Fatalwar Delu Part 12
🤡 FATALWAR DELU 🤡
Part 12
Kingboy Isah 👑
Short story
ZAMANI WRITERS ASSOCIATION
Na dan jima a tsaye ina dube-dube kana na zauna domin kuwa Allah ya gani kafafuna kamar su cire saboda gudun da nayi na ceton rai. Don haka na zauna kasa ba tare da tunanin komai ba da nufin in dai huta kafin in tashi in nemi hanyar gida. Wanda tuni nasan in dai ba sawuna na rika haskawa ba, ba zan iya kai kaina gida ba, na dan jima a wajen ina zaune daga baya na fara jin wani irin gurnani wanda hankalina sam bai aminta da shi ba, don haka na mike na fara has-haska ta bangaren da na jiyo gurnanin. Duk da kasancewar ba komai a wajen amma naji zuciyata bata aminta ba, don haka na dau hanya bayan na fara bin sawuna. Na dade ina tafiya tukun na karaso gida ni kaina nayi mamaki ba karamin gudu nayi ba ashe shiyasa nayi nisa sosai. A haka na kwanta a gajiye da tunane-tunane har bacci yayi awon gaba da ni. Washe gari har sai da na dan makara sallar asuba saboda jikina duk ciwo yake.
Da safe muna tsakar cin dumamen tuwo ni da Bukar na dubeshi a tsanake na bashi labarin duk abinda ya wakana tsakanina da Fatalwa Surayya, harda sakon da ta bani na gaya masa, kana na dora da cewa, “Don Allah ka daure muje ka ba wannan fatalwar hakuri ko sa shafa ma garin nan lafiya nima in samu in tafi gida”. Bukar da ya gama saurarona tsaf yana bina da wani irin kallo na kama raina min wayo ya ce, “Ai Nura ka ma daina bata bakinka don kuwa duk abinda zaka fada ba zuwa zanyi ba. Ni wani lokacin ma kallonka nake kamar zautacce, in ba zautaccen ba to wa zai rika batu irin wannan. Wai ni Bukar in fita tsakar dare in je daji wajen Fatalwa domin neman afuwarta sai kace an fadama karen hauka ne ya cijeni. Kai dai da ka saba gane-ganenka ku cigaba da yin abunku ni ina gefe wallahi”.
Na sake kallonsa a karo na barkatai, kana na kara kora masa bayani game da illar rashin zuwansa idan har ta fusata ta waiwayeshi, amma sai ya ce ai ba ma zaiyi gangancin fita da daren ba balle su ganshi su cutar da shi. Jin hakan yasa nayi shiru na kyalesa, amma a kasar zuciya ina tausayinsa da kuma tausayin kaina domin nima yanzu a matukar tsorace nake da lamarin Fatalwar nan, musamman dazun da muke waya da mahaifina a kan dalilin da ya sa har yanzu ban taho ba na kasa bashi amsa domin na rasa ta yadda zan bayyana masa wai fatalwa ce ta hanani tahowa. A haka dai na cigaba da gargadin Bukar wanda shi kanshi ya fara ganin alamun tsoron fatalwar a tare dani ba kamar farko da yake ta yi mun bayanin illarta amma na ki gaskata zancensa ba.
Da rana haka muka nufi wajen Hamsa’u da nufin cin abinci amma na kudiri anniyar ko kadan ba zan yi mata maganar da ta shafi soyayyarmu ba, domin kuwa ina tune da kashedin Fatalwar Surayyah na jiya, sai dai ko kadan bana jin zan iya samun Hamsa’u kai tsaye ince na janye alakar soyayyar da muka kulla jiya-jiyan nan, domin ba shakka sai ta daukeni mayaudari. A haka muka karasa, tun daga nesa kuwa take sakar min murmushi wanda ni kaina banyi aune ba sai gani ina mayar mata da martani, zuwa can kuma sai na tsuke fuska yayin da muka karasa wajen da sallama muka nemi waje saman iccen majalissa muka zauna. Duk da mun iske layin mutane amma Hamsa’u sai da ta fara zuba mana abinci wanda na tabbata ya fi na kudin da muka saba saya, muna ci tana zubawa mutane abinci amma bata daina wai-waiyena ba tana murmushi, ni kuwa ina kallonta amma naki yarda in saki fuska gudun abinda ka iya zuwa ya zo, sai ma na fara bin mutane da kallo da nufin gano wanda ka iya zama dan leken asiri ko kuma ita kanta Fatalwa Surayyah cikin badda kama amma banga alamun haka ba.
