Uncategorized

Abban Sojoji Page 54 Book 2 Complete Novel

“`The father Of Soldiers“`

 

Story &  Written 

       By 

 Hafsat Bature

  _💋Boss Bature💋_

_Zuwa ga masu karkasamun littafin duk wanda ya ƙara haɗamun document,ban yafe ba!babu yarda za’ae ni ina cikin rubuta littafi na biyu,wasu kuma sun haɗamun document na book 3 don iyayi da kuma ƙarfin hali,sai ja mun surutu sukeyi nacewa naja littafi har book 3 duk da idan naga dama har book 5 ma sai inyi bani naji zan iya ba😒😏🙄😒, wasu har gardama sukeyi mun nacewa book 3 suke so complt,bayan ni iya book 2 nake cikin rubutawa ma_

🤍❤💖

Kiran na shiga drivern ya ɗaga,cikin sauri ta kara wayar a kunnanta tare da yi mashi sallama tace”kayi haƙuri bawan Allah,ban fahimci zancen ka bane,dan Allah ka ƙara yi mun bayani yarda zan gane,”

   drivern yace”ƙanwarki ce Amal na kawota Abuja,yanzu haka ita kaɗai ta rage acikin tashar nan,kiyi hanzari kizo ki ɗauke ta saboda dare yana yi kuma ni yanzu nakeson na juya,”

  Cikin sauri tace”ka turomin da address ɗin wurin gani nan zuwa,”

     Amsa mata yayi da toh,sannan ya kashe kiran,ba da jimawa ba sai ga message ya shigo wayarta na address ɗin inda suke,

  Da sauri Amani ta ƙarasa wurin wardrobe ɗinta tare da buɗewa ta ɗauko mayafi tayi rolling ɗinshi akanta,sannan ta dawo ta dauki purse ɗinta dake ajiye asaman bedside drawer ɗinta,

        gaba ɗaya duk tabi ta dabarbarce ko escort bata nema ba, da kanta ta shige motarta,ta fisgeta da gudun gaske ta fice daga cikin gidan,driving take tana ta faman sambatu”Ya Allah ka tabbatar mun da abunda nake tunani,Allah yasa Amal ce ƙanwata,Ya Allah kasa itace,wayyo Allah da naji daɗi,

      ji take kamar motar bata sauri,tamkar tayi fiffike ta tashi sama don ta ƙarasa da wuri,

tun bayan da Drivern ya turama Amani adireshin wurin inda suke shiru bata ƙaraso ba,gashi dare sai ƙarayi yake,kuma babu wani passenger daya rage acikin station ɗin sai ita kaɗai kwallin kwal,sai kuma wasu daga cikin mazauna station ɗin,tana zaune acikin motar baiwar Allah ba ƙaramin galabaita tayi ba,ga gajiyar tafiya ga kuma ciwo da take fama dashi,don har yanzu zazza6in nan bai bar jikinta ba,ganin cewa zasu 6ata mashi lokaci gashi yana da wani uzuri mai mahimmancin da yake so yaje yayi,hakan yasa yace ma Amal ta fito daga cikin motar,daƙyar ta iya miƙewa tare da saukowa daga cikin motar ta fito waje tare da tsayawa tana jiran jin me zaice,

Ruƙo hannunta direban yayi sannan yajata izuwa wurin wani benci yace ta zauna anan ta jira ƴar uwarta tazo,kada taje ko’ina,shi zai wuce don yana da uzuri,

  Hankalin Amal ba ƙaramin tashi yayi ba ganin direban zai tafi yabarta acikin station ɗin gashi babu wata ƴa mace aciki sai ita kaɗae,

  Shi kanshi baiso hakan ba,saboda amanace aka bashi,amma ba yarda zaiyi,ya zamar mashi dole ya juya ya koma da motar,

   tana ji tana gani direban nan ya shige motarshi tare da janta yabar cikin tashar da ita,

  Lokaci guda wani irin sanyi ya lullu6eta,nan da nan jikinta ya shiga rawar ɗari,hatta haƙoranta sai faman kakarwa suke yi suna fidda sauti kaf kaf suna game wa da juna,ƙanƙame jikinta tayi tana ta faman ambaton sunan Allah abakinta,

  Tana cikin wannan yanayin tajiyo takun tafiyar mutane daga gefen hagunta,cikin sauri ta juya don taga su wanene,gabanta ne yayi wani irin faɗuwa ganin wasu giggan tantirai su uku suna tunkaro wurin da take,sai faman nunata sukeyi da hannu da alama ma abuge suke,sun sha takai masu karo suna tafiya suna tangal tangal kamar zasu faɗi,

   ganin hakan yasa Amal ta miƙe cikin sauri ta soma tafiya tana waiwayonsu,muryar wani daga cikinsu ne tajiyo yana cewa”kai karfa ta kufce mana,naga kamar tana so ta tsere mana,” haba ina ae Amal na jin wannan maganar ta manta da yanayin da take ciki,takai hannu tare da tattare rigar jikinta ta watsa aguje kamar zata tashi sama,suma ganin ta fara gudu yasa suka bi ta aguje don su taddota,

