kamar taɓaɓɓiya.

 

Kwanaki uku aka yi bikin naɗin sarautar takawa zuwa galadima, shi kuma ya yi wa rumaisa sarautar garkuwar galadiman kano.

 

Kwananta arba’in da haihuwa, ya biya musu umara, shi da ita da ammi da mama, suka tafi domin nuna Godiyar su ga Allah.

 

Kamar yadda mai sunan baba yayi alƙawari, Iman ta je ta ga danginta, mutane masu karamci da tarin dukiya.

 

Kamar yadda ammi ta yi alƙawari, sabir na isa shiga makaranta, ta basu ɗan su, lokacin ruma ta kammala secondary school, sai dai da laulayin wani cikin ta shiga makaranta, take karantar criminology. Kamar yadda suka yanke shawarar hakan ita da takawa.

 

Cike da tausayawa mai sunan baba yake kallon iman, ta shirya ranar graduation ɗin su, cikin ta kamar yayi magana saboda girma, scaninc ya nuna tagwaye ne a cikinta.

 

Mai sunan baba in dai yazo baya bari ta yi aikin komai, manyan mutane sun halarci bikin kammala karatun su iman.

 

Hajiya Lubabatu brain cancer ta samu, kanta ya din ga ɗurar ruwa, aka fita da ita ƙasashen ƙetare, sai dai duk da an saki Jabir, bai iya zuwa yayi jinyarta ba, sai ƴan uwanta.

 

Mahmud ya koma aiki, idan ya zo kuwa, kullum sai ya je duba Mummy, sai dai abun nata babu cigaba, kullum ciwo ƙara jagwalewa yake yi, an kai ta asibiti dressing ake yi, amma ƙuna sake jagwalgwalewa take yi, tana wani irin wari.

 

Turaki ya tattara iyalin sa yayi watsi da su, duk wani abu na kyautatawa tsakanin su, ya daina yi musu, Jamil aka din ga iƙrarin ya mutu a hannun DSS saboda babu wanda ya san a in da yake.

 

Mai sunan baba kan Iman ta haihu, ya canza musu gida, gida mai kyau sosai da sosai, daga Lagos yake sayo kaya yana aiko wa da Usman da Aliyu kayan takalma, computer da yadiddika da lesuna da ga Aba yana aiko musu da shi, iman da ruma da nusaiba suka haɗa kuɗi, suke tura masa suma suna karɓar takalma da laces.

 

Yaya Abubakar da yayi aure, jigawa ya koma, saboda a can yayi karatu ya saba da mutane, kuma cikin ikon Allah ya samu aiki a can.

 

Alhaji Aminu ya din ga jan mai sunan baba a jiki, yana koya masa yadda ake importing kaya daga ƙasashen ƙetare, mai sunan baba ya ce a koyawa su Aliyu, sune suka fi ga harkar kasuwanci, kar son rai ya shiga lamarin tun da yana aiki da hukumar hana fasa ƙwauri.

 

Tagwayen mata aka yi wa Iman aka ciro mata, masha Allah kyawawa tamka su suka yi kansu, lokacin mimi ma ta yi nauyi sosai, aka sha shagalin suna, an yi wadaƙa da shanu da nono a haihuwar nan, mai sunan baba ya sanya sunan Ammi da mama.

 

Abdallah ma a DSS ya samu aiki, yana abuja tare da Bashir, cikin ikon Allah babu wanda Allah bai ɗaukaka a ƴaƴan mama ba, kuma galibi duk a sanadin rumaisa ne.

 

Kasuwanci ya buɗewa su Yaya Aliyu, suka tattaga aure, mama ta ce duk su yi Allah ya taimaka.

 

Mahmud ma yayi aure, Yasir kuwa sai ƙarshen shekara yake samu yazo ya koma, zaman canada ya yi masa daɗi yana ta karatunsa, ga wata irin shaƙuwa tsakaninsa da ƴar anty laila.

Mijin anty laila yana ta jaddada mata, shifa idan Yasir ya kammala karatun sa, a nan zai samu aiki su cigaba da zamansu, sannan kuma da ya kammala karatun ya bashi anam.

 

Ƴan mazan mama, gidaje uku suka saya, a jikin nasu, suka faɗaɗawa mama shi, dan cewa tayi dan Allah yayi musu arziki ba zata bar unguwar nan ba, tana fatan suma su ci albarkacin ruma da ƴan uwanta.

 

Hakan ya sa suka gyara layin, aka yi masa kwalta da kwalbati, aka sassaka sola, wannan ya shiga da abun alkhairinsa wannan ya fita.

 

Mummy ta koma tamkar mushe da rai, saboda wari, kuma tana ji tana gani, gida ya koma hannun ammi, ta malleke komai da take ta ƙoƙarin hana faruwar hakan.

Ba tare da ƙyashi ba, ammi ta din ga nemawa ruƙayya magani, ta ce in dai tana raye ba zata bari ɗan marigayi galadima ya wulakanta ba.

 

Adam ya sauyawa ruma gida, manyan motocin take ja, da ƙananun shekarunta sai ta birgeka, saboda har a lokacin ba ta haɗa shekara ashirin ba, ta saka ya ɗaukko mata ɗan mai unguwa mai hanata shiga lambu sata, yake kai Sabir makaranta ana biyansa kuɗi mai yawa.

 

Adam ya ɗauke mata komai, dan haka kuɗin kasuwancin ta a sama suke, sai dai tayi ta kyauta kasancewar ta mai kyauta ce.

Ba ƙaramin girmama rumaisa suke yi ba, saboda rawar ganin da taka a rayuwar Adam, dan shi kansa duk wani abu da zai taɓa mutuncinta, ko tayar mata da hankali fito na fito yake da shi.