Har mun kusa kammala cin abincin, wani saurayi dan dogo ya zo ya tsugunna gaban Hamsa’u yana yi mata magana, na lura tun da ya zo ta murtuke fuska murmushi dake saman fuskarta ya dauke. Har muka gama cin abincin saurayin na mata magana kasa-kasa yayin da ita kuma ta ke cicin magana bata ko amsa masa, bansan lokacin da naje na tsugunna a gefen kular abincinta ba ta dayan bangaren hade da mika mata kudi na ce, “Gimbiya kuma sarauniyar mata ga kudinmu”. Ta kalleni a dan kunyace ta ce, “Aa ka barshi”. Nayi dan jim ina kallonta kana na ce, “Ina wannan ai ba mai yuyu bane, ni na isa yin wannan gangancin ai idan kika ki karbar kudin nan to zama zanyi in ta aiki kama daga wanke-wanke shara zuba abinci har sai na tabbatar nayi aikin da ya kai adadin kudin” Ta danyi murmushi a lokacin da ta zubawa wani abinci zata sa mai cokali, nayi saurin daukar cokalin na saka cikin robar abincin na amsa ina mikawa mutumin cikin fadin, “Yauwa bari na fara aikina tun yanzu”. Yar dariya tayi gami da cewa, “Wallahi baka da dama”. Da jin haka na mike hannayena gabanta hade da cewa, “Ga hannun hagu, ga hannun dama duk ina da su” . Nan ma murmushi tayi wanda ke nuna har cikin ranta taji barkwancin nawa.
Na dan natsu ina kallonta na dan lokaci yayin da ita kuma murmushi kawai take, amma taki hada ido da ni, Na dan jinjina kai hade da cewa, “Hmm! Allah sarkin baiwa, na dade ina ganin murmushin furanni masu launi kala daban-daban ba tare da sanin taya ko kuma daga ina murmushin na su ya samo asali ba, sai yanzu da nake kallon fuskarki na gano amsata, ba shakka daga gareki duk suka koya”. Hannu ta sa ta rufe fuska tana murmushi, daga gefe naji wannan saurayin yaja tsaki ya mike a fusace ya bar wajen, na bi bayansa da kallo ina murmushi, daga bisani na juya ga Hamsa’u na cigaba da kora mata zantukan kauna. Bukar kuma da ya gaji da jira ganin bani da alamar tafiya ya mike ya ce shi yayi gaba sai na zo. Ni kuwa tuni na lula duniyar masoya, abincin ma kusan tare muka cigaba da sayarwa, don ni ke mika mata kwana ko cokali wani sa’in harda zuba mai. Muna yi muna hira, na dan jima a wajen zuwa can kamar ance in kalli ta gabanmu inda mutane ke wucewa, charaf! idanuna suka kai ga wata tsohuwa da ke wucewa ta gabanmu fuskata sam babu annuri wata uwar harara da take banko min tamkar idanunta zasu fado kasa.