   Gaba ɗaya duk tabi ta rikice tana gudu tana waiwayonsu hakan yasa ta hau saman titi batare da saninta ba,kafin tayi wani aune tuni wata mota tayi awon gaba da ita,wata irin razananniyar ƙara Amal ta saki yayin da ta baje asaman titin idonta na kallan sama,jini na zuba ta saman goshinta da kuma hancinta,da la66anta duka sun raunata,

   Waro ido waje tantiran nan sukayi ganin abunda ya faru,aikuwa a gaggauce suka zura da gudu don kar ace sune suka kashe ta,

    Hankali tashe suka tsayar da motar,sannan atare suka fito daga cikinta da hanzari suka tunkari wurin da yarinyar take kwance,gaba ɗayansu suna sanye da kakin sojoji ajikinsu,

    Zuƙunnawa daya daga cikinsu yayi yana kallon fuskar yarinyar dake ta faman faɗin”innalillahi wa’inna ilaihirraji’un,”

   “bata mutu ba,har yanzu tana numfashi amma tana bleeding ya kamata muyi saurin kaita asibiti,”

   Na zuƙunnan ne yayi magana,sannan batare da 6ata lokaci ba,yasa hannunshi tare da sungumarta asaman kafaɗarshi cikin sauri suka wuce da ita cikin motarsu,a back seat ɗin motar ya zaunar da ita,sannan shima ya shiga daga gefenta ya zauna tare da ruƙota jikinshi,

  Shi kuma ɗayan ya shiga gaban motar tare da yi mata key,yaja ta aguje suka juya domin zuwa kai yarinyar asibiti,

   Adai dai lokacin da Motar tasu take ƙoƙarin shiga shantalelen titin dake a left hand dinsu,Motar Amani ta kunno kai ta titin dake a right-hand ɗinsu, a wani slow Amani ta zuge glass ɗin motarta tana bin tasu motar da kallo saboda kukan mutum da tajiyo acikin motar ba ƙaramin ɗaga mata hankali yayi ba,aranta tana cewa”Allah yasa dae ba wani mummunan abunne ke faruwa acikin motarcan ba,”

  Tana ƙarasa maganar taja motarta da gudun gaske ta ƙarasa cikin tashar motocin,wuri ta samu tare da yin parking ɗin motar,cikin sauri ta fito tana faman gyara mayafin dake ajikinta,hannu tasa tare da ciro wayarta dake acikin purse ɗinta,sannan ta dannawa direban kira,cikin rashin sa’a aka sanar da ita cewa numbar da take kira a kashe take,

   hankalinta ba ƙaramin tashi yayi ba,

  A ruɗe ta soma cewa”kodai ƙarya mutumin nan yayi mani ne?amma meyasa zai kirani a waya ya sanar dani cewa ƙanwata Amal ya kawo Abuja,kuma sannan yanzu na kira wayar shi a switch off,Ya ilahi amma dae bai kyautamun ba wlh,”

   tana cikin wannan zancen zucin sai ga waɗannan tantiran guda uku da suka biyo Amal,ganin su yasa Amani tayi tunanin ko ta tambayesu may be a dace,

  da hanzari ta tunkare su tare da yi masu sallama,

   a firgice ɗaya daga cikinsu ya shiga cewa”wlh ba mu muka kashe ta ba,kawai mun ganta ne acikin tashar nan zaune ita kaɗae,shine muka biyota don mu tambayeta ina iyayenta suke ne….”tun kafin yakai ƙarshen maganar tashi wani daga cikinsu ya buge mashi baki tare da cewa”Ƙarya Haramun!Aunty bari na faɗi maki gaskiyar lamari,mu ɗinnan da kika ganmu 6arayi ne masu yankar aljihu,mun biyota ne domin mu kwamushe ƴan kuɗaɗen dake hannunta tana ganin mu sai ta watsa aguje,tana ta faman gudu kamar zata tashi sama kawai sai ga wata mota tayi Wuff ta ɗauke ta sama……..’

  gaba daya basu acikin hayyacinsu da alama giyar ce takai masu karo,sai faman kora mata bayanin abunda bata tambayesu ba suke,

  Murya na rawa Amani tace”dan…Allahh ban gane akan me kuke magana ba?wacece kuma kuka bi aguje har mota ta buge ta?wace yarinya ce,!kuyi mun bayani,ni ina neman ƙanwata ne Amal,ɗazu wani driver ya kirani a waya ya sanar dani cewa ya kawota inzo in ɗauke ta kuma shine ma yaban addreshin wurin nan,”

  Har haɗa baki suke yi wurin cewa”ae itace yarinyar da muke yi maki magana akai Aunty,ae yanzu haka ma yarinyar tana acikin motar waɗanda suka banketa,yanzun nan suka bar wurin nan da ita,

  Tun kafin ya ƙarasa maganar Amani ta juya da saurin gaske ta nufi motarta saboda tunawa da tayi da Motar da tagani ta gifta ɗazu da kukan yarinya acikinta,

  buɗe motar tayi tare da shigewa ciki taja ta da gudun gaske,tana jiyo muryar waɗannan matasan suna cewa”Aunty Allah tsare hanya,”

   