 

Ƴan unguwarsu ruma har murna suke su ga danƙareriyar mota a ƙofar gida, sun san akwai kaɓakin alkhairi ranar.

 

Hajiya Lubabatu ce ta fara mutuwa, ba tayi arba’in ma Mummy ta bita, ammi ta ji mutuwar nan ba kaɗan ba, hakan ya sa ta ce duk ta yafe musu, kuma ta rungumi Fauziyya da ruƙayya ta cigaba da riƙo, baba uwani a can garin su mahaifinta aka ganota, Cancer ya kama mata ƙafafuwa ita ma, babu kuɗin da za ayi mata aiki, ammi ba ta yi shawara da wani ba ma, ta tura sidi aka biya kuɗi, aka cire mata ƙafafuwan ta saya mata keken guragu tare da bata jarin sana’a.

 

Rumaisa kafin ta gama makaranta sai da ta haifi ƴan maza biyu, ta din ga Addu’a “Allah kar ka sa na yi irin ta mama na haifi ƙanwar maza, ba zan iya ba” takawa ya din ga yi mata dariya ya ce ashe kina sane ki ke tsiyata ku.

 

Idan ta tuna wasu rashin hankalin da tayi a baya, ta ji kamar ta yi wa kanta duka, babban abun da ya bata mamaki, bai wuce duk shekarun nan takawa yana ajiye da wasiƙar da ta rubuta masa, na cewar ya taɓa mata nono, yayi ta tsokanarta yana dariya.

 

Samha kuwa rayuwa ta juya mata baya, dan abun da Jamil ya aikata, da wanda tayi ita ma, ya zame mata baƙin fenti, aka rasa mai aurenta, duk gayu da ƙwalisar samarin duk suka watse.

 

Runaisa ba ta bar harkarta ta zane-zane ba, dan har rubuce-rubuce take yi, kamar wasa ta zama popular manyan mutane suke sayen zane-zanenta.

 

Cikin ikon Allah rumaisa ta zama criminal lawyer, sunanta ya shahara sosai, ga ta lawyer, ƙwararriya wurin zane-zane da rubuce-rubuce, kuma ƴar kasuwa.

A duk lokacin da aka yi hira da ita, ta kan ja hankalin mutane a kan cewa a duk lokacin da aka samu ɗa mara ji kamarta a cikin al’umma, kar a tsangwame shi, a ja shi a jiki a duba wace irin baiwa Allah ya yi masa a dafa masa a kanta, saboda Allah baya halittar abun da ba shi da amfani. Kamar dai ita da tun a tasowarta ko makaranta ba ta so saboda rashin jin ta, amma cikin ikon Allah a yanzu, ilimi na addini da na zamani sai dai ta koyar da wani bisa jagoranci da jajircewar mahaifiyarta yayyenta da kuma mijinta ta zama abun da ta zama a yanzu.

 

 

 

 

TAMMAT BI HAMDILLAH!!!

 

 

GODIYA TA TABBATA GA UBANGIJIN TAIKAI MAI KOWA MAI KOMAI, DA YA BANI IKON FARA RUBUTUN NAN YA BANI ARON RAI DA LAFIYA NA KAMMALA SHI. ALLAH YA SANYA A AMFANA DA DARUSSAN DA KE CIKI, AKASIN HAKA KUMA ALLAH YA YAFE MANA.

 

SAƘON GAISUWA TA MUSSAMAN, UWAR KIRKI UWAR ALJANNA UWA TA TA KAINA, MALAMA NAFISU ADAMU, DA MUKA FARA TARE HAR NA KALLAMA ALKHAIRIN ALLAH YA KAI MIKI HAR GADON BACCINKI.

 

 

GODIYA TA MUSAMMAN GA ƳAN UWANA.

ZEE KUMURYA NIMCY LUV, TARE DA SAURAN MARUBUTA MAIMOON, MARYAM MAI ƘOSAI ANTY ZEETY, KUNA DA YAWA GASKIYA DUK INA JI DA KU DAI.

 

BAN MANTA DA KU BA, MUTANEN DA SUKA BANI TALLACE TALLACENKU

MAMAN MEENAT COLLECTION

MAMAN KHADIJAH MAI SABAYAR ƳAN GAYU TARE DA MAMAN ILHAM KUN GA DAI YADDA SUKA KANKARO RUMA A GIDAN AURENTA, KAR A GAJI DA CIGABA DA PATRONIZING KAYANSU, TESTED AND TRUSTED RUMA TA YI AMFANI DA SU KUN GANI.

 

WAƊANDA SUKA YI SUPPORTING ƊINA, WURIN SAYEN LITTAFINA, ƳAN NORMAL GROUP, SPECIAL DA AKE TURAWA TA PC, ƳAN AREWABOOKS DUK INA GODIYA, DA SUPPORTING ƊINA ALLAH YA ƘARO MUKU ARZIKI DA BUƊI MARA YANKEWA.

 

WAƊANDA SUKA DIN GA FITAR MINI TARE DA KARANTAWA, BA TARE DA KUN SAYA BA, DA WANDA SUKA YI MINI AMFANI DA SHI WATA SIGAR BA TARE DA IZININA BA, INA YI MUKU TUNI DA ALLAH BAYA YAFE HAKKIN WANI A KAN WANI, IDAN KUN SHIRYA BIYANA HAKKINA.

0009450228

AISHA ADAM JAIZ BANK.

 

 

DOMIN GYARA SHARHI, KO SHAWARA ƘOFATA A BUƊE TAKE.

SAI MUN SAKE HAƊUWA A GABA.

AYSHERCOOL

08081012143.


Proceed with your download by clicking the below button

 

Be With Us

 

DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.

Back to top button