Gabana ne ya fadi, lokaci guda na tuno da fatalwar Surayyah wacce kafin yanzu shaukin kauna ya mantar da ni itama. Tsohuwar na dan gitta mu na dubi Hamsa’u hade da cewa, “Shin ko kin san matar can, na ga tana hararenmu”. Ta dubeta hade da kada kai tana mai cewa, “Waccan da alamu ba yar garin nan bace domin kuwa ban santa ba”. Gabana ya sake faduwa, da alamu zargina ya tabbata tana iya yuyuwa aljannun leken asirin Surayyah ne. Ai duk sai naji firar ma ta fita a kaina, a gaggauce na yiwa Hamsa’u sallama ina fadin na tuno ina da wani uzuri a gida. Nan dai na tafi ina ta sake-saken zuci bayan nayi dabara na ajiye mata kudinta, don kuwa na karya alkawarin Surayyah Fatalwa jiya na ceci rayuwata a hannunta ta hanyar yan dabaru yau kuma idan hakan ya sake faru na tabbata ba lallai ta saurareni ba, tuno kashedin da tayi man na cewa kar in sake kula wata ‘ya mace. Sai gashi a ranar farko na shure wannan sharadi. Tuno wata mafita da nayi ne yasa nayi murmushi ba don na gamsu da lalai hanya ce mai bullewa ba, amma dai zan jaraba, domin hausawa sunce da jarabawa jirgin sama ya tashi.
Kamar kullum yau ma muna gama cin abinci wajen karfe 8:30 Bukar sai sauri yake ganin tara ta kusa, bayan ya shirya ya min sai da safe, bisa mamaki sai gani yayi na dauki filo da bargo ina mai fadin kulle dakin ai nima yau a wajenku zan kwana. “A wajenmu kuma me yasa ko dai kaima jaririn da ka kwaso ranar ya fara isarka”. Nayi murmushi hade da cewa, “Haba shi din banza kawai kwana ni dayan ne duk ba dadi dake ko a gida ban saba ba”. Jin hakan Bukar bai kuma yin wata maganarba ya kulle dakin muka juya muka tafi da sauri a cewarsa karfe 9 ta kusa. Ai kuwa bamu dade da zuwa dakin abokin nasa ba, muka fara jin karar dukan karfe wanda ke shaidawa jama’ar gari karfe 9 yayi. Nan da nan aka fara guje-gujen shiga gida. Muma muka shige shago muka kulle bayan kowa yayi fitsari a cewarsu ba fitar dare, kuma na amsa da cewa na yarda ban fita. A nan nake tambayar Bukar da abokinsa Mati wanda muke a shagonsa, na ce “Shin shi wancan mai buga kararrawar shi baya da tsoro ne halan, ko kuwa yana bugawa shima yake rugawa a guje ya shiga gida?”.
Su ka danyi murmushi kafin suka ce, ai kararrawar a kofar gidansa take, yana gama bugawa yake fadawa gida ya rufe kofa, shima mai gari ne ya bullo da wannan dabarar kasancewar kauye wasu ba su da agogo basu sanin karfe 9 tayi. Na jinjina kai, nan dai muka taba yar hira mune har wajen 11:30 amma hirar ma a hankali muke yi a cewarsu mu da muke shago dole muyi taka tsan-tsanar kar fatalwar nan ta jiyomu ta kawo hari. Bayan mun gama hirar nan take nima na bi lafiyar katifa da fargaba a raina na abinda ka iya zuwa ya zo a cikin daren nan da nake kyautata zato na fusata fatalwa Surayyah na kuma tabbata sai ta biyo ni har nan din da na gudo, a haka dai har bacci ya daukeni. Can cikin bacci naji ana dukan kofa tamkar za’a karyata, kusan tare muka farka muna haska fitilu wannan karon firgita harda ni, ko da yake ni ya kamata na fi kowa ma domin ni nasan abin da na janyo wa kaina da kuma su da nake kokarin jogana musu. “Waye”. Muka fada kusan a tare, shiru ba’ayi magana ba, amma ana cigaba da dukan kofar. Nan take na fara jin zufa na keto min duk da kasancewar sanyi-sanyi ake yau, na mike a hankali har na fara tafiya na ji an rike min kafa, na juya a tsorace, sai gani nayi ashe Bukar ne, cikin muryar rada ya fara fadin, “Nura don Allah don annabi ka rufa mana asiri karka je ka bude kofar nan ka jawo mana bala’i, ni sai yanzu ma nake nadamar barinka biyo mu nan. Sai kace na manta fatalwar kai take bi”. Na saki baki ina kallonsa, bugon da akayiwa kofar da karfi ya samu zabura gaba dayanmu…………
🥱 Me ma zance? Ok to kuyi hakuri ba guduwa nayi ba laifin caji ne