    ***************************

SEHRISH

Sam ta hana idanunta bacci saboda jiran dawowar babban yaya,yau harya haura lokacin daya saba dawowa hakan ba ƙaramar damuwa ya jefata ba,harta sauya kayan jikinta izuwa na bacci riga da wando masu laushin gaske orange colour,tun wuraren ƙarfe sha biyu daidai takai mashi fruit a ɗakinshi,Coffee ne kawai bata kai mashi ba saboda tasan cewa bazai shaba idan ya salafce,don ta lura cewa yafi buƙatar shi da zafi zafinshi,don wani sa’en har yana tururi yake shan shi,

   sai faman safa da marwa takeyi acikin ɗakin har sai da ƙafafunta suka soma yi mata raɗaɗi sannan ta koma tare da samun wuri gefen gadonta ta zauna,lokaci guda kuma ta soma sakin hammar bacci,duk yarda sehrish taso ta hana kanta bacci amma abun yaci tura,sai gata kwance abaje tana ta faman sharar bacci asaman gadonta, 

  da yake ta sama ranta abun sai gashi ta farka wuraren ƙarfe daya na dare,daƙyar ta iya mikewa tsaye tana kallon clock ganin ɗaya ta buga yasa taji gabanta ya faɗi rasss,tsoranta kar ace ya dawo tana cikin sharar baccin nan,

  Cikin sauri ta taka izuwa wurin window ɗinta,hannu tasa tare da janye curtains din sannan ta zuge glass ɗin tana hangen wajen harabar ajiye motocinsu,anan ta hangi motarshi ajiye alamar ya dawo kenan,

    dafe saitin zuciyarta tayi gabanta na faduwa a fili tace”Nashiga uku ashe ya dawo,yanzu ya zanyi kenan nasan ranshi zai iya 6aci akan ban kai mashi coffee ɗin ba,”

  cike da takaici taja guntun tsoki tare da cewa”duk wannan baccin ne daya ɗauke ni,da hakan bata faru ba,yanzu ya zanyi kenan gashi dare ma yayi sosai,in naƙi kai mashi matsala, in nakai mashi ma hakan zai iya jamin wani abun kuma,”

  taƙarasa maganar tare da yanke shawarar takai mashi kawai,hannu takai tare da daukar mayafinta,ta rufe kanta dashi,sannan ta zura silifa aƙafarta,a hankali ta buɗe ƙopar ɗakin kamar mara gaskiya haka ta dinga tafiya har ta isa kitchen,shiga ciki tayi tare da wuce wa kai tsaye wurin cupboard,hannu tasa tare da curo cup ɗin data ware mashi nashan coffee ɗinshi,batare da 6ata lokaci ba ta zuba mashi coffee ɗin da zafin shi aciki cup,asaman plate ta aza mashi kofin sannan ta nufi hanyar fita,tana ƙoƙarin fita daga cikin kitchen ɗin sai ga Hayaam ta faɗo ciki,ba ƙaramin tsorata Sehrish tayi ba don har saida takusa zubar da coffeen dake hannunta,ido azare take kallonta don bata tsammaci mutum ba adai dai irin wannan lokacin,

  tun da tazo gidan take ƙumshe aɗakinta tana baccin lalaci,koda ta farka bata fito waje ba,sai yanzu Allah yayi ta samu ta fito,short gown ɗin nan ce ta ɗazu ajikinta,kan nan nata ko arziƙin dankwali babu balle mayafi,sai dai gashin kanta data ɗaure abayanta,

   Murya a sanyaye sehrish tace”Sannu da fitowa,ya gajiyar tafiya,”

  Ƙayataccen murmushi hayaam ta saki tare da cewa”yawwa ƴan mata,gajiya tabi jiki yanzu ina jina normal,”

  Ta ƙarasa maganar tare da kallon cup din dake ruke a hannun sehrish tace”Wannan fa?ke zaki sha ne”?

  girgiza kai sehrish tayi tace”a’a banawa bane,babban yaya zan kaimawa ne,”

  yamutsa fuska amani tayi tare da cewa”Oh ashe ya dawo cikin gidan kenan,”

  Sehrish tace”eh,ya dawo,”

“ra’ayin kanki ne kai mashi coffeen ko kuma shi ya buƙata ne”?ta kuma jifarta da tambaya,

    “Ai shi ba’a yi masa katsalandan,shi yace na rinƙa kai mashi a kullum wuraren ƙarfe sha biyu idan sun dawo daga aiki,” ta bata amsa tare da kama hanya zata wuce,

  Cikin sauri hayaam ta sake shan gabanta tare da cewa”gaskiya bai kamata ace ƙaramar yarinya kamarki tana kai mashi abunsha adai dai irin wannan lokacin ba,sam wannan tsarin baiyi ba,yakamata ace yanzu kina kwance kina bacci ko don saboda zuwa school yana da kyau ki rinƙa yin bacci da wuri,” 

..murmushin yaƙe sehrish tayi sannan tace”nagode da shawararki,amma wannan aikina ne kula dashi,kuma nasaba da yin hakan”

   ganin hayaam zata 6ata mata lokaci yasa tayi saurin wuce wa batare da ta saurari sauran abunda zata ce mata ba,

  jinjina kai hayaam tayi tare da cewa”yarinya dani kike magana,wato har wani faɗamun take itace mai kula dashi,shisshigi kawai da kutsi,” ta faɗi hakan tare da jan dogon tsoki ta wuce bedroom ɗinta,

   lokacin data ƙarasa part ɗinshi baya acikin falon hakan yasa kai tsaye ta wuce bedroom ɗinshi,sallama tayi mashi amma shiru ba’a amsa mata ba,almost 4 times tana zabga mashi sallama amma tsit babu alamar za’a amsa mata,

  saurarawa tayi don taji ko zata ji motsin shi aciki,nan ma shiru ranta ne ya bata cewa kawai tashiga cikin bedroom ɗin nashi,

   ƙafa tasa tare da shigewa ciki,nan take ƙamshin turaren nan nashi ya daki hancinta har saida ta ɗan ja da baya saboda yarda ƙamshin ya shigeta kai tsaye,sauke ajiyar zuciya tayi tare da ware idanunta tana bin bedroom ɗin nashi da kallo,wayamm tagani babu shi acikin ɗakin,tsayawa tayi tana tunanin ko’ina ya shiga ne,kodai bai dawo bane?amma kuma ae ga motarsu can awaje alamar sun dawo,har ta yanke shawarar barin ɗakin,zata juya kenan eyes ɗinta suka sauka akan fruits ɗin da takai mashi,wanda ta ajiye mashi asaman table din dake kusa da gadonshi,a rufe takai mashi kayan marmarin amma sai taga an cire plate din data rufe su dashi,alamar ya fara shan fruits ɗin kuma ya dakata,ranta ne ya bata cewa may be yana acikin toilet ne,

   murmushi ta ɗanyi sannan ta ƙarasa wurin table ɗin tare da ajiye mashi cup of coffee din  agefen kayan marmarin,

  tsayawa tayi tana tunanin ko dae ta tsaya ya fito daga cikin toilet ɗin wata’ƙil zai buƙaci wani abun bayan wannan,wata zuciyar kuma ta bata shawarar cewa ta tafi kawai tabar dakin saboda dare yayi sosai,

   tana cikin wannan tunanin,sgr ya fito daga cikin toilet,waist ɗinshi na ɗaure da short towel wanda bai kai guiwar ƙafafunshi ba da alama wanka yayi aciki,

sam bai lura da mutum a cikin bedroom ɗin nashi ba,gadan gadan ya tunkari wurin dressing mirror ɗinshi,cikin rashin sani tafin ƙafarshi ya hau saman 6awon ayabar daya ci ɗazu,ya maƙale masa a jikin shirt ɗinsa saida zai shiga wanka ne ya lura dashi yasa hannu  ya ka6e shi ya faɗi anan ƙasa,aikuwa nan take wani irin mugun sul6i ya kwashe shi bazato ba tsammani gaba ɗaya ya tafi a burkice zai faɗi,a firgice sehrish ta juya tare da yin ƙoƙarin taimaka mashi cikin sauri ta ruƙo shi nan take ƙarfin shi ya rinjayi nata gaba daya suka faɗa saman shimfiɗeɗen gadonshi a manne da juna,tashin hankali da ba’a sama shi date,

  wata irin nauyayyiyar azuciyar zuciya Sgr yashiga saukewa,tabbas ya ɗan firgita saboda bai tsammaci hakan ba,bai ta6a yin irin wannan gangancin ba,hada ƙarin sam ya manta da  6awon ayabar a wurin bai jefa shi dustbin ba,da ace sehrish bata ruƙo shi ba awannan lokacin da ba ƙaramin buguwa zaiyi ba yanda yake dogon nan,

   atare zuciyoyinsu suka shiga bugawa da ƙarfi da ƙarfi,gaba ɗaya sehrish ta gama tsorata abun tamkar a amafarki take ganin shi,ta gaza yarda cewa itace tare da Surgeon general Rafayet kwance asaman gado ɗaya kuma amanne da juna,

   gaba ɗaya jikinshi ya rufe nata hatta face ɗinta tana a saitin wide chest ɗinshi,tana jin yarda yake ta faman sauke ajiyar zuciya,da kuma yarda heart ɗinshi ke beating very fast,

   tsit kake ji daga ita harshi an rasa mai wani kwakkwaran motsi,danshin ruwan dake ajikinshi ba ƙaramin sanyaya mata jikinta yayi ba,daƙyar take iya breathing saboda hancinta daya manne da fatar ƙirjinsa,haka la66anta ma suna manne da fatarshi,

  Boss man ɗin fa ya gaza ɗago da jikinshi daga nata,ba don komai ba sai don yarda abun yazo mashi unexpected,ba ƙaramin jinjinawa lamarin yayi ba shi kanshi,

   Jin yarda yarinyar keta kokawa wurin fitar da numfashinta,yasa ya daure tare da yunkurawa zai tashi daga jikinta,baiyi wani aune ba towel din dake ɗaure a qugunshi ya shiga warwarewa gaba daya dama daurin ya saki,

  Shi kanshi baisan lokacin daya mayar da jikinshi asaman nata ba ya kwantar da kanshi a saman left shoulder dinta,bakomai ne yasa yayi hakan ba face gudun kar towel din jikinshi ya saki agabanta,don muddin hakan ta faru tofa wannan karon ba sume mashi zatayi ba,zuciyarta ce zata buga tabar duniyar saboda tsabar firgici don ya lura yarinyar ba ƙaramar matsoraciya ba ce,

    wani irin yanayi mara misaltuwa taji atattare da ita,jikinta yayi wani irin sanyi sanyi kasala kasala haka,sam bata jin nauyin jikinshi akan nata sai ma yanayin da hakan ya jefa ta,

    idanunta na’a rufe sam tagaza buɗesu ba don komai ba sai don tsoran abunda zai biyo baya,a matuƙar tsorace take hakan yasa ko kwakkwaran motsi tagaza yi,lumshe idanunshi yayi yayin da hancinshi ke gogar fatar wuyanta,fragrance ɗin turarenta ne yake kaimashi ziyara acikin hancinshi,ƙamshin ba ƙaramin daɗi yayi mashi ba,har lokacin tana jin yarda numfashinshi ke fita afatar jikinta,

  almost 15mins suna cikin wannan yanayin,tajiyo hannunshi a hankali ya zura shi adai dai saitin waist ɗinshi don ya gyara ɗaurin towel dinshi,wannan moving ɗin da ya runka yi da hannunshi awurin yana gogar jikinta ba ƙaramin kashe mata jiki yayi ba,amace ta mace gaba ɗaya tashiga wani irin yanayi na daban….,

   sai da ya samu ya ɗaure towel ɗin sannan a ƙaro na biyu ya ɗago da kanshi don ya raba jikinshi daga nata,nan take sehrish ta saki wata irin razananniyar ƙara gaba ɗaya ta gigita shi,ashe raɗaɗin Earring ɗinta ne daya sargafo gashin kanshi ya harɗe acikin ɗan kunnan,wannan ɗagawar da zaiyi ajikinta shine sumar kanshi taja ɗan kunnan nata da ƙarfi wannan ne dalilin dayasa ta fasa ƙara,cikin sauri Sgr ya mayar da kanshi tare da kwantar dashi agafen fuskarta,fashewa da kuka sehrish tayi sosai saboda ba ƙaramin zafi taji ba,don wurin harya fara fidda ɗigon jini,a hankali ya buɗe blue eyes ɗinshi tare da bin kunnan nata da kallo yarda sumar kan nashi ta harɗe acikin earring ɗin shine yafi komai bashi mamaki,tunani ya soma yi taya za’ai ya cire gashin nashi acikin ɗan kunnan nata?dole akwai buƙatar yabi a hankali wurin zagayo da hannun na dama don ya cire shi,

   A hankali ya ɗago da fuskarshi daga gefen fuskarta,ya kasance cewa suna facing ɗin juna sosai,hatta numfashinsu yana haɗewa dana juna,wannan shessheƙar kukan da takeyi ne yaja hankalinshi wurin kallon fuskarta,la66anta har kerma sukeyi yayin da idanunta ke arufe,

  Muryar shi ce ta katseta da cewa”I don’t wanna hear that sound again,”

  Cikin sauri sehrish ta tsagaita dayin kukan gaba daya,ta koma tana faman sauke ajiyar zuciya,

  buɗe idanunta tashiga yi waɗanda ke cike tab da ruwan hawaye,tun kafin ta ƙarasa ware idanun nata take hangen hasken blue ɗin kwayar idanun shi,a hankali ta ƙarasa buɗe idanun sosai akan kyakkyawar fuskarshi dake fuskantar tata,duk da irin bugun zuciyar da take ji amma hakan baisa ta mayar da idanunta ba ta rufe su,

   A natse ta soma bin pink lips ɗinshi da kallo shape ɗinsu ba ƙaramin kyau ne dasu ba,tausasan gaske,mayar da eyes ɗinta tayi akan dogon hancin shi da tsinin ke dab da nata hancin,ta jima tana kallon hancin nashi daga bisani kuma a hankali ta aza idanunta acikin nashi nan take taji wani irin bugun zuciya,

    sai faman lumshe idanunshi yake yana kuma opening ɗinsu saboda baccin da yake ji,dama agajiye ya dawo cikin gidan,a hankali yake ɗan waresu akan idanunta,anatse yake bin long eyes lashes din idonta da kallo,har yanzu akwai sauran tears dake dripping a cikin idonta,sun jiƙa eyes lashes ɗin nata sharkaf,

   Eyes balls ɗinta yabi da kallo a lokacin itama nata na’a kan kwayar idon tashi tana ƙarewa launin idon nashi kallo,kasa janye idanunshi yayi acikin nata,kamar yarda itama tagaza janye nata acikin nashi duk da tsoran kwayar idon nashi da take ji, 

   Suna cikin wannan yanayin a hankali ya zagayo da right hand ɗinshi ta saman kanta,ya ƙaraso dashi wurin ɗan kunnan nata sannan ya haɗa da hannun shi na hagu ya shiga ƙoƙarin cire gashin nashi daga jikin earring ɗin nata,

        runste ido sehrish tayi saboda zafin da take ɗan ji a wurin,ganin hakan yasa ya haɗe fuskokinsu awuri guda,jin yarda lips ɗinsa suka manne da nata tamkar zaiyi kissing ɗinta hakan ba ƙaramin rikitar da ita yayi ba,

   duk yarda yaso ya cire gashin daga jikin ɗan kunnan abun ya gagara ganin hakan zai 6ata mashi lokaci yasa yayi deciding tsinka gashin kan nashi daya sargaho earring ɗinta,

   Cikin sa’a ya katse gashin nashi yabar mata sauran siraran da suka ruƙo dan kunnan nata,

   Sai da ya raba ɗan kunnan sannan yaji wata irin kasala ta baibaye shi,lokaci guda ya rasa karfin janye jikinshi daga nata,ya dai samu ya ɗan janye face ɗin shi daga nata,sai kan head ɗinshi ya koma asaman boobs ɗinta,lamo yayi yana jin wani irin yanayin da bai ta6a ji ba arayuwarshi har wani bacci sosai ya dinga fisgarshi,sehrish kuwa tuni bacci yayi awon gaba da ita don bazata iya jurewa wannan yanayin ba,hannunta na asaman waist ɗinshi ta ƙankame shi sosai ajikinta,hada ƙarin hakan ya ƙara kashe mashi nashi jikin,

  Mamakine ya kama hayaam ganin cewa har yanzu Yarinyar bata fito daga part ɗin sgr ba,ashe tun bayan da sukayi magana da sehrish ta koma bedroom ɗinta sam tagaza samun natsuwa shine ta dinga leƙowa don taga ko yarinyar ta fito daga part ɗin nashi,amma shiru babu alamar cewa ma zata fito,hakan ba ƙaramin ƙona mata rai yayi ba,nan tashiga zargi kala kala acikin zuciyarta tana cewa”ko uban mi ya tsayar da ita ɗakin shi a irin wannan lokacin,ni dama banyarda da yarinyar can ba,daga ganinta irin sumu-sumu kasau ɗinnan ne,wlh saina yi maganinta bazan bari taci gaba da shiga sashen shi ba,

    tun tana sa ran fitowar sehrish harta haƙura ta koma bedroom ɗin data sauka,shiga ciki tayi tana ta faman sambatu kamar wata zararra duk akan sehrish ne take wannan 6acin ran,

  

   ******************

*Junaid Romeo*

Bacci yake yi amma gaba ɗaya jikin shi kerma yake yi sosai da sosai,sai faman mutsu mutsu yake yi da alama baijin daɗin jikin shi,wata irin Zufa ce take tsattsafowa daga jikin shi saƙo da lungu na jikinshi gaba ɗaya ya kasance ajiƙe yake sharkaf,a wani irin firgice Junaid ya farka arazane yana faman zazzare manyan idanunshi da suke cike tab da kwalla,

  Yana ƙoƙarin kai hannu ya tashi Abbansu dake kwance a gefen shi,sai ga wani baƙin hayaƙi ya fito daga Cikin mirror ɗin ɗaƙin mai yawan gaske baƙi wulik,bin hayaƙin junaid yayi da idonshi yana kallon shi a matuƙar tsorace,tattarewa hayaƙin yayi wuri guda kai tsaye ya nufi wurin shi,gaba ɗaya ya tunkare shi,ganin hakan yasa junaid faɗawa jikin abban nasu tare da ƙanƙame shi gaba ɗaya duk yabi ya firgice,kafin Abban nasu ya farka tuni wannan baƙin hayaƙin ya mamaye jikin junaid ta ƙofar hancin shi yabi ya dinga kurɗaɗawa cikin jikinshi,fashewa da matsanancin kuka junaid yayi yana ambaton sunan abban nasu,”Abba ka tashi dan Allah,abba pls ka tashi,bansan meke shirin faruwa dani ba,Abba ka tashi kaga halin da baby junaid ɗinka yake ciki”,

  duk wannan koke koken da junaid keyi abun mamaki ko motsi Abban nasu baiyi ba,sosai junaid ya dinga jijjiga jikinshi yana ambaton sunan shi amma shuru bai farka ba,babu alamar cewa zai farkama,

   Allah sarki,sun sangartar da junaid sosai wanda hakan yasa bai iya ambaton wata addu’a acikin bakin shi ba,sai ihu da yake yi yana koke koke,ko addu’ar bacci wannan junaid bai ta6a yi ma kanshi ba,saboda ya saba kullum in Abbansu na nan shike yi masu addu’ar su kwanta atare,in kuwa abbansu bai nan anyhow yake baccin shi batare da tunanin yin addu’a ba,tsantsar son da suke yi mashi ne yasa basu son ya wahala ko kaɗan,junaid bai ta6a zuwa islamiyya ba don koyon wani abu na addini,amma Abbansu da kuma ƴan uwanshi suna zaunar dashi su koyar dashi wasu abubuwan sosai,a kwanakin baya har malami abbansu ya samo wanda zai dinga koya mashi karatu,tun rana ta farko da malamin yazo zai koya mashi karatu basu ƙara ganinshi ba,6at aka neme shi aka rasa,kusan sau huɗu hakan na faru duk in Abbansu ya samo malamin da zai koyar dashi addini daga yazo sau ɗaya sai a neme shi arasa,hakan yasa daga baya ya haƙura da neman malaman da zasu koyar dashi,musamman da yaga ƴan uwanshi na koyar dashi acikin gidan sai hankalinshi ya kwanta da hakan,abun da baisani ba kosu da suke koya mashi agabansu yake nuna ya fahimta kuma ya gane karatun amma da zarar yabar wurin karatun tofa komai ya zube acikin kanshi,yadawo zero 0

   Wani irin sanyine ya gauraye ko’ina na sassan jikinshi,lamo yayi abayan abban nasu yana faman sauke ajiyar zuciya,a wannan yanayin kuma bacci yayi awon gaba dashi,🥺

   Meke shirin faruwa ne!?

A hankali ta soma buɗe idanunta dake ɗauke da bacci biji biji ta soma gani kafin daga bisani suka washe ta dinga ganin komai normal,jin babu nauyin mutum akanta yasa ta gane cewa sgr ya bar jikinta,cikin sauri ta miƙe zaune tare da kai idanunta inda yake kwance yana bacci,zuba mashi ido tayi tana kallon shi,yanayin yarda yake baccin zai tabbatar maka da cewa yana cikin kwanciyar hankali da natsuwa,

   A hankali takai hannu tare da jan blanket ɗinshi ta rufe mashi jikin shi har wurin wuyan shi sannan ta saki bargon,

   tamkar karta tafi tabarshi haka ta dinga ji,hannu takai tare da ruƙo sumar kanshi mai laushin gaske,ta tattare mashi ita tare da yin gefe guda da Ita,hakan ne ya bata damar kallon kyakkyawar fuskarshi sosai,

  Cikin sanyin murya tace”inason farin ciki ya cigaba da wanzuwa a wannan kyakkyawar fuskar taka,kuma insha Allah zan tabbatar da hakan,zan cigaba da addu’a akan Allah ya mallakamin kai amatsayin abokin rayuwata,duk da nasan cewa zaiyi wuya hakan tafaru saboda kafi ƙarfina sosai nesa ba kusa ba”

   Jiki asanyaye taƙarasa maganar yayin da ta juya tare da saukowa daga saman gadon nashi,sai da tafara kashe mashi hasken ɗakin sannan ta fuce daga part ɗin nashi,

  

A 6angaren Amani kuwa tunda tabi bayan motarsu da gudun gaske,bata ci nasarar taddo tasu motar ba saboda suma gudun sukeyi tuni sun 6ace ma ganinta,jiki asanyaye tayi parking ɗin motarta agafen titi,tamkar zata fashe da kuka haka ta dinga ji,hannu takai tare da ɗaukar wayarta dake ajiye asaman laps dinta,missed calls ta gani na Abbas har kusan shida,duk bata ji ringing ɗin da wayar keyi ba,saboda bata cikin natsuwarta hankali atashe tace”nashiga uku!Ashe abbas ya kira ni bansani ba,yanzu mai zan faɗa mashi,gashi ban hadu da wadda akace Amal ce…”

   fuskarta a yamutse tayi maganar,yatsun hannunta har kerma sukeyi wurin dialing ɗin numbarshi tabi kiran da yayi mata,tana fara ringing ya ɗaga kiran,cikin sauri takara wayar a kunnanta,saurarawa tayi tana jiran jin me zaice,

   “Ki dawo gida inason ganinki,”

Yana faɗin hakan yayi rejecting ɗin kiran nata,

  Nan fa ido ya raina fata,a kasalance ta tashi motar tare da karya kwana ta miƙi hanyar komawa gida,

*************************

Sosai Amal ke kuka tana ambaton sunan Allah abakinta duk tabi ta zauce,

  Rai a6ace JAHAN yace”yarinyar nan tayi mun shiru!nagaji da jin tsiwarta,duk tabi tayi confusing ɗina,Ayaan kodai ka toshe mata baki ko kuma in dakatar da driving ɗin nan don ni bazan juri tsiwarta ba,”

   cikin sanyin murya Ayaan yace”pls take it easy Jahan,yarinyar nan fa ba ƙaramin jiki take ji ba,ita kanta bazata iya control ɗin kanta ba saboda raɗaɗin ciwon da take ji,”

  Uban tsoki jahan yaja yana faman hura hanci,adai dai lokacin suka ƙaraso da Amal katafaren asibitin sgr,shiga da motar ciki yayi tare da samun wuri yayi parking ɗinta,fitowa Ayaan yayi kafaɗar shi ɗauke da Amal kai tsaye ya wuce da ita cikin asibitin,

  Jahan kuwa zaman shi yayi acikin motar yana jiran ƙarasowar ayaan ɗin,don yace bazai shiga cikin asibitin ba,ya miƙata kawai ya fito su juya,

   Ayaan na shiga ciki da sauri reception nurses suka kar6e ta,tare da wuce wa da ita medical room don a kwantar da ita,

   tsayawa yayi yana faman zarya a wurin,kiran jahan ne ya shigo wayarshi cikin sauri ya ɗaga kiran tare da karata a kunnan shi,

   tunkafin yayi magana jahan yace “what are u waiting for Ayaan!tun da ka miƙa ta awurinsu ka fito kawai mu juya gida,”

   amsa mashi yayi da okey,sannan ya kashe kiran,

  harya juya zai fita daga corridor ɗin,yajiyo muryar wata nurse tana dakatar dashi,tsayawa yayi tare da juyawa yana kallonta,ƙarasowa tayi da sauri cikin harshen turanci ta soma yi mashi magana”sir yarinyar taƙi bari mu dubata,da alama tana da damuwa sosai,akwai wani suna da take ta ambato abakinta,in badamuwa muna so ka shigo daga ciki kayi mata magana,may be ta samu natsuwa,”

   batare da musu ba,Ayaan yabi bayanta har cikin ɗakin da suka kwantar da Amal,sai faman kuka takeyi tana kiran Sunan Aunty amani,tana cewa dan Allah su kira mata ƴar uwarta karta mutu bata sata a idonta ba,

   ganin shi yasa sauran nurses ɗin dake aciki suka ja da baya tare da bashi wuri don ya wuce,

  Ƙarasawa ayaan yayi tare da samun wuri daga gefen gadon da take kwance,yama rasa ta yarda zai shawo kan yarinyar don tayi nisa bata jin kira sai faman sharara kuka takeyi ta cika ko’ina da kukan nata,

   tsawa ya daka mata,aikuwa a firgice ta mayar da idanunta akanshi yayin da jikinta yashiga yin kerma saboda tsoran da taji,

  Yarda ya zare mata idanunshi ba ƙaramin tsoro taji ba musamman launin kwayar idonshi da takasance ash colour,

  Lokaci guda tayi tsit tana faman zazzare idanu,

  dama yayi mata hakan ne don tayi shiru,sassauto da murya yayi tare da cewa”faɗamun menene damuwar?bakyaso ne ayi treating wounds ɗin dake ajikin ki?ko so kike ki mutu ne?

  Cikin shesshekar kuka tace”banso na mutu,inason ganin Auntyna ne,dan Allah ku kira mun ita tazo naganta kafin na mutu,inason ganinta,”

   tsananin tausayinta ne ya kama shi,bin idanunta yayi da kallo ganin yarda hawaye ke kwaranyo daga cikinsu,yarinyar dae ba ƙaramin jiki taji ba da alama,

   ajiyar zuciya ya sauke tare da cewa”yanzu baki da lafiya,ki bari su duba jikinki,in yaso zuwa gobe ni dakaina zan kira maki auntynki a waya,kin amince da hakan”?

   amsa mashi tayi da eh,sannan ya miƙe tare da yi masu sallama,ya fuce daga asibitin,

   shaf shaf suka bar Asibitin da motarsu,

Koda Amani ta koma gida,abbas baiyi mata faɗan komai ba,ko tambayarta inda taje baiyi ba,hakan ba ƙaramin daɗin yayi mata ba,dama fargabarta kenan karya tuhumeta akan ina taje acikin daren nan,

Domin Sauke Littafin book 3 Sai Ku Dannan inda aka saka Download Now!


*SANARWA SANARWA*💃💃💃💃

*ME TAKEN NA AMARYA HUTAA$$*

*MUNA FARIN CIKIN SANAR DAKU CEWA MUNA BADA HAYAR KAYAN AMARYA(WEDDING GOWN), KAYAN BRIDAL SHOWER, KAYAN BIRTHDAY PARTY, KAYAN FITAR SUNA, SANNAN MUNA BADA HEAD AND SHOULDER, MUNA DA POSS, MUNA ALKYABBAR KAI AMARYA KO TARON WALIMAR SAUKA, MUNA DA KAYAN FULANI FARARE NA YARA DANA MANYA MUNA DA NA AMARYA BLUE BLACK, SANNAN MUNA GYARAN JIKIN AMARYA DA UWARGIDA CIKIN KWANA UKU CAKAL ZAKIGA KIN KOMA TAURARUWA MAI WALWALI.  MUNAYIN TURARUKAN WUTA DA HUMRA DA KOLACCAR, KOWANNE KALA KIKE BUKATA AKWAI CIKIN FARASHI MAI SAUKI.*

*LOCATION KANO*

08062073990

Ina kuke mata hamshakai wayanda suka amsa sunan su wajen mazajen su ina mata masu son qamshi shin ko kunsan tsafta bata tafiya seda qamshi ina masu son turare mai riqon gida tareda qamshin shi mai sanyaya zukata mardie collection tazo muku da dadadan turarukanta masu lasting riqon gida harma da jiki ku tuntube mu da nmb kamar haka 08136666994 inda zaku samu kaya kamar haka 

Wadrobe balls 

Madarar kulleccham 

Vaseline kulleccham 

Kajiji

Halut

Couscous 

Khumrah 

Da dai sauransu harda abin wanke toilet yayi tas komi dafe warshi wato BETHALEX METAL ku garzayo kar ayi baku

Ina kuke mata hamshakai wayanda suka amsa sunan su wajen mazajen su ina mata masu son qamshi shin ko kunsan tsafta bata tafiya seda qamshi ina masu son turare mai riqon gida tareda qamshin shi mai sanyaya zukata mardie collection tazo muku da dadadan turarukanta masu lasting riqon gida harma da jiki ku tuntube mu da nmb kamar haka 08136666994 inda zaku samu kaya kamar haka 

Wadrobe balls 

Madarar kulleccham 

Vaseline kulleccham 

Kajiji

Halut

Couscous 

Khumrah 

Da dai sauransu harda abin wanke toilet yayi tas komi dafe warshi wato BETHALEX METAL ku garzayo kar ayi baku

It’s not just good …it’s finger linking good faster than fast food, better fine dining.

Snack

Awarah 

Farah

Zobo

Samosa

Cup cake etc 

Contact me 09063302182or 09012179727.

Back to